Showing 147001 words to 150000 words out of 217237 words
ac wacce har ta fara saukar min da mura.
Wata yar karamar laptop direban ya miko min da pen sai wani littafi mai kamar diary, sannan dauko wata jaka wacce nake kyautata zaton ta Ahmad ce yai gaba ni da Ahmad din muka rufa masa baya, kana ganin kofar shiga dakin taron kasan taro ne na manyan mutane, domin an zuba securities a gurin gwanin sha'awa. Na yi zato ko sai mun yi musu wata magana ko nuna wani abun sannan su bar mu shiga ga mamaki ne sai kawai na ga an bude mana kofa, daf da zamu shiga cikin gurin Ahmad ya risuno saitin kunnena ya rada min.
“Ki kashe wayarki”
Yana fadar hakan yai gaba abunsa ya shiga cikin gurin, ya bar a bakin kofar tsaye da mamaki, to miye wani abun mamaki? Wata kila baya son aji muryarsa ne shiyasa yai haka. Umarninsa na bi na dauko wayar na kashe sannan na maida ta a jaka na shiga cikin gurin.
Ina shiga na fara rabon ido, babu mutane sosai amman kusan rabin taron duk turawa ne, wasu a taeburin manyan baki wasu a teburin masu daukar darasi irinmu, ga wani katon majigi da ke saman gurin wanda da shi suke ta nunawa mutane abubuwansu.
A zagayayyen tebur muka zauna ni da shi, sai dai kujerar tawa tana fuskantar tashi ne kamar yadda shi ma yake fuskanta ta, amman idonsa yana gurin abunda ake nunawa a majigin.
Nikam sam hankali baya gurin abunda ake fada yana gurin mutanen dake gurin ne, idan na kalli wannan na kalli wacan har na kallo Ahmad, da idon yai min alama da na maida hankalina gurin abunda ake, ba musu na tattara hankalina na maida gurin mutanen, muna zaune a gurin har kusan karfe daya. Direban dazun ne wanda ya kawo mu ya sake shigowa gurin ya nufo inda muke zaune ya kai bakinsa saitin kunnen Ahmad ya fada masa wani abu. A take na ga yanayinsa ya sauya, sai ya tashi tare da diraban suka fita, ni dai ina zaune a gurin har ya dawo a yanzu kuma baya kallon kowa sai ni, just me and me alone, har aka tashi daga taron 1,30pm bayan an bi ko wane tebur an dora takeaway da ruwa da lemu.
An yi mana hoto da turawan da kuma sauran wadanda suka zo taron, sannan mutane suka fara watsewa, nima na tashi ganin ogan ya tashi shi be dauki komai ba daga abunda aka kawo masa na sha da ci sai direbansa ne ya dauka ni kam na kai hannu na dauki abuna, ko ruwan ban bari ba, balle kuma yar karamar takadar da aka dora mana sama wacce nake kyautata zaton kudi ne. A kofar fitowa suke bawa mutane memo da magazine da kuma calender.
Sai da muka shiga motar sannan ya kalleni ya kalli kayan hannuna har na ji yar kunya.
“Ina wayarki?”
“Tana cikin jaka”
“Mu gani”
Ya zuro min farin hannunsa.
“Na kashe ta fa”
Ganin be janye hannun ba kuma be dauke idonsa daga kaina ba yasa na saka hannu a jakar na dauko wayar na mika masa, a zato na dubawa kawai zai yi ya bani sai na ga ya zura ta aljihu, kamar nai magana sai kuma wata zuciyar ta hana ni.
Ba mu yi nisa sosai da hotel din na ga direban ya faka motar gafe ya fita ya zaga bayan motar ya dauki abubuwan da ya dauko a gurin taron sannan ya rufe, Ahmad kuma ya fita daga motar ya shiga mazaunin direba yaja motar, ni kam ina zaune baya abuna sai dai sanyin ac yayi min yawa har na fara jin kamar ciwon kai na son kamani.
A nesa da masallacin gada biyu ya faka motarsa ya bude ya fita sannan ya zagayo inda nake ya bude min.
“Zanje nai sallah ki dawo gaba”
“Ban iya tukin mota ba”
“Ban ce ki tuka ba, a front seat zaki zauna”
Na fito na bar kayan a baya sannan na rufe motar na bude gidan gaba na zauna ina ta mamakin karbe min waya da yai, can kuma na tuna da abunda yai min jiya, wata kila dan kar ayi ta kirana ne muna tare kuma baya son hayaniyar kiran, amman ai sai ya bar min wayata yace kar na kunna.
Ni dai ina zaune a motar har aka sauko daga sallah juma'a mutane suna ta wuce, sannan ya bude motar ya shigo yai mata key muka hau titi, a hankali yake tukun kusan ko wace mota ta zo sai ta wuce mu, kusan da mu da masu tafiya kasa duk daya idan ma akwai tazara kadan ne.
“Kin na rasa yata ko?”
Na juyo na kalleshi sai na ga ba ni yake kallo ba, amman tabbas na san da ni yake domin daga ni sai shi ne a motar.
“Eh”
“Na rasa mahaifina ma, na rasa Matata mahaifiyar Baby”
Ya sake fada still be kalleni ba.
“Allah ya musu rahama”
Be amsa da amin ba, sai yai wata maganar ta dabam.
“You got lucky baki tana rasa kowa ba, the pain of losing someone is unforgettable, mahaifina na fara rasawa, mahaifina yana da ciwon suga, a lokacin da abun ya taso masa an fitar da shi waje, a cairo ya rasu a lokacin na shiga tashin hankali sosai, kin san saboda me?”
Na girgiza kai.
“Saboda Hajiyata, ya mace zata ji idan ta rasa mijinta? Ya da zai ji idan ya rasa mahaifinsa? Ya yar'uwa zata ji idan ta rasa mahaifinta? A lokacin nauyin Hajiya da Siyama da nawa ni kaina sai taro duk a kaina, tausayin kaina tausayin Hajiya tausayin Siyama, mu biyu kawai Allah ya bashi, daga ni sai Siyama, Hajiya tana son yayana sosai, sai dai duk haihuwarta yaranta rasuwa suke daga ni sai Siyama muka tsaya, shiyasa take son Siyama sosai wani lokacin tana kiranta da autarta, kamar yadda nima take so na sosai har take kishina, tana ganin kamar wata macen zata karbe mata ni, lokacin da muka rasa mahaifi komai na mu ya tsaya cak, ciki har da rayuwarmu domin mahaifinmu shine komai na mu, kullum Hajiya tana cikin damuwa Siyama ma haka”
Yayi shiru ya kai hannunsa ya dauki gorar ruwan da ke cikin motar ya bude ya kurba sannan ya aje.
“Daga lokacin na fara tunanin gina rayuwata, da ta mahaifiyata da kuma ta kanwata, a lokacin ne na fara neman aure har akai nasara na auri wata yarinya, she's my first wife but not my first love, domin na aureta ne ba wai dan na san miye soyayya ba a lokacin, a gida daban muka tare, daga lokacin da nai aure sai rayuwa ta ta canja daga matashi wanda yake zaune a gidan mahaifinsa zuwa mai mata da yake zaune a gidansa, na aje aikin da nake na soja a lokacin na cigaba da kula da kamfanin mahaifina na zinari, a cikin na bude makaranta wa Hajiyata duk wani abu na makaranta a hannun Hajiya yake zuwa, a da kullun tare da Hajiya muke karyawa komai kusan tare muke amman da nai aure sai abubuwa suka sauya, daga lokacin sai Hajiya ta fara ganin kamar matar da na aura tana kokarin mallake ni ne, sai ta cilasta min dole sai na dawo a cikin gidan mahaifina na kama part daya na zauna da ita, ita kuma tace ba zata zauna da Hajiya ba, daker na samu kanta ta amince muka zauna tare, sai kuma ta hanani cin abincinta tana cewa zata saka min magani a ciki, ta fara takura mata ta saka abubuwan da ya kamata ace mai aiki ce zatai, da ta kasa jurewa sai ta nemi fita Hajiya tace na sake ta, a haka nai aure har uku yana mutuwa saboda takurar Hajiya, ban zamu wacce ta dade ba sai mai sunanki, mace mai hakuri kamar ke, mai kawaici da sanin ya kamata, ita ta haifa min Baby Namra, a cikinta na biyu ne ta rasu, a ranar da ya rasu ni kaina bana iya gane kaina, domin rasa abokin rayuwa yana nufin rasa wani bangare na jikinka...”
Ya karasa muryarsa na rawa, hannuna na kai na dauki daya daga cikin tissue da ke cikin tissue ibox na mika masa sai ya karba.
“Thank you”
Ya tare gefen idonsa sannan ya sake kurba ruwan, ya bude gilashin motar iska ya shigo wata kila sanyin ac baya wadatar da shi.
“Sai ta bar ni da Baby, after that na sake aure biyu ya mutu, dayan saboda Hajiya dayan kuma saboda matar bata son Baby sai ta rika kishin yata tana ganin kamar ina nuna mata so da yawa ne, daga lokacin sai an gimgine maganar aure a gafe, na cigaba da rayuwata da yau da kullum, sai gashi na samu kaina cikin farinciki a haka muke rayuwa da kanwata da mahaifiyata da yata sai kuma sauran dangi na yan'uwa, amman dai a familyn mu mu kadai muka rage yayan Abbah, so the day I lost Baby, ba zan iya fada miki abunda naji ba, at first ban ji komai ba sai daga baya, kuma na kasa blaming kowa sai ke saboda a gurinta ta rasu, and she always talking about her friend i mean your daughter, tace na baki hakuri be kamata nai fada da mahaifiyar abokiyarta ba, so the day that i decided zan baki hakuri....”
A nan din m shiru yai sai hawaye ya gangaro ta gefen idonsa.
“Ina son yata sosai....”
Ya fada yana rumtse idonsa na wani lokaci kamin ya bude.
“Tana da sakewa, tana da kyauta duk da kasancewar ta karama, ga ta da wayo, ga son mutane bata da abokin shawara sai ni bata da abokin wasa daga ni sai Siyama wacce ta zame mata kamar kawa, sai kuma Hajiya wacce ta zame mata mahaifiya, Baby bata da kawa ko daya sai yarki da ta samu daga baya, that's why take yawan damun kanta kullum sai ta ganta.... ”
Ya lumshe idonsa yana sauke ajiyar zuciya da karfi.
“Abubuwa da yawa suna faruwa saboda ni, kai ma idan kana tare da ni wani abun zai iya samunka Dan Allah ka sauke ni a nan”
Na fada ina kawarda fuskata wasu hawaye masu zafi da radadi suna sauko min, a yau kan na manta da damuwata labarin Ahmad ya ban tausayi, domin rasa uba, ya, mata, abubuwa ne da basa fassaruwa da ko wane kalar yare. Murmushi yai ya miko min tissue da na bashi
“Take your tissue back”
Na karba na share hawayen, sannan ya miko min ruwa na karba na kurba sai na rike gorar, ina jin kamar wani hawayen zai sauko min.
“Can I imagine your life without your parents?”
Dam dam dam na ji gabana ya yanke ya fadi, kallonsa nai kamin na kalli gorar ruwan dake hannuna.
“Uba wani jigone na rayuwa, bayan Allah da manzosa, iyaye ne suke da muhalli na biyu a rayuwar ko wane dan'adam, daga lokacin da ka rasa uba za a fara kiranka maraya, saboda uba gangone na gingina, shi zai nemo ya kawo a ci, shi zai tufatar ya ciyar ya shayar ya ilmantar, uba wani jigone na rayuwa, gata ne, uwa kuma ita ce gaba daya rayuwar, idan babu uwa duk farincikin da zaka samu a duniyar nan ragaggene no matter what it's, uwa abokiyar tafiyar rayuwa ce, abokiyar shawara abokiyar kuka abokiyar dariya abokiyar farinciki abokiyar bakinciki, idan da yai kuka ka ji ba a rarrashe shi ba, to babu mahaifiyarsa a kusa ne, macen da zata dauki cikinka tun yana da second daya har yai wata tara ta haife ka ta jure kashi da fitsarinka ta rayu da kai a ciwo da ba ciwo, har ka mallaki hankalin kanka? Uwa ita ce gaba daya duniyar. No never... I can't imagine my life without one of them they are my super supporter's my everything”
Na karasa cikin kuka, ina jin wani irin shauki da kaunar iyayena ya kara kamami, iskar bakinsa ya busar ya jingina da kansa jikin kujerar motar yana kallona kamar bashi ba.
“Zan kai ki gida gurin Hajiya ki yi sallah”
Na share hawayena ina kallonsa.
“Mun tashi daga aikin ne?”
Na gyada min kai yana kokarin parking motar still idonsa na kaina.
“Idan haka ne ai kara na wuce gida kawai”
“No gurin Hajiya za ki yi sallah”
Bance masa komai ba sai na maida dubana gurin yan yatsun hannuna, ina jin faduwar gabana yana karuwa ga wani uban ciwon kai da ya saka ni a gaba, ban san miyasa yau Ahmad ya zame min wani dabam ba shi ba.
Key yai ma motar muka hau titi wannan karon ba mu yi tafiya mai nisa ba muka isa gidan, horn daya ya danna aka bude masa gate, ya kunna kai a cikin gidan, be yi farkin a ko'ina ba sai bakin kofar falonsu, fita yai shi kadai yace na jira shi a motar ya shiga cikin, be jima ba ya fito ya bude min motar yace na fito, haka na fito ina jin jikina ba kwari na shiga ciki, kamar dai wacan karon wannan karon ma Hajiyar da far'a ta tarbe mu sai dai yanayin yadda take kallon fuskata tana nuna alamar tausayi.
Bayan mun gaisa, tai ma Kanwarsa magana tace ta kai ni ciki nai sallah, da sauri yarinyar da aka kira da Siyama ta tashi tai min jagora har dakin Hajiyar, a bathroom dinta nai alwala ko da na fito an shimfida min carpet an dora Hijabi sama, sai kawai na dauka na saka na fara sallah azahar a lokacin uku ta kusa. Ina sallah shaidan ya fara yayo min tunani kala kala, kamin na gama sallah jikina har rawa yake, ina gamawa na cire hijabin na dauki veil din abayata na yafa na fito falon inda Hajiyar take na zauna, Ahmad ma yana zaune a falon ina son nai masa magana na kasa.
“Siyama kawo mata abincin”
Ya fada yana kallon yanayi gaba daya idona ya fito fuskata ta sauya.
“Wayata ina son magana da.... ”
Tun kan na karasa ya tari numfashina.
“Zan baki anjima”
Wannan karon kallonsa nai da kyau.
“Wa na rasa Ahmad? Uwa ko Uba, ko yaya? Ko kane? Fada min”
Mikewa tai tsaye yana kallona sai nima na mike tsaye. Can kasa kasa na jiyo Siyama na fadin.
“Ku fada mata gaskiya mana, dole ne ta sani”
“Siyama fita ki bar falon nan”
Ahmad ya fada mata a tsawace, kamar tana jira ta juya ta fice cikin fushi.
“Ka fada min wanda na rasa, ba zan iya dawo musu da rai ba, iyakar abunda zan yi hakuri ne”
“Muje na kai ki gida”
“Ka bani wayata”
Na daka matsa tsawa da wata irin murya daban taba sanin ina da ita ba, gaba daya jikina rawa yake.
“Ina da kanen, idan an rasa Uba sun zama marayu wa zai kula da su, idan na rasa Uwa wa zai maye musu gurbinta shikenan sun rasa gata”
Na fada ina rufe ido kamar mai nazari.
“Allah baya barin wani dan wani duk a can muka fito iyayenmu sun tafi sun bar mu, kuma a can zamu koma gaba daya”
Mahaifiyarsa ta fada idonta cike da hawaye, takawa na fara yi sai na ji kafar ta malgwade ina neman faduwa har sai da tai saurin rike ni, a hakan na sake unguri takawa kafafuwan suka fara rawa sai ta na tsaya cak, da nai unkuri na uku sai na tafi zan fadi har sai da Ahmad ya rike ni da kanshi ya zaunar akan kujerar.
“Ki natsu sai na kai ki gida”
“Ka kaini yanzu”
Na fada kai tsaye tare da mikewa tsaye na fara tafiya cikin karfin hali, ba shiri na ji numfashina yai sama wani hudu ya baibaye idona, jikina kuma yai arba da kasa.....
__________________________
Allah ka jikan mahaifina kai masa Rahama ka saka aljanna ta zama makomarsa, Mahaifiyata kuma ka karasa mata lafiya da kwanciyar hankali da natsuwa ka yafe mata kurakuranta kasa ta cika da imani 🙏 da duka sauran iyayenmu musulmai 😭🙏
Rashin iyaye wani ciwo ne da ba a manta shi 💔💔💔 may Allah see us though. 🙏
7/21/21, 10:47 PM - Buhainat: *GOBE NA...*
By Khadeeja Candy
4️⃣7️⃣
A yau kam kamar an halittoshi ne kawai domin kallon Halimatu, ya kasa zama kamar yadda a tsayin ma ya kasa yin nesa da ita sai daf da gadon da take kwance, fuskarta yake kallo, be taba tsaya ya kalleta kamar haka ba, daman can ahali shi ba mutum ne mai tsaya ya kwankwace mace ba.
Amman a yau yana jin kwanciyar hankali da natsuwa a kallon Halimatu, dogon hancin ya fara kurawa ido kamin idanuwansa su sauka akan karamin bakinta, fuskarta circir bata da rama kuma bata kumbura sosai ba ta cike abunta gwanin sha'awa, farin fuskarta dana jikinta har wani shining yake, ga jikinta Ma-sha-Allah irin wanda ake so a mata, tana da jiki sai dai ba can sosai ba, akwai kurciya sosai da yarinta a siffarta da surarta amman ba irin ta under 20 ba, irin wacce zaka kalleta kai zaton Amal ce yarta ta farko ba Adnan ba, babu abunda ta rasa a siffar ya mace sai na tsuwa da kwanciyar hankali.
Ta saman idonta yake hango damuwarta, labarin abunda ya same ta ta kuma yadda yake tunanin Gobenta zata kasance, be san miyasa yake tausayinta da yawa ba, yes be taba jin labarin daya taba masa zuciya ya hana hankalinsa kwanciya ba kamar nata, sai dai be taba tunanin hakan zai saka wani kusanci a tsakaninsu ba, the way da ya daukota ya kawo gurin Hajiyarsa, yadda yake ta kokarin boye mata mutuwar mahaifinta and ya bata tahirin rayuwarsa a free, ko da yake yayi hakan ne saboda kawai ya nuna mata ko da ta rasa ba ita kadai ce a cikin jarrabawa ba.
Kansa ya daga sama ya sauke numfashi a hankali, hannayensa duka biyu na zube cikin aljihu, can kuma ya sauke kan yana cigaba da kallonta, wani sinadarin tausayinsa ke fita daga cikinta yana shiga zuciyarsa, tausayinta ta cika zuciyarsa makil, a yadda take ya mace ace tana cikin irin wannan kalubalen na rayuwa ita din abar tausayi ce matuka.
Hannunsa ya saka aljihu ya fiddo wayarta, hakan nan kawai yaji yana sha'awar