Showing 141001 words to 144000 words out of 217237 words

Chapter 48 - GOBE NA Compelet Book by Khadijah Candy.txt

24 Sep 2025

208

kallon office din, misalin daya da mintuna wata ta shigo da abinci ta ba aje min, takeway ne na jalof da naman kaza a ciki. Nikam ban ci ba duk kuwa da kasancewar ni kadai ce a dakin sai na saka abina a jaka.
Biyu na yi na shiga bandakin da ke office din nai alwala na fito nai sallah sannan na dauki wayata na kira gida na fadawa Hafiza ta fadawa Mama an canja min aiki dan haka yau sai 5pm zan dawo.
Har karfe uku ban duba email din ba ban kuma tura komai ba, har sai da Yunus din ya sake dawowa ya nuna min yadda ake da kuma wandanda ya kamata a turawa Ahmad din.

Karfe biyar na yi na dauki jakata na fito daga office din, ko da na fito Rilwal da Blessed basa gurin sun gama aikinsu sun tafi.
A lokacin da na isa gida na labartawa Mama da dukan yan gidan abunda ya faru tsakanina da Ahmd da kuma abunda Suwaiba tai, a nan Hafiza take fadar wai Suwaiba ta kirata kwanan baya tana tambayar inda nake aiki ita kuma ta fada mata ba ta yi tunanin wani abun ba ashe dan ta samu zuwa ta ci min mutunci ne.
Su namra na bawa abincin office din, suna ta murna sun ga har da nama a cikin gurin rabon abun har ya so zame musu fada sai da Husna ta shiga tsakani.
Bayan na huta na ci abincin da aka girka gida, na watsa ruwa na sake shiryawa cikin wasu tufafin na nufi bankin da ke kusa da mu, kudin gasar da na ci nake son cirowa na samma kowa wani abu a ciki sannan nai sauran lalurorin da suke gabana. 200,000 na ciro na saka a jaka ta cikin tsoro domin a lokacin an fara kiran sallah sai nake ganin kamar akwai wasu a biye da ni duk kuwa da ba ni kadai na ciri kudi a atm din ba.
Ina yin gaba kadan sai wata farar mota mai bakin gilashi ta faka a gabana, na san ba zai wuce Abraham ba amman hakan be saka ni jin tsoro ba har sai da ya bude motar ya fito.

“Ki daina cirar kudi a atm idan yamma yayi, wani zai iya sa miki ido wasu ma ba diban kudin suka je yi ba kallon masu cire kudin suka je yi”

Ban ce masa komai ba nai gaba kamar zan wuce sai ya saka ya cin min.

“Kin gani jin labarin ki ya kara min kaunarki, kuma ya kara kafafa min guiwar aurenki, ni kadai zan rayu dake ba wata kyama ba wani tunani, ina da kudi zan sakar miki su ki jidadin rayuwarki”

“Ba kudi ne jindadin rayuwa ba, da su ne da masu kudin ba su shiga kunci ba, ni farinciki nake nema da kwanciyar hankali”

“Na sani shiyasa zan baki ai”

“Baka isa ka bani farinciki ba, baka isa ka keta min haddi da aurena ba har nai ciki yanzu kuma ka biyo ni kace zaka aureni, addininmu dabam al'adarmu dabam, baka san zafin da nake ji a raina ba, baka san yadda mace take ji idan an keta haddinta ba, saboda kai namiji ne, mace tana jin matukar bakinciki ko hannunta a rike balle a keta haddinta, kasan saboda me? Saboda martabarta kimarta mutuncinta jindadinta farincikinta yana a nan ne, to kai ka zubar min da duka wannan ka saka uwar mijina da mijin da ya sake ni suna min kallon karuwa wacce ta zubar da mutuncinta tai fasikanci da wani namijin har ta samu ciki, wannan tabon ba zai taba gogewa ba, idan kuma ka zo ne saboda ka kashe ni da bakincikin kallonka da nake kana da dama”

Na karasa cikin kuka.

“Idan nisanta kaina da ke zai saka ki farinciki, i will do that, amman bana da niyar saka ki bakinciki, sai dai sama miki farinciki ada bakincikin fyaden da nai miki kawai yake damuna, amman a yanzu har da rayuwar kuncin da kike ciki, kina da zuciya mai kyau kuma kina da hakuri”

Bayan ya fadi haka ya bude motarsa ya shiga yai mata key ya bar ni a gurin tsaye. Sai da na daina hango motarsa sannan tari napep na shiga. Ko da na isa gida har an gama magariba, bayan na sallame mai napep na lura da motar Abdallah, na yi zaton yana cikin gidan ne sai ji nai ya kirani, ina juyowa na hango shi ya fito hanyar masallacin unguwar sai ya nufi gurin motarsa ya tsaya, hakan yasa nima na karasa kusa da shi na tsaya.

“Ki yi hakuri da abunda Suwaiba tai miki, ban san yadda akai taje gurin ba kuma ban fada mata cewar kina kawo min abinci ba, kin san zuciya kowa da irin tasa ba tai tunani ba a lokacin da ta aikata abunda ta aikata dazun kuma ban jidadi ba”

“Tana da gaskiya Abdallah, tana tsoron wata ta karbe nata miji mai karamci da sanin ya kamata, mai kula, mai tausayi, mai taka tsantsan akan komai, kai kadai ka yarda da ni Abdallah baka taba yarda cewar na aikata laifi ba, kai kadai ka yarda cewar ban aikata zina, kai ne kadai ka yarda fyade ka min har na samu ciki, amman Hajiyarka da Abdulhamid ba su yarda da ni ba, kai na zarga a lokacin da aka min fyaden kuma na fada maka, amman gujeni ba baka kyamace ni ba, baka fasa so na ba, baka kasa taimaka min ba, so na be taba sa ka nemi aikata alfasha da ni ba, baka taba kyamar yayana ba, Wallahi ina son ka Abdallah ina son ka har kasan raina”

Na karasa cikin kuka mai tsanani. Har ga Allah ban taba jin son wani da namijin a raina kamar yadda nake jin Abdallah a raina ba, sai bayan komai ya lalace na gano shine mutumen da ya dace da ni.

“Ke dai ba kya gajiya da kuka, shiga ciki Suwaiba tana jiranki”

“Ina son na fada maka wani abu, mutumen da yai min fyade, ya dawo yan so na”

“Wooo What....!”

Ya furta da karfi muryarsa na amayar da mamakin da ke cikinsa.

“Waye? A ina ya ganki?”

“Labari mai tsawo ba zai yiyu a yanzu ba”

“Waye shi kin san shi ne?”

Na girgiza kai.

“Ban san shi ba, sunansa Abraham, dan sanda ne, yana aiki a unguwar gwaza, kuma shi ba musulmi ba ne”

Na daga kaina sama ina shanye kuka.

“Abraham.....”

Ya maimaita sunan sannan ya jinjina kansa.

“Shiga ciki za ku yi magana da Suwaiba”


Na gyada kai alamar gamsuwa sannan na saka hannuna na share hawayena sannan na juya na nufi gidanmu. Ko da na shiga na samu Suwaiba zaune falon mama tana ta rutsar kuka kamar ba ita ba, tana ganina ta soma bani hakuri tana fadin na yafe mata, a iya sanina Abdallah baya duka balle nace dukanta yai ya cilasta mata zuwa ta ba ni hakuri sai dai idan wani abun ya fada mata ko kuma cilastata yai.
7/21/21, 10:47 PM - Buhainat: I think you'd like this story: "GOBE NA (My Tomorrow)" by KhadeejaCandy on Wattpad https://www.wattpad.com/story/247701926?utm_source=android&utm_medium=com.whatsapp&utm_content=story_info&wp_page=story_details_button&wp_uname=KhadeejaCandy&wp_originator=ZkyWKvWuHXhIRzZDEluZ%2BuUXayIbDBikXAQA%2BM4xeAsJY%2Fh9rtovTCoQphCdFYUPM4K1nHTquOLcFfifZUhwZ0RRyERddTi4AY1OYORg8gUhN9fNU%2FLr6t3SMGO9O8M2

*GOBE NA...*

By Khadeeja Candy


4️⃣5️⃣

ABDALLAH POV.

Zuciyarsa cike take da tunanin abunda Halima ta fada masa, ba sau daya ba ya sha jin sunan Abraham a gurin Abdulhamid, sai dai da kamar wuya ya iya fada mta kai tsaye idan har shi din ne? Mi zai saka ya tonawa kansa asiri? Mi mai zai saka yayi mata fyaden tun farko? Miyasa yai shigar yan fashi? Sai dai ya yarda Halima ba zata masa karya ba, tun da ita din bata san Abraham ba, kuma bata san cewa shi din ba musulmi ne ba, idan har ba shi ya fada mata ba.
Yana tsaye jikin motar Suwaiba ta fito daga cikin gidansu Halimatu ta nufo i da yake da hijabinta har kasa, be tsaya jiran ta karaso ba ya bude side dinsa ya zauna yai ma motar key tana shiga ya tashi motar.
Ta yi zaton hanyar gida zai nufa sai ta ga ya dauki hanyar family house dinsu.

“Doc baka hakura ba?”

Ta tambaya cikin kuka, ko kallon inda take be yi ba har ya shiga titin unguwarsu.

“Na ba ka hakuri kace ita zan bawa hakuri ita ma na bata, amman be isa ya saka ka yafe min dan abunda nai ba”

Sai a lokacin ya kalleta.

“Dan abunda kika yi? Da ne ma? Kin san irin kuncin da Halima take fuskata kike neman kara mata wani? Ko ba u so a tsakanina da ita ai ita din yar'uwata ce kuma kin sani, ko dan yan'uwantakan da ke tsakaninmu be isa ya saka ki raga mata ba ko da ma ace ita ce ta nemi fada da ke? Ko karuwata ce ai ya cancanci ki kyaleta saboda mutuncina, amman wai dan shashanci da aurena akanki ki shiga public place kamar nn kina magana any how, idan auren zan yi kin isa ki hana ni ne ko fadan ki sai ya saka na fasa?”

Tun da ya fara fadan take kuka har ya faka bakin kofar gidansu.

“Da gaske sakina din za ka yi?”

“Ko dai ban sake ki ba, dole na samawa su Inteesar wata uwar mai tarbiya da sanin ya kamata”

Da sauri ta hade hannayenta.

“Dan Allah kai hakuri, ka sake ni idan sakin zai saka ka huce haushi daga baya sai ka maida ni amman karka kara aure dan Allah, wallahi na bari ba zan sake ba”

“Yanzu kuma na gano har da hankali baki da shi, idan aure zan yi kin isa ki hana ne? Ba a aure na aureki? fitar min a mota”

Ya fada a tsawace fuskarsa babu alamar wasa.

“Dan Allah ka yi hakuri...”

“Nace ki fita....”

“To yaushe zaka dawo ka dauke ni?”

“Ban sani ba”

Yadda ya daka mata tsawa ne yasa ta saurin bude motar ta fita. Sam bata taba ganin Abdallah a cikin irin wannan yanayin ba, su kan samu sabani wani lokacin ko da shine da gaskiya sai tai fushi da shi a haka kuma zai bita ya bata hakuri su shirya, amman be tana yunkurin fada mata bakar magana ba, yau kam ta kai ya saka hannunsa ya mari fuskata hakan be masa ba sai da ya cilastata ta je ta bawa Halimatu hakuri abunda yafi kona mata rai kenan, bayan yai mata baraza da saki yanzu kuma ya cilasta mata zama gidansu har yana zancen kara aure.
Lallai sai yanzu ta tabbatar ba kadan yake son Halimatu ba, saboda kawai ta taba yau duk yai mata wannan har yana fadar wai ta taba mutuncinsa, bata kara jin ta tsani Halimatu ba sai da yai reverse da motarsa ya barta bakin gate din tsaye tana kallonsa.
Kai tsaye gidan Hajiyarsa ya nufa, har lokacin tunanin abunda Halima ta fada masa yake, yana ta neman dalilin da zai saka mutumen yi mata fyade, yana bukatar fadada bincike, kamar yadda yake bukatar jin komai daga bakinta.
Sai da yai parking sannan fita daga motarsa ya nufa kofar falon Hajiya wacce ke bude, hango ana mopping yasa shi tsaya bakin kofar yana kallon Hajiyar wacce ta nufo inda yake rike da filo. Fitowa tai waje harabar kofar da aje fillon saman wani center carpet da aka shinfida mata gafen kofar ta zauna, tana tsastsagar hakora hakoranta biyu na makka suna bayyana.
A gabanta yaje ya zauna, yana mika mata gaisuwa.

“Lafiya Kalau, Husaini ya gida? Wani gurin ka fito ne hala?”

“Eh Suwaiba na kai gidansu”

“To wani abu suke a gidan ne?”

“Kai ta nai ta kwana biyu dai”

Hajiya ta tashi daga kishingiden da take tana kallonsa abunda bata taba ji ba.

“Ban gane ta kwana biyu ba? Miya faru? Tsabani kuka samu ne”

Be boye mata komai ba daga abunda ya faru har hakurin da ya saka ta bawa Halimatu, a maimakon Hajiya ta bata laifin sai ta koma ganin laifin Abdallah.

“Wato sai yanzu na gano ba karamin so kake ma matar nan ba, nima dan ina mahaifiyarka ne na hana ka kuma ka hanu, miyasa za ka ga laifin Suwaiba? abunda Halima take ni kaina ina jin haushi balle kuma ita da take matarka”

“Matata Hajiya na sani, amman ba zan lamunci matata ta ci mutuncin yan'uwana ba, ko akwai so ko babu Halima jinina ce, yadda mahaifinmu be yarda mu raina yan'uwansa ba haka ba zan yarda ni matata wacce na auro take karkashin kulawata ta raina min yan'uwa ba, ta tsaya a matsayinta na matata, Halima kuma tana nan a yar'uwata”

“Uhm Allah dai ya kyauta idan baka mutu ba komai gani kake, ita ma dai ban da iskanci ya zata rika aika maka da abinci guri aiki neman suna? Bayan tasan kai kanen mijinta ne? Wallahi yarinyar nan bata da kunya sam na raina tarbiyarta”

“Hajiya kin dai tsani Halima kuma bata miki komai ba, matsalarta daya ta auri Abdulhamid kuma Abdulhamid din nan danki ne, ina laifi ta taimaka masa ta aure a halin da yake ciki? Amman kin dauki tsana kin dora mata bata miki komai ba Hajiya, yanzu ai zaki ga ranar ta, zaki gane ta yi jihadin auren danki, ba aure zai yi ba? Yanzu ba budurwa zai auro ba? Duk wanda be san ba shi da lafiya ba yanzu zai sani, ke da shi yanzu za ku gane idan Halima tana da hakuri ko babu”

Tun da ya fara maganar ta zuba mishi ido, ta rasa gane wani irin so yake ma Halima nan, da baya ganin laifinta kuma baya son a ga laifinta.

“Ta dai rubuce ka ta shanye Huisani ina tunanin ko ni da nake mahaifiyarka ba ka so na kamar yadda kake son matar nan, bata samu kan dan'uwanta ba kai ta samu kanka shiyasa kullum ciki mata bauta kake ita da yayanta”

Murmushi yai.

“Hajiya miye laifin Halima dan ta auri Abdulhamid kuma bata aureni ba? Kuma ba cewa tai dole sai ta aureni ba”

“A lokacin da ka ce min kana son ka aureta, wallahi na yi murna sosai, kuma na jidadi domin na fi kowa son hada zumunci da iyala Malam Usman saboda alakarsa da mahaifinku, kuma ita wannan Suwaibar ba kiba take ba zaka auro mai dan kubakuba Wallahi naji dadi tunda ita Halima jikinta luwailuwai yake, aa wai kawai sai na ji zance ya canja ban san yadda akai ta ja hankalin Hassana ba ko dan tana ganin kamar ya fika arziki oho, shi da ba ruwansa da zancen aure ma taja hankalinsa har ya zo da maganarta, kuma bayan tasan kana sonta, yanzu da auren ya dora da sai ka rika kallonta a gidan dan'uwanka kuma kana sonta? Wani abun haushi ma har da aurenta take neman maza waje ko shiyasa ta aureshi dan ta samu damar hakan Allah masani, yanxu kuma aure ya mutu kana nuna alamar sonta taya zamu shirya da dan'uwanka? Kuma jama'a ku ce musu me? A family ayi ta mana kallon tumakai”

Kamar yace wani abu sai wata zuciyar ta hana, ya san dai duk yadda zai yi ma Hajiya bayani ba fahimta za tai ba, ba kuma zata daina ganin laifin Halima ba, shi kanshi be jidadin abunda tai ba a wacan lokacin sai dai ya dauki abunda ta aikata da rashin tunani da kuma kaddarar da ke binta.
Agogon wayarsa ya kalla.

“Hajiya zan wuce gida sai da safe”

“Allah ba mu alheri, na manta ban fada maka ba, surukan Hassan sun kira sun roki alfarmar a daga auren har nan da December”

“Sun kara wata hudu kenan”

“Allah ya kaimu ya sanya alheri”

“Amin”

Daga haka ya juya ya fice daga gidan.




HALIMATU POV.

A daren na rabawa kowa abunda zan bashi, babu wanda be yi murna ba. Washe gari aka tashi da hadari a garin sai dai hakan ba hana ni saurin shiryawa yarana suka wuce makaranta ba, ni kuma na shirya na nufi gurin aiki ina ta Allah Allah kar a sako da ruwa. Na yi sa'ar samun napep na shiga ina fada masa inda zai kai ni, mu tsaka da tafiya ya soma nuna min wata mota da ke binmu mai motar na mana hannu da mu tsaya. A lokacin da na leka sai na gane Abraham ne na rasa yadda zan yi da shi, me zan masa ya fahimci bana son ganinsa ma balle saurarensa. Ban bar mai napep din ya tsaya ba sai da muka kusan isa kamfanin sannan na bukaci mai napep din ya sauke ni, mai napep din na yin parking Abraham ya faka gaba da mu kadan ko kudin shi ban bashi na nufi gurin da Abraham din yake rai a bace. Ko da na isa ya sauke gilashin motarsa aiko take na nufeshi da masifa.

“Me kake da bukata ne? Miyasa zaka rika bibiyarta? Bana son ganinka bana son wata alaka ta shiga tsakanina da kai, dan girman Allah ka kyale rayuwata na huta”

“Ihu fa kike yi? Ba ki tsaya kin saurare abunda zan fada miki ba, na san ba kya son ana ganina a gidanmu shiyasa na biyo napep din da kika hau”

Har na bude baki nai magan sai na ji tsayuwar mota a bayana, juyowar da zan yi na yi arba da Ahmad yana sauke gilashin motarsa.

“Lafiya?”

Sai na kalleshi na kalli Abraham sannan na sake kallonsa na ce.

“Lafiya kalau”

Ban san dalilinsa na tsare Abraham da ido ba, sannan ya sake kallon yace.

“Shine mutumen da yake bibiyarki?”

Na kalli Abraham wanda yai saurin tada gilashin motarsa yana mata key.

“A a makocin mu ne”

Be sake ce min komai ba ganin Abraham din ya bar wajen, sai shima yai ma motarsa key ya karasa cikin kamfanin, sai a lokacin na sallami mai napep din na karasa cikin kamfanin da kafa, ina shiga abokan aikina suk fara min murn wai an canja min aiki an bani wanda ba shi da wahala kuma mai albashi da mai tsoka, na yi murna kamar yadda su ma suke tayani murnar sannan na wuce office dina ina sanye da tufafin da na fi so kuma suka fi karbata wato abaya.
Ganin Ahmad da nai a cikin office din tsaye jikin window ya bawa kofar baya hannayensa duka biyu zube a aljihu, gaba daya office din

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login