Showing 180001 words to 183000 words out of 217237 words

Chapter 61 - GOBE NA Compelet Book by Khadijah Candy.txt

24 Sep 2025

178

saboda ni ba zan iya komai da mace ba, shiyasa na bukaci boye soyayyarmu tun farko bana son wannan sirrin ya bayyana, gano cewar Abdallah yana son ki shi yafi komai bata min rai, kuma lokaci ya kure Haima komai ya lalace, na kasa yarda da ke na rabu da ke, and silata abokina ya keta miki haddi”

Hawaye ya fito daga idonsa.

“A lokacin ne na gano cewar na rabu da matar da ba zan taba samun irinta ba har na mutu, na rasa komai ba ni da mata ba ni da yaya, babu irin neman maganin da ban yi ba amman na kasa samun lafiya saboda Abdallah”

Ya karasa yana murmushin bakinciki wanda hausawa ke cewa yafi kuka ciwo, sai ya kalleni.

“You got lucky za ki auri mutunen da zai ba ki abunda ni da aminu muka kasa ba ki.... And the way da ya dage da neman tona sirrinmu i know yana son ki sosai”

Waiga nai da zimmar na kalli Ahmad amman sai ban ganshi a gurin ba.

“Ba so na yake, abunda kai min kai da Aminu ya tsorata ni daga son wani ko aure a yanzu, murum data na yarda da shi a rayuwata Abdallah shi kadai nake da tabbacin na zai cutar da ni ba....”

“And you can't marry him....”

Ya fada kai tsaye yana kallona da murmushi a fuskarsa hawaye na sauko masa.

“Ba zai yiyu ki aure ni ba, kuma ki auri twina brother dina, bayan kuma ina raye, Hajiya ba zata yarda ba, hakan kuma na zai kara min komai ba sai tsanar Abdallah, and i know duk yadda za ki so shi ba zaki so shi kamar yadda ni kika so ni ba, I'm your first love i know ko yayana wata rana sai kin ji so a zuciyarki kamar yadda ni ma ba zan iya cire soyayyarki a raina ba, so you can't marry my brother kuma ki rayu da so a zuciyarki, no matter what Abdallah zai baki Hajiya ba zata tana son ki ba, saboda tana ganin kin shiga tsakanin yayanta”

Mikewa nai tsaye sai shima ya mike.

“Ban sani ba ko zan sake ganinki ko a a, ban sani ba ko za su yanke kin hukuncin dauri rai da rai ne ko kuma za su halbemu ne i don't know, but i wish you all the best in your entire life, and I'm sorry for what I did”

A lokacin ne hawaye ya fara sauko min kamar ba gobe, tausayinsa ya rufe ni ya sadakar ya san cewar kashe shi za ayi kenan, maganganunsa suka rika min yawo a cikin kai, cewar ba shi da mata ba shi da yafi komai tsaya min a rai, kasa tafiya nai sai kallonsa nake ina hawaye kamar yadda shi ma ya rika waigena yana kuka kamar ba shi ba. Har na nufo inda motar Ahmad take na bude na shiga ban daina hawaye ba, yana kallona hankalinsa ya tashi.

“Me ya faru? Mi yai miki?”

Kasa magana nai sai kokarin saida hawayen nake, hakan yasa shi fusata ya bude motar sai fita nai saurin riko rigarsa ina girgiza masa kai.

“Be min komai ba”

“Then why are you crying?”

Na yi saurin share hawaye.

“Ba komai”

Kallona yai for a moment sannan ya rufe motar muka kama hanya, sai da muka hau titi ya dauko ruwa ya miko min, na karba na bude ya sha ruwan sosai sannan na rufe na aje. Har muka isa gida ban ce masa komai ba shi kuma be fasa kallona ba, bayan yayi farkin na fita cikin motar.

“Thank you”

Na furta ba tare da na jira abunda zai ce ba na shige cikin gidan, a wunin ranar sai na kasa sukuni cikin abunda nake tunani har da zancen samun lafiyarsa wanda yace Abdallah ne, kamar ya? Shi ya masa wata allurar ne ta zame masa haka? Amman Abdallah ya san da da wannan kuwa? Mi zai saka yayi masa haka?
Kamar ya san ina tunaninsa sai akai sara ka gaba, kiransa ya shigo wayata, sai dai wannan karon kasa daukar wayar nai har tai ringing ta katse sai ya sake kira sannan na dauka. After mun gaisa yace min.

“Abdulhamid yace kin je gurinsa yau”

“Eh”

Na amsa masa a takaice duk da na san ya kira ne saboda ya san dalilin zuwana.

“Okay”

Har zai aje wayar na ce.

“Abdallah zan iya tambayarka wani abu?”

Shiru nai na wani lokaci har sai da yace.

“Ina jin ki”

“Da gaske kai ne silar ciwon Abdulhamid?”

Shiru yai daga can cikin wayar sannan kamin ya aiko min da tambaya.

“Kamar ya?”

“Ya fada min kai ne sila, taya?”

“Magana ce mai tsawo Halima zan na same ki gida daman akwai maganar da nake son yi da ke”

“Ka fada min dan Allah, zuciyata ta kasa yarda kuma na kasa natsuwa”

Ina jin yadda ya sauke ajiyar zuciya sannan yace.

“Abun ya dade tun muna samari ne, na tashi da son yara musamman maza, and Abdulhamid ya san da haka, kamar wasa wata rana muna magana nace masa zan riga shi aure, shi kuma yace ko na riga shi aure ba zan haifi namijin da nake da buri ba, ni kuma na ce masa shi kuma ba zai ma taba haihuwar ba har sai na haifi namijin, and na gano haka ne after Suwaiba ta fara haihuwar Mata, and last barin da tai ma macece, yayi min kofi ne and after that Hajiya ta ba mu maganin kare kofi saboda abubuwan da suke faruwa, na shi ya kare nawa kuma ya rage kaifi that's what i know”

***
( Wannan abun ya faru a gaske, Hasana da Husaina, Husaina tai ma Hassana kofi cewar ba zata taba aure ba, ita kuma Husaina tace mata ko tayi auren ba zata taba haihuwa ba, har yau kuma suna nan da rai sun fara manyanta Hassana ba tai aure ba Husaina kuma bata haihu ba)

***

Ajiyar zuciya na sauke ina mamakin yadda sukai wa junansu illa.

“Zan zo gobe akwai maganar da nake son yi da ke”

Ban sake ce masa komai ba na kashe wayar, a ranar na kwana da mamakin abun a zuciyata. Sai mafarka da safe kamar wata marar lafiya, haka dai na shiryawa su Amal suka tafi makaranta sannan ni kuma na shirya, yau ma abayar na saka sai dai wannan ash color ce tsabanin jiya da na saka black, sai da nai ma Inna da Mama sallama sannan na nufi gurin aikina kamar yadda Ahmad ya bukaci na dawo aiki bayan hutu daya ba ni wai sai na samu lafiya.
  Napep na hau bata sauke ni ko'ina ba sai kofar gate din kamfanin, na gaisa da masu gadin kamar yadda na saba sannan na nufi ciki, a reception ma sai da na tsaya na gaisa da Blessed mace mai kirki da son mutane, sai da ta tambayi abunda ya hanani zuwa aiki kwana biyu na fada mata cewar bana jindadi ne, sannan na wuce na nufi office dina. Ina kai hannu na tura kofar office din gaba daya sai naga kamar ba nawa ba, hakan yasa na dawo waje da sauri na sake kallon kofar sannan na sake shiga, gaba daya an kawata office din da abubuwan kawa kamar gurin taron biki, idanuwana sama na shiga cikin ina ta kallon kyale kyalin da ke saman sai wani kamshin rose ke tashi an kuma jera fulawar rose har saman kujerar da nake zama. Ji nai kamar na taka wani abu mai tsantsi hakan yasa na kalli kasa da sauri sai nai arbar da fulawar rose an yi rubutu da ita cikin mayan haruffa.

*WILL YOU MARRY ME...*

Wani irin faduwa gabana yai, da ni ake ko da wata abunda nake gani a fina fine nake karantawa a litattafai yau shi ne a gabana, motsin da na ji a bayana yasa na juyo da sauri kamar a rikice nai arba da mutum duke a gabana......

______________

I can advertise your business with some of my pages and status just chat me. 08036126660😊🙌
7/21/21, 11:10 PM - Buhainat: *GOBE NA...*

By Khadeeja Candy


5️⃣6️⃣

Red suit ne jikinsa babu abunda ke fita daga jikinsa sai kamshin turare, kallona kawai yake sai dai ba irin kallon da ya saba min kamar zai cinye ni ba, wannan karon ido a lumshe yake kallona kamar mai jin bachi. Nikam gaba daya jikina rawa yake ban tana ganin a fili ba ba a taba min irin haka ba ban kuma saka ran wani zai min ba, juyawa nai na karewa office din kallo na sake kallonsa daga ni sai shi ne a office din amman na kasa yarda cewar da ni nake, na kasa yarda ba mafarki nake ba har sai da na runtse ido ya bude na sake runtsewa na bude sannan na yarda ba mafarki nake ba, daman shine mamakin da yace zai ba ni? Na nuna kaina sai ya gyada min kai.

“Will you be my wife for the rest of my life?”

Ya fada da bakinsa still yana duke a gabana, hannunsa rike da dan karamin box da zobe ciki. Rasa nai abunda zan yi idan na ce masa no ransa ba zai masa dadi ba, sai dai be kamata yai min haka ba at least i need to think ina bukatar nai shawara, but what else i can say more YES.

“YES.....YES....YES...”

Na maimaita har sau uku ina gyada masa kai idanuwana na cika da kwalla da ban san na minene ba, rashin ba ni damar yin tunani ko shawara ko kuma mamakin abun ko kuma amsawar babu shiri? Ko kuma na bakuntar sabon al'amari? Ba zan ce na murna ba dai domin a yanzu ban zan iya tantance a halin na ke ba farinciki ko akasin haka?

“Oh Yes Babe my search is done”

     Ya furta, gaba daya hannayensa ya hada ya matse sosai ya runtse idonsa yana wani irin murmushi da ba zan ina fassarasa ba, sannan ya mike tsaye ya kama hannuna for the first time ya yana kokarin saka min zoben da nake mamakin yadda akai ya san size din yatsuna, after ya saka min zoben mai haske da kyalli kamar na gold sai dai wannan zaiba ne, kallona yai ya dora hannunsa saitin zuciyarsa.

“You're here in my heart, you're my destiny, you mean to be mine, so let's give love another life....”

Faduwa yai gabana kamar mai neman gafara ya jimke hannayensa ya lumshe ido.

“Duk yadda zan fada miki irin farincikin da nake ciki a yanzu, to zan yi karya ne kawai, but i can promise you one thing nothing can keep us apart, all i want is to live with you, i will be someone that you can always turn to, i will be everything you want, you mean the way to me, i will fix what it broken, Lims i need you”

Sai kuma ya mike tsaye yana kallona da murmushin da zan iya kiransa da dariya, ya zagaya bayana ya zagayo ya sake haka kusan sau hudu sannan ya sake tsawa a gabana yana sauke numfashi, har lokacin ina tsaye a gurin ina murza zoben da ya saka min, har lokacin bana jin murna farinciki, bakinciki damuwa ko akasin haka, I'm not happy kuma i'm not sad. The way da yake fadi wasu maganganu sai na ji kamar ba shi ba, domin a yadda yake a da zaka iya rantsewa Ahmad ba zai iya furtawa wata kalar so ba, watan kuma ni Halima, dana dago sai idanuwa suka sarke cikin nasa na saka kawarda nawa, shi kam daman kamar hakan yake so sai Murmushi yake sakar min, hawaye ne suka sauko min, sai ya matsa kusa da ni sosai.

“You should know this love i share was never mean to die, co's i don't wanna see you cry, i will never treat you bad, ban tana yarda so nake ba sai Lims kin san yadda nake ji a raina? Kamar na dauke ki na hade you're the queen of my heart, wani irin farinciki nake ji marar misaltuwa”

Ya shafa kansa tare da daga kan sama yana busar da iskar bakinsa, ya nufi gurin windows office dina ya tsaya sai kuma ya juyo ya kalleni.

“Ba zan iya tuna ranar da wani farinciki ya same ni kamar haka ba....”

Maballin gaban suit din ya bude ya nufo inda nake ya kama hannuna ya dora saitin zuciyarsa.

“This where you belong, i hold you close to me”

Da gaske zuciyarsa bugawa take da mugun karfi kamar zata fado kasa, duk yadda nake jin bugun zuciyata nashi ya ninka nawa sau dari, janye hannun nawa nai har lokacin na kasa cewa komai, bakina yayi nauyi sosai a kaina kuma ina jin kamar babu wasu kalmomi ciki, a hankali na ji ana busa min iska a idona sai na lumshe ido ina shakar iskar bakinsa mai kamshin strawberry, har na daina jin iskar ban bude idon ba sai da na ji an bude kofa an fita sannan na bude idon a hankali, ban ganshi a gabana hakan ya tabbatar min da cewar ya fita daga dakin kenan. Kujera na nufa na dauke fulawar rose din ya zauna na rumgume ta a hannuna ina ta kallonta kamar ance min makomata tana ciki, na hade yawun bakina yafi a kirga kamin ya sake duba daya zauna a hannun kamar dan ni akai shi, kamar ance na juya na kalli windows sai na hango shi tsaye yana kallona. A wunin ranar kasa aikin komai nai sai jikina yai kamar wacce akai wa allurar rashin kuzari ga kuma magana da na kasa cewa komai, gaba daya sai m afka duniyar tunani, i think kuma ia say i will never fall in love, amman me kenan? Ko da yake ba zan ce ina son Ahmad ba kuma ba zance na tsane shi ba, amman makomar yarana fa? Shi ma zau dauke su kamar yayansa? Ko kuma zai yi min irin na Abdulhamid ne? Mahaifiyarsa za tai maraba da ni ko kuma dai ita ma kamar Hajiyar Aminu da ta Abdulhamid take? Da gaske zai iya rike ni tsakani da Allah ko kuma a a, ba zan iya gano haka a yanzu ba all what i have to do is nai Istihara na sanarwa Allah matsalata na kuka masa damuwata sannan na nemi mafita a gurinsa, na nemi zabinsa a tsakanin auren Ahmad ko akasin haka.
  Na sani duk yadda zan tsorata da auri ko na guji aure, shine dai matarba da cikar kamala ta, shine zai kare mutumcina yai min katanga daga duk wani abu da zai iya samuna a kafin igiyar aure, so ba ni da wani zabi da ya wuce na kaunaci sunnar manzo na nai bibiyaya ga Ubangijina, kuma na yarda da wannan kaddarar ko da kuwa ita ma kamar wadancan take domin shine cikar imanina.
  Kamar ance daga ki gani sai ganin mutum nai jikin kofar office din ya rumgume hannayensa yana kallona, sai murmushi yake kamar wanda be taba shiga damuwa ba, kamar jira yake na dago sai ya karaso ciki ya tsaya gaban teburina yana min kallo daya saba.

“Za ki yi magana da Hajiya ta yanzu nan, tace tana son magana da ke, bata yarda da ni ba”

Ya fada min a hankali kamar mai magana da yaro karami yana son ya fahimta. Be jira cewata ba kamar yasan ba abunda zan fada din ya ciro wayarsa ya kira number ta ya saka a hands-free sannan ya kwanto jikin teburin yana cigaba da kallona, kamar wanda kallon nawa yake kara masa karfin ido. Ina jin lokacin data dauka sai yace.

“Hajiya ga ta”

Ya miko min wayar ni kuma na mika hannu na karba ina kallonsa kamar mai tunanin abunda zan yi da ita.

“Yata.... Da gaske ne abunda Gwarzo ya fada min? Wai kin amince za ki aure shi.....?”

“Eh haka ne...”

Kamar an matsi bakina haka maganar ta zo min subul da baka. Shi kuma sai ya turo bakinsa ya aiko min da kiss marar sauti daga inda yake tsaye.

“Alhamdulillah Allah mun gode maka, Allah ya tabbatar da alheri a tsakaninku, ya kawardar fitina da sharin sheidan da na zuciya, ya kawar da idon makiya”

“Amin”

Wannan karon shi ya amsa yana wani lumshe ido.

“Yanzu kin yarda?”

“Na yarda kuma na fi kowa farinciki zan yi ma Siyama wannan albishir din, Allah ya maka albarka, kai da kanka ka nemo matar ka I'm very happy”

murmushi yai ya yanke wayar, ni kuma na mike tsaye na fara shirin tafiya.

“Daga yau idan na fito daga gida zan biyo na dauke ki, idan kin tashi aiki kuma ni zan kai ki”

“Amman....... ”

“Shiiiiiiiiii”

Ya dora hannunsa saman bakinsa yana min alama da nai shiru.

“Kuma idan kin je gida ki bar mahaifiyarki ta san abunda yake faruwa, nima zan yi magana da Hajiya zata sanarwa wadanda ya kamata ina son dai cikin satin nan na tabbatar da gaske kin zama tawa, idan an daura aure ban ki ba amman ba zan yarda sati ya shige ban biya sadakin wannan kyakkyawar Babyn ba”

The way da yake magana ban ga alamun da wasa yake ba, amman ya yake min haka kamar mai ba ni aiki? Ko dai ya manta ni bazawara ce? Wani irin biyan sadaki a yanzu kamar wanda ya matsu ko kuma nace wace aka gaji da ita? Anya yau Ahmad lafiya yake kuwa? Daga zancen saki aure sai kuma maganar manya su shiga lamarin kamar wani abunda ba gaske ba? Daman a cikin surprise dinsa har da wannan ko kuma yanzu idea ta zo masa? Kamar wacce yai ma wani magani sai na kasa ce masa komai sai kallonsa nake ina mamakin al'amarinsa, kamar wanda aka ce masa zan gudu, a take ni tsaro ma ya kamani.


_________________

Finally Halima tace Yes to a bani goro 🙄
7/21/21, 11:10 PM - Buhainat: *GOBE NA...*

By Khadeeja Candy


5️⃣7️⃣

“Ban san abunda Hassan yake nema a duniyar nan ba, ban san wani abu da ya rasa ba, ban san kadarar da ta kai shi fadawa wannan mummunar sana'ar ba, na jama kansa masifa... Wata kila a kashe su wata kila a barsu su kasara rayuwar gidan kaso, amman ko da an sake su an kunyata su tun da an bayyana fuskokinsu kowa ya gansu, a lokacin da ya kamata ace ya samu farinciki sai kuma wannan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login