Showing 30001 words to 33000 words out of 217237 words
kai kanki babu dadi balle irin wannan mai dalili. Tun da na fara aikin shekara hudu ban tana jin aiki ya gundure ni ba, ban taba jin na tsani aikina kamar yau ba, idan na kalli inda Kabir yake zaune sai na ji babu dadi ba ni kadai ba har Emanuel ya damu da hakan saboda yanayinsa da na gani, ban tana jin damuwa da lamarin Kabir kamar wannan karon ba, tausayinsa ya hanani sukuni kamin lokacin tashi aikina yai har na tsalwala.
Biyu da mintuna na tashi daga aiki daman wani lokacin nakan tashi haka wani lokacin har uku saura ko uku da wani abun. Tafiya nakecikin kamfanin ina tunanin abunda zai sake samu na, domin ina jin a jikina kamar kullum wani abun zai yi ta samuna ko wani na kusa da ni marar dadi.
7/20/21, 8:30 AM - Buhainat: *GOBE NA...*
_My Tomorrow_
By Khadeeja Candy
1️⃣2️⃣
“Hajiya barka da tashi ya kafafuwan?”
A natse yake mata magana kamar yadda ya saba, ita kuma ta dago ta kalleshi da kyau tana tauna ragowar goron da ke bakinta.
“Hassan kwana nawa rabon ka da gidan nan?”
Shiru be amsa mata ba. Hakan ya bata damar cigaba da yi masa fadan a zuciyarta kuma tausayinsa ne fal a ciki.
“Ana rayuwa haka? Ko wane bawa ai da kalar kaddararsa, amman sai ka rika saka kanka a damuwa ba kai ka dorawa kanka abun nan ba”
Kunya ce ta lullube shi, duk kuwa da ya san gaskiya Hajiya take fada masa and he know rashin lafiyarsa na daga cikin abunda ya fi ko wane daga masa hankali, tun abun baya damunsa yanzu har ya kai matsayin da idan aka auna jininsa za a iya cewa ya hau, babu inda be nemi magani ba a duniyar nan amman babu alamun sauki balle ma saukin, babu abunda be yi ba tun daga na hausa har zuwa na gargajiya amman shiru kamar an shuka dusa. Shi yanzu abun tsoro ma yake ba shi domin yana ayyana a ransa kuma yana jin kamar ba zai taba warkewa ba, burin da ko wane mai rai yake da shi na son yai aure shi kan na shi yana nesa da shi, tun ana kiran yaushe zai yi aure a family da friends har ta kai yanzu dai su tsarge shi suna kiransa da tazuru wasu kuma su ce masa mijin aljana wanda hakan ba karamin ciwo yake masa ba.
“Karka yanke kauna daga rahamar Hassan, daman ita rayuwar duniya tana cike da jarrabawa, kuma kowa da irin tasa, karka fasa neman magani kar kuma na ce ba zaka nemi aurenba, ka kwada neman auren kamar yadda kake a da, wata kila a dace wata kila kuma kamin lokacin auren yai sai Allah ya baka mafita”
Ya gyada mata.
“Zan cigaba Hajiya, duk dai ina jin kamar ni haka Allah yai ni”
“Babu wata cuta da bata da magani a duniyar, idan ka cire tsufa da mutuwa shine kawai basa da magani, a kullum ina cikin yi maka addu'a kuma In-Sha-Allah za a karba mana ko ma an karba, kowa da irin jarabarwarsa Hassan ga yar'uwarku nan aure ya mutu ai duk cikin jarabawa ne bayan ta fito kuma ciki ya zube wata kila ma kuma ta zubar da cikin ne ta huta da wahalar duniyar”
Kallon rashin fahimta yai Hajiya, idan tace yar'uwasa zai fara kawo sisters dinsa da suke daki daya kamin ya hango na wani gurin, a cikin familynsu ma sisters dinsa ma ai suna da yawa abunka da mai yawan yan'uwa.
“Wace Hajiya?”
“Halimatu...... ”
Haka ya ji sautin sunan sahibarsa kamar daga wata duniyar, Halimatuu... Ya maimaita cikin mamaki da bakinciki jin abunda ya faru.
“Taya? Garin ya?”
“Ai kasan abunda ya faru da Namra ko to shine sanadi yau kusan kwana uku ma da faruwar abun ko hudu kuma cikin da ta fito da shi ya zube har sai da akai mata wankin mara anjima na ke son zuwa na ganta”
“Innalillahi wa'inna ilaihirraji'u, ai kamar saki daya ne ya rage ko?”
“Saki daya ne kuma ya karasa kai wannan mutumen ba shi da imani sam ”
Wani irin na rashin jindadi ne ya ziuarci Abdulhamid, sai yaji kamar kanwarsa da suka fito ciki daya aka saka, a take ya fara ayyana irin yadda Halimatu zata ji halin da zata kasance duk kuwa da ya san dama can ya san ba dadin zaman auren take ji ba. Wanda yake yawan alakanta hakan da kansa domin yana ji a ransa da ace yadda yai soyayyarsa da Halimatu a boye da ya samu cikar burinsa da yanzu shi take aure da yanzu duka yaran na shi ne,ya dade yana fargabar zuwan wannan ranar yau ga ranar ta zo da ba zai iya yi mata komai ba.
_Bana da tabbacin wanda zan aura zai rike ni amana Abdulhamid, amman ina da tabbacin kai idan ka aure ba zaka wulakanta ni ba, bana jin idan ka aureni zaka iya rabuwa da ni har sai idan mutuwa ce ta dauke daya daga cikin mu_
Cikin kuka take masa maganar muryarta har rawa take.
_Ki yi hakuri Haima, ba zan iya cutar da ke ba, ba zan iya aurenki na zaunar da ke a gidana ba bayan na san bana iya yin komai da mace, idan nai hakan na cutar da ke kuma duk abunda zai biyo baya laifina ne ba na ki ba_
_Wallahi zan jira ka zan zauna da kai har zuwa lokacin da zaka samu lafiya, ko wane masoyi yana da burin yin wani abun na faranta rai na sadaukarwar ga masoyinsa, Abdulhamid ka ba ni dama dan Allah zan aureka a haka kuma zan jira har zuwa lokacin da zaka samu lafiya_
_No ba zaki gane abunda na ke nufi ba, ban tsammaci cewar zai kan wannan lokacin ban samu lafiya ba_
_Ka hanani bayyana soyayyarka, daman saboda ka san ba zaka aure ni ba ko? Yanzu kuma ka hanani aurenka_
_na hana ki bayyana soyayyata saboda na san wannan ranar zata so wata kila na samu sauko ko akasin haka, kin ga yanzu da ban samu sauki ba babu wanda ya san mun yi soyayya da ke, da ace na samu sauki kuma da yanzu ne zan bayyana soyayyata, ki fahimce ni mana Haima Wallahi ina kaunar ki amman ba zan iya hana ki auren lafiyayyen miji ni na aureki, ba kuma zan hana ki auren kowa ki jira ni ba domin ban san lokacin samun lafiyata ba, kuma iyayenki a yanzu ma sun damu su aurar da ke, Allah ya riga ya rubuto ba zan aureki ba...._
Duk wani magana da Hajiya ke yi be ji ko daya ba saboda ya lula a duniyar tunanin abunda ya faru tsakaninsa da tsohuwar soyayyiyarsa yana murza zoben da ta saka saka mata da kansa a wani lokaci can baya.
“Hassan....”
Da sauri ya dago ya kalli Hajiya domin ya ji kiran kamar daga wata duniyar.
“Na'am Hajiya?”
“Ba ka ji abunda na ce ba ne?”
“Na ji.... Na ji.. Na ce eh ba ki ji ba ne?”
“Saboda me?”
“Haka nan kawai”
“Haka nan kawai sai ka ki zuwa aiki? Abun ya fara taba har da aikinka ne?”
Sai a lokacin ya fahimci abunda Hajiya take magana akai domin a dazun amsa mata kawai yake ba tare da yaji abunda take fada ba. Mikewa yai tsaye yana murmushi.
“Zan je aiki mana Hajiya, ban fahimta ba ne sai yanzu”
“To Allah ya tsare yai muku albarka”
“Amin Hajiya sai na dawo”
Ya fito yana jin cewar a yanzu ne ya dace ya nemi magani ko dan Halimatu, idan ma bar warke ba zai aureta a hakan matukar a yanzun zata aminta domin yana jin cewar shi kadai mutumen da zai iya yarda ya aureta da yaya a yanzu kuma ya mantar da ita komai.
HALIMATU POV.
Wani abunda ya bani mamaki rashin samun abun hawa tun daga kan babura har napep duk wanda na tara ba ya tsayawa. Abun har mamaki ya bani na rika shafa kaina ina lalabawa wai ko basa ganin nane amman sai na jini a mutum kuma ai ina ganin mutane an kallona sai dai tsayawa su dauke ni ne basa yi. Tun ina tsaye ina taro har ta kai ga na fara takawa ina bin gefen titi, da na gaji da tafiyar sai na samu guri na hutu, na sake cigaba da tafiya sai yamma lis na isa gida ban taba jin gajiya irin ta yau ba damin ban taba shan wahalar tafiya kamar yau ba. Na tararda kowa da kowa na tsakar gida kamar yadda aka saba yin shimfida a harabar gidan a zauna ana ta fira da dare dare. Suna ta min sannu da zuwa ni dai ban bi ta kansu ba na wuce zuwa falon Mama sai na samu Abdallah a zaune yana game da wayarsa Namra na gefensa tare da Aiman da Adnan sun zagaye shi Amal kuma na saman cinyarsa tana kallon wayar, tsayawa nai ina kallonsa shi ma ya dago ya kalleni fuskarsa ba yabo ba fallasa.
“Sannu da tafiya”
Sannan ya mike tsaye yana gyara rigar shaddar da ke jikinsa.
“Kin ce na dawo miki da yaranki ko? To ga su nan sai ki saka su makarantar ai”
Yana fadar hakan ya raba gefena ya wuce ni kuma na bishi da kallon takaici da mamakin karfi hali irin nasa, yara dai nawa ne kuma na zabi na saka su da kaina to ina ruwansa, tun ba yau ba Abdallah na da son shiga rayuwata tun igiyoyin aure suna kaina ina yawan nuna masa bana so amman baya fasawa. Ba wai bana son ya saka su karantar ba ne canja musu makaranta abu ne mai kyau wanda ni ma nai tunanin hakan sai dai bana son yadda yake son shige min ne da yawa, har ga Allah bana jin zan iya karbar wani tayi daga gurin Abdallah na so, taya zan so mutunen da na kaunace dan'uwansa kamar na mutu, mutumen da be san darajar aure ba kuma mutumen da be taba martaba ni saboda ina da igiyar aure ba, mutumen da a kullum fatar mutuwar aure yake min.
Adnan na aika a shago ya siyo min suga da madara da biredi na hada tea mai sanyi na sha, domin yau ban saka komai a cikina ba sai ruwa, a lokacin da zan fita ban ci komai ba ga shi na ci tafiya a kafa kamar marar galihu. Na yi sa'a bana sallah hakan kuma ba karamin dadi yai min ba, domin yau ko ta kan Amal ban bi na hau kafita na fara sheka bachi kamar wacce ta shekara batai bachi ba.
Ban farka ba sai 11pm a lokacin wasu sisters nawa sun yi bachi su kan yara ba a maganarsu daman can abu ne mai wahala su wuce 10 ba su yu bachi ba ko lokacin da muke gida suna ganin game balle nan da babu. Wani irin ciwon kafafuwa ne ya taso min kamar wata tsohuwa da kaina na zauna ina matsa abu saboda azaba. Na yi minti talatin a haka sannan na tashi na shiga bandaki na tsaftace kaina na canja pad na fito na nufi dakin Mama.
Na same ta tana hamma kamar dai ni da bachin be wadatar da ni ba, kusa da ita na zauna ina amsa mata cewar lafiya kalau gajiya ce kawai ta saka ni bachi.
“Ya jikin abokin aikin na ki?”
“Jiki ba dadi Mama ance ma wai jini zai iya taba kansa ni abun ya bani tsoro sosai, amman matarsa sai ci min mutunci take”
“Akan me? Miye hadinki da matarsa?”
Na jera mata komai kamar a gabanta ya faru, sosa abun ya bata mata rai har take yabon matar da rashin kunya da kuma tunani, mun dan dauki lokaci muna tattaunawa maganar kamin na soma mata shimfida da zancen Sadi.
“Wai Halimatu ba zaki share maganar nan ba? Yanzu fa aurenki ne ya mutu kin dawo cikin kenanki kin zauna su ma muna fatar rabuwa da su ke kin dawo maimakon ki fara tunanin yadda Goben ki zata kasance ki samu mijin aure shine kike neman batawa yarki da kanki suna? Ke yanzu kina ganin wani ma idan ya ji kina da yara hudu zai aure ki ne? Ai ba kowa ke son mace mai yaya ba ma, sannan wani ko ya so ki ba zai yarda ke je masa da yaya ba”
Kallo mamaki nai mata.
“Mama yaushe aurena ya mutu ma balle har ace wani ya zo nemana? Kuma ni yanzu ai ban shirya ma aure ba”
“Baki shirya ma aure ba? Kika magana kamar ba yar musulmi ba? Ke yanzu ko dan ki bawa Aminu haushi ai kyayi aure da wuri, sannan ga kanenki nan suma neman rabuwa na ke su ke kuma kin dawo har ki fara tunanin zama? Halimatu kina da tunani kuwa?”
Babu juyin duniyar nan da ban yi ba dan na fahimtar da ita irin matsalar da na fuskanta a gidan Aminu wanda ya saka aure ya fita a raina amman ta kasa fahimta, idan na dauko zancen kotu kuma sai ta tare ta nuna min ba haka har na gaji na taso na baro mata dakin. As usual na farka raina babu dadi babu walwalah daman na saba tashi a haka tun ina gida Aminu balle kuma yanzu da abubuwan suka kara min yawa.
Kudina na saka na siyo ma yarana koko da kosai na basu suka sha suka koshi, na san ba za su iya jiran na gida ba domin sun saba da cin abinci da wuri, balle kuma abincin gida na taru ba ba lallai ayi musu yadda zai wadatar da su ba. Bayan na gama da su na aika aka siyo min madara da biredi na hada tea ina sha. Wayata da ke gefena ce tai kara alamar sako tun daga saman screen din wayar na karanta da sakon tare da sunan mallakin sakin.
“Good Morning.”
Dauke kai nai ganin Abdallah na dauka ma ko zai yi zuciya ya kyaleni ashe ba shi da zuciyar ma, ina jin lokacin da wayar ta koma ringing na ki kulawa saboda bana bukatar kallon mai kiran ba, abunda ban sani ba ashe kawata ce Hajara take kirana ba Abdallah ba, ankarowa da hakan yasa nai saurin picking.
“Hello Hajara”
“Na'am Halimatu ya gida ya aiki? Ko baki kusa da wayar ne?”
“Eh ina breakfast ne ya yaran?”
“Lafiya kalau ga ni kofar gidanku ki fito mu gaisa”
Mamaki ne ya kamani.
“Kofar gida kuma? Miyasa ba za ki shigo ba?”
“Ke dai ki fito kawai”
Mamaki ne ya kamani ba dan kankane ba, taya Hajara zata so har gidanmu bata shigo ba tace wai na fito mu gaisa?
Wata kila wata maganar ce mai muhimmanci ita ce amsar da zuciyata ta bani a take na bar cin abincin da na ke na dauka hijabina na saka Amal ta biyo bayan muka fita tare. A bakin kofar gidan mu na yi arba da motar Isma'il sai dai ban kawo komai a raina ba a zatona ko tana cikin motar ne, haka ne yasa na karasa ya buga kofar gilashin motarta. Saukar gilashin motar sai yai min almara mijin Hajara ne kadai a motar ba tare da ita ba, mamaki ya hanani cewa komai sai sakar masa ido yai, shi kuma yana ta faman zuba min murmushi kamar auduga, bude motar yai ya fito yana ta kara min murmushi da haurensa na makka fari.
“Hajara tace min na fito tana kofar gida”
“Eh haka ne, amman dai ya kamata mu kamin a dora da bayani ko”
“Ba da kai ba da ita”
Na maimaita masa saboda ya fahimta amman sai ya kara dilmiyar da ni.
“Da ni zaki gaisa ba da ita ba”
Ya fada Yan mikawa Amal hannu ta zo sai tai bayana ta boya kamar wacce bata san shi ba.
“Ina fatar kina lafiya”
Nauyi baki na yi na kasa ce masa komai har ya sake jefo min wata tambayar.
“Ya gida ya yaran?”
“Lafiya Kalau”
Na juya da sauri sai ya kira ni.
“Halimatu... ”
Har na yi kamar ba zan juyo ba sai kuma na juyo na kalleshi. Bude motarsa yai ya dauko wata ledar ya miko min.
“Ga wannan inji kawarki tace a gaishe ki”
“Ka maida maita ka fada mata bana son gaisuwarta kuma ka fada mata karta sake aiko ka a kofar gidanmu da sunan gaisuwa”
Dariya yai yana gyara tsayuwar agogon hannunsa.
“Halimatu kenan, ba zuwa Hajara ne kawai ba, ni kana na ga akwai bukatar na kawo gaisuwa kuma na jajanta miki akan abunda ya faru”
“Da alama baka fahimci da wane yare nake maka magana ba, amman idan ita idan ka isar mata zata fassara maka”
Ina fada masa hakan ta juya na koma cikin cike da mamakin karfin hali irin na Hajara, shi ma kansa Isma'il din mamaki ya bani domin na lura ba shi da kunya irin yadda na ke da Hajara ai ko ni na tallata masa kaina a tunani be kamata ya amsa min ba.
Bayan na koma cikin gidan na shirya, na fito da zimmar zuwa gurin aikina ba, abun mamaki sai na kasa samun abun hawa kamar dai wacan karon, ganin haka yasa na canja shawara daga zuwa gurin aiki na nufi Hauwa International School, wato makarantar su Namra kamar da wasa na tari wani mai napep ya tsaya hakan ba karamin dadi yai min ba ban ko tsaya fada masa inda zanje ba na shiga ciki da murna yadda kasa wance bata saba shiga Napep ba, ina cikin fada masa inda zai kai ni wayata tai ringing, sai da Hajara ta jera min kira hudu sannan na daga rai a bace.
“Minene?”
“Haba Halimatu ai ko dan ya kamata ki mutunta Mijina”
“Naga alamar ke da mijin na ki kamar ba ku da hankali Hajara, na gargade shi ke ma kuma na gargade ki karki sake yi min wannan wasa”
“Ni dai van kora dan wani gargadin ki ba, na kira ne kawai na fada miki ban fada masa abunda ya fito dake daga gidan mijinki ba, kuma ban fada masa abunda ya samu Namra ba, kuma ni mijina ba zuwa yai ya fada miki cewar yana son ki ba, cewa ina son ki abu ne mai tsada a gurin mijina ya fara gadaki ne ya ga ruwanki...”
Ta karasa tana dariya sannan ta kashe wayar ba tare da jiran irin amsar