Showing 111001 words to 114000 words out of 217237 words
Khadeeja Candy
3️⃣6️⃣
Na kasa jefarda takardar kuma na kasa fadawa kowa cewar ya bani takardar kamar yadda na kasa fadawa yan sanda. Shi kuma be fasa chusa kansa a cikina ba, har kara ma da bibiyata kawai yake amman a yanzu har yarana yake yi ma siyayya ta kudi mai yawa ya kai musu a scul a gida kuma ya aiko min da ita, a kullum ina fargabar idan Mama ta tambayi wanene shi wa zan fada mata ba? Bayan karyar da nai mata cewar wani ne dana hadu da shi yake min haka yai ma su Namra, amman idan aka samu akasi yarana ko kuma Mama da kanta ta ganshi fa? Duk wanda ya gan ni da kafiri zai yi mamaki abunda ya hada ni da shi ina diyar musulmai.
Sai dai a yadda na fahimta kamar shima yana gudun mutane domin baya min magana a inda yakr ganin jama'a da yawa, sai idan ina a kebance kamar idan zan hau napep ko na sauka ko zanje wani gurin sai kuma da dare zai aika yace ana min sallama. Duk kuwa da ban tana fitowa da sunan amsa sallamar da yake min ba, hakan be hana shi aiko min lokaci zuwa lokaci ba, kamar yadda yake yawan bibiyata yana rokon na saurareshi.
Ni kuma na kasa saurarensa saboda bana jin aminci a tare da shi wata kila saboda ba addinin mu daya da shi ba oho, sai dai a yadda na lura yana da kamun kai da taka tsantsan da kuma natsuwa wacce ba ko a musulman mu ba kowa kake samu da wannan ba.
Ba ni da wata fargaba a yanzu sai ta abubuwa uku,wannan Abraham din sai kuma Aminu wanda shi ma ya saka ni a gaba da yawan bugo min waya da sunan zai gaisa da yayansa tun yana kira ina dagawa na bawa yaransa har ta kai yanzu idan ma ya kirani sai dai na mika musu wayar su su yi magana da shi, hakan kuma be hana idan ya kare magana da su yace su ba ni wayar idan ni kadai ce ko kuma da kanen sai na yanke kiran idan a gaban Mama ne kuma na kan dauka saboda ta gargade ni cewar na daina kin karbar wayarsa ko dan darajar yarana, ina yi mamata biyaya ne kawai saboda ina gudun bacin ranta gudun kar tace ban dauki shawararta ba, amman har ga Allah bana kaunar jin sunan Aminu ma balle jin muryarsa, shi kuma yanzu har wani zillon rashin kunya yake domin wani sa'in har cikin gida yake shigowa ya gaishe da Mama da Baba sannan ya fita, ga wata bakar al'ada da ya tsiro ta daukar yaran yana tafiya da su gidansa ko wani gurin daban su wuni can sai dare zai kawo su gida. Idan na nuna zan hana sai Mama tace min ba haka ba. Wani lokacin sai dai nai ta jin haushin a zuciyata kawai amman ban isa na nuna a fili ba saboda kar mama tace saboda ita nake yi.
Na tattara komai a yanzu na aje a gafe, babu da bukakata da damuwa kamar abu na ukun nan wato neman aiki, duk inda naji wata ma'aikata ko wani kamfani sai na mika takarduna, sannan na saka addu'a a gaba nai ta yi ko Allah zai saka a dace.!
Bayan na gama sallah isha'i ina rike da wayata ina latse latsena kamshin turaren Abdallah yai min sallama kamin muryarsa ta daki dodon kunnena, a take na nemi natsuwata na rasa sai na ji duk na kwadaitu da son ganinsa fuskarsa a take na aje wayar na unkura ina gyara Hijab dina na mike tsaye ina juyowa sai nai arba da mutum, faduwar gaba ta same ni a lokacin wacce take yayin yin haka a duk lokacin da nai arba da Abdallah, abun ka da wacce ta rude sai na kasa komawa na zauna daman dakin babu kowa sai ni kadai da aljanuna idan ma ina da su, ratsawa nai gefensa na da zimmar na fita domin a bakin kofar yake tsaye ya zuba min idonsa kamar ya cinye ni, ban san yadda akai ba na kasa lura da kyau har na buga kaina da garun kofar a take goshina ya fara zogi ni kuma na saka hannu ina murzawa jikina na ta rawa kamar marar gaskiya, har lokacin be dauke idonsa daga kaina ba kuma be kauce daga kofar ba. A dole na koma na zauna saman kujerar da ke kusa da inda nai sallah, amman me sai na gagara samun natsuwa domin jikina na bani cewar idonsa na kaina. Sai da ya ji muryar Inna ta doso dakin tana masa lale marhabun sannan ya karaso cikin dakin ya zauna a saman carpet din da na tashi wanda nai sallah, idonsa ya koma gurin kafafauwa ya sakar musu ido kamar mai son tantance abu, ni kau na daga abuna sama na dora saman kujera na lullube su da hijab, sai kallon ya koma gurin hannayena, su ma na nade abu cikin hijab din sannan ya kalli Inna wacce ta shigo ta zauna.
“Abdallah yaushe rabonka da gidan nan”
“Bana samun zama ne sosai yanzu shiyasa aikin yana min yawa, ya gida ya kwana biyu?”
“Lafiya kalau ya gurin su Hajiya?”
“Tana lafiya tana gaishe ku”
“Muna amsawa mun kwana biyu ba muje ba itama bata zo ba, ina Suwaiba da su Inteesar?”
“Duka suna lafiya, na ga Baba a waje ai mun gaisa ina Mama?”
“Ta dan zagaya makota jikin ne idan yai mata nauyi sai ta zagaya saboda asibiti ma ance ta rika dan takawa tana shiga mutane”
“Allah sarki gidan yau ku ne akwai a ciki? Duk ina yan matan Baba?”
“Wallahi duk sun tafi wankin Amaryar da ake nan makota, kawarsu ce take aure kuma ta zama kamar yar gidan nan har yaran duk suna can shiyasa ka ga gidan babu kowa”
“Okay”
Ya amsa yana maida dubansa gurin wayata wacce ke kusa da shi, kamar na kai hannu na dauka sai ganin nai ya dauki wayar yana ta shafa screen din domin tana da password ba zai iya bude ta ba, ganin shiru yayi yawa yasa Inna ta tashi ta bar mana dakin daga ni sai shi sai fankar sama da ke ta aiki ba mu iska kasancewar akwai nepa.
“Zan nemawa su Namra transfer zuwa government schools”
Ya fada ba tare da ya kalleni ba, kamar yasan zan tambayi dalili sai ya ce.
“Saboda na san ba za ki iya cigaba da biya musu school fees a wannan private school ba”
Har ga Allah na ji babu dadi amman ban nuna masa ba, domin ban san dalilinsa na yin hakan ba, wata kila ya gaji da taimakon da yake ba ni ne a yanzu ganin kamar ba zan taba aurensa ba.
“Allah yasa hakan shi ya fi alheri”
Na fada da muryata da ke nuna lamarin be min dadi ba. Sai ya kalle ni kamar yana mamakin jin haka daga bakina.
“Ba zaki tambayi miyasa nai haka ba? Ba ki damu ki san dalili ba?”
“A lokaci da ka shige musu gaba har suka samu karatu a wannan makarantar ban tambayi dalili ba saia yanzu da zaka canja musu? Ka yi min alheri da yawa Abdallah wanda ni na san har na mutu ba zan taba iya biyanka shi ba.... Ba zan zarge ka da komai ba”
Mikewa yai tsaye ya jefo min wayata tare da jan tsaki.
“Ba ki hadu ba Halima....”
Yana fadar hakan ya fice, ban ce masa komai ba na fiddo hannuna dake cikin hijab na dauki wayata, ko da na kunna sai ganin screen din nai ya tsaga. Hakan da Abdallah yai be karamin komai ba sai kuzarin neman na kaina, kamin aikin ya samu ina son mai amfani da kudin hannuna na fara sa'a domin zaman banza ba nawa ba ne a yanzu.
Kwana uku da faruwar hakan ya kawo min takardar transfer dinsu har gida, a ranar Mama take tambayata dalilinsa na yin hakan nima na ce mata ban sani ba, sai da na labarta abunda ya faru asibiti.
“A duk yadda akai ba a iya yanke alakarki da Aminu saboda yaya sun shiga tsakaninku yaran har hudu ba ko daya ba”
“Za a iya yankewa mana Mama, Aminu ai be damu da yaran nan ba tun suna gidansa balle yanzu da ba sa tare da su”
“Ai yanzu ne yake sanin darajarsu Halimatu, ba ki lura da yadda Aminu ya canja ba? Ba ki lura da irin kulawar da yake bawa yaransa ba?”
Hafiza ta tsire baki.
“Ni fa ina ganin kamar so yake yace Halimatu ta koma masa...”
Ni ko nai karaf na ce.
“Allah ya kiyeye gatari da saran shuka, ni da Aminu a lahira idan na shiga aljanna wata kila na hango shi a bakin kofar wuta, dan yana da wahala idan Allaj ba kona shi ba akan zalincin da yai min”
“Halimatu kenan kina kara girma amman har yanzu hankali ya ki zuwa miki, kin kasa duban yaran dake gabanki ko dan su ai kya kyautata wasu kalaman akan mahaifinsu”
“Mama har yanzu ban gama warkewa daga tabun Aminu ba, saboda shi na samu kaina a duk wani hali da nake ciki a yanzu, mutumen da zai dube ni ya kira ni da mummuna yace ina ta haifa masa yara saboda na tsufar da shi, ya sake ni saboda na fada masa cewar dan'uwansa yana neman lalata yarsa? Sannan yai taraiya da kawata? Haba mama wace irin mutunci kike tunani zai shiga tsakani na da Aminu? Ni kadai na san irin kalubane da na fuskanta a gidansa”
Na karasa idananuwana na cika da kwalla, sannan na unkura na tashi na nufi inda jakata take na dauka daman da shirina na fito.
“Mama idan ko Hafiza idan su Namra sun dawo daga scul ki fada musu ba za su sake zuwa ba daga yau, saboda kar su saka rai, zan bawa Aisha kudin Napep ta je ta dauko su dan nasan kamin na dawo lokacin dawowarsu daga school yayi”
“To Allah ya bada sa'a ya tsare”
Cewar Mama. Hafiza kuma ta kalleni daga sama har kasa tace
“Allah yasa mai kamfanin yana kallonki yace ya samu mata”
Ni kuma nai dariya.
“Ai na girmi aure yanzu, ko nawa za a bani ba zan iya aure a yanzu ba, mun dai yi kuma gama da yarda Allah”
“Kara dai da kika ce da yardar Allah, aure ai shine martabar mace, kuma kin san ba ido zan saka miki kina zama a gida ba ko? Mutanen unguwa ma sai su yi ta yi da ke, musamman idan kika fara aikin nan wani ba tunanin alheri zai miki ba, yanzu sai ki ji an fara tsegumi, daman can ana lissafa mu na yan mata wai mun ki aurarda su.... ”
Mama ta tari numfashina tana ta kora bayani, ni dai kan uffan ban sake cewa ba, nai musu sallama na fice, har nai addu'a fita daga gida, ban daina mamaki da sake sake a raina ba, na kin ganin laifin da Aminu da Mama take da kokarin wankeshi a idanuwana, ga kuma zancen aure da take kokarin bijiro min da shi, anya ya gama da warke daga radadin azabar kunar da Abdulhamid da Aminu suka min da har zan yi tunanin aure? Ko da ma ace yana gabana ballantana yanzu da bana sha'awarsa.
Na isa gurin da zanje cikin lokaci domin na tsarawa kaina isa gurin da misalin tara na safe sai ga ni na isa takwas da rabi da yan dakiku a kai, duk kuwa da kasancewar babu wanda ya san da zuwana a kamfanin hasalima ni kaina ban san mai kamfanin ba ban san tsari da dokokin kamfanin ba amman ina kyautata zaton a lokacin ne za a samu duk wani wanda ake tsammani samu a kamfani.
Kamar dai ko wane kamfani shi ma wannan yana da masu gadi dake sanye da uniform mai sunan kamfanin wato Crown Company Limited. Sai dai ba su kadai ba har da Sojoji a gurin.
Sai da suka auna jikina idan bana dauke da bom sannan suka ba ni damar shiga ciki, ba ni kadai suke yi wa haka ba, har masu mota sai sun bude musu bayan mota sun duba sannan su basu damar wuce ciki.
A iya zamana garin gusau ban taba shiga cikin kamfanin ba, to me ma zai kaini tun da ba siye ko siyarwa zan yi ba, a yanzu ma dan ina neman aiki ne kamar yadda nake cewar kamfanin yana neman ma'aikata yan boko wadanda za su iya communicating da wasu mutanen amman da yalshen nasara wato turanci.
Sai dai ban san inda ake bi a shiga kamfanin ba, domin na lura da kofar kamfanin ta kasu gida uku wasu na fita da shiga a ta farkon wasu a ta biyu wasu a ta uku, tsaye nai a gurin ina ta tunanin wacce zan shiga, ta farko haka zuciyata ta raya min dan haka na nufi kofar gadan gadan, a nan ma wasu matsaran ne rike da abun awonsu kamar dai na bakin gate.
Sai dai da alama su basa barin mutum ya shiga sai idan ya nuna musu wata yar takardar wacce nake ganin kowa yana ba su su duba kamin su barshi ya shiga ciki. Hakan yasa ban karasa a gurin ba sai na juyo na nufi kofar tsakiya wacce mutane suka fi fitowa a cikin, wani abun burgewa ma kofar ita take bude kanta sai jujjuyawa take gwanin sha'awa, ina kokarin kutsa kai na shiga cikin kamfanin na Abban Baby Namra ya fito daga ciki yana sanye da shadda mai ruwan madara, ba laifi na dan saki fuskata domin har ga Allah na yi nufin gaisheshi sai kawai na ga ya hade fuska kamar bakin hadari daman can fuskar tashi ba a washe take ba, balle yanzu da ganina yasa ya kara hade ta kamar yaga mala'ikan mutuwa. Hakan kuma be hana na mika masa gaisuwa ba, amman sai yai min banza ya wuce abun shi, a take na ji duk na muzanta domin akwai mutane a kofar kuma na san wasu sun ji gaisuwar da na mika masa. Sai kuma duk na ji haushin kaina, miyasa na gaishe shi tun da farko ma? Miyasa ban kyale shi ba na yi tafiyata? Why na nuna na sanshi ma?
“Miya kawo ki nan?”
Kamar daga sama na ji tambayarsa da wata bakar murya tashi, har daka min tsawa yake kamar wata yarshi.
“Ban sani ba”
Na fada cikin tsiwa ba tare da na kalleshi ba na cigaba da tafiyata ina jin haushin kaina, na gaishe shi ne saboda ina ganin kamar akwai mutunci a tsakani ko dan abokatar da ke tsakanin Baby Namra da Namra, ko da yake daman daga ganinsa ba zai yi mutunci ba sai wani jijji da kai sai kace shi yafi kowa arziki a gari, Allah kadai ya san abunda ya kawo shi kamfani ma wata kila shi ma wata alfamar ya zo nema amman sai son nuna isa.
“Wai miya kawo ki nan”
Na fada a fili ina tsire baki har wani namijin da ke reception din ya dago ya kalleni.
“Na'am....”
Sai na dan saki fuskata nai masa murmushi.
“Sannu dai Malam daman na ji kamar ance kamfanin ku yana neman ma'aikata”
“Eh amman ba zuwa ake ba, ta email ake turo mana sako”
“Minene mail dinku?”
Ya fada min sannan na sake ce masa.
“Sai dai matsalar ban taba zuwa kamfanin ba, ban kuma san tsare tsaren kamfanin ba ban san mi kamfanin yake ba”
“Kamfanin mu yana siye da siyar da zinari tare da narkawar da kuma saffarashi ta hanyar yin abun wuya dan kulleni ko kuma wani abun na kayan ado na jiki ko na riguna”
“Na gode sosai, ta mail din zan tura cv na?”
“Yes idan sun duba suka ga kin cancanta za a kira sai ki zo”
“Na gode”
Na fada masa ina dariya.
“Your welcome.”
Tare da murmushi as respond. Ni kuma na jiyo na fito daga kamfanin, abun ka damai salo sai da nai ma security guard din sallama sannan na kama hanya, ban yi wata tafiya mai nisa ba na hango Kabir zaune a gafen hanya tufafin jikinsa sun yi datti ga surar kansa ta taru gaba daya ya soma canjawa ga wani abun datti da jikinsa yai. Karasa gurinsa nai da sauri ina kiran sunansa sai ya dago kansa da sauri ya kalleni ban san lokacin da na fashe da kuka ba. Hannu na saka a jakata na dauko dubu biyu na mika masa, be karba ba ba kuma yi min alamar zai karba ba, hakan yasa na risina na aje masa kudin na soma tafiya ina hawaye ina waigensa, har na tari napep na shiga be daina kallona ba kuma be kai hannu ya dauki kudin ba.
Gaba daya rayuwarsa ta baya sai ta dawo min sabuwa, Kabir mutum ne mai tsafta ga far'a da son mutane, musamman ni yana kula da ni yana nuna min kauna, duk kuwa da yake haramtacciyar kauna na nemana bayan yasan ina da aure.
Na fi alakanta ganin da nai a haka da rashin mahaifiya a raye domin na tabbatar da ace mahaifiyarsa tana raye ba zata bar danta a haka ba, domin ba duka yake ba balle ace ana gudunsa ba zagi yake ba, kusan sun ta haukar nan ta same shi ko magana baya yi.
Wallahi har na isa gida hawaye ba su daina zubar min ba, sai da zan fitaa napep din sannan na share hawayena na sallame shi na shiga gida, ashe wani kukan zan tarar a gidan mu, na shiga n samu hankalin kowa a tashe, ka rasa wanda zai fada min cewar Amal ta samu hatsari.
“Wai miya faru ne?”
Na tambaya ganin kowa yana ta bina da kallo.
“Amal ta samu hatsari”
Inna ta fada min muryarta a hankali.
“Ko dai ta mutu? Ku fada min?”
“Ba mutuwa tai ba tana asibiti ma”
Hafiza ta amsa min.
“Garin ya ta samu hatsarin?”
“Aisha taje daukarsu daga school sai ta tarar wai Aminu ya dauke su, sai ga kanwarsa ta zo yanzu ta fada mana wai Amal ta samu
Hatsari, so yake ya kashe miki yayan”
“Wace asibiti?”
“Wai Yarima bakura yanzu yanzu ta