Showing 198001 words to 201000 words out of 217237 words
da dora hannunsa saman cinyata.
“A a bana son sani”
Sai yai murmushi ya sauka saman gadon ya dauki takalminsa da hannunsa na hagu ya kashe kumamun dake ta yawo a cikin dakin sannan ya dawo ya zauna a inda nake yana kokarin kai hannunsa kirjina aka tana kofar da sauri na dauki mayafina na rufe kaina shi kuma ya dauke hannunsa daga jikina.
Yunus ne ya shigo rike da ledodi a hannunsa, after sun gaisa da Ahmad ya gaisa da ni sai kuma ya soma zolayata.
“Amarya ashe ashe ba mu sani ba....”
Wani kallo Ahmad yai min hakan yasa ban biyewa wasan da yake min ba.
“Yunus ka fa san ni bana son wasa da iyalina please take note”
The way da yai masa maganar babu wasa ko kadan a tare da shi, sai dai hakan be hana Yunus din yin dariya ba.
“Daman na zo ne na dauke ta ayi mata hoto Hajiya tace a shirya mata komai da ita za a je”
“Ban gane ka dauke ta ayi mata hoto ba? Ta dai baka hotonka karami ko?”
“Ba shi kadai ba ka san za a mata passport”
“Okay kuma kai zaka kaita ayi mata”
“Alhaji bana da matsala idan kai zaka shige gaba ayi mata komai, yanzu dai ya jikin naka?”
“Al-hamdulillah zan mata komai”
Ya fada yana kallona. Sun dan dade suna fira kamin yai mana sallama ya tafi. A lokacin ne na zuba mana abincin a plate daya ni da shi, be wani ci sosai ba hakan yasa nima na ji ba zan iya ci ba, ya bukaci na hada masa tea.
“Shiyasa ka rame baka cin abinci”
“Sai na samu lafiya zan ci abinci na koshi na more”
“Ba gashi na zuba maka yanzu ba ka ci ba”
“Ba wannan abincin ba, wacan abincin wanda aka dade ba a hadu ba, kuma na yi marmari da yawa”
Murmushi nai ba tare da na kalleshi ba na cigaba da hada masa tea, da na kawo masa masa be karba ba sai yace na bashi da kaina, haka na rika ba shi tea kamar wani karamin yaro.
“Sha mana”
Na kurba kadan na bashi ya sha, bayan ya gama mukai sallah isha'i. Ban tashi daga saman carpet din ba sai ga Hajiyarsa ta shigo tana tambayar ko akwai abunda muke bukata.
“Sai dai ko shi ni ai gidan zan tafi”
“A a nan za ki kwana, wannan kuka da kuka min dazun idan kika je gida ai sai ki yi mafarkin kukan kuma”
Ta fada tana murmushi ni kuma nai kasa da kaina kunya ta rufe ni, Ahmad kan dariya yasa kamar ba shi ba.
“Ashe dai ana so na”
Kasakasa na wasa masa harara. Sai Hajiya tai murmushi.
“Allah dai yai muku albarka kuma ya ba ka lafiya ka koma gida cikin iyalinka”
Daga ni har shi muka amsa da amin, sannan tai mana sallama ta fice. Duk yadda na so ya kwanta saman gadon ni na kwanta kasa sai yaki, ala dole sai dai mu kwanta saman gadon a tare ko kuma shi ya sauko kasa mu kwanta.
“Gadon ai ba zai dauke mu ba”
“Ai ba dole sai mun wadata ba, ko kuma mu kwanta kasa”
“Ya za'ayi kana rashin lafiya ka dawo kasa ka kwanta?”
“Kin san dai ba zai yiyu mu kwana daki daya kuma a daban daban ma wannan ai haramun ne ma”
“Inji wa?”
“Inji ni”
Ya nuna kansa, ban san lokacin da na saka dariya ba. A dolen dole muka kwanta kasa ni da shi, muka lulluba da Bedsheet daya yadda ya rumgume ni a jikinsa yana shafa ni kai ka rantse da Allah ba ciwo yake ba.
Da asuba sai da na dumama masa ruwa yai wanka ni kuma na shiga nai alwala ko da ya fito na gama sallah na gaishe shi na shimfida masa carpet din yai sallah bayan ya gama na karanta masa fatihar ya sha sannan na hada masa tea.
Misalin bakwai da wani abu direbansu ya kawo mana breakfast ba laifi nan ma da na zuba mana ya ci wata kila saboda mun ci tare ne ko kuma dan na yi magane jiya yasa yau ya ci oho. Sai tara da wani abu mahaifiyarsa ta shigo, ni kuma na fita na basu waje. Ina tafiya wayata tai kara alamar shigowar sako, number Abdallah ce.
“Ina fatar mijin da kika aura ya rike ki amana Halima, i wish you all the best
....”
Shine abunda ke rubuce a cikin sakon, ban miya sa ba sai duk na ji wani iri. Har na koma dakin jikina a sanyaye yake.
“Na yi magana da Hajiya akan ko a daga tafiyar nan har gaba sai ce ba zai yiyu ba, amman dai ta aminta za a saka da addu'a din”
Ban ce masa komai ba na hau saman gadon na zauna na dora kaina sama wuyansa.
“Babe are you okay?”
Na kalleshi.
“I'm fine, Allah ya baka ikon rike ni amana”
“Amin”
Ya sumbaci goshina.
“Ba zako taba kuka da ni ba In-Sha-Allah i love you so so so much”
Ya fada try to hug me with both hands.
“Baka jin ciwo ne?”
“Da sauki dai gaskiya”
Murmushi nai na rumgume shi. Ban dauka da gaske yake ba har sai da muka je tare da shi aka min komai na tafiyarmu a yadda nake ganinsa na jidadi domin baya nuna alamar ciwon ko da akwai ma yana boye min, domin ya fada min duk bayan awa uku sai hannun ya taso masa da ciwo amman yanzu kam Al-hamdulillah.
Tare da shi da direban da ke jan mu ya sauke ni kofar gida, sannan shi kuma ya wuce. Da na shiga gida sai Hafiza ta rika zolayata kamar ba kanwata ba iskanci kala kala ko kunyar Mama da Inna bata ji, ko da yake daman can Hafiza ba wata doguwar kunya ce da ita ba. After na yi wanka na canja tufafin jikina ina gyarawa su Amal kayansu Inna ta shigo tana tambayar wai da gaske ne taji a gurin mama cewar da ni za a tafi.
“A a aiko hakan yayi Allah ya bashi lafiya”
“Amin”
“Inna”
“Na'am”
Har ta juya na kirata ta juyo.
“Dan zauna dan Allah”
Ba musu ta zauna saman katifar da muke bachi, a nan labarta mata abunda nake zargi a ciwon Ahmad da kuma a abunda ya faru tsakanina da Abdallah a maimakon ta yaba min sai ta rufe ni da fada.
“Sakaryar banza sha sha ba, marar tunani, komai Abdallah yai miki kar karki manta dan'uwanki ne kuma saboda yana son ki yai, ai ko a munafurce mutum ya nuna maka kauna ya fi wanda ya fito kirkiri yace baya son ka”
“Amman Inna shine fa yai masa wannan kofin”
“Idan shi din ne ai sai ki bishi da lalama ba da hauka ba, Abdallah ya gama miki komai a rayuwarki Halimatu be cancanta ki saka masa da wannan ba, ke dai kan baki da tunani sam sakarya kawai”
A fusace ta fice ta bar dakin ni kuma sai duk na ji babu dadi, na rasa abunda zan yi na ji sanyi a raina na rasa tunanin da zai nuna min na yi daidai ko akasin hakan.
ABDALLAH POV.
Tun da Hajiya tai furucin nan sai ya ji kamar an zare masa rai a cikin jiki, har lokacin kuma ya kasa ganin laifin Halima, iya abunda yake tunani Ahmad ya kira mata abubuwa ne akansa ita kuma ta yarda shiyasa ta zo har cikin gidan Hajiya tai masa kalamai marasa dadi.
Sai dai daga lokacin da Hajiya tai masa furucin cewar ko bayan ranka ya auri Halima bata yafe masa ma ya cire zancen aurenta ya aje a gafe, hakan kuma ba zai saka kaunarta ta goge a zuciyarsa ba, sai dai yana da yakinin idan ba Halima ya aura ba ba zai taba samun cikar burinsa ba na haihuwar da namiji, a iya kwallafa rai ya kallafa mata rai da zato da kuma tunanin idan ya aureta burinsa zai cika na haihuwa da namiji kuma zai samu damar kusanci da abar son sa.
“Yanzu na gane ba laifinta ba ne, har da naka kana da son ka Abdallah taya zaka runtse ido ka tsaya kai da fata akan cewar sai ka aureta? Matar da dan'uwanka ya saka? Kuma dan'uwan naka ma twins brother dinka? Kuma yana raye? Bayan kasan bana son yarinyar nan, hakika na tsorota da lamarinka, idan har zaka ita cutar da dan'uwanka to ni ma zaka iya cutar da ni”
“Subhanallahi Hajiya wace irin magana ce wannan? Abdulhamid shi ya fara cutar da ni, domin yayi min kofin ba zan taba haihuwar da namiji ba, kuma Hajiya kin san yadda nake son namiji, yana daya daga cikin dalilin da yasa nake son na auri Halima”
“Kum illata kanku kun cutar da kanku, amman kai kafi cutar da dan'uwanka, ko da baka haifi namiji ba ai kai ka yi auren har ka haihuwa? Shi fa? Dubi inda ya kare yanzu da yana ko ya ce da ban kalli yar na ji sanyi ba? Amman damuwarsa bata dame ba ka, kai neman da namiji kawai kake? Babu ruwanka da matsalarsa, kana kallon yadda yake ta fafutukar neman magani amman baka taba tausaya masa ba Allah ya wadaranka Abdallah, ka so matar aure, kuma matar dan'uwanka saboda selfishness reasons, Halima ce kawai mata a duniya? No saboda ka musguna ma dan'uwanka ne kuma kana ganin idan ka aure ta zata iya haifa maka namiji tun da last child dinta mace ce kuma tana haihuwar maza da mata ne, Wallahi karya kake kai baka isa kai abunda Allah be yi ba, komai kofin ka ba zaka iya yi wa kowa abunda Allah be masa ba, ashe ba laifin Halima ne kawai ba har da kai, ta yi tunani a lokacin da ki aurenka ta auri dan'uwanka ko ni ce haka zan aikata domin kai abun tsoro na, ka maida kanka wani kalar mutum dukanku kun zamar min wasu iri”
Ta karasa tana fashewa da kuka, sai yai sauri sauka daga saman kujerar da yake zaune ya matsa kusa da ita ya kama hannayenta yana hawaye.
“Hajiya dan Allah ki yi hakuri, Wallahi na bar zancen Halima har abada, kuma In-Sha-Allah zan nemi maganin kofin zan karya shi, dan Allah karki kuka saboda ni”
Kawarda fuskarta tai tana share hawayenta.
“Da bakincikinka zan ji ko da na dan'uwanka? Tun jiya na kasa bachi saboda abunda na ji, na rasa wane kai din wane iri ne?”
“Zan canja Hajiya i promise you this”
Ya fada yana kokarin kwantar mata da hankali.
7/22/21, 9:15 PM - Buhainat: *GOBE NA...*
By Khadeeja Candy
6️⃣1️⃣
Ta waya nake labartawa Hajara abubuwan da suka faru, ba laifi ita kam yaba min tai akan abunda nai wa Abdallah.
“Daman can ni dai hankalina be kwanta da wannan mutumen ba, kuma taya zaki auri yaya ki auri kane dukansu suna raye, yanzu wannan abun da kika yi har Mahaifiyarsa ta kara shiga tsakani ai dole ya kyale ki ki samu kwanciyar hankali, ko ba komai kuma ta ji abunda Abdallah yai ma dan'uwansa ko dan haka ai dole ta daina kin ki”
Na tabe baki kamar tana gabana na ce.
“Haka dai kike gani, amman a iya tunanina abu ne mai wahala Hajiya ta iya so na, kiyayya ta riga ta shiga”
“To can ta matse musu mu ai ba mu da case da su a yanzu, za mu je mu ci amarcin ma a waje ma ba a kasar nan ba”
Ta fada tana keto wata shegiyar dariyar jindadi.
“Wani irin amarci kuma Hajara? Jinya dai ko?”
“Ke kar ki maida ni yar iska mana, idan kun je jinyar sai ya saka miki ido yana hadiyar yawu? Mazan yanzu? Ko kana gidanku ma ya ka kare balle ana tare? Make sure dai kim gyara kamin ku tafi”
“Jinya fa zamu je hajara, kuma gobe zamu wuce ina wani zancen gyara”
“Ko yanzu dai lokaci be kure ba, ai ba dole sai kin yi wani shegen shaye-shaye nan ba, bari Abban Afrah ya dawo idan ya amince min zan je gurin Hajiya Bilki na karbo miki wani set da take badawa na amare, sha daya ake amman aikin shekara yake, kuma idan kika sha baki bukatar kara shan komai da sunan gyara, kuma ba wani da yawa bane ba sai kin wahala ba, amman fa ki shiryawa aiki dan ni kaina wallahi sai da na ci kwakwa balle kuma ke da kika kwana biyu ba a hadu ba”
Daga ni har ita dariya muka saka, daman can Hajara ta san irin wadannan abubuwan shiyasa kullum gidanta baya rabo da su har mamaki take a lokacin da ina auren Aminu amman bana sha kamar ita.
“Amman fa gaskiya kusan 32k take bada shi, kuma kudin da ke hannuna ba zai wuce 14k ba idan ma yayi, kin ga bikin nan naki ma ya fado min gaf amman dai kamin a tare na san na shirya In-Sha-Allah kuma na san ba zata yarda ta bada shi a akan bashi ba domim bata da yarda sam duk sabonka da ita”
“Karki damu turo min account dinki zan miki transfer yanzu”
“Shegiya amarya ki ce har kin ji dala? Ehhen”
Dariya nai na watsa da carbin da ke hannuna.
“Ba na shi ba ne, wannan kudin ya dade ban baki komai ma a ciki ba kin ga sai na hada na turo miki”
“A a lalai ba ni da case matar Amadu ki ce abun akas yake... ”
Sai da tai ta wasa da zolayarta ta da saba sannan mukai sallama ta turo min account din na tura mata kudin da kuma dan ihisanin da nai iyar yi mata. Sannan na aje wayar na janyo akwatina ina hada kayan da nake son zuwa da su, sai da na gama sannan na tashi na shiga na yi wanka na saka atamfa na shafa yar hoda kadan na saka hijabi na nufo dakin Mama.
Fada na samu tana yi ma Aisha sai na samu guri na zauna har ta gama sannan na ce.
“Mama zan koma asibitin”
“To jikin na shi dai da sauki ko?”
“Gaskiya da sauki sosai, domin ya daina jin zugin tun jiya, yanzu nauyi ne kawai yake masa, tafiyar ma dan mahaifiyarsa ta ki yarda ne shiyasa da an fasa”
“Ai kara a aje din ko ba komai hankalinta zai kwanta, za ta fi samun natsuwa, Allah ya kara masa lafiya”
“Amin Mama kin kara yarda aikin Abdallah ne ko?”
“To akanki Halima waya isa ya taba dan gidan Hajiya?”
Da karashe da murmushi ni kuma nai dariya ina mikewa tsaye, sai da nai mata sallama na shiga nai ma Inna sannan na fita, direban da ya dawo da ni dazun dan nai wanka ne na samu a waje.
“Ah daman baka wuce ba?”
“Cewa yai na jiraki har ko yaushe ne na dawo da ke”
Murmushi nai na bude mazaunin baya na shiga na zauna ina tuna gargadinsa na dazun cewar na rika saka niqab. Muna isa cikin asibitin na kiran sallah azahar, ko da na shiga dakinsa na samu Siyama zaune saman kujera rike da wayarta sanye da rigar likitoci.
“Matar Yaya sannu da zuwa”
Na amsa ina murmushi.
“Yauwa sannu kanwar yaya ya kike?”
“Ba kalau ba tun dazun nake jiran driver ya kai ni gida wai sai ya dawo da ke sannan za akai ni Hajiya Siyama guda gida”
Ta fada tana hararar bandakin, daga can cikin bathroom din ya amsa mata da.
“Ba a dauko Hajiya matar Alhaji ba ke Hajiya kanwar Alhaji sai a dauko ki? Waya ce ki bari saurayin na ki ya barki, ko wani ya hanaki fitowa da motarki?”
Ta matsa kusa da ni tana min rada.
“Haka fa yake idan ya samu lafiya ba ma zaman lafiya ni da shi...”
Nikam kasa cewa komai nai sai dariya nake.
“Lims gulma ta take ko?”
“A a”
Ina amsa masa ya fito daga bandakin fuskarsa na ta haske irin ta sabon ango. A take ta dauki jakarta ta mike tsaye tana fadin.
“Ni dai na tafi Allah ya bada sauki”
Na amsa da amin ina binta da kallo shi kuma ya kabbatar sallah, hakan na bani damar tashi na shiga bandakin nai alwala na fito na jirashi har ya gama sannan na gabatar da tawa. Da kansa ya zuba mana abincin a plate daya spoon ma daya ya saka ya dora abincin gafena nikan sai kallonsa nake domin na lura tun jiya yana kokarin aikin da hannun.
“Hannun ba ya maka nauyi sosai ne?”
“Ba sosai yake min ba ina sai jin kamar jijiya ta rike ne”
Ya debo abincin da kansa ya kai mu a baki sannan shi ma ya ci. Shi yai feeding dina har na koshi sannan na karbi plate din na aje, sai kuma yaja ni jikinsa ya rumgume.
“Mata da miji idan suna zaune ba a zama nesa da juna ki koyi wannan yana kara soyayyar da shakuwa ko wani gurin muka je za mu rika tunani da kewar junanmu”
Yana gama fadar hakan ya saka hannunsa cikin hijabina yana kokarin kaiwa kirjina.
“Ba bari muji da akai wanka sun wanku”
Ya fada cikin rada sai nai saurin raba jikina da nashi.
“Baka da lafiya amman sai rashin ji kake....”
“Ahen ahen ahen please nahhhh”
Yayi maganar ta sigar shagwaba kamar wani dan 3 years sai marairaice min yake yana tabe baki irin yadda yara suke idan suna son abu. Nikam abun dariya ma ya bani wannan kuma ai ya zama ba jinya ba, duk yadda nai kokarin nisa da shi sai ya ce min ba haka ba. Sai da mutane suka fara shigowa sannan ya shafa min lafiya.
A yau kam na ga yan'uwan Ahmad sosai a asibitin wata kila saboda gobe zai bar kasar ne yasa suke ta zuwa kamar ana turowa idan wannan ya fita wata ko wani ne zai shigo, duk basa shigowa hannu sake masu kawo abinci ko siyayya wasu kuma idan za su fita sai su ba ni kudi, mun gaisa da wasu da yawa daga cikinsu ya gabatar da mu kuma ya gabatar ni a gurinsa kowa sa cewa yake sun ji abu daga sama wai ba sanarwa.
“Amaryar ce sai da haka shiyasa, sai da dabara”
“Ato ko dai kwace kai wa wani ne?”
Cewar wata tabashiyarsa tana dariya.
“To wannan tsaleliyar matar zan samu a banza, ai kinsan sai na yi da gaske, duk masu neman wasa suka tsaya ni kuma nai muku na shirwa”
Duk suka saka dariya har ni. Bayan sallah magariba na fara shirye shirye zuwa gida