Showing 72001 words to 75000 words out of 217237 words
yi wannan maganar a yanzu ba, za ki kara sakata cikin damuwa ne, kar ma ki kawo ma Abdulhamid wannan tunanin dan Allah, ki aje wannan maganar na gafe”
“Wallahi ba zan aje ba, dan ba zan yarda ta cutar min da ɗa ba”
Tana fada hakan ta kashe wayar. Zaunawa yai a kujerar ya dafe kansa.
HALIMATU POV.
Da yamma Abdulhamid ya shigo asibitin, shi ma na ga damuwa da tausayi a fuskarsa da kuma kulawa a mu'amalarsa. Ni kuma na kasa sakewa da shi ko da na minti daya, irin kallon da nake ma Aminu na ke masa a yanzu. Bayan magariba polices suka zo suka suna min bincike sai a lokacin na yi dauriyar da na bude bakina na rika amsa musu tambayoyinsu, sun tambaya ko zan iya gane mutane na amsa musu da a a domin fuskokinsu a rufe suke kuma muryarsu ma a boye take, sun dauki duk bayanin da ya kamata su dauka sannan suka tafi.
Kwana na biyu a asibiti suka sallame ni ganin na samun sauki, sai dai a cikin magunguna da suka ba ni har da na hawan jini kamar yadda suka fada min cewar ina da shi, a ranar da zan koma gidan mijina sai na ji kamar zan koma a cikin wata duniyar ta dabam, domin a asibitin ina ganin mutane familyna abokaina da kuma yayana suna cire min kewa ba kamar a yanzu ba da zan koma ni kadai.
An gyara komai a gidan kamar babu wanda ya shigo, kofar ma an canja ta kamar yadda aka canja gate din, har na shiga dakina Abdulhamid be ce min komai ba, ni ma kuma ban ce masa ba, daman kuma ni me zan fada masa? Ce masa zan yi ka yarda da ni? Ko na tausaya min? Ko kuma ya zo mu yi kuka tare? A daren ranar ji nai kamar ba zan iya bachi ba dan haka na tashi nemam maganina da ke saka ni bachi amman ban samu ba. Na tsorota sosai rashin ganin maganin da nai domin na san akwai wanda ya ga maganin har ya saka hannu ya dauka. Wanin kuma ba zai wuce Abdulhamid ba domin shi kadai nake da tabbacin zai iya bincika duk abunda yake so a gidan nan.
A haka na kwana bachi ba bachi ba, minti daya biyu uku na farka, kamin ya sake daukata kuma sai an dade, da safe shi ya shirya mana abun karyawa da kansa ya shigo ya tashe ni na fito falo, amman sai na kasa cin komai, shi kan ya ci biredi ya sha tea sannan ya tambaye ni akwai wata matsala? Ko abunda na ke bukata na girgiza masa kai.
“Okay zan aiko miki da takeway da rana, da dare ma idan za a dawo zan siyo mana wani abu, me kika so ki ci?”
“Bana bukatar komai”
Kallo kawai yai ya dauke kai ya shiga dakinsa ya shirya ya fita. Daga lokacin sai zanantakewar mu ta sake sauya sabon salo baya bari nai girki sai dai ya siyo mana abinci, na sa yana min hakan ne domin ya nuna min ya damu da ni bayan kuma ya kasa kwanta a gadon da nake kwana kamar da, ya kasa sakewa da ni kamar da, sai yawan kallona da yake kamar mai tunani, zuciyata na raya min be natsu da ni ba, wani lokacin ina jin kamar barin gidan shine mafita a agare ni da kuma shi, Har nai sati da sallamowa Hajiyarsa bata sake daga waya ta kira da sunan ta tambaya ya jikina ba balle har ta zo ko ta aiko a dubani, Abdallah ma tun a lokacin da ya miko min waya a asibiti ban sake jin duriyarsa ba, ba ma wacce ta fi ba ni mamaki kamar Suwaiba matarsa wacce bata zo ba kuma bata kirani ta tambayi lafiyata ba balle tai min jaje, abun har ya daure min kai wata kila kuma ita ta fara bin bayan Hajiya ne wajen tsanata duk da ban san na musu komai ba, ni kam bana dacewa da iyyen miji, haka uwar Aminu da kanensa suka tsane ni, ko da yake bana da sa'a da dacen rayuwa shiyasa saka hakan yake faruwa da ni.
Bayan mun gama cin abincin dare ya fada min cewar na shirya gobe za mu je asibiti, be fada min dalilin zuwan ba ni kuma ban cire tsammanin wani ko wata za mu je gani ba, ashe abunda ban sani ba gurin gwaji zai kai ni gwaji zai kai ni, mamaki ya cika ni, har na kasa boye damuwata da kuka a lokacin, sai dai ban ce masa komai ba duk kuwa da kasancewar a yanzu na kara katsewa da lamarinsa. Mijina be yarda da ni ba kenan.
“Zanje office na dawo kamin a gama, saboda akwai layi sosai”
Kai kawai na iya gyada masa na bishi da kallo har na daina hangoshi. Miyasa ba zai fada min naje nai gwajin ba? Mi yasa ba zai fada inda za mu je ba tun jiya? Idan ma aka samu ina dauke da hiv ko wata cutar Abdulhamid rabuwa zai yi da mi kenan? Lallai na sake sarewa da lamarin maza!
Ina zaune a gurin ina bin layi hawaye na min zuba har aka kawo kaina, duk wanda ya gan ni a cikin wannan yanayin zai yi tunanin ko ina tsoron kar ace ina dauke da cutar ne. Bayan an dibi jinin nawa na fito na baro asibitin ba tare da tsayawa sauraren komai ba, ba fargaba nake kar ace ina dauke da cutar ba, na kasa raba dayan biyu a tsakanin neman Abdulhamid ya sake ni ko kuma na cigaba da hakurin zama da shi? Da kafa nake tafiya ina ta kallon ababen hawa da mutanen da ke kai kawo ba dan bana da kudin napep ba sai dan ina jin kamar tafiyar kasa zata sama min sassauci, ban san inda zanje ba tafiyar kawai nake duniyata na juya min. Wayata na ji tana ringing alamar kira ban tsaya komai ba na saka hannuna a jaka na fiddo wayar ba tare da na duba sunan mai kiran ba nai picking.
“Kin fito daga asibitin ne?”
Muryar mai kiran ta karantar da ni ko waye ne.
“Na fito ina bakin titi”
“Bakin titi gurin me?”
“Ban sani ba....”
Na amsa ina jin kuka kamar zai kubuce min.
“Daidai ina kike tsaye?”
Waigawa nai na duba hagu da damana sannan na soma masa kwantanci.
“Ina kusa da Exclusive City”
“Okay shiga ciki ki zauna ga ni nan zuwa”
Kai na gyada masa kamar ance yana kallona sannan sauke wayar na share hawayen da suk zubo min na nufi Exclusive City din, babba guri ne na manyan mutane yan kasaita, gurina da masoya suka fi zuwa saboda tsarinsa da kuma abubuwan kawa da aka tanadar a gurin ga abinci kala kala, haka na ke jin ana yawa fada duk da ban taba zuwa ba sai yau.
Duk sai na ji dabam abun ka da wanda be saba ba, duk kuwa da kasancewar gurin kowa be kula da kowa ba, akwai guraren zama da yawa amman sai na ji na tsawwala kamar ba zan iya zama a gurin ba.
“Akwai wanda kike jira ne?”
Daya daga cikin ma'aikatan gurin ne yai min tambayar yana sanye da rigar aikinsa.
“Aa ina son na zauna a gurin da babu mutane sosai”
“Okay ga vip 1 can ga kuma vip 2 can, za ki iya zama a daya daga ciki”
Ya fada yana nuna min vip 1 da ke kasa da kuma 2 din da ke sama, zuciyata ta fi natsuwa da 2 din ganin shi a sama yake kuma bana iya hango komai daga inda tsaye hakan na nufi na cikin ne zai iya hango na waje, tsabanin na waje da ba zai iya hango wainar da ake toya a cikin ba. Kai tsaye na nufi hanyar da zata kai ni VIP 2 din, ina shiga na samu gurin fiye da yadda nake tsammaninsa domin tsakanin wani teburin da wani a akwa doguwar tazara ga kamshi da iska mai dadi na kadawa, komai na gurin ja ne gwanin sha'awa sai wani dan sauti da ke tashi mai dadi ta taba zuciya mai kuma daidai da kowane irin yanayi.
Ko wane tebur kujera uku ce zagaye da shi amman ban da tebur daya mai kujera biyu masu fuskantar juna. Zuciyata ta fi natsuwa da shi fiye da sauran hakan yasa na nufi gurin na ja kujera daya na zauna. Wata irin natsuwa ta sauko min ba natsuwa irin ta masu kwanciyar hankali ba, natsuwa da samun damar yin kuka issasshe ta samu damar tausayawa, ta samu damar yin tunani da kuma nemawa kai mafita....!
7/21/21, 10:44 PM - Buhainat: *GOBE NA...*
By Khadeeja Candy
2️⃣5️⃣
“Abun nan fa ya wuce iya abunda kike tunani, Wallahi mutanen nan ba za du yi karya ba, kuma ga zahiri kina gani, abubuwa sai kara kwabewa suke”
Aminu ne yake wannan maganar yana shafa kansa cikin tsananin damuwa, hannunsa na dama rike da takardar transfer.
“Iko sai Allah, ni wani abun yana bani mamaki Wallahi, taya za ka biye maganar bokaye? Tun farkon fari ma mi ya kai ka gurin ya saka tsinbo? Da har za su fada maka karya da gaskiya ka yarda”
“Hajiya ai dubiya yanzu babu wanda yake zaune, ba maza ba mata ba kowa kuma yadda lamurran nan suka fara lalacewa ai dole na saka a bincika min, ba ni kadai ba ko Alfa da ya kai ni sai da abun ya daure mata kai”
“Allah kadai ya san gaskiyar wannan lamarin wata kila ma gurin malaminta ka fada, ko kuma shi alfan yana goyon bayanta ne, shiyasa suka hada kai ai maka haka”
“Babu wani zancen goyon baya Hajiya fa a zahiri kike ganin komai sai lalacewa yake”
“Kai fa baka iya tashin hankali ba, kai yanzu dan Allah Aminu har ka kawo maganar dawowa da Halimatu a gidanka? Mace da bata kaunar uwarka bata son yan'uwanka? Ka duba ja ga har kazafi tai wa Sadi fa? Wallahi har a bada ba zan taba son Halimatu ba”
“Hajiya abunda ba ki sani ba, ko wane dan'adam yana da good side of him kuma bad side, Wallahi Hajiya ba dan ina son dawowo da Halimatu ba, acire zancen arziki, Hajiya Halimatu ta fi Murja hakurin zama da ni, Halima ko bata son abu bata nuna, sannan ko fada nai mata ko na ci zarafinta sai dai tai kuka ta ba ni hakuri, and tana kokarin ganin ta gujewa bachin raina, zan iya tafiya inda nake so nai iya adadin kwanakin da nake so na dawo bata ce min komai, amman ban isa nai ma Murja haka ba Wallahi Hajiya, idan na dawo tara na dare Wallahi sai Murja ta yi min fada, amman a lokacin da Halima take nan zai iya kai wa 1 na dare a waje kuma ba zata ce min komai ba, Murja ta bi ta saka min ido akan komai nawa, ba ni d sukunin daukar waya na latsa a cikin gidana idonta na kai”
Hajiya ta saki baki.
“Ban gane idan kai dare tai maka fada ba? Uwarka ce ita? Ita ta aje ka ko kai ka aje ta da zata maka fada? Ita ba mata ba ce da ba zaka mata magana ba”
“Hajiya ba za ki gane ba ne, idan ranta ya bace, jikina har rawa yake Wallahi”
“To acan gurin malaman da kaje ba su fada maka komai akanta ba?”
“Me za su fada min? Ni yanzu ba ta nata nake ba, ta Halimatu na ke domin sun fada min matukar ban mayar da ita ba, ba zan taba ganin komai daidai ba, kuma ga alama nan kina ganin bayan rage min mukami da akai yanzu an min transfer zuwa enugu, duka duka yaushe ne rabuwar mu? Idan aka kara dadewa kila ma bara zan koma, tun da sun ce ita ke da kashin arzikin duk abunda na samu saboda ina tare da ita ne, ni da farko ma na dauka ko sammu ne kai mi shiyasa ma har na biye ta Alfa ya kai ni gurin ashe ba asiri ba ne rabuwar da mu kai ce, Hajiya ki duba fa ki ga abun hawa ma neman gagara ta yake, motata na mata gyara uku abunda ban taba ba, yanzu na siye sabuwa ita ma engine dinta ya tsaya, sabuwar mota fa Hajiya Motar miliyan biyar ace engine dinta ya tsaya”
“Wai kana nufin ba da motar ka zo ba?”
“Wallahi Alfa ne ya sauke ni bakin gate, tun jiya motar ta tsaya tana can gurin ma su gyara”
“To abun nan fa d daure kai ni na fi zargin sammu gaskiya, asiri ne akai maka, ko ita ai zata iya maka asirin na ka lalace tun da ta ga ka sake ta, ko kuma abokan aiki ko makota”
“Hajiya Malami hudu msgana daya suke, babu wanda yace asiri ne, ni dai ki taimaka min ta dawo dan Allah”
“To ai ban ga ta inda zan iya taimaka maka ba, matar nan fa ma aure tai gidan wani take”
Dafe kansa yai.
“Kai Hajiya, ko wane da idan yana cikin matsala gurin uwarsa yake zuwa ta sama masa mafita, amman ke sai kokarin kin yarda kike da ni”
“Ba yarda ne ban yi da kai ba, nawa binciken zan yi akai”
“To ki kara bincika mu ji idan za a samu results daya, ni yanzu yarana nake son na fara dawowa da su hannuna, na san ina dauko yaran nan hankali zai dawo kaina dan bata hada su da kowa ba”
“Tana son su za tai aure ta bar su?”
Cewar Hajiya tana tabe baki.
“Wannan ai na dabam ne, idan naja yaran a jikina na nuna musu su janyo uwarsu ai dole hankalinta ya dawo nan, Wallahi shegen son ya'ya ne da ita Allah kadai ya san yadda akai ma tai aure ta bar su”
“Kudi ta bi, shi wanda ta auran ba ance dan uwanta ba ne kuma mahaifinsu ya bar musu dukiya, ai kudi babu abunda basa sakawa, ni ganin na ke komai kai ba zata bar wacan mijin ta dawo maka ba”
“Zata dawo ai kin dan yadda take so na, kuma daman first love shine so ai, kuma ni na san Halima na so sosai Wallahi, zata dawo da gudu ma”
“Uhm... ”
Mikewa yai tsaye.
“Motarki na nan Hajiya?”
“Wallahi na aiki Musa direba da ita Mafara sako zai karbo min, ka kira Sadi ya kawo maka motarsa daya mana ai mota biyu ne da shi”
Ba musu ya koma ya zauna ya ciro wayarsa ya kira kanensa Sadi. Ringing biyu zuwa na uku ya daga.
“Sadi kana ina?”
“Gani kusa da gidan Hajiya”
“To ina gidan karaso ka sauke ni gida”
“Okay”
Bayan na sauke wayar, Hajiya ta cigaba da yi masa maganar so take ta karkarto hankalinsa da barin zancen maido Halimatu domin ita a ganinta ba mafita ba ce, zuciyarta ta fi natsuwa da sammu akai masa ko dai Halimatun tai masa ko kuma wani dabam, ba a wuce minti ashirin ba Sadi ya shigo gidan cikin sabuwar shadda light yellow da hula kubu sai kamshin turare yake. S tsaye ya gaisa da Hajiya domin shi ma a hanya yake akwai inda yake son zuwa.
“Gida zaka sauke shi”
“Ina motarka ne?”
Sadi ya tambaya yana barin kallon Hajiya wacce tai masa maganar.
“Wallahi ta samu matsala wai engine dinta ta buga”
Aminu ya fada cike da damuwa a fuskarsa.
“What, motar da ka siyo satin nan ko dai wacan tsohuwar”
“Tsohuwar ai siyar da ita nai, wannan dai sabuwar”
“Garin ya?”
“To ni ina ma zan iya cewa ga dalili, abubuwan ne dai sai hamdala”
“Allah ya kyauta, tashi muje”
Sai da Aminu da Hajiya suka amsa da Amin sannan ya mike tsaye suka fice tare. Har gida Sadi ya kawo Aminu, bayan ya bude motar ya fita Sadi ma ya bude ya fito wai bari ya gaisa da Madam. Aminu na shiga cikin falon Murja da taso da sauri ta rumgume shi tana masa oyoyo sai shagwaba take zubawa kamar wata karamar yarinya.
“Ina tare da shi fa Hajiya”
“Dan kana tare da shi sai ya hanani nunawa mijina soyayya?”
Murmushi Sadi yai ya dauke idonsa ya nufi kitchen.
“Bari na sha ruwa”
Kitchen din ya shiga da kansa ya dauko cup ya bude freezer ya dauko robar ruwa ya bude ya soma bulbulawa. Kamar daga sama ya ji am rumgume shi ba shiri ya dire ruwan da yake sha ya juyo da sauri yana kallon kofar kitchen din.
“Kai dan Allah sarkin tsiro, ya shiga dakinsa”
“Amman ai zai iya saukowa yanzu kuma ya shigo nan”
Ya fada da rada hankalinsa a tashe yana kallon kofar kitchen din dan ya san the worst thing da zai aikata shine ya bar dan'uwansa ya san alakar da ke tsakaninsu.
“Ka daina zuwa kwana biyu, i miss you”
Ta fada tana dora hannunta a saman lips dinsa sai lumshe ido take da fake eyelashes dinta.
“Murja alakar mu ta da ba kamar ta yanzu ba ce fa, saboda dan'uwana kike aure dole nai tsaka tsantsan”
“Auren dan'uwanka ya hana alakar mu cigaba ne? Tun farko ba kai kaja ba, da aka aurena zan auri yayanka ne, sai wani kwana kwana kake min jikina kawai kake so”
Saurin turarenta yai daga jikinss ya fito daga cikin kitchen din jin kamar motsin fitowar Aminu a falo, kai tsaye ya nufi kofa ya fice daga falon gaba daya. Dariya murja tai ta nufi dakin mijinta, da taimakonta yai wanka ya shirya cikin farin yadi marar nauyi sannan ta gabatar masa da abincin rana. Cin abincin suke yana ta sake2 yadda zai bullo mata, so yake ya fada mata cewar yana son ya dawo da yaransa a gidansa amman yana jin tsoronta, baya son bacin ranta idan ranta ya bace ji yake kamar zai mutu, ko motsi dai sai ya rasa natsuwarsa saboda tsoron abunda zai fito daga bakinta, haka Allah ya saka masa tsoronta kamar mutuwarsa, idan ranta ya bace har kuka yake mata gurin bata hakuri abunda be taba yi ma wata mace ba, ko Hajiyarsa baya tsoro yadda yake tsoron Murja.
AHMAD POV.
“Na dauko Baby Namra daga gidan Hajiya, ka dawo gida da wuri karka wuce 8”
Sai da ya hade yawun bakinsa sannan ya amsa mata ta okay.
“Yayi