Showing 162001 words to 165000 words out of 217237 words
cikin kwakwalwarsa, sun ce bashi magani zai dauki lokaci mai tsawo kamin ya samu lafiya kuma za a kashe kudi sosai, amman idan an masa aikin kuma aka yi a sa'a zai iya samun sauki cikin kankanen lokaci”
“Ba za a iya yi masa a nan ba? Zuwa india ai za a kashe kudi da yawa”
“To ke zaki kashe kudin ne? Ko kudin a aljihunki za su fito? Ko kuma kudin na ki ne? Are you the money or the money is yours? Ke kin fiye son shiga uku”
Ya fada yana mikewa tsaye ya nufi fridge din ya bude ya dauko lemun ya nufo inda nake.
“Already na fada musu su shirya komai daya kamata, kawai dai na fada miki ne just to let you know”
Ya miko min lemun, karba nai da mamaki a fuskata haka yake wani lokacin, daga abun arziki ina tausayin kudin da zai kashe sai ya ce min wai ba ni ce kudin ba, and look at him now kamar ba shi ne ya gama hade fuska dazun ba, sometimes yana abu kamar wani mai aljanu.
“Kamar mai aljannu ko?”
Jin ya fadi haka yana murmushi yasa nai saurin mikewa tsaye ina girgiza kai, a zatona a fili nai maganar har ya ji.
“No mai Al.... Jifai nake nufi....”
Na fada da sauri sai yai dariyar da ta bayyana hakoransa.
“Ashe na canka daidai yadda naga kin rike lemun daman na san gulma kike a zuciyarki ki ce wannan mutume kamar mai aljanu”
Nima dariyar nai sosai har idona ya cika da kwala ashe ma ba a fili nai maganar ba, canka yai ni kuma garin kare kaina sai na fallasa kaina. Murmushi yake yana kallon yadda nake dariya kamar ba ni ba.
“Cute you, dariya na miki kyau”
Daidaita natsuwata nai, na koma na zauna na rike lemun.
“Tashi muje mu ci abinci”
“No ana kawo min abinci a office everyday”
“Ba zaki koma office din nan ba sai gobe that's final”
Hannunsa ya kai ya dauki keys din dake saman tebur din.
“Amman handbag dina tana office din”
Sai ya miko min keys din.
“Je ki jirani a mota”
Ba musu na karba keys din na juya na fice daga office din, na san inda yake aje motarsa dan haka na nufi gurin kai tsaye na tsaya a gurin ina jiransa, be jima ba ya fito tare da wata mata wacce rike da jakata ta kawo min jakar shi kuma ya karbi keys din ya bude motar ni ma na bude na shiga front seat. Tun da ya kama hanyar restaurant din be ce min uffan ba sai dai lokaci zuwa lokaci yana kallon inda nake, ni ma kuma ban ce masa komai ba, zuciyata nata raya min abubuwa da dama har muka isa gurin.
Motar na tsayawa na bude na fito shi ma ya fito yai gaba ina binsa a baya, restaurant din da Abdulhamid ya taba cewa na tsaya a ciki na jira shi ce, wacce na shiga ciki na zauna a kujerar da Ahmad din ya rufeni da masifa saboda na zaunarna kujerar da ban san ta wacece ba a gurinsa.
A yau ciki muka shiga har vip din inda set din yake, da kansa yaja min kujerar, sai na kasa zama kuma na gagara cewa komai and na kasa dauke idona akansa, gabana sai bugawa yake da sauri kamar zai fito.
“Zauna mana”
Ya fada so calmly yana min wani irin kallo da na kasa natsuwa. Na zauna kamar yadda ya umarce ni amman kamar wata karago haka na zama, idan zan juya gaba daya zan juya idan zan juyo gaba daya zan juyo, kana kallo kasan bana cikin natsuwa ba kuma natsuwa irin ta wanda yake cikin tashin hankali ko zullumi ba ko fargaba ba, no natsuwa dai irin ta Wanda yake ganin wani abu kamar a mafarki.
“Me za a kawo miki?”
“Just water”
Na fada ina kallon waiter din.
“Kawo mana Jalof plate biyu da lemu”
Ya fada masa sannan ya kalli.
“Is hardly na ci abinci a public place like this, bana cin abinci a awaje yawanci Hajiya ta ke girka min, sai dai ina yawan zuwa gurin nan tare da mahaifiyar Baby lokacin da take raye just to make her happy, saboda ta saba zuwa gurin tun tana budurwa, a yau ma na san sai Hajiya tace min miyasa ban ci abinci a gida ba, kuma saboda ke ne, na zamu so nan ace me zaki ci ki ce ruwa ba, you must eat with me”
Magana yake min a hankali kamar mai kokarin fahimtar da ni. Wani abu nake hangowa a idonsa wanda nake kokarin karyata kaina kansa. Ba shiri na mike tsaye ya dauki jakata na rataya.
“I don't think i deserve this, ya kamata ka cigaba da mutunta kujerar matarka”
Ina fadar hakan ban tsaya komai na na nufi hanyar sauka daga gurin har ina sauri kamar zan fadi. Ina fitowa gurin na tari napep na shiga, hawaye suka fara sauko min, tsoro nake ji kamar Ahmad ya bijiro min da abunda Aminu, Abdulhamid, Abdallah, Abraham suka bijiro min da shi, idan ya tambayi so a gurina na amsa masa da a a ban kyauta ba, sai dai ni ban shirya ba, na gaji da halin maza, ba zan sake aikata kurskuren auren mutunen da zan yi kuka a karkashin igiyar aurensa ba.
Idan na tuna Aminu da Abdulhamid duk haka suka min kamin daga baya su saka ni dakin kuka su juya min baya, babu muhallin kowa a zuciyata a yanzu, idan har akwai wanda ya cancance ni a yanzu Abdallah ne, ba kowa ba, ba zan yarda Ahmad ya yaudare ni na fada soyayyarsa, a yanayin gidansu da irin girman da suke da shi, ba lallai ne idan ya aure ni ya ga kima ta ba, domin mu talakawa ne masu rufin asiri ba masu arziki ba, idan har mahaifiyar Aminu zata raina talaucin mu ya zama silar da ya saka ta kara wulakanta ni tana cewa ina kwashe arzikin danta ina kaiwa gidanmu ina ga mahaifiyar Ahmad?
Secondly idan Abdulhamid be iya hakuri da ni ya zauna da ni a gidansa da aka min fyade ba taya wani zan ji labarina da rana tsaya kuma yace zai hadiye ƙashi ya zauna da ni babu kyama? Shin idan ma na yarda wata kadarar ta sake samun a gidansa zai iya zama da ni ko kuwa shi ma juya min baya zai yi? No I'm not just ready.
Mai napep na isa kofar gidanmu sakon kar ta kwana na shigowa wayata daga number Ahmad.
“Miyasa kika ce baki cancanci haka ba? Miyasa kika tafi kika barni? Why kike jin tsoro? Mi zuciyarki ta raya miki a kaina?”
“Nothing, you're just my friend”
Ita ce amsa da na bashi bayan na karanta sakon, sannan na share hawayena na fita daga napep din.
“No I'm not just your friend”
“I'm not”
Ita ce amsar da ya maido min a take. Sai kawai na goge sakon, na sallame mai napep na shige gida, kallo daya Mama tai min ta fahimci damuwa, tai ta min tambayoyi a gurin aikinki ne ko a Abraham din ne domin na dade da labarta mata komai akansa, sai kawai na ce mata babu komai.
Misalin tara da wani abu na dare, Aminu ya kira wayata, rabon da na ga kiransa a wayata har na manta, kusan tun da Ahmad ya saka aka mai masa duka be sake zuwa ba ko kirana ko da da sunan duba yaransa ne. Ba tare da tunanin komai ba na dauki kiran, sai ya sanar min yana kofar gida dan Allah na fito magana zai yi da ni.
Tashi nai na jari hijabina na saka na fadawa Inna wacce nake zaune a dakinta sannan na fita wajen, kusa da kofar gida na same shi zaune a cikin motarsa da ke fake. Tsaye nai jikin motar na ce.
“Gani”
“Ki shigo ciki dan Allah”
“Duk abunda zaka fada ka fada a nan”
“Maganar da zan yi tana da muhimmanci dan Allah ki taimaka ki shigo”
Jin haka yasa na bude motar na shiga, ina kallonsa sai na ga idonsa sun kumbura sun yi ja sosai alamar ya ci kuka ba kadan ba har ya sauya masa kala. Mun dauki lokaci mai tsawo zaune a cikin motar be ce min komai ba kuma ya kasa kallon inda nake, ni kuma mamaki ya cika ni ina tunani yau kuma da wacce ya zo.
“Yau ce rana ta karshe Halima, da zan daina rokon ki dawo gareni, a yau kan na yarda na rasa ki har abada, a yau na yarda na yi kuskuren da ba zai taba gyaruwa ba, a yau ina rokon Allah ya baki miji na gari wanda zai taimaki rayuwarki, wanda zai baki soyayyar da kika rasa a gidana, wanda zai nuna miki kulawa, ya fifita ki ya tausaya miki, wanda ba zai wulakanta ki ba kamar yadda nai yi.....”
Yai shiru sai kuma ya kai hannunsa ya kama hijabi ya jimkeshi sosai a hannunsa.
“Wallahi ji nake kamar na bude bakina na dauke ki na saka a ciki na hadeye ki zauna a cikina har a bada amman babu wannan damar, na riga na rasa ki har abada, ina son ki Halima ina son ki san da wannan ko bana raye, duk abunda nake miki a baya ina yi ne kawai ba dan bana son ki ba, ina yi nw kawai saboda sharin zuciya da kuma ajizanci na dan'adam, dan Allah ki yafe min”
Wasu irin hawaye yake yana kallona numfashi na fitar masa daker, a take jikina yai sanyi.
“A lokacin da kike fada min illar abunda nake yi, da cutar dake na ke yi ban ga hakan ba sai yanzu da lokaci ya kure min, na tuba tuba na gaskiya, amman ba ni da tabbacin idan Allah zai yafe min abunda nai, kuma ina jin tsoron haduwa da shi, shin a yanzu idan nai jinya na mutu jinyar zata zama silar kankarewar zunubaina ko kari? Saboda ni na jawa kaina”
“Ban gane wannan maganar ba...”
Na fada muryata na rawa, dayan hannunsa ya kai ya dauko farar takardar ya miko min.
“Ba kawarki kadai nai mu'alama da ita ba, amman ina da kyautata zaton ita ta laka min ciwon, domin na naji labarin kawarki Sa'adatu tana dauke da cutar bayan na tuba na daina mu'alama da ita, ban yi tunanin komai ba ban kawowa raina komai ba, har sai da wannan abun ya faru dukan da sojoji suka min da aka kai ni asibiti, sai suka min gwaje gwaje, a ciki na samu wannan, bayan na warke na koma gida na sake zuwa asibiti biyu ina samu result daya, and do you know what? Da aka saka Sadi yai gwajin sai aka samu shi ma yana dauke da ita, haka ma Murja kuma ina kyautata zaton dukansu ta dalilina suka samu..... ”
Tuni hawayena ya jika takadar da ya kunna min wutar cikin motar ina karantawa.
“Hiv Aminu?”
Ya gyada min kai yana kara jinke hijabi hawaye ma sauko masa. Ban tana jin tausayin Aminu ba tun bayan rabuwar mu sai yau.
“Zina ba tai ba Halima, bata haifar min da komai ba sai bakinciki da talauci, na yi wa yar wani an yi ma yata, na yi da matar wani kanena yayi da matata, yanzu kuma ta jefani a ramen da babu mai ceto ni, daga ni har Sadi har Hajiya ba mu da kwanciyar hankali da natsuwa tun daga lokacin da abun nan ya faru har yau ko abincin kirki Hajiya bata iya ci......”
Ya karasa yana jingina kansa jikin sitiriyarin motar ya fashe da wani irin kuka mai taba zuciya.
_______________________
Wayyo Aminu ya bani tausayi 😢😭
To ita kuma Halima me take nufi da Ahmad? 🤔 ko da yake tana da gaske ance duk hadarin daya baka kashi..... 🤥
Har Gobe ina Team Abdallah 😘😘😘
7/21/21, 10:48 PM - Buhainat: *GOBE NA...*
By Khadeeja Candy
Ina godiya sosai Maman Sayyed, sakonki ya riske ni, Allah ya bar kauna kuma ya ba ni ikon yi kullum 🥰
Gaisuwa ga duk makarantan labarin Gobena, a duk inda suke Allah bar kauna 🥰🌸❤️
5️⃣1️⃣
Wani lokacin Allah yana mana talala mu yi ta aikata zunubi har sai idan ya tashi kama mu sannan yai mana damkar da zata saka mana nadama da dana sani, a duniya kenan da Aminu ya fara haduwa da sakamakonsu, to ina kuma a lahira? Sai dai ina kyautata masa zato kasancewarsa musulmi kuma ya gane kuskurensa ya tuba, Allah yana son bayinsa masu tuba.
Na shiga gida da tunanin Aminu a raina, ba ma ni ba a halin yanzu Aminu be isa ya tunkari wata mace yace yana sonta ba, sai idan mai dauke da irin lalurarsa ce ko kuma idan boyewa zai yi, wata kila ma yayan da yake aibantawa yana cewa na haifa masa yara da yawa zam tsofar da shi sune kadai yaran da Allah zai ba shi. A ranar na kudirta a raina cewar ba zan fada musu cewar mahaifinsu yana dauke da cuta ba, fada musu ba zai haifar musu da komai ba sai tashin hankali duk kuwa da kasancewar akwai kurciya a tare da su, ba lallai ne su fahimci komai ba.
Har ga Allah na jidadin da cutar ta kama Sadi da Sa'adatu ko ba komai dukansu sun ci amanar aure kuma sun ci amanata, Sa'adatu kawata ce ta zabi tai mu'amala da mijina bayan kuma ita ma din tana da aure da yara, sadi kuma ya ci amanar dan'uwansa yai ma yar dan'uwansa fyade, ko da yake har da sakacina a wasan lokaci na barinsu da nake suna kebewa a tare yawan shige masa da take ban taba hanawa ba, saboda ban kawowa zuciyata komai a kansa ba, ko da yana zina ban tana ayyanawa a raina cewar zai iya lalata yar dan'uwansa ba, ashe duniyar ta dade da canjawa daga sanin da nai mata, a yanzu babu yarda a tsakanin yaranka da kowa, domin bayan Namra na yi ta ganin labarai masu sosa zuciya wasu uncles dinsu zasu lalata su wasu kuma ubansu na ciki ko makota, kai har malaman makarantar boko da islamiya ba a bari ba, hakan yasa na kara saka ido akan duk wani motsi na yayana ba mata kadai ba har mazan domin suma ba a yanzu ana lalata su, mun kai wani zamani da babu aminci a zukatan mutane kowa kokarin cutar da kai yake.
A washe garin ranar sai na tashi kamar wata marar lafiya, ba labarin Aminu kadai daya saka jikina sanyi ba har da tunanin Ahmad abunda ban tana ba, ko da dai rana ban tana kwantawa ko tashi da tunaninsa ba. Sai dai jiya na raba dare da tunanin abunda yai min da wasu alamomi da sai a yanzu nake fahimtar inda ya dosa.
“Hello Lims fatar kin tashi lafiya Happy birthday”
Shine farkon abunda ya fara shigo min a waya, kamin na bank dina su turo min. Ni kan har na manta da wani zancen birthday sai yanzu.
Aje wayar nai na fito tsakar gida na debi ruwa na shiga daki na juna a electric kettle, haka na bi yarana na zuba musu ruwa sukai wanka sannan suka karya suka saka uniform. Zuwa nai na gabansu na risina ina kallonsu wani irin farincikin marar misaltuwa ya lullube ni lallai yara rahama ne, no matter how suke rashin ji ko suke cutar da junansu.
“Allah yai muku albarka ya shirya ku da duk yaran musulmi, ya tsare ku.”
Duka suka amsa da amin, daya bayan daya na busu da addu'a ina dafa kansu ina karantawa har na gama sannan school bus dinsu ta iso, da gudu suka fita daga gidan kowa yana kokarin ya riga dan uwansa gwanin sha'awa. Da kallon kauna na bisu zuciyata cike da shauki ina murmushin jindadi da yi ma Allah hamdalla. Ina juyawa sai ga Namra ta dawo tare da Adnan suna rike da wani katon kwali wanda daker ma suke iya daukarsa, an nade kwalin da fata jar leda mai kyale.
“Momy Momy gashi inji direban Bus yace wai a baki”
Jin hakan yasa nai saurin tashi na karasa na karbi kwalin.
“To Momy bude ki sam mana abunda ke ciki”
Namra ta fada jikinta har rawa yake.
“Kin san abunda ke ciki?”
“No”
“To kuje makaranta idan kun dawo zan ba ku nima ban san miye a ciki ba”
“Momy to waya baki?”
“Namra... Ba yanzu kika karbo sakon ba? Ni ina zan san wanda ya bani to?”
“Momy ai shi mai bus din mu ba son ki yake ba ko?”
Ta tambaya tana sako min ido, sai a lokacin na daka mata tsawa domin na fara gundira da tambayoyinta.
“Ban sani ba, wuce kuje sarkin gulma”
Dariya tai ta nufa kofar fita da gudu daman tuni mai bus din ya danna musu horn alamar yana jiransu.
“Daddy na yace idan wani ya zo son ki na fada masa, kuma sai na fada masa wannan”
Hafiza wacce ta nufo dakin da nake ta tari numfashinta.
“Tsohuwar munafuka ki ce tace masa i love you”
“Mama Hafiza i hate you”
Ta karasa fada sannan ta fice daman shi Adnan tun da ya aje kwalin ya koma ita ce dai ta tsaya gulma. Aje kwalin nai a tsakiyar falon Mama na gagara budewa, ko ba a fada min ba na san Ahmad ne yai domin shi yasan yau nake birthday gashi kuma direban motar scul dinsu ce. Hafiza ce ta bude kwalin sauran yan'uwana duk suka zagaye kwalin kowa yana son ya ga abunda ke ciki, katuwar kwalbar strawberry guda biyu ta fara fitarwa sai cake dan madaidaici wanda aka rubutawa happy birthday, a kasan cake din wani madaidaicin kwali ne, da kanta ta bude kwalin sai ta ciro wata farar takardar sannan ta ciro turare man shafawa da wata sarka wacce nake kyautata zaton zinari ne.
“Oh my god oh my god see love abeg duk Babban Baby Namra ne ya aiko ko?”
Ta tambaya tana kallona, sai na rasa me zan ce mata idan nace a a na yi karya tun da fa gaskiyar a bayyane, ban gama tunanin irin amsar da zan bata ba na ji ta fara karantawa wasikar dake tare