Showing 207001 words to 210000 words out of 217237 words

Chapter 70 - GOBE NA Compelet Book by Khadijah Candy.txt

24 Sep 2025

221

kam ai na fi kowa sanin ya samu lafiya kam, ba mu bar kasar ba sai da Ahmad ya dauke mu ni da ita muka shiga wani shagon siyerda kayan sakawa da na ado muka siyo sannan muka shiga na yara na siyoma su Namra da Amal teddy Adnan da Aiman kuma mashin din wasar yara da wani madubi mai canja kala, Inna muka na siyo mata turare ita da Mama.
Sai a lokacin na gane ashe kayan mu na nan sun fi nasu na can arha domin duk abunda muka siya idan Ahmad ya fada min kudinsa a kudin Nigeria sai na jinjina abun.
Karfe 2:00pm daidai jirginmu ya sauka a Abuja babban birnin taraiyar kasa FCT.









_____________

Fatar kun yi sallah lafiya Allah ya maimaita mana 😍🙏
7/26/21, 1:29 PM - Buhainat: *GOBE NA...*

By Khadeeja Candy


6️⃣3️⃣

Mun iso Zamfara cikin aminci da farinciki, tun airport yan su Ahmad suka tarbo mu da muka iso sai muka tararda gidan kamar ana wani karamin ba a gaskiya na yaba da yadda yan'uwan Ahmad suke nuna kulawa da son zumunci.
Mun tarar an mana girki ga lemu kala kala gwanin sha'awa, a nan na kara sanin wadanda ban sani ba daga familynsa su ma muka suka san ni. Sai da na huta na ci abincin sannan Siyama ta shigo tace min Hajiya tace idan na kintse za a sauke ni gida, aiko da sauri na tashi daman tun dazun babu abunda nake sai tunanin gida da mamarin ganin nawa Familyn.
Direbansu aka saka ya kai ni har gida a nan wata murnar ta barka duk da kasancewar mun dawo Tuesday ne yara suna makaranta amman su ma manyan hakan be hana su murna da ihun ganina ba. Ban tabbatar da na yi missing gida ba sai da na ganni tsundun a ciki, wai har na yi tafiya na dawo sai abun ya koma min kamar a mafarki lallai rayuwa tana da ban tsoro kuma lallai duk abunda yai farko dole yana da karshe.
A nan ma an shirya min wani abincin irin namu na daidai gwargwadon hali bancin Kifin data saka a shimkafar jalof har da nama ta siyo ta soya min ta siyo min lemun Coke, a yadda naga tana ta murna da ganina ni kaina na san ta yi marmarina.
Gidan be kara haukacewa ba sai da su Namra suka dawo daga makaranta a nan wani sabon murna ya tashi suka dinga hawa suna sauka kowa Momy Oyoyo, wani irin farinciki naji ya baibaiyeni at least nima dai abun alfahari ce ga iyalaina duk da ban yi musu wani abun na gwaninta ba ko na azo a gani.
Ana gama sallah magari sai ga kiran Ahmad ya shigo wayata, bayan mun gaisa yake tambayar yaushe na tafi wai ban nemi izininsa ba ni kam dariya ma abun yaban.

“Ban fa tare ba”

“To miya raba dambe da fada? Ko baki tare ba ai igiyar aurena tana kanki, kuma tarewan zai wuce kwana biyu ne ko uku”

Na zaro ido.

“Wane irin kwana uku sai kace yar roba? Haba dai ina laifin wata uku hudu”

“What......! Ai ba zan iya barinki ko wata daya ki yi ba, kin san fa ina bukatar kusa da ni kuma ga wannan dan uwan naki zai iya zuwa fa”

“Haba dai ai mahaifiyarsa ta riga ta shiga tsakani, dazun Mama ke fada min wai karshen watan nan za a sake shiga kotu, ga Hajiyar ma lafiya bata isheta ba, yanzu ai ba ta nawa yake ba, ai na yi aure dole zai daga min kafa”

“Baki san halin Namiji bane Lims maza suna da wani irin hali, idan suna son abu ko?hmmmm ni dai gaskiya ba zan iya bari ki yi wata uku ba a cikin watannin nan Allah kadai ya san wanda zai ganki ko bayan shi Abdallah wata sani ko wani dabam na nan yana dakonki”

Dariya nai sai ya fara rantsuwa.

“Wallahi Allah kuwa ba zaki gane ba ne, ni kuma bana son ana ganinki kuma idan kina gidanku ba natsuwa zan yi ba kara dai na san kina dakina na rufeki abuna”

Na sake dariya, mun dade muna fira dashi kamin ya bijiro da fitinarsa nai masa sallama na tashi nai sallah isha'i...
Akwai wani irin natsuwa da kwanciyar hankalin da farinciki a cikin aure musamman idan ka dace, akwai akasin hakan kuma ga wanda be yi dace ba kamar yadda nayi da farko, ko da yake ko a yanzu ina kyautata zaton dacewar ne kawai da alamun da na gani a gurin Ahmad wanda ban gani ba a gurin wani namijin. Sati biyu da dawowata amman duk wanda ya gan ni a yanzu sai yayi magana cewar na canja jikina yayi kyau fuskata har wani sheki take, ramar da nai na cike ta a yanzu ni kaina na san na canja ban tare ba amman abinci da na sha sai wanda na zaba ni da yarana, ko wace safiya ka'ida ne sai ya kira ni ya tambayi yana tashi da rana haka kin ci abinci? Kina da wata damuwa haka yake min a kullum da dare kuma ko wace rana sai ya zo.
Tun satin daya shige Hajara ta kawo min kayan gyara jiki na kirji da wanda zai saka jikim tai ta sheki ga dilken da nake zuwa gidan Zil-touch tana min a duk bayan kwana biyu, na maida hankalina sosai gurin siyen wasu abubuwan da na ssn bana da su a gidansa dan aure ko kuma wandanda suka lalace cikin har da siyer da kayan dakina da zimmar yin sabbi.
Ranar wata lahadi ina zaune sai ga Siyama ta shigo bayan mun gaiss da gaisa da mutanen gida sannan na shiga na dauko mayafina domin ya fada min zata zo ta dauke ni muje gidan saboda na duba wallpaper da aka saka min idan ta yi, na nuna masa ba sai naje ba sai ya ta kura akan lallai sai naje a dole na amince.
Tare muka fita da ita bayan mun isa kofar gate din tai horn aka bude mata, mu na shiga cikin gidan na tarar an sabunta sabon fentin bangaren Hajiya gwanin sha'awa. Na yi zaton part din Hajiya za mu fara zuwa kamin mu shiga part din Ahmad din wato part din da zan zauna, amman sai Siyama ta fara shiga da ni part din Ahmad, an kawata gurin da sabon fenti sai kamshi yake, ina shiga falon nai arba da sabon cushion da curtains duka maroon color, dinning din na sabo, an zuba komai sabo a kitchen da bedroom din ma sabon furniture ne mai kyau, sauran dakunan ma duka sabin furniture ne. Gaba daya sai na ji kamar an sare min gabobin jiki na rasa abunda zance, sai a lokacin na gane abunda Ahmad yake nufi da cewar kar na wahalar da kaina shi baya bukatar komai ni yake so ba wani abu nawa ba.

“Komai ya miki? Idan akwai abunda be miki ba ki fada sai a canja ko a kawo kamin lokaci ta kure”

Siyama ce take maganar tana janyo kofar kitchen din. Tsaye nai a gurin kamar an dasani na rasa abunda zance wani guntun hawaye ya tsaya min a ido. Sai ta sa dariya

“Daman Wallahi Ya yace yanzu ana nuna miki sai kin yi kuka, har muka dinga dariya ashe da gaske yake”

Murmushi mai na share hawayen.

“Idan ban yi kukan farincikin ba Siyama na me kike son nai?”

“Kawai ki gode Allah”

“Al-hamdulillah”

Na furta fili da badini, sannan muka fito daga part din ina ta tunanin yadda zan labartawa su Inna abun, cikin tsananin kunya na shiga part din Hajiya, ko zaman ban yi ba Siyama ta labarta masa cewar na yi kuka sai yai murmushi yana kallona.

“Ni ai na san halin kayata”

Bayan mun gaisa da Hajiya ta sa aka kawo min lemu sannan ta fada min.

“Nasa Ril_kamshi ta hada miki turare kayanta suna da kyau”

Wallahi ni nai kamar na saka kuka a gurin, da wanne zan ji da abunda Hajiya tai min ko da na Ahmad? Ko kuma da kaunar da suke nuna min ni da yayana? Sai na rasa da wane baki zan yi mata godiya na rasa kalmomin da zan hada su isar da sakon godiyata yadda ya kamata.
Ban wani dade sosai ba Ahmad yace na taso ya maida ni gida, Hajiya bata bar ni a fito haka nan ba, sai da ta hada min yan turaruka da man shafawa kamar yadda ta saba ta bawa Siyama ta kawo min.
Tun da muka bar gidan na kasa dauke idona akan Ahmad, wani irin kaunarsa da kimarsa suka cika min ido, farincikin da nake ji a raina ma shine sila, ina ta tunanin kalar da zan siye yanzu ya dauke min wannan nauyin.

“What”

Ya tambaya yana murmushi ganin irin kallon da nake masa. Sai ya kai hannunsa ya kamo hannuna ya saka yatsunsa cikin nawa kana ya sumbacin hannun nawa.

“Na san zaki ce zaki wahalarda kanki gurin siyen kaya wata kila dan abunda ke gareki ma ya kare, so tun da ina da hali da dama me zai sa na bari ki yi? I just wanted you to know that ke nake so, kuma ina son farincikinki”

“Thank you, i mean Thank you”

“You shouldn't”

Ya fada yana kara kissing din hannuna, da hannu daya yake tuki dayan hannun kuma yana rike na nawa hannun har muka isa wani shagon dinki.

“Zauna a nan ina zuwa”

Na fada min sannan ya bude motar ya fita, ya shiga shagon sai gashi ya fito tare da wata mace kabila, sai da ya shiga ya zauna sannan ta leko ta gilashin motar ta gaishe da da far'arta.

“Ya aikin ya gidan?”

“Lfy kalau Alhamdulillah, ki fada min address dinki zan zo na auna ki”

Na fada mata kamar yadda ta bukata sannan ya tashi motar muka bar wajen, mun dan yawata cikin gari kamin ya dawo da ni gida sai zolayata yake wai yana da kanwar hannu a dube ni ban tare ba amman har na yi fresh skin dina sai shinning har wani jan kumatuna yake.

“Allah kin ma fini fari fa, ji hancin har tsawo ya kara”

“To ai ba kai ya kamata ka fada ba mutane ya kamata ace sun fada”

Kallo tai baki sake.

“Su waye mutane? Baki san ni bane lims a kalleki ace kin yi kyau? Hmmmm”

“To ai mata ba maza ba”

“Har matan mana baki san yanzu akwai mata yan iska masu kwacewa miji mata ba? Maganar Allah ni ko mace ba zan yarda ta tsare ki da ido ba ba yarda zan yi ba”

Bude motar nai na fita ina dariya sai ya sauke gilashin motarsa ya kira ni jiyowa nai na dawo.

“Ina son na fada miki for the very last time bana son wata mu'amala na shiga tsakaninki da Aminu, na san akwai yayansa amman na dauke masa komai idan ba abunda ya zama dole ne a matsayin na uba ya gabatar da shi ba, idan zai yi magana da ke akan komai ya kira wayata da ni zai yi magana ni kuma sai nai magana da ke”

Babu alamun wasa a maganarsa kamar yadda fuskarsa ta nuna.

“In-Sha-Allah”

Ya gyada min kai ya bi ni da kallo har na shige cikin gida sannan na ji tashin motarsa.
Bayan kamar thirty minutes da dawowata mai dinki ta isko ni har gida ta auna ni.




ABDALLAH POV.

A cikin ko wane shafin rayuwar dan'adam akwai kaddarar rayuwarsa mai kyau ko marar kyau, wani ta so masa da sauki wani da wahala wani daga karshe ya samu cikar buri wani kuma ya koma a gurin mahallincinsa ba tare da rai ya samu abunda yake so ba.
Sai dai yarda da ko wace irin kaddara yana cikin cikar imanin bawa, yarda samu da rashi na Allah ne yana karawa bawa kwanciyar hankali da wadatar zuci, a iya yarda yanzu kam Abdallah ya yarda akwai son Halimatu a cikin kaddararsa, akwai rashin aurenta a tarihin rayuwarsa.
Iyakar hijadin da yai ne shine na rufe babin tahirin sonta a zuciyarsa wanda a da ya kasa haka sai a yanzu da ya yarda da kaddararsa kuma ya yarda ya rasa Halimatu har abada! Domin ko bayan Ahmad da yake da tabbacin ba zai sake ta ba, idan ma ta Allah ta kasance ace ya mutu ita tana raye aurenta ba zai taba yuyuwa ba domin Hajiya tace ko bayan ranta bata yafe nasa ya auri Halimatu ba, a dayan bangaren kuma idan ya zauna yai tunani a yanzu da son kai ya fitar masa a zuciyata, ya kan tausayawa dan'uwansa na rayuwar da yai da kuma wacce sai fuskanta a gaba, sai a yanzu ne yake ganin rashin dacewar auren Halimatu bayan kuma dan'uwansa yana raye, a yanzu yana jin cewar Halima ta cancani farinciki ko da ba a gurinsa ba ne idan har zata samu farinciki da kwanciyar hankali ya kamata ya kyaleta tun da ba zai taba aurenta ba, sai a yanzu yake nadamar neman aurenta da yai da auren wani akanta sai a yanzu gane girman laifin daya aikata a wacan lokacin idonsa ya rufe baya iya ganin laifin kansa baya iya ganin laifin Halima saboda so ya rufe masa ido da kuma neman haihuwar namiji.
Sai dai har zuciyarsa na dauke da kaunar da kuma muradin son haihuwar namiji domin maradinsa ne tun kamin yai aure, har yanzu ya kasa sauke burin da yake da yakinin ba zai taba tabbatuwa ba domin dan'uwansa ya riga ya soke shi da mashi.
Abubuwa uku suka fi tsaya masa a rai, haihuwar Namiji, matsalar dan'uwansa sai kuma damuwar da Mahaifiyarsa ta dauka ta saka a ranta na matsalar Abdulhamid.



HALIMATU POV.

Na yi zaton kamin na tare za a kawo min kayan duk kuwa da kasancewar ban masa maganar lefe ba, amman shiru ana ta shirye shiryen tarewar amman be aiko min da komai daga cikin sutura ba, hakan yasa na cire kudina na siye tufafina masu kyau lace da Atamfa da shadda lace yar ubansu a gurin Khadeeja Candy, na kaiwa tela ya dinka min tun kamin ranar da za a tare din.
Ba wani shirye shirye zan yi ba, bayan wunin biki wanda ya zama al'ada a ko wane biki na budurwa ko bazawara, ana sauran kwana uku wunin alert ya shigo watana mai nauyi har sai da na zare ido, ina ganin sunan wanda ya turo min nai murmushi na shiga contact list da zimmar kiransa sai ga kirashi ya shigo wayata. Cikin shauki da kauna na dauki kiran ina murmushi kamar ance yana gabana.

“Na ga Alert”

“Eh abububuwan da za ku yi na mothers day din, za su iya dai ko?”

“Haba dai wannan kudin ai yayi yawa”

“Da gaske?”

“Haba dai”

Na fada a shagwabe sai shi ma ya rama yadda nai masa.

“Haba dai Babe”

Daga ni har shi sai muka saka dariya kamin ya dauko min zancen yadda su a nasu gidan za su yi masu wunin da irin abubuwan da za su tsara nima na fada masa abubuwan da nake son yi da rabawa mutane.

Wanda yake cewa ba zai barni nai sati biyu a gida ba sai gani na yi wata har yan kwana biyu sama domin shi ma kansa da babu ishesshen lokaci ba zai samu damar aiwatarda komai na gidansa ba, Hajiya ma ba zata samu wadataccen lokacin yin wani abun ba, balle kuma ni uwar bikin gaba daya.
Na yi gayyata sosai har wandanda ba su san na yi aure ba sai da suka sani, an dafa abincin kusan kala hudu domin Ahmad ya wani wadataccen kudin da zan yi duk abunda nake so har na rage, lemu ma kala kala a siya, bayan yan abubuwan dande dande da lashe lashe da ake sakawa a takeway da kaskon turare da turaren wutar da kofi ko plate a bawa mutum idan zai je gida.

Nina makeupover (I like you girl 😘) ce ta gyara min fuskata na fito kamar wata yar sha biyar kowa sai yaba ni yake, ga dinkina dan ubansu na farin lace da farin mayafi kana ganina a cikin jama'a kasan ni ce amarya domin na haska kowa, duk wanda ya ganni sai yace na yi kyau. Na jidadin da Ahmad ya aiko mana da mai daukar hoto duk kuwa da kasancewar ya san akwai waya amman hakan be hana shi turo kwararen mai daukar hoto ba.
Cikin farinciki da jindadi akai yinin biki kowa sai sambarka yake, bayan sallah isha'i manyan motocin na alfarma suka faka kofar gidanmu kowa sai kallo yake wadanda ba su san wa zai aura ba a unguwar sai kallo ake ana mamaki masu neman salsala kuma suka fara.
Mama da Inna sun min nasiha sosai akan hakuri da biyaya kamar yadda suka saba min a kowane aure nawa da nake na dawo, sai dai wannan bana fatar dawowar fatana ba rubuwa da Ahmad har sai ta Allah ta kasance.
Yan'uwan mahaifina ma sun min nasiha suka min fatan alheri tare da addu'ar Allah yasa gidan zamana ne.
Ana kokarin fita da ni Hafiza ta zo ta rada min a kunne.

“Lims din Amadu dan Allah idan kin yi sallah ki saka da mu a addu'arki Allah ya kawo na mu na gari, wadannan yan iskan samarin masu zuwa zance kawai ba neman aure sai bakin rowa Allah ya bamu da su”

Dariya nai na kalleta sai tace.

“Wallahi fa ki duba aure na uku kika yi, mu nuna nan ko daya ba mu yi ba, kuma ba farin jinin ne babu ba, masu son auren da gaske ne basa zuwa”

“Komai ai yana da lokaci Hafiza, ni din da na riga ku aure baki ga yadda auren ya kasance min ba? Kowa ai da jarrabawarsa, wani abun nesa yake wani a kusa, idan akai hakuri za a cin ma komai”

“Na sani ni dai ki saka mu a addu'a, kin ga Inna da Mama da yan unguwa ai ba su san wannan ba, yan mata hudu a gida, Yaya nata aure tana barinsu ina lafiya, yan kanennan na mu ma sai taso suke za su cin mana a tsawo”

Ban

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login