Showing 132001 words to 135000 words out of 217237 words

Chapter 45 - GOBE NA Compelet Book by Khadijah Candy.txt

24 Sep 2025

187

ni ce babba a cikin yayanki, ya kamata na zama mai hankali da tunani ko? Da hangen nesa amman duk ban zama ba”

Zaunawa nai kusa da ita na kai jikina a cinyarta na kwanta ina kuka.

“Fada min matsalarki miya faru”

“Mama Abdallah..... Ya fada min a yau ba zai aureni ba”

Murmushi tai.

“Halimatu kenan, daman taya za'ayi Abdallah ya aure ki? Bayan dan'uwansa ya aure ki? Kuma dan'uwan nasa yana nan a raye? Mu ma ai ba zamu bari ki aikata wannan kuskuren ba, domin na san kiyayya da gaba ce zata shiga tsakaninsu wanda mahaifiyarsu ba zata so hakan ba”

“Amman.... Ba.... Haramun...ba ne... ”

“Ke kika san wannan, abubuwa da yawa yanxu al'adarmu ta mayarda su haram saboda kunya da gudun samun tsabani, kin yi kuskure Halimatu da dai tun farko ne kina da damar zabar Abdallah ki bar Abdulhamid amman ba ki yi ba, tun farko Abdallah ya kamata ki aura na ta nuna miki amman kika kasa ganewa, mutum da be taba kyamar yayanki ba, be taba nuna gajiyawa a taimakonki ba, shine mutumen da ya kamata ya zama abokin rayuwarki tun farko”

Dagowa nai na kalleta.

“Amman wani abu be taba shiga tsakanina da Abdulhamid ba....”

“Mutane ba su san da wannan ba”
 
Tashi nai daga dakin gaba daya, na nufi dakina, na zauna saman katifata ban ji ina bukatar komai ba sai kuka da nadama. A ranar ban rumtsa ba har sai da na rubuce labarin kaddarar rayuwata tas a jikin takardar da Abraham ya karbo min.
  Da akam ban yi niyar zuwa ba, amman yanzu zanje saboda yara wadanda ke ta daukin zuwan.
  Misalin takwas da rabi na dare aka aiko ana kirana, na san be wuce Abraham ba, wannan karon ban musa ba na saka Hijabina na fita, a inda ya saba tsayuwa na nufa yana tsaye a gurin jimgine da motarsa yana kallona har na karaso.

“Ya kike?”

“Ina lafiya”

Na amsa ba tare da na kalleshi ba. Sai kuma yai shiru yana kallona.

“Kamar kina cikin damuwa”

Sai a lokacin na kalleshi.

“Kaine karin damuwata, da zaka daina bibiyata da na samu salama, ka tafi na yafe maka, kaima kana cikin kaddara ta ne”

“Za ki aureni kenan?”

“Ba zan aureka ba”

Na amsa masa ina kuka.

“Ko da zan musulunta?”

“Ko da zaka aikata abunda ya fi musulunta, idan zaka musulunta ka musulunta saboda Allah kawai, saboda gudun azabarsa, saboda tsoronsa saboda kaunar Annbinsa, karka musulunta dan ni domin ni bana tabbata amman Allah tabbatacce ne, wanzanje wadatacce, tsarkaken, tsabtatacen, ka musulunta saboda tsoron wuta da kwadayin aljanna, zaka iya musulunta a yau saboda ni gobe Allah ya karbi rayuwata, shi zaka ci gaba da musuluncin ne ko zaka daina? Amman idan ka yi saboda Allah shi Allah tabbatacce ne, imaninka zai tabbata har Aljanna, kada kai komai saboda ni a yanzu ba aurene a gaba na ba, bana jin zan sake soyayya ma balle aure”

“Saboda me....?”

“Saboda mutumen da nke so, ba zai taba aurena ba, ya fada min zai mutu da so na a ransa, ni kuma zan rayu da kaunarsa har izuwa ranar da ajalina zai riske ni... ”

Na karasa cikin kuka.

“Wane mai sa'a ne wannan?”

“Wani ne wanda ya so ni a lokacin da duniya ta guje ni, ya taimaka a lokacin da bana da mai tsaya min, ya so yayana a lokacin da ubansu ya guje su”

“Then miyasa yanzu ba zai aureki ba?”

“Saboda na auri dan'uwansa, mutumen da ka keta min haddi a gidansa, dan Allah wannan zuwan ya zama na karshe a gurina, ka barni na ji da damuwata”

Na karasa ina hade hannayena ina rokonsa.

“Ke ba ki yarda haduwar mu kaddara ba ce? Taya za ka yi mace fyade a dare a lokacin da kake boyon kanka, sai kuma ka dawo da rana ka kawo kanka ba tare da fargabar komai ba? Da zaki buda zuciya babu abunda za ki gani sai kaunarki, son ki yasa na ke sha'awar barin addinina na dawo na ki, zan iya hakurin zama da ke a haka da soyayyar wani a ranki, da sannu zan koya miki so na har ki aminta....”

“Babu namijin da zai koya min so a yanzu, sai da safe.... ”

Ina fadar hakan na juyo na nufo gida ina jinsa yana kirana na kina amsa har na shigo gida.
Tun daga ranar babu ranar da bana bachi da bakinciki, sai a yanzu na gane cewar na yi kuskure a lokacin da babu hanyar gyara kuskuren.
Daga lokacin ban sake zuwa aiki ba, umarnin Abdallah ya hau kaina na cewar na bar aikin idan ba za su canja min tufafi ba, ban tafi na fada musu ba sai dai na san mawuyacin abu ne su yarda su canja min, balle kuma na jawa mai kamfanin fada da mahaukaci ko ya ma suka kare oho.
 
A ana gobe children day, Aminu ya sallamo min, ban fita ba hakan yasa ya nemi izinin shigowa cikin gidan ya shigo ya same a falo ina gyara tufafin su Aiman. Da sallama ya shigo na amsa masa kaina babu dankwalina ga gashin kaina ya sha tsiro kanana gwanin sha'awa.
  Tashi nai naje na dauko Hijabina na saka sannan na dawo na zauna.

“Yanzu Halima kin fi son rayuwar yaran nan ta tagayyara? Ba sa nan basa can? Haba Halima ko ba dan ni ba ko dan yara ai kamata ki duba...”

“Kamin ka sake ni ya kamata kai wannan tunanin ba a yanxu ba, a iya tunani baka shaye shaye Aminu sai neman mata miyasa kwakwalwarka take ta nuna maka cewar zan dawo gareka?”

“Shi ma Wallahi na daina, na riga na gane kuskurena Halima, kuma na yarda abunda ka aikatawa yar wani za a aikatawa, kuma zaka dandani dacin abunda ka aikatawa matar wani a gurin matarka”

“Shiyasa ka rabu da ita kenan? A lokacin ne ka gane cewar ina da matsayi a rayuwarka, shiyasa na dawo gareni, na jidadi idan har ka shiryu da gaske, domin har gobe kai ubansu Namra ne”

“Ban taba ganin mace mai hakuri da kawaici ba irinki Halimatu, wata mace bata taba so na kamar yadda kika so ni ba, ban gane hakan ba sai byan na rabu da ke, da farko arzikina ya fara karaya, sai aka fada min saboda na rabu da ke ne, arzikin yana tare da ke, amman kin san me? A yanzu na gane mutanen nan karya suke fada, ba saboda na rabu da ke na sara wasu abubuwan ba, saboda na ci amanarki ne kuma a maimakon na zauna da ke a haka sai na sake ki, na kuma kyale ki da hidimar yara, wanda hakkina ne, shiyasa Allah ya nuna min sakamakona tun a nan duniya”

“Hakan yana da kyau ko ba komai ai yasa ka shiryu, ina maka murna”

“Ba murna kadai nake son ki taya ni ba, ina son ki dubeni da idon rahama ki tausaya min dan Allah”

“Idan ma ka zo nn ne saboda ka fada min ka shiryu to ka yi kuskure, ka daina dogon mafarki a kaina, ni a yanzu na maka nesa, tun daga lokacin da na baro gidanka ban sake sha'awar zama da kai ba”

“Yaran mu hudu fa Halima, kin fison ki auri wani ki bar uban diyanki? Wa zai kula da su kamar yadda ke za ki yi?”

“Ka auro musu wata uwar mana, idan baka da wacce kake so ni zan iya nemo maka”

“Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un”

Ya fada yana dafe kansa, ni kuma na dauke kayan na fice daga falon na bar shi ciki. A ranar da zamu je gurin da ake bikin na ranar yara da duniya, na shiryawa yarana cikin kananan kaya sannan ni kuma na saka bakar abaya, tun takwas da rabi mu ka bar gidan gudun kar mu yi latti kuwa da kasancewar akwai mintuna talatin kamin a fara.
Ba a bar mu mun shiga ba sai da na nuna musu dan karamin katin hannuna, sannan suka bude mana kofa, wani irin katon filine mai kamar stadium an jera kujera sai kuma wata yar rumfa da akai daga sama wacce na kyautata zaton ta manyan bakine, ko da muka shiga har an fara gabartawa ana yi wa mutane maraba, a inda aka nuna min na zauna gurin na musamman inda yaran manya da iyayensu suke zama, tsabanin dayan bangaren da yake na talakawa irina, akwai taron mutane sosai ba Lalla ne ka iya ganewa kowa ba.
  Bayan na zauna na kalli wata macen yar sanda dake tsaye kusa da ni na tambaya gurin da ake aje takadar ta nuna min wani dan karamin daki da zan shiga, a gurin na bar su Namra na shiga ni kaina sai na samu wani kwando na gefe ta tarin wasiku a ciki, a gefen kusuwar kwandon na jefa wasikar sannan na fito. Bayan na dawo na zauna ina rabon ido na hango Ahmad zaune gaban teburin manyan baki, wani irin faduwa gabana yai sai nai kokarin kawardar fuskarta ima satar kallonsa, sanye yake da shadda ash color sai da hula kalar shaddarsa, idonsa kuma anye da bakin gilashi wanda ya kara masa kyau da kwarjini.
Fuskarnan a hade sai sham kamshi yake, yana kallon mutane one after the other. Sai a lokacin kunya ta kamani ya kamata naje nai masa godiya abunda yai min, ban je ba ban ma sake komawa kamfanin ba, ko ya suka kwashe da Kabir din ma oho, sai dai ina da tabbacin a ranar Kabir be gane ni bane saboda ina sanye da tufafin da ban taba sakawa ba, kuma gashi ana ruwa.
Duk wani abunda ake idonsa na kai, kamar yadda nawa ma yake kai, garin kalle kalle na na hango Abraham zaune a daya daga kujerun da aka tanadarwa yan kallo, muna hada ido ya dago min hannu yana min murmushi ni kuma nai saurin kawar da fuskata. Muna zaune a gurin har akai abubuwan da za ayi sannan aka fara gabatar da wasar numbobi jikin katin aka fara kira har aka kira number mu 17.
Fita muka yi tare da yarana muka shiga filin da aka tanadar mana, sai a lokacin na lura da cewa ba ni kadai ce uwa bahaushiya ba a gurin, akwai wasu uwayen hausawa biyu bayan ni.
An raba an sawa gida uku uku ne, wanda hakan yasa hankalin kowa ya dawo kanmu ciki kuwa har da Ahmad.
Da farko daukar kwai ne akan spoon daga gurin wani dogon tebur zuwa inda ko wace uwar take, yaranta za su dauko da gudu su kawo mata sai ta karba ta saka a gidansa, idan aka girga ko daya be fashe ba to ka ci wannan gasar, na biyu kuma debo ruwa ne murfi bottle zuwa inda anke har a cika wani karamin bokiti, na ukun kuma ko wane yaro sai saka safa a kafarsa ta dama sai yai tafiya da ta hagun har ya isa gurin mahaifiyarsa idan be taka kasa da safar ba su ma sun cinye.
A hudu kuma wanda shi ne na karshe za abawa ko wane yaro damar rubuta dalilinsa na son cin wasar da kuma wanda zai sadaukarwa.
Yara uku kawai suka bari na shiga da su duk kuwa da kasancewar dukansu Abraham ya siya musu tickets din, sai dai sun yi hakan duba da wanda za a hada ni da su, daga mai yara biyu sai uku. Sai da suka fara bawa ko wane yaro takardar da biro suka ware kowa dabam yai rubutunsa sannan suka karba,sannan aka soma wasan.
Ba zan yabi yarana kadai ba, domin a na ga wasu yaran da suma suka maida himma suna ta kokarin ganin sun ci kamar yadda nawa yaran ma suke har abun ya soma bani tsoro, na sani idan ban ci ba yarana ba za su ci dadi ba, kamar yadda nima ba zan jidadin ba ko dan kwallafa rai a kudin ba, akwai ciwo ace ka shiga gasa kuma baka ci ba.

Sai da muka fara karawa da mutane farko mu kai nasara a na biyun ma muka yi nasara haka a hana hudu har na karshe ma Allah ya ba mu nasara duk kuwa da kasancewar a lokacin jikinsu Namra da Adnan da Aiman yayi sanyi domin sun gaji sosai.
After mun gama aka saka muka koma saman muka tsaya tare da magabatarwa, sannan suka karbi account number kowa, a lokacin da muka shiga garsar mun fi mu ashirin da daya amman da aka gama mu shi kawai aka tsayar a gaban gurin.
Sai da aka fara karanta abunda yan ko wane team suka rubuta a takadar, idan an gama sai a fadi number team din sannan a fadi sunan wanda ya rubuta, sai kuma yan team din su daga hannu.
A lokacin da aka kawo gurin na mu, abunda Aiman ya rubuta shi Adnan ya rubuta haka ma Namra.

‘Momy ta mana alkawari idan mun ci zata biya maka kudin makaranta da su, kuma zata siya mana kayan wasa’

A gaskiya na ji kunya na ji kunya sosai a lokacin da aka karanta cewar wai idan na ci zan biya musu kudin makaranta, duk sai na ji kamar na muzanta, a gurin fadin abun wasan ne ya sha babban ita Namra ta ce teddy, Aiman yace keke, Adman kuma yace mashin din nan na yara. A gurin sadaukarwa kuma kowa yace idan ya ci zai sadaukarwa Momy wato ni kenan, ban da Namra wacce tace idan ta ci zata sadaukar wa kawarta wace ta rasu wato Baby Namra. Ba kadan abun ya taba min zuciya ba, wato har yanzu Namra bata manta da kawarta ba.
3rd position aka fara sanarwa, wato team 13, a take gurin ya garwaye da ihu ana ta taba musu a lokacin ne bugun gabana ya soma karuwa, ina cikin masu tabawa ammn hakan be hana ni tsorata ba, ni da sauran masu jiran sakamakonsu.
A na biyun ma an yi ihu, an taba musu wato team 6. Mai sanarwarwa wacce yar jarida ce a gidan redio sai da ta dauki lokaci tana jan rai har sai da tsoro ya kama duk wani wanda ke cikin wasan hakan tasa na runtse ido ina ta addu'a, Namra kuma ta rike min rike da duka karfinta ta rumtse ido.

“The winner is....... Is..... Is....... ”

Haka tai ta jan abun kamin ta fadi.

“Team 17........”

Wani irin mahaukacin tsalle Namra ta daka ta dire tana ihu tare ta rumgume Aiman suka fashe da kuka. ba ita kadai ba, ni kaina hawaye na ke abu ga mai shawaye kusa, Adnan ma rawa ya fara har su jujuyawa, kowa taba mana yake ciki har da Ahmad da ke kallonmu da Murmushi a fuskarsa.
Sauran ba su ci ba suka sauka daga stairs din sai muka rage team uku kawai, sam ban lura da mahaifiyar Ahmad ba har sai aka kirata ta bada award ga mutanen na uku, a lokacin ne nake jin suna kiranta da tsohuwar shugabar ma'aikata, a na biyun aka kira wani kwamishina ya ba su award.
A lokacin da aka zo gun mu sai aka gayyato Ahmad Muhammad Gwarzo, sai da ya fara ba ni cak din kudin sannan sannan ya gaisa da Adnan da Aiman, kana ya risina ya shafa kan Namra ya sumbanci goshinta.

“How are you my dear”

“I'm fine”

“Congratulations”

“Thank you Sir”

Ita ta mikawa Award din sannan ya tsaya aka dauke mu hoto kamar yadda akewa kowa. Idanuwa ba su sauka a gurin kowa ba sai Abraham wanda ke a tsaye yana taba mana tare da yin well done da hannunsa yana murmushi. Sai da aka gama komai sannan muka koma gurin mu muka zauna tare da sauran mutane na kusa da mu suna ta tayamu murya, kasa hakura nai har sai da na kira waya na sanar a gida sannan na maida hankali gurin shiri na gaba wato karanta wasikun uwa.
Duk wacce aka karanta wasikarta akan ce daga uwar wane da wane matar wace, sai ta taba mata mai gabatarwa ta yi maganganu akanta sannan a cigaba.






AHMAD POV.

Ba kasafai ya cika son irin wadanna taron ba, saboda dadewar da ake ga kuma tahaniyar mutane da speakers wandanda suke takura masa. Amman a haka ya daure tun da kusan shine babban bako a gurin kuma abunda aka saba yi a ko wace shekara ya zame masa dole a bana ma ya tsaya ayi da shi. Babu abunda ya burge shi kamar kalaman Namra na cewar idan ta ci zata sadaukarwa yarsa Baby Namra abunda be yi tunani ba, ko ba komai hakan da tai ya saka masa sonta kuma ya saka ransa yayi fes a taron, duk kuwa da kasancewar a farkon ganinsu be yi murna ba, babu abunda be ayyana aransa ba na ganin har da ita a gasar.

Yana kallon agogon hannunsa ake karanta wasiku wanda yake sa ran ba za a gama karantasu da shi ba, be natsu sosai ba har sai yaji mai gabatarwar tana maranta labarin wata kalar murdaddiyar rayuwa, wata kalar rayuwa ce mai wuyar fassarawa, mai wahalar gaske, ga tarin tausayi da taba zuciya duk wanda labarin ya samu masauki a kunnensa, ga shi kadai ba kusan duk wanda ke gurin sai da zuciyarsa ta sosu da labarin msu saurin kuka a take suka fara hawaye.

“Daga wata uwa mai kaunar yayanta.... ”

Mai gabatarwar ta karasa cikin muryar kuka tana daga takadar sama.

“Wace uwa ce wannan dan Allah? Wacece ita? Dan Allah ko wacece ke ina son ganinki ina son na ganki kawai, hakika ke jaruma ce jajirtacciya, kuma tsayayyiya mai karfi zuciya you deserve an award....”

Taja mashina sannan ta cigaba.

“and... Dan fashin da yake bibiyarki zai iya cutar da rayuwarki ki san da wannan, ni ko ba zan iya ba ki kariya ba na san jami'an tsaro za su ba ki, kuma In-Sha-Allah zan tsaya miki har ki samu salama, ba bayyana ki zan yi ba, ba nunawa kowa fuskarki zan yi ba balle har na fadi sunanki, taimakonki zan yi, and i promise you a cikin albashi na na wannan watan kina da 20,000 dan Allah

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login