Showing 201001 words to 204000 words out of 217237 words

Chapter 68 - GOBE NA Compelet Book by Khadijah Candy.txt

24 Sep 2025

198

sai ya fara kallona kamar mai mamaki, nikam yau na rantse gida zan kwana ko da karbar sakon da Hajara tace min zata kawo idan an gama sallah isha'i.

“Ba dai gida za ki je ba ko”

“Gida mana, tun da gobe za mu tafi ai kara na ce gida tun yanzu sai na kwana can nai musu sallama”

“A a ni ba zan iya kwana babu ke ba”

“Can da da kake kwanan fa?”

“Can da ai ban rabi jikinki ba, yanzu kuma na saba kwana biyu nan ba zan iya ba gaskiya, haramun ne ma”

Ya fada yana riko hannuna.

“A a Mama tace na dawo gida na kwana so that nai sallama da su Namra”

Marairaice min yai.

“Tsoro nake ji, kuma ciwon zai iya tashi idan baki nan”

Yanayin yadda yai maganar yasa ban san lokacin da dariya ta subuce min ba. Shi kanshi dariya yai ya rumgume.

“i love you Babe, gaskiya ba zan jidadi ba idan baki kwana a nan ba, amman babu yadda na iya, dole nai hakuri”

“Yauwa na debi kala biyar na tafiya yayi? Kar na deba da yawa ya sama kauna”

Na fada daman ina son nai masa tambayar tun jiya.

“Ki kara”

“Za mu dade ne?”

“Ba sani ba tukuna, wata kila za mu dade wata kila ba za mu dade ba ya dangata daga yadda suka ba mu, amman kin san ko na ji sauki sai dai Hajiya ta dawo ta bar ku can ko?”

“Saboda me? Ba kai aka kai ba?”

“Kin san idan mutum ya dade yana jin kishin ruwa idan ya samu ruwan ba ya musu shan hankali”

Kallonsa nai da kyau ina mamakinsa a dacan idan aka ce min Ahmad zai yi haka wallahi zan karyata.

“Anya dai kai ne?”

“Ni ne fa, ai dan iskan cikin gida ne ni, Allah dai ya bani lafiya”

“Lafiya ai ta samu marar lafiya ba zai yi abunda kake ba”

“Ina ma kika sani hmmmm Allah dai ya kai damo ga harawa, ya nuna mana mu dan yi nisa da Hajiya akwai kara'i”

Ya karasa yana kwafa yana kokarin kyalkyalata, dariya nai sai yai kissing kumatuna yana shafa bayana, sai kuma ya dago fuskata ya soma tsosar bakina try to remove my Hijab, sai da nai da gaske sannan na raba jikina da shi.

“Komai abunki dai dole ki jira driver ya zo or else ki kwana nan dan ba zan bari ki hau Napep ba ana kalle min kaya”

A nan ma dariya nai ina ta jin kunyarsa sai dai na lura sam ya sauya kamar ba shi ba kunyar ma bata gabansa, hannunsa kuma baya zama kurum matukar muna zaune dakin daga ni sai shi. A dole nai jiran ya kira driver a waya ya iso, kamin na bar asibitin sai ya nemi na dora masa ruwa.

“Kin ja min wanka matar nan duk kin lalata ni”

Juyowa nai na kalleshi da mamaki ina kokarin fita, sai ya kanne min ido daya ya aiko kin da sakon kiss. Ni kam dariya nai na fice daga dakin.
Ko da na isa gida na tararda Hajara na jira na, tana ganina taja hannuna muka nufi dakina na kori su Namra da ke ciki muka zauna saman katifa ta, sai ta bude jakarta ta dauko abun ta bude tana mika min daya bayan daya.

“Wannan idan zaki kwanta bachi zaki shafa shi a kasan mararki, za ki ji sanyi kamar kankara, wannan kuma a kasa za ki tona ki zuba garshi a kasa sai ki saka wannan karamin a gabanki wannan kuma ki zuba a garwashin sai ki yi tsuguno za ki ji na cikin ya nairke kamar mai kuli karki taba ki barshi haka ya kwana a jikinki sai da safe ki wanke da ruwan dumi, wannan garin kuma da madara za ki sha, shi kuma wannan na kwayun ki hade shi duka da ruwa hmmmmmm to kwanta ki yi bachinki ba kya bukatar komai Hajiyata shi wannan hadin ma ba a bawa mai kishiya saboda gudun hada fada ko haddasa saki, sai dai idan kun dawo ki yi dilke da sauran gyaran jiki”

Rumgume ta nai ina murna idan ba kawar amana kawar arziki ba wa zai maka wannan?

“Na gode sosai Hajara”

“Babu komai Allah dai ya baku zaman lafiya”

“Amin ya rabbi”

Na rakata har gurin motar mijinta mu kai sallama na dawo cikin gida, shi da na sha tun cikin dare na sha da wanda tace na yi tsuguna duk nai.
Ni kaina sai da na soma tabbatarda lallai akwai alamun maganin mai kyau ne, domin tun a jikina na ga canji fitsari da nake ma ina yi ina jin zafi abunda ko da ina budurwa ban ji ba. Tun da farar safiya ya kirani muka gaisa yace na bawa Mama wayar ya gaisa da ita yai mata bakwana sannan na kaiwa Inna ita ma sukai bankwana sannan ya aje wayar bayan ya fada su Namra ba za su je ba yau wai zasu mana rakiya airport. Misalin tara ya aiko da mota, gaba daya sai naji wani iri kamar kar na tafi saboda kewa ko zuwa wata area ma ina jin kewa balle kuma tafiya ce ta kasa da kasa, kamin na shiga motar sai da nai ta kuka ina jin kamar idan na tafi ba zan dawo ba, ba su Namra kadai suka raka mu ba har da Aisha da Hafiza. Kai tsaye gidansu Ahmad din aka wuce da mu mun ga tarba ta musamman Hajiya kamar ta hade ni ita da sauran mutanen da suka zo musu bankwan, ban saka Ahmad a ido ba sai da zamu bar gida sannan ya shigo dakin Hajiya domin ni a dakinta ta aje ni su Namra suka tsaya falo. Ya shigo cikin shiga ta alfarma kamar ba shi ba ko kunyar Hajiya be ji ba ya zauna kusa da ni yana karbar rubutun data miko masa, sai da ya shaye tass sannan ta bashi wani ya shanye ta dauko masa ruwan addu'a a nan kam yai fir wai ba zai sha yawun wani ba, rubutun ma dan kar ya mata gardama ne.

“Ni naga ma abun da sauki sosai Allah ya kara lafiya”

Ta fada cike da jindadi sannan ta fice, shi kam kamar yana jira ya mika hannu ya riko ni.

“I miss you”

“Dakin Hajiya muke fa”

Na fada ina kallon kofa domin na san ba karamin kunya zan ji ba idan ta gan mu. Dariya yai ya saki hannuna nawa. Ba mu wani dade sosai ba muka fito daga cikin gidan har na nufi motar da muka shigo sai Siyama tace.

“A a ba ita zaki shiga ba ga motarmu can”

Ta nuna min wata bakar mota wacce Ahmad da Hajiya suka shiga, a tare muka nufi motar sai ga Amal ta fito daga wacan motar da gudu tana fadin wacce na shiga zata shiga. Ina kokarin yi mata fada Ahmad ya bude front seat ya ce ta zo, a tare da shi ta zauna gidan gaba, ni da Hajiya da Siyama kuma muka zauna a baya, ina ta jin kunya sai dai na lura Hajiya bata kula wannan ba sai ma kokarin fira take da ni idan an kai wani gurin tace min ga kaza nan.
Sai da muka isa sakkwato muka huta a wata hotel sannan muka wuce airport, ko da muka isa ya rage sauran minti talatin jirgin ya tashi zuwa Abuja, a nan mukai duk abunda ya kamata sannan mukai sallama da su, Siyama har da hawaye ta rumgume dan'uwanta tana masa addu'ar samun lafiya sannan ta rungume Hajiya nima ta rumgume ni.

“Matar yaya ki kula min da yayana kin ji”

“In-Sha-Allah”

Daga haka mu kai sallama da su tare da yarana sannan muka shiga cikin jirgin ina ta jin kewar gida, kujerar da ke kusa da window ce tawa sannan ta Ahmad sai kuma ta Hajiya a baya kuma ta wani ce da nai zaton direba ne domin shi ya tuko mu duk kuwa da shigarsa bata nuna hakan ba. A lokacin da jirgin zai tashi duk muka saka belt sai jin dagawarsa nai hakan kuma ba karamin tsoro ya saka min ba abunka da wanda be taba shiga ba. Ina ta addu'a domin gani nake na yi kusa da mutuwa tun da jirgin ya daga sama.
Ba zan iya sanin awanin da muka dauka ba kamin mu isa Abuja wata kila ma yan mintuna ne tun da ance jirgi sauri ne da shi, sai dai naji Hajiya na fadin mun yi sauri.
Sallah akwai na san mun yi a wani gida da nake kyautata zaton na yan'uwansu Ahmad ne, ko awa daya ba mu yi ba a gidan muka koma airport din abinci ma sai a can muka ci, gaskiya garin Abuja na da kyau mayan gidaje ta ko'ina ga tituna gwanin burgewa ga yanayin garin da sanyi ba kamar Sokoto ko Zamfara ba.
Manyan shuke shukensu ma abun kallo ne, airport din ma gwanin burge wa kowa ka gani tsab da shi sai hada hada ake ba ruwan kowa da kowa.
Wani jirgin muka shiga ya daga da mu zuwa kasar nasara....


Na sha bachi kam sosai a cikin jirgin a duk lokacin da zan farka sai na gan ni a kafadar Ahmad, can kuma ya tashe ni ya bani tea a wani karamin kofi da biscuit shi ma ba wani mai yawa ba, bayan na gama sha wata mace mai sanye da uniform ta zo ta karba. Mun dade sosai muna tafiya kamin mu isa, a iya sanina mun baro Nigerian da yamma lis amman da muka sauka nan sai na ga safiya ce fal, ga wani uban sanyi mai ratsa kashi. Cikin airport din Ahmad ya fiddo rigar sanyi ya saka min a saman abayar da ke jikina ya bani safa na saka na a hannuna a kafa ma ya bani na saka sannan na cire talkamina ya bani wasu talkamin masu rufe na saka shi ma ya saka kamar yadda Hajiya ma ta saka sannan muka nufi gurin tex. Kusan tun da muka bar airport din sai na ce ban hadu da bakin mutum ba har muka isa hotel din da aka kama mana bana aikin komai sai kalle kalle, ashe a Abuja ance min baki ga komai ba yanzu ne kallo yake.
Komai na su a cikin tsari yake gwanin ban sha'awa ga bin doka da oda, tun da muka sauka cikin jirgin Ahmad ke rike da hannuna har muka isa dakinmu da aka bare mana.
Ina zaunawa bachi yace sallamu alaiku, sai jin nai yana tashina.

“Lims ta so mu yi wanka sai ki yi bachin mu kuma za mu karasa asibitin”

“No nima zan bi ku”

“A a Hajiya tace na barki ki huta”

“Da gaske”

“Ai ba zan miki karya ba”

“Yaushe tace ban ji ba kuma ai tare muka shigo nan”

“A waya ta kira ni”

Ya nuna min wayarsa. Yana kokarin rika hannuna.

“Taso muje mu yi wanka mu yi sallah jirana take”

“To ka shiga ka fara yi sai....”

“A a nan ai babu wanda zai sa mana ido ki saki jikinki”

“Aa wallahi ba zan iya ba a yanzu”

Na fada ina girgiza masa kai, sai ya dafa kaina.

“Why da rantsuwa? Wata rana ke zaki bukaci haka ma”

A gabana na cire tufafin jikinsa sai da na kawarda fuskata ya daura tawul ya wuce bandakin ba tare da jin komai ba, ni kam gaba duk naji wani iri ji nake kamar wacce bata mu'amala da wani ba haka na ji, gaba daya komai sai na koma kin sabo musamman Ahmad da na lura lamarinsa azimun ne.





_________________

Na so na karasa pages din kamin sallah amman Allah be nufa ba, dan haka zamu tafi hutu sai bayan Sallah idan mai kowa mai komai ya amince mana In-Sha-Allah.
7/25/21, 4:10 PM - Buhainat: *GOBE NA...*

By Khadeeja Candy


6️⃣2️⃣

Sai da ya fito daga wankan sannan na shaga, da sabulu kawai nai wankan domin babu soso a ciki sabulun ma ba irin na mu na Nigeria ba ne, bayan na gama na daura karamij tawul din har na nufo kofa na fito sai kuma wata zuciyar tace min kara dai na maida tufafim jikina kar na fita da wannan guntun tawul ai da kunya.
  Ina kokarin daukar kayan na saka sai jin nai an yaye labulen bandakin daman ba kofa ba ce bandakin na glass ne sai lalulen da aka saka dan kare wanda yake wankan.

“Ba ki gama ba ne”

Ya fada yana kallona tun daga saman kaina har kasan kafafuwana. Tsaye nai da kayan ka kasa sakawa na kasa ajewa na kasa fitowa wata irin kunya mai tsanani ta rufe ni. Sai da ya hade yawu sannan yai murmushi ya juya yana fadin.

“Fito ki saka tufafin ki, ni ba wani abu zan miki ba”

Kallon jikina nai tawul din karami ne sosai ta yadda idan na duka za a iya ganina idan kuma ban rike shi da kyau ba zai iya subuce min ya fadi. A haka na daure na fito ganin babu wata mafita na nufi gurin akwaitina da zimmar na fito da doguwar riga na saka, sai jin mutum nai a bayana ya dora hannayensa saman kafadata yana sharce min ruwan da ke kai bakinsa saitin kunnena ya rada min.

“Ki daina jin kunyata, ni mijinki ne kuma zaki wahalar da kanki ne kawai, ni kaina ina da kunyar amman akan halila gaskiya babu wannan ina sakewa nai yadda nake so, ni da ke abu daya ne a yanzu”

Ya karasa tare da tsosa kunnena, wani yarrrr na ji rabon da na ji irin haka har na manta, kamar wacce aka daurewa baki haka na zama da kansa yaja hannuna zuwa gaban akwatinsa ya bude ya dauko wani mai mai kamshi ya zuba a hannunsa ya fara shafa min kamar nai magana sai kuma a kasa, haka ya ji ko'ina na jikina ya shafa min man har a cikin yatsun kafata, sannan ya fara kokarin kwantar da ni saman gadon a nan kam Allah ya bani ikon magana

“Ban yi sallah ba”

Bakin da nai magana da shi ya kurawa ido gaba daya idanuwansa sun canja kana kallonsa kasan natsuwarsa ta dade da barin jikinsa, can kuma ya kalli cikin idona sai kuma ya sake kallon bakina tare da kai hannunsa ya taba lisp din a hankali sannan ya sake ni ya juya ya nufi bandaki, ni kuma na mike tsaye daidai ina gyara tawul din dake kokarim subucewa gaba daya, kamar an koroshi haka ya dawo da gudu ya rika ni ya fara kissing din bakina yana wani irin haki yana shafani kamar wanda aka ce za a raba da ransa idan be sumbance ni ba.
Ban san iya lokacin da mu ka dauka a haka ba, tun muna tsaye har tsayin ya gagara muka kwanta saman gadon, wanda hakan ya bashi damar kai hannunsa a kirjina yai wasa da shi yadda ransa yake so. Sai da aka soma kwankwasa kofar sannan ya daga ni da sauri ya nufi kofar sai dai be bude ba sai ya tsaya daga jikin kofar.

“Waye?”

Ya fada yana cizon lisp dinsa tare da aje numfashi a hankali.

“Kai fa nake jira tun dazun”

“Hajiya gani nan zuwa yanzu please I'm sorry”

Ya fada yana maida numfashi sai da ya tabbatar ta tafi sannan sake nufo ni yana murmushi.

“Na manta Hajiya na jirana idan na fita zance ke kika tsayar da ni a nan”

Bance masa komai ba nai kasa da idona, wannan karon kafafuwansa biyu ya raba ya kai bakinsa gurin hancina sai da ya tsotse shi tasss sannan ya dagani ya fara kokarin cire tufafin jikinsa. Juyaawa nai na bashi baya tare da yan Bedsheet din na rufe jikina, ina jin sautin dariyarsa da kuma maganganun da yake fada na rashin kunya har ya shige bandanki, nima dan murmushin nai ina lumshe ido, ni kaina a yau wani shauki ya ziyarce ni wanda na manta rabon da na ji irinsa, wata irin natsuwa da annashuwa suka sauko min, na kasa daina murmushi har ya gama wankan ya fito, ya sake shiryawa cikin wasu riga da wandon ya fesa turare sannan ya kwanto bayana yai kissing din gefen wuyana yasa hannunsa ya kama hannuna yatsunsa cikin nawa.

“Ki yi bachi ki more”

Juyowa nai da sauri da zimmar nai masa magana sai bakina ya gogi nasa numfashina ya gauraya da nasa, babu abunda yake kallo sai bakin nawa.

“Talk”

Ya fada bakinsa na gugar nawa, a dole nima a haka nai masa magana bakina da nasa na gogar juna.

“Ina son naje nima ai”

“So kike mu je can mu taru mu lalace? No za ki tsaya a nan ki huta kamar yadda Hajiya tace idan sun ba ni gado bayan kin huta zan aiko a dauke ki, kuma zan siyo miki sabon line da zaki rika amfani da shi a nan so that ki kira Mama ki sanar mata mun iso”

Ya karasa tare da kissing dina sannan ya daga ni ya nufi akwatinsa ya rufe ya dauki abubuwan bukata ya saka aljihu,sai kuma ya sake nufo ni da kansa ya dago ni ya rumgume ni ya sake kissing dina sannan ya fita tana dago min hannu. Da kallo na bishi har ya fice ina mamakin hali da dabi'unsa idan aka fada maka Ahmad zai iya zanzarewa yai haka saka rantse da Allah karya ne kace ba zai aikata ba, ni a rayuwata ma ban taba auren namiji marar kunya kamar Ahmad ba, shi komai nasa kirkiri yake kuma da gasken gaskiya to wa ma zai ganshi yace shi aka kawo jinya?
Fitarsa da kamar minti bakwai aka kwankwasa kofar dakin
Tashi nai jikina nata kamshin turarensa na dauki rigata na saka sannan naje na bude, wata farar mace na gani dauke da tray din abinci ta miko min, sai na rufe dakin na juyo na dawo, burger burger and snacks sai drink da safafen kwai, ban kula abinba na nufi bandaki da murmushin daya kasa bari kumatuna, wanka nai sannan nai alwala na fito har lokacin murmushi nake ina jin wani irin shaukin kaunarsa a raina. Haka na bi na rama ko wace sallah sannan bude abunda aka kawo na ci wanda zan iya ci na bi lafiyar gado na kwanta bachi son raina nai ta bachi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login