Showing 48001 words to 51000 words out of 217237 words

Chapter 17 - GOBE NA Compelet Book by Khadijah Candy.txt

24 Sep 2025

184

za ku yi, ku sake min wani rai ku sake kashe ni ba ni da abunda zan ba ku bana da azurfa ma balle zinari Wallahi bana da komai”

“Okay Anas dauko mana yarinyar can idan ubanta ya dawo ya ba mu kudi sai ya karbo ta”

Ban san lokacin da na girgiza musu kai ba.

“Aa Wallahi ba yarsa ba ce, ba babanta ba ne kuma bata da lafiya dan Allah ku rufa min asiri karku dauke ta”

Ina ganin ya nufi gurin da Amal take na nufi gurin da rarrafe ina kuka majina na min zuba, fisgota yai da hannu daya ta mikar da ita tsaye sai ta lauye kafafuwanta ta fara kuka irin kukan na yaran da aka tayar daga bachin da be ishe su ba ballantana ita da lafiya bata ishe ta, kafafuwanta na rike na fashe da wani irin kuka marar sauti.

“Anas sake ta”

Kamar umarni mutumen da aka kira da Anas yake jira sai ya sake Amal da sauri ni kuma na rumgumeta, ita kuka ni kuka.

“Kin ce ba ki da abunda za ki ba mu ko? To ni ina da abunda zan ba ki ta so nan zan bar ma mijinki sako, idan ya dawo ki fada masa ya aje mana kudi kamin mu sake dawowa...”

Yana fadar hakan ya mikr tsaye ya nufo inda na ke, da wani irin karfi na rashin imani ya fisge Amal daga jikina ya wulgarda ita kasa ya ja bayan rigar atamfar da ke jikina kamar wata baiwa ya nufi bayan kujerar da sauran suke zaune da ni.
A gurin ya yaga mutuncina, a gurin ya karya martabata, a gurin yai min bakin digon da ban taba mafarkin yi ma kaina ba, a gurin ya tarwatsa rayuwata, a gurin ya gussar da ragegen farincikina, a gurin ya saka min tsoro da fargaba da bakincikin GOBENA. a gurin ya biya bukatarsa ina kuka da  gurnani kamar wance bata taba sanin da'namiji ba a rayuwarta.
Ba badurwa wa ce ni ba balle nai kukan karbar budurcina da yai dai dai nai kukan karbe martabata da farincikina.
Har ya daga daga jikina ya gyara wandonsa ban daina kallon fuskarsa ba, so nake ko yayana na ga wanda ya keta min haddi, ji nake kamar ace ina da ikon cire a lokaci na raba shi da rayuwarsa, hawayen da suke sauko min a lokacin ne suka tabbatar min da kukana be kare ba, bakincikina be gushe ba. Risinowa yai kamar zai sumbanci bakina ya dauki zobensa da ya fadi mai alphabet din A ya saka a saman hannunsa sannan ya bar jikin kujerar ya koma gurin da sauran yan'uwansa suke.

Ina jin lokacin da suka fita daga falon da kuma tashin motarsa, wasu hawaye masu zafi suka sauko min daga inda nake zaune, ban taba jin wulakanci da kaskanci kamar na wannan ranar ba, ban tana jin na tsani rayuwata kamar yau, ban tana jin kyamar kaina kamar yau ba, na dade ina kare mutunci da martaba da aurena ko babu amman a yau wani wulakantacce marar daraja ya kawar da duk wannan.
  Komawa nai a gurin na kwanta kamar gawa, numfashin da ke fita daga hancina ne yake tabbatar da rayuwata,  zuciyata na zafi da ciwo kamar an saka takobi mai kaifi an yanka ta gida biyu. Sannu a hankali na fara jin numfashin kamar baya wadatar da hancina hakan yasa na bude bakina ina fitar da numfashina a hankali.
Ina jin kukan Amal amman na kasa dagawa na je gurin da take, jikina ya mutu kamar wacce akai wa allura, wayata ma dake kitchen ringing take sai dai yau ba ta Amal na ke  ba balle wayar. Kukan Amal da ringing din wayata suka ba ni wani yanayi na dabam, yanayin da ya saka ni tausayawa kaina da kuma yata Namra, ina ta auna irin halin da ta tsinci kanta ko kuma wanda zata tsinci kanta a ciki nan gaba...
  Ina kwance a gurin har dare ya raba, a lokacin Amal ta ci kukanta ta gaji ta tayi bachin wahala, sai a lokacin Allah ya kawo min kuzari har na iya rarrafawa na shiga dakina da rarrafe na iss bandaki, ba karfin jiki na kawai abunda na rasa ba har da na zuciya wanda shine silar rasa na jikin gaba daya. Duk yadda nai unkurin mikewa tsaye sai na kasa kamar wacce bata da fafuwa haka na zama, ba ciwo ko nauyinsu na ke ji ba, jin su nake kamar babu su a jikina raunin da ke zuciyata yana sauka har cikin jikina, ba jimin yai ba, amman a yau ina jina kamar cikkakkiyar budurwar da aka fasawa budurcinta.
Allah nai ta ambata a zuciyata, bakina kuma yana da rawa alamar kuka be kara min ba ko ma nace ban fara shi ba, jin jikina nake kamar ba nawa, daker na iya mikewa tsaye ban san abunda ya same ni ba sai zamewa nai na fadi kasa, ban sake unkurin tashi ba, a gurin na kwanta ruf da ciki hawaye na ce min sallamu alaikum har aka fara kiran farko na sallah asuba. A lokacin ne na samu kuzari har na gwada tashi tsaye bayan an zauna na yan mintuna.
Allah kuma ya amincin min na iya kunna hitar da ke bandakin na zauna a cikin tub din na rafka wani uban tagumi, ina ta neman inda hawaye za su fito min na rasa. Sai da na hada ruwan nai wanka na tsaftace kaina sannan na fito na dawo bakin madubin gadon ana zauna ina ta kallon kaina. A zahiri kaina na ke kallo amman a badini GOBENA na ke hangowa ya zata kasance? Miyasa abubuwa mabanbanta suke ta faruwa da ni? Idan na fita daga wannan sai na fadawa wannan? Mijina ne ya fado min a rai! Idan Abdulhamid ya ji zai zauna da ni? Zai cigaba da so kamar yadda yake? Zai kaunace mi mu cigaba da zama kamar mata da miji? Wata kila kuma ya juya min baya waye zai so wani namijin ya kusanci matarsa balle irin wannan da kika fashi? Ban san lokacin da na dauki Vaseline din dake gaban madubi ba na jefi gaban madubi da shi a take ruwan madubi ya tarwatse wani irin kuka mai taba zuciya ya ziyarce ni, sai ga ni a kasa ina kuka da hargagi kamar mahaukaciya, kamar wacce aka tsakala sai na yi saurin tashi zaune ina girgiza.

“A a ba zan fada masa ba, wannan sirina ne ni kadai ni kadai ya dace na rufe abuna babu wanda zai sani, ba zan taba fada masa ba, ba zan iya rusa farincikin aurena da kaina ba, ban shirya fuskantar wani kalubalen na rayuwar aure ba a yanzu, ba zan fadi abunda zai saka Abdulhamid ya tsane ni ba, ba zan fada masa abunda zai saka ya kyamace ni ba, ko wannan bakincikin zai kashe ni ba zan fadasa kowa ba, wannan kaddarar Halimatu ce ita kadai”

Wannan karon a fili nai maganar ina ta karfafawa kaina guiwa, duk kuwa da ina jin wani bangaren na jiki da zuciyar ya son sauya min tunani daga boyewar zuwa fadawa Abdulhamid gaskiya. Wani irin kuzari da karfin hali ya zo min a take nemi rashin karfin na rasa, tawul din jikina na cire na saka doguwar riga na fito falo da zimmar duba Amal sai na samu kaina da duba bayan kujerar na kasa dauke idona daga barin kallon gurin ina ta aina abunda ya faru hawaye na min zuba. Ba tare da tsoro ko fargabar komai ba na fito harabar gidan ina ta kalle-kalle kamar bakuwa, dubun asuba be hanani ganin ko'ina a gidan ba, ba su fasa mana komai ba bayan gate din da suka bar mana bude. Ba tare da tsoron komai ba na nufi gate din na da kaina  na rufe, ba tsoro ba, a yanzu ina jin ko mutuwa na shirya mata balle kuma tsoro. Falo na dawo na zauna na zubawa Amal ido kamar ance min ita ce maganin damuwata, wayar da ke kitchen din ce ta fara ringing cikin sauri na tashi na shiga kitchen din sai na tararda wayar kife a kasa hannu na kai na dauko wayar sai screen din wayar na gani a tsage sai dai hakan be hana ni ganin kiran Abdulhamid ba da sunan da nai saving din numbersa ✨🔐Final choice❤😍 tare da aljanun da nai yi ma sunan kwaliya da su. Samun kaina nai da kasa daukar kiran har ya katse wani ya sake shigowa ya katse sannan sako ya biyo baya.

“Baby na kira tun jiya ba ki daga ba ina son jin muryarki na isa lafiya. Pls ki kula min da kanki”

Ina gama karanta sakon na narke cikin wani sabon kuka na rumgume wayar a kirjina, ina ta jin kamar ba zan iya boyewa Abdulhamid, idan na boye masa ban masa adalci ba.

“Amman kuma idan na fada masa zai yarda? Zai gasgata ni bayan ba su dauki komi ba? Ba su fasa mana gate ba balle kofa, ba su harba bindiga ba balle na ce makota su ne shaida ta?”

A fili na ke ta aiko tambayoyin ina mai jin kamar akwai wani a kusa da ni ya amsa min su. Waya turo su? Da gaske kudin suka zo karba ko kuma daman can mutunci suka zo yagawa? Turo su aka ko su suka turo kansu? Ina suka ji ko suka san cewa Abdulhamid ya samu kudi ko zai samu kudi? Ban ankara ba na ji an tayarda ssallah Asuba hakan yasa nai hanzarin baro kitchen din na dawo dakina, alwala na fara yi sannan na gabatar da sallah asuba, na sani sarai ba kyau kukan da ba na tsoron Allah ba a sallah amman na kasa tsayarda da hawayena har nai sallah na gama, babu komai a addu'a ta sai tarin Allah ya isa da neman tsarin Allah daga shiga wata damuwar.

Misalin bakwai na fito falo jikina na min nauyi kamar ba nawa, gurin Amal na nufa na dubata har lokacin bachi take sai dai jikinta da zafi kamar jiya, hannu na saka na dauke ta na nufo daki da ita kamin na shiga dakin ta farka da kuka tana kiran sunana, amman na kasa amsa mata sai kokarin rabata da tufafin jikinta nake. Wayata ce ta sake ringing haka yasa na aje Amal na nufi inda wayar take, Final choice ne rubuce akan wayar har na yi kamar kar na dauka sai kuma wata zuciyar ta hanani hakan yasa na danna picking na kara wayar a kunne ina hawaye.

“A ka'ida idan kika daga wayata sallama kike fara min cikin nishadi da walwala, sannan gaisuwa ta biyo baya amman yau babu ko daya”

Ya fada bayan ya dauki lokaci yana sauraren numfashina, lumshe ido nai na bude hawaye na sauko min har lokacin ban samu kwarin guiwar fada masa damuwata, idan na fada masa ban san iya halin da zai shiga ba ban san ya zamantakewar aure zata kasance ba! Ban san ya zamu rika kallon juna ni da shi ba.

“Tabbas akwai damuwa a tare da ke matata, sai dai bana da tabbacin damuwar ta rashina ne a kusa da ke ko kuwa wani abun ne dabam, na ji ba dadi gaskiya domin har ga Allah bana son abunda zai bata miki rai a yanzu Haima, bana son wani abu ta zai taba zuciyarki saboda ina matukar kaunarki.....”

Wasu zafafan hawaye ne suka sauko min ban san lokacin da naja dogon numfashi na sauke ba.

“Fada min waya taba ki?”

Ya sake tambaya, sai na girgiza masa kai kamar yana gabana, sannan nai saurin share hawayena.

“Babu komai babu komai I'm fine”

“No you're not pls....”

“Trust me babu abunda ya faru kawai dai ya farka ne jikina babu dadi kuma i miss you so much”

Daga can cikin wayar ina iyo jiyo sautin murmushinsa tare da aje numfashin jindadi a lokaci daya.

“Karki damu yau zan dawo ai ni kaina i miss you alot, fada min me kika ci?”

“Yanzu zan karya ban farka da wuri ba”

“Haima bana son kina zama da yunwa fa, ace har yanzu ba ki karya ba? Pls ki daina haka bana so okay”

“Yes ba zan sake ba”

“Je ki karya zan sake kiranki, i love you”

Kai kawai na iya gyadawa na sauke wayar daga kunne na hawaye na min zuba kamar ba gobe, a hankali na zauna a gurin ina jin wani abun marar dadi yana ratsa zuciyata.

“Wani ya taba ni Abdulhamid wani ta taba maka mata, wani ya keta haddin matarka wani ne ya rusa raguwar farincikina, wani ne ya saka ni a dakin da ake dandana dakin fyade da ke da ke tarbar ko wace mace mai aure ko budurwa wacce namiji ya keta mata haddi, an yi ma yata jiya kuma ni akai yi wa? Right.... ”

“Yes kuma wannan sirrina ne ni kadai babu wanda zai sani be kamata kowa ya sani ba, ko da Mama ce ba zan fadawa kowa ba, ni kadai na sani kuma ni kadai ya kamata na dandana dacin abun daman”

Magana nake da kaina ina ta kokarin karfafawa kaina guiwa. Hawayena na share na mike tsaye sai wasu suka sake zubo min, saurin runtse ido na nai gam na dantse bakina tareda hannuna na hagu.

“Za ki iya, za ki iya Halima.... ”

Shine abunda na ke ta fadawa kaina kamin na ji muryar Amal tana kwala min kira.


*Khadija Abubakar Alkali*
7/20/21, 8:32 AM - Buhainat: *GOBE NA...*

By Khadeeja Candy


1️⃣8️⃣

Sai da na gyara Amal na gasa mata jikinta sosai da ruwan dumi wanda hakan yasa ta dan kara sakewa har na hada mata tea ta sha ta rike yankan biredin a hannu sannan na shiga gyara ko'ina na gidan.
Duk kuwa da kasancewar barayin ba su mana barna ba ko barin wata alama da zata saka a gane cewar sun shigo cikin gidan ba, ba su balla mana gate ba balle kofa ba su yi harbi ba balle su tafi da wani abun, babu ma wanda zai shigo cikin gidan ya yarda wani ya shigo da sunan sata.

Sanin cewar Abdulhamid na son sakwara yasa na dafa da miyar agusi, bayan na gama na shiga nai wanka na dawo palo na zauna rumgume da Amal jikinta da dan zafi sai dai ba kamar jiya, ni kuma zuciyata cike da zafi fiye da ko yaushe har bana iya controlling hawayena. Sai daf da magariba Abdulhamid ya dawo sai da na wanke fuskata sannan na fita na bude masa gate, iya kar kokarin da zan iya yi na boye damuwa na yi amman hakan sai ya ci tura saboda damuwar da ke raina a yanzu mai girma ce.
  Tun daga muryata da kin son hada ido da nake da shi ya fara karantar damuwata.

“Kin fada sosai Haima idonki kuma ya kumbura gaba daya ba ki cikin natsuwarki, na fada miki zan taso daga Abuja zuwa nan amman ba ki kira kin tambayi lafiyata ba bayan ba ki saba haka ba”

Cikin rashin natsuwar da kirkirar irin karyar da zan masa na kalleshi ina hade yawu, sai a lokacin na tuna cewar yunin ranar ban saka komai a cikina ba sai ruwa shi ma ba da yawa ba, a rayuwar yau na manta da an taba halittar yunwa a cikin duniyar nan.

“Hankalina ba kwance ba Amal ba lafiya”

“Subhanallahi miya same ta?”

Ya fada yana rufe motarsa ya matsa kusa da ni ya kama hannuna yana murza yatsuna a hankali. Dagowa nai ya kalleshi a maimakon na amsa masa sai hawaye suka sauko min.

“Je ki dauko mayafi na kai ki ki ganta yi sauri”

Ya fada cike da kulawa a zatonsa Amal tana gida ne ba a gidansa ba.

“Tana nan a falo jiya na dauko ta... ”

Saurin sakin hannuna yai ya nufi kofar falo, wanda hakan ya ba ni damar share hawayena na bi bayansa, ina shiga na same shi kusa da Amal zaune yana taba jikinta fuskarsa dauke da murmushi, a hannun kujerar na zauna ina ta kallon bayansa, a zahiri bayansa na ke kallo a badini kuma makomar aurenmu na ke hangowa a tsakanin fada masa gaskiya da kuma boyewa, idan na fada masa zai jure? Zai zauna da ni a haka? Idan ma na boye mi ye amfanin boyewar? Wace iri zan ci?

“Ashe ma da sauki kike ta kuka haka har kin tada min da hankali”

Ya fada yana juyowa ya kalleni ba karamin jihadi nai ba na aron murmushin da ban san da zaman sa a duniyata ba na yafa a fuskata.

“Al-hamdulillah amman dazun jikinta kam akwai zafi sosai, kuma ina ta fargabar rashin fada maka da ban yi ba na dauko ta ka yi hakuri”

“Karki damu ai lalura ce”

Ya ba ni amsar yana maida hankalinsa gurin Amal. Ni kuma na tashi na shiga bedroom cikin rashin kuzari na hada masa ruwan wanka ina mikewa tsaye na ji an rungume ni ta baya.

“I love you so much Haima, kuma na zo miki da albishir In-Sha-Allah ina daf da samu lafiya ko yau kamin na baro Abuja sai da na ga wani likita kuma kwarare ne, ki cigaba da hakuri very soon za ki zama kamar ko wace matar aure”

A hankali na sauke ajiyar zuciya sannan na share hawayena na juyo ina fuskantarsa wasu hawayen na sauko min fuskata kuma da murmushi har na bude baki nai masa magana sai ya rumgume ni a zatonsa hawayen murna ne. Mun dauki lokaci mai tsawo a haka kamin ya sake ni ya shiga wanka ni kuma na fita na hado masa abinci na kawo masa dakinsa.
  Bayan sallah isha'i na fara shirye shiryen mai da Amal gida gurin Mama saboda nasan Amal idan har tana ganina ba zata iya kwana ita kadai ba ko kuma ita da wani ba, kamar yadda nake zaton Abdulhamid ba zai min lamanin kwana shi kadai ba ni na kwana da yata, na yi zaton zai ce na barta ta har na wani lokaci ko kuma gobe amman be ce min komai ba be hanani ba kuma be ce min na kai ta ba.
  Bayan na gama shiryata nai masa magana cewar ya kai ni a motarsa na maida ita gida, ga mamakina

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login