Showing 183001 words to 186000 words out of 217237 words
kaddarar ta fado masa...”
Hajiya ce take wannan maganar hawaye na fitowa daga idonta, wani irin abu ta ji ya tsaya mata a zuciya tun daga lokacin da gaskiya ta bayyana har yau yana nan tsaye ya tokare mata kirji. Abdallah ya sauke ajiyar zuciya, shi kanshi shi jidadin halin da dan'uwansa da mahaifiyarsa suke ciki ba, no matter how bad your blood is, jininka jininka ne, and idan akwai wanda zai yi blame me a yanzu Ahmad ne domin shine silar faruwar hakan, duk kuwa da yasan abunda Abdulhamid yake ba abun kwarai ba ne, amman yana tunanin ya tona masa asirine saboda ya saka Halima ta so shi kuma ta guje Abdallah, miyasa da ya gano haka ne be fadawa Halima a sirrance ba sai a san yadda za a bullowa lamarin, amman ya zabi ya tozarta shi haka wanda silar hakan ga mahaifiyarsa a kwance tana fama da jinya. Idan har Ahmad zai iya kitsa cuta a zuciyarsa kamar haka then be yi deserve ya aure Halimatu ba, domin shi ma ba a san iya abunda yake sakawa a zuciyarsa ba kuma ba a san abunda yake a karkashin kasa ba, ya fada masa sai ya nuna masa shi din ba kowa ba ne a gurin Halima that's for sure sai yayi, duk abunda yai ko zai yi zai tashi a tutar babu ne, ko mazan duniyar nan sun kare he don't think zai bar Halima ta auri Ahmad, rayuwarsa tana nuna masa babu wanda ya cancanci Halima sai shi, duk da ya san Hajiya ba zata bari ba a yanzu wata rana zata bari, so zai jira har zuwa lokacin da zata yarda but right now all what he want is yai magana da Halima. Tun da har Ahmad ya saka bakinciki a zuciyar mahaifiyarsa shi ma sai ya saka a tasa zuciyar, sai ya nuna nasa kudinsa da wata isarsa ba su isa su siya masa soyayyar Halima ba.
“Duk yarinyar nan ce taja komai nasadinta komai ya faru, sam babu alheri a tare da ita, bata nufar mu da khairan ai sheran”
Hajiya ta fada tana kokarin dora laifin akan Halima a ganinta sanadinta ne asirin Abdulhamid ya tonu har haka ya same shi, domin shi mutumen daya shige gaba akai bincike aka tona asiri saboda Halima yai dan haka komai ma ya faru ita ce sanadi. Abdallah dai be ce komai ba sai saurare kukan mahaifiyarsa yake.
“Da na san haka zai Faru Wallahi da tun farko ban bar shi ya aureta ba, Halima ta zame mana fitina a cikin iyali, ta lalata mana komai na rayuwa Allah ya isa tsakanina da ita, ban san me nai mata ba ta tattara duka farincikin nawa ta dauke, ta tarwatsa mana komai har ta kai yau ga ni kwance saboda bakincikinta”
Sai a wannan karon Abdallah yace.
“Laifin wannan dan iskan ne, shine yai komai ai”
“Amman ai sanadin ne ko? Waya sani ko ita ta saka shi ma”
“Amman ai ba ita ta saka Abdulhamid a wannan harkar ba”
“Ko ba ita ta saka shi ba, asirinsa saboda wa ya tonu? Allah yana son mai rufawa dan uwansa asiri, idan ba dan su kunyata mu ba taya za su nemi yi masa wannan cin mutuncin”
Shiru yai yana jin tsanar Ahmad tana kara hauhauwa a zuciyarsa.
AHMAD POV.
Be taba yarda da gaske yana son Halima ba sai yau, domin farinciki da yake ji a tare da shi ya wuce misali. Taya zai kwatanta yadda yake jinta a zuciyarsa na amincewarta kawai ashe daman tuni ba tausayinta kawai yake ba har da son ta, driving yake amman gaba daya hankalinsa yana gunta after every one minute sai ya kalleta with smile on his face. Wani irin abu yake jin yana masa zillo a zuciya babu abunda yake ayyana aransa sai idan ya kai kasance a mijinta ya zai tsinci kansa? A hankali ya busar da iskar bakinsa ya kalleta wannan karon idanuwansa sun samu masauki a cikin idonta, sai tai saurin kawardar idonta shi kuma yai murmushi ya cigaba da tukinsa har suka iso cikin unguwar.
“Ya isa”
“Why?”
“Ba sai ka kai ni kofar gida ba, zan sauka a nan”
“Okay Lims komai kike so shi zan miki”
A gafen hanyar ya faka motarsa yana kokarin fita ta bude mata tai saurin budewa ta fita, sai da ta rufe motar sai ya sauke gilashin motar ya kira sunanta.
“Lims...”
Jimm tai kamar ba zata juyo ba sai kuma ta waigo ta kalleshi a tsorace.
“I love you...... I love you so much.... And i know i love you.....”
Kasa cewa komai tai kuma ta kasa matsawa daga inda take, kamar yadda ta kasa dauke idonta daga barin kallonsa, kallonta yai for few seconds sannan yai reverse ya juya ya koma inda ya fito, sai da ya fita daga unguwar sannan ya dauki hanyar gidansu cikin wani irin farinciki marar misaltuwa, abunda be taba saka ran samu ba. After yayi parking habarbar gidan ya fito yana wasa da makullin hannunsa ya nufi part din Hajiya. Kamar ya san shi suke jira yana shiga Siyama ta taso ta sauri ya rumgume shi.
“Congratulations”
“Thank you Sis”
Ya saketa ya nufi gurin mahaifiyarsa kamin tace komai ya rumgume ta.
“Na gode Hajiya, you're such a wonderful Mom, thanks for everything”
Ya saketa ya zauna kusa da ita yana kallonta.
“Na fi kowa farinciki a yau, kasan saboda me? Ka nemo matarka da kanka, kuma wacce kake jin ta kwanta maka a rai, duk a baya ma ma san kana nemo amman sai matsala ta shiga ciki, to wannan karon bana fatar sake faruwar wani abu, a duk macen da zaka aura na kan jin kamar zata malleka ka ta kwace ka ne, amman wannan yarinyar ina jin natsuwa sosai a tare da ita, na dade ina maka fatar auren bazawara musamman irin wannan mai hakuri, domin wasu zaurawa wahala ce take fito da su daga gidanjen mazajensu wasu kuma kishiyoyine suke fito da su, duk mace da zata taba aure ta fito tai zaman zawarci ba tare da ta zubar da mutuncinta ba, hakika wannan matar abar girmamawace domin zawarci abu ne mai tsada kuma mai wuyar sha'ani, duk mace da tai zaman aure ta fito tai zaman zawarci to tayi rayuwa ne guda biyu mabanbanta, akwa challenges da yawa a rayuwarta, tun daga kan uwaye yan uwa masu neman aurenta yayanta mijin da ta fito gunss ko ya rasu, zaka tarar ta fuskanci kalubale, wanda a gaba idan za tai aure zata jure hakuri domin samun ribar auren, akwai fa'ida sosai a auren bazawara Gwarzo sai a yanzu zaka sani”
Ya hade yawun bakinta sannan ta sake kallonsa tana murmushi.
“Abu na biyu kuma ina tunanin lokaci yayi daya kamata ace na bar ku kun tafi duk inda kake so kai da matarka kui rayuwarku yadda kuke so”
Yayi saurin girgiza mata kai.
“Nonono Hajiya, Wallahi ba zan iya ba a yanzu ne kika fi bukatar na zauna a tare da ke, ko ba komai Siyama mace ce zata tai aure, gidan wani zata je ni kuma aurowa zan yi na kawo, akwai abubuwa da zaki bukata wanda dole ni ko matata ne za mu yi miki, ba ki da wani zabi daya wuce ki bar mu mu zauna a tare da ke”
“Idan kuma ita bata so fa? Wasu matan basa son zama da iyayen miji na sani, musamman ma irina”
“Me zai hana ta so? Halima tana da hankali, zata so zama da ke Hajiya, kuma ai kowa da part dinsa ba part daya ba ne, to me zai saka dukanku ku takura?”
Murmushi tai.
“Allah yai maka albarka ya hada kanku ya sa wannan auren alheri a tsakaninku”
Shi da Siyama suka amsa da amin.
“Na fada mata yai magana da mahaifiyarta domin sanarwa duk wanda ya dace, saboda ina son a cikin satin nan na san an tsayardar maganar”
“Ouhhhhh Yaya da sauri haka?
Cewar Siyama sai ya kalleta yana murmushi yace.
“I swear to Allah ji nake kamar da na yi sake kadan kamar haka zan iya rasata, idan son samu ne ma idan anje tambaya a daura auren a can, idan ya so duk wani shirye shiyen sai ya biyo daga baya, idan ma tace ba zata tare ba sai da da shekara ba ni da matsala”
Siyama ta tsire baki.
“Wannan Lims din dai ana ji da ita”
Hajiya ta yi murmushi tana kallonsa.
“Kana da abokin takata ne hala?”
“Yes Hajiya kin san mace ko bata da kyau ai bata rasa masoyi, balle ita kuma akwai wani cousin dinta da nake tsoron sherinsa kuma kin san cousins ba su da kyau”
Gaba dayansu sukai dariya har shi.
HALIMATU POV.
Na manta rabon da wani ya furta min kalmar so haka kai tsaye, gaba daya sai na ji kamar ya sare ko wace gaba ta jikina, kalmar tai min nauyi a zuciya har ta sauko min a kirji. Gaba daya rayuwar yau ta zame min kamar mafarki at first na tafi office na tararda abunda ban yi zato ba kuma na amince ba akan cilas ba kuma ba dan zuciya tana ki ko tana so ba. Da kafa na karasa gida sai dai ban labarta wa kowa komai ba ciki kuwa har da mahaifiyata, to idan ma zan fada mata ta ina zan fara? Me zan fada mata? Yarana ya zan ce musu? Zai karbe su kamar ubansu? Ko kuma zai musu na Abdulhamid ne? Miyasa ban tambaye shi duk wannan ba na amince masa zan aure shi? I don't think na shirya yin wani auren na bar yarana.
Har akai sallah isha'i ina ta tunani daya, bayan Mama ta sallame sallah na tashi na koma kusa da ita na zauna sai kuma na kasa cewa komai.
“Wata maganar kike son yi?”
Kasa nai da kaina gabana na faduwa sosai na ce.
“Mama yanzu idan nace zan yi aure be yi kusa?”
“Kin taba ganin mace tai kusa da aure ko ta makara?”
“Ba haka ba ne, ina tunanin rayuwar na da fito ne”
“Idan kina kallon rayuwarki ta baya, to har a bada gobenki ba zata taba yin kyau ba, ki yi fatar samun gobe mai kyau, ke a yanzu kamar kan titi kike idan kika ce za ki tsaya waiga bayanaki to mota zata zo ta gabanki ne ta kade ki ta takaki tai miki illa, amman idan kika fuskanci gaba sai rayuwarki tai kyau fiye da yadda kike tsammani, shi bawa ba a son yana yanke kauna daga rahamar Allah”
“Mama na yi wani abun da nake jin kamar ban yi daidai ba, Ahmad ya nemi aurena kuma na fada masa cewar na amince zan aure shi sai dai a yanzu ina ta jin damuwar amincewar da nai, saboda yarana...”
Ina kai aya na ga Mama na murmushi.
“Bayan kin amince kuma shaidan yake son raya miki wani abu a zuciya? Ko yanzu ai lokaci be wuce ba za ku iya yin magana, amman dai duk mutunen da zai rika yayana ai kana gane shi ne tun gida, bana tunanin Abdulhamid ya taba daukar yaranki ko sau daya ne a mota? Amman Abdallah da shi wannan har makaranta suka saka su, kina tunanin mutumen da zai san abunda ya faru da ke da halin rayuwar da kika tsinci kanki a ciki zai yi tunani saka ki cikin wani kunci?”
Kallonta nai a raunace na ce.
“Mama wasu maza suna da son kansu ne, kuma idonsu kan rufe har sai sun samu abunda suke so”
“Haka ne, amman shi aure fahimtar juna ake so a ciki, za ki iya samunsa ku tattauna, idan ya aminta falillahil hamdu idan kuma ya nuna miki ba haka ba zai ki sake wata shawarar”
Mama tana da gaskiya matsalar yara mai sauki ce domin zan iya magana da shi akan. Har na bude baki an sake wata maganar sai muka ji sallamar Abdallah, daga uwar dakan da muke muka amsa masa yanayin yadda Mama ta kalleni kana gani kasan mamakin ganinsa take, ni kam na san da zuwansa. Tun da ya shigo idonsa na kaina har ya gaisa da Mama be daina kallona ba, idan sabo kuma na saba da irin wannan kallon daga gurin Abdallah. Bayan sun gaisa Mama ta tashi ta fice daga dakin sai ya rage daga ni sai shi ne a ciki. Shiru ne ya biyo baya be ce min komai ba ban ce masa ba, can ya ciro wayarsa ya soma latsawa.
“Me ke tsakaninki da Ahmad Gwarzo?”
Kamar daga sama na ji tambayar, ba zan yi mamaki ba idan Abdallah yai kishi daman ya saba kishina tun da yana so na.
“Babu komai”
“Yaushe muka fara haka da ke?”
Ya fada yana kallon irin kallon nan dake nuna da gaske yake.
“Ba karya nake ba, babu komai tsakanina da shi”
“To idan ke baki da wata manufa akan shi shi yana da ita akan ki”
“Kamar yaya”
“Son ki yake mana ko be taba fada miki ba?”
Na yi shiru kamar na ce masa ya fada min a yau har ya nemi amincewar aure na kuma na amince sai kuma wata zuciyar ta hana ni domin na san abun ba zai yi ma Abdallah dadi ba.
“Be kamata ki karbi soyayyar wani ba a yanzu Halima, wanin ma kuma Ahmad Mutunen daya dora miki laifin kisa sanadin hakan kwakwalwarki ta tabu, a iya tunani yanzu kin yi hankali kina da tunanin ya kamata ki gane mai miki so ya gaskiya ki aure shi”
“Kai kake min so n gaskiya Abdallah na sani, amman kuma aurenka abu ne da ba zai yiyu ba”
Gyara zamansa yai yana kallona.
“Kamar dai ba ke ba Halima yau ke da kanki kike fadar aurena ba zai yiyu ba”
“Saboda Hajiya da Abdulhamid”
“Hajiya idan zamu iya bata lokaci zata fahimta”
“Ba zata taba so na ba Abdallah har kasa ta nade ba zan taba zama fara a gurin Hajiya ba, bana son na sake aikata wani kuskuren idan na aureka a yanzu mutane za su zage mu Abdulhamid kuma zai ga cewar bamu kyauta masa ba”
“Gaba daya ya canja miki tunani Halima, ya dauke miki hankali, ya chusa miki wasu abubuwan da babusu akan ki, amman ya kamata ki yi tunani ko da ba zaki aure ni ba be kamata ki auri Ahmad ba, bakinsan komai akansa ba, Halima bana son alaka tana shiga tsakaninku, idan har zan roki wani abu ku yi a yanzu to zan roki ki aje aikin nan a kamfaninsa”
Ya fada da kamar fada har yana nuna ni, Yanzu kam bana jin Abdallah ya tsani Ahmad saboda ni kawai wata kila har da abunda yai ma dan'uwansa, sai dai duk kusanci ni na Ahmad be kai da Abdallah ba duk irin taimakon da zai min yana bayan na Abdallah, idan har Abdallah zai ce kar na auri Ahmad Wallahi zan iya ko dan na faranta masa ne balle kuma aje aiki wanda shi ya fi komai sauki a gurina tun da har ya bukaci haka, bana jin akwai wani abu da Abdallah zai bukata a duniyar nan na kasa masa ko da kuwa raina ne, balle abunda ran ya mallaka.
“Zan aje aikin gobe In-Sha-Allah”
Na fada ina kallonsa, ina kallon lokacin daya ja dogon numfashi ya sauke sannan ya busar da iskar bakinsa ya mike tsaye ba tare da ya ce min komai ba ya nufi kofa, sai kuma ya juyo ya kalleni ido cikin ido.
“Wallahi ina son ki Halima”
Wani tausayinsa ne ya kamani da kuma tausayin kaina a lokaci daya.
“Ba wai kaddarar mu ce kawai a haka ba, rayuwarmu ce, wata kila idan mu kai hakuri za mu iya cin ma nasara....”
Shine abunda ya fada sannan ya fice daga dakin, ni kuma sai na nemi jindadi na rasa, taya zan kalleshi na fada masa cewar zan auri Ahmad? Ya zai ji? Ya zai kalli abun? Zuciyarsa zata iya dauka? Ashe da na ce zan rayu da kaunarsa ba zan iya ba? Kar idona ya rufe na sake aikata abunda be dace ba, da gaske Ahmad ya cancanci zama abokin rayuwata ko kuma wata kaddarar ce take bibiyata? Gaba daya sai na kasa ganewa, kamin na ankaro hawaye ya fara wanke min fuska.
Ban kwanta ba sai da nw labartawa Mama abunda Abdallah yake bukatar nai na aje aikin.
“Kuma za ki aje?”
“Mama kina tunanin akwai abunda Abdallah zai nema a gurina da ba zan masa ba?”
“Halima karki yarda ki sake aikata wani kuskuren, wannan karon bana jin kaddarar ce sai dai son zuciya, domin komai a bayyana yake auren Abdallah a gareki ba zai yiyu ba, ni kaina ba zan bari ba, ba zan hana ki aje aiki ba amman kar alakar Abdallah ta shafi alakar da ke tsakaninki da Ahmad, kar kuma ki bari alakar da ke tsakaninki da Ahmad ta shiga tsakaninki da Abdallah”
Shine abunda ta fada min sannan tai shirin kwanciya. Ni kuma na tashi na koma dakina na kwanta cikin yarana, ina ganin kiran Ahmad na shigowa wayata amman ba kasa dauka. Washe gari ko su Namra ba su riga ni fita daga gidan ba ba dan zan aje aiki kadai ba sai dan na gujewa shiga motarsa kamar yadda ya fada zai rika kai ni yana dauko ni kullum wanda hakan na san ba karamar matsala zai ja min ba, ko da takwas tai ina cikin office dina sai dai yau an kwashe komai kamar ba gurin da aka jera rose ba a jiya. Na zauna saman kujera ina ta tunanin yadda zan fada ma Ahmad cewar zan aje aiki na san dole zai tambaye dalili. Ina jin wayata ta yi ringing na dauko ya duba number shi cikin sauri nai picking.
“Morning Lims”
“Morning too”
“Ga ni kofar gida fito muje”
“Ina office”
“Amman ba na fada miki ni zan rika kai ki ba?”
“Akwai maganar da nake son nai da kai mai muhimmanci”
“Okay Babe gani nan zuwa”
Ya yanke kiran ni kuma na aje wayar ina ta kallon hoton yarana da ke screen din wayar. Ba a dauki lokaci mai tsawo ba sai ga shi ya turo kofar office din fuskarsa da annuri.
“Karki sake min irin wannan game din seriously bana son kina hawa Napep”
Uffan ban ce masa ba, duk kuwa da na san ba zan iya dauka ba taya za a ace kullum ya kawo ni aiki ya maida ni, ko da yake aje aikin