Showing 168001 words to 171000 words out of 217237 words
ya same ka ta dalilina, ba zan jidadi ba, ban san inda zan saka kaina ba, ban yafewa kaina ba”
Na karasa cikin muryar kuka, kara matsowa yai kusa da ni ya kai hannunsa kamar zai taba ni sai kuma ya fasa ya juya bayansa, yana maida numfashi, can kuma ya juyo ya kalleni.
“Za ki iya zuwa gurin motata ki jira ni?”
Na gyada masa kai da sauri daman tuni hawaye sun wanke min fuska jikina rawa kawai yake kamar mazari.
“Good girl je ki yanzu”
Na juya ina share hawayen na fita na koma office dina na dauki jakata da wayata na nufi inda motarsa take. Kamin ya iso duk na matsu, sai dai na lura da mutane sun fara saka mana ido cikin har da blessed wacce idan ta gan ni na fito ba a lokacin tashi ba take ce min wai zan fita da oga ne ko?
Tun kan ya karasa ya matsa remote din motar ta fita key ni kuma na bude na shiga na zauna, yana shigowa ya tashi motar muka bar kamfanin.
Ganin muna ta tafiya ba tare da ya min magana ba yasa na ce.
“Ba ka ce min komai ba”
Kallon idona yai da ke cike da hawaye.
“Lims sarkin kuka, ki kwantar da hankalinki babu abunda zai same ki”
“Ba ni ba kai”
“Ni kuma ke ce damuwata”
“Haba ranka ya dade...”
Ya katseni
“Ahmad”
“Ahmad....”
Na maimaita cikin sautin kuka sannan na cigaba.
“Wannan ba abun wasa ba ne, Wallahi zai iya cutar da kai, duk mutunen da zai iya keta haddin aure ya lalata rayuwar wata to zai iya komai, ban san adadin abunda ya aikata ba, ban san iya abunda yai ma wasu ba, wata kila ya tana kisa, ban sani ba, zai iya cutar da kai, kana tunanin idan wani abun ya same ka ni zan jidadi? Zan iya walwala?”
“Duk wannan hawayen saboda ni? Mi kake nai?”
Ya tambaya yana faka motarsa gefen titi.
“Ka kwarara tsaro a gidan da kamfani, kuma ka fadawa police halin da kake ciki”
“Police ba za su iya ba ni tsaro ba, kuma ki kwantar da hankalinki babu abunda zai same ni”
Ya miko min ruwa.
“How ta yaya zaka ce babu abunda zai same ka bayan Abdulhamid ya bata kuma....”
“Abdulhamid yana hannun DSS”
“What....?”
Na masa wani irin kallo na mamaki.
“Yes su suka kama shi yana Abuja”
“Ho.. How.... Do you know kai kasa aka kama shi?”
Na nuna shi da yatsana.
“No bincike yasa aka kama shi, har Abraham din suna can tare”
“Miya faru? Fada min?”
“Nima ban sani ba”
“Then taya ka san an kama su?”
“Mataimakin DSS na jihar nan he's my friend, shi ya fada min”
“Miyasa aka kama su? Kai ka saka aka kamasu?”
“Saboda me? Idan ma zan saka a kama wani ai Abraham zan saka a kama ba Abdulhamid ba, na fada masa matsalar Abraham ne kawai ana cikin bibiyar sa ana bincike ta masa, sai ga wannan ya faru da Abdulhamid din, shi ya fadi Abraham aka kama su”
“Amman miyasa aka kama su din?”
“Kin san sana'ar da Abdulhamid din yake yi?”
“Yana saida mota kuma yana aiki”
“Ya taba baki labarin Abraham, ko kuma shi Abraham din ya taba baki labarin Abdulhamid”
“A'a”
“Shiyasana fada miki, Abraham din ba son gaskiya yake miki ba, ba zai bar abunda yake saboda ke ba, ba kuma zai fallasa miki sirrinsa ba, da dawo gareki ne kawai saboda yana son haihuwa, kamar yadda ya fada miki zai iya mutuwa a ko yaushe idan asirinsa ya tonu, ya taba fada miki cewar yana da mata?”
Na girgiza kai da sauri.
“A a”
“To yana da mata tana can garinsu enugu, dukansu su biyu suna wani business, kuma babu mai sanin alakarsu sai su i think basa yawan ziyarta juna ne saboda gudun kar a zarge su”
Bude motar nai na fita ina shakar iskar waje. Sai shi ma ya bude gefensa ya fito ya zagayo inda nake.
“Hakan na nufi Abdulhamid ya san cewa shi yai min fyade kenan?”
“Be zama lallai ya sani ba, domin ba kowa zai yarda abokinsa ya keta haddin matarsa ba, zai kuma iya yiyuwa ma shi ya saka shi, ko ma dai minene gaskiya zata bayyana”
Dana lumshe idona sai hawaye suka sauko min. Ina jin lokacin da Ahmad yaja dogon numfashi ya sauke.
“Sometimes, Allah yana jarrabar bawanaa ba dan baya son bawan ba, daga baya kuma sai ya kawo masa sauki, a yanzu ne zaki gane ba karamin taimakinki Allah yai ba da ya raba ki da Abdulhamid, shi kan shi uban yayanki da za ki bibiya tahirinsa wata kila za ki samu wani abun ya same shi, ko kuma zai same shi a gaba, shi kansa Abraham din da kin yi kuskuren aminta da shi kin aureshi da kin jefa kanki a cikin wata matsalar, trust me Allah yana son ki, and i think lokacin kukanki ya kare, wani jindadin nesa, wani za ki ga sai ya tsufa ta hanyar yaya zai samu, wani kuma sai ya sha wahala, wani kuma ya jidadin farko daga baya wahalar ta zo, ki gode Allah Allah ya kawo miki sauki tun a yanzu”
Bude idona nai na kalleshi, sai na ji ya kara kwanta min a rai, yana da gaskiya wani jindadin nesa yake, wani kuma ba za a taba jindadin ba har abada.
“Bana son ki saka kanki a damuwa, bana da tashin hankali a yanzu kamar damuwarki, Doc Nura ya fada min cewar idan zuciyarki ta sake bugawa zan a iya rasa ki, so bana tafar haka, kina bukatar ki rayu ko dan saboda yayanki da ni, ina ji a raina cewar ni kadai ne namijin da zan juya duniyarki ki jidadi, na baki abubuwan da kika rasa, na ranta ran mahaifiyarki da yan'uwanki, ba alfahari nake ba, ba kuma ina fada da wata manufa ba, dukan abunda zan yi a yanzu dan na saka ki cikin farinciki ne na mantar da ke damuwarki, a yanzu kam bana jin zan iya bari ko kuda ya cutar da ke lims, wahalarki ta yanke da izinin Allah”
Ji nai kamar ya daure ni, indai jin kalamai ne na sha jinsu daga bakin maza, amman baka gane gaskiyar kowa sai ka zauna da shi, sai dai idan na kalli Ahmad sai na ga kamar be yi kama da mutanen da za su iya wannan ba. Sai dai idan har kalamansa suna nufin soyayya ko aure to ban shirya ba a yanzu, bana jin akwai namijin da ya cancance ni a yanzu sama da Abdallah.
“Zamu iya komawa Gurin Aikin?”
“No na fito da ke nan waje ne saboda ki samu natsuwa and fresh air, yanzu kuma ki zan kai ki gida ki huta just for today daman yau birthday ki ne you're princess”
Na juya na shiga motar, shi ma ya zagaya ya shiga yai mata key.
“Kamin na hadu da ke, idan na tuna babu matata babu Baby Namra babu Mahaifina sai na ji duniya ta ta koma upside down, ammn daga lokacin kaddarar rayuwarki ta same ni sai komai ya canja, na zama jarumi na ji cewar nima zan sake samun farinciki, a duk lokacin da na tuna da yata sai na tuna ki sai na ji bakincikin rashinta ya tafi”
Kallonsa nai sai ya sakar min irin murmushin nan da ake cewa ya fi kuka ciwo.
“Ya isa a nan zan sauka sai na hau napep”
“Ba ki son a gan ki da ni ne ko? Fine”
“No bana son ina shiga motar mutane ne, yanzu sai ka ji ana magana”
“That's why na baki mota ai dan na dauke miki wahalar hawan napep, kuma tsakani da Allah ina jin bakincikin hawan Napep da kike saboda namiji ne zai tuka ki”
“Idan ka bani motar ka bude hanyar da za su kara zargina, a fara magana akai”
“To shikenan zan aje miki har lokacin da za ki bukata”
Har na bude motar da zimmar fita sai kuma na kalleshi.
“Baka fada min wani irin business suke ba?”
“Nima ban sani ba, amman ko minane idan sun gama bincike ai kowa zai ji”
Na fita daga motar sannan na rufe mishi motar sai ganin nai ya sauke gilashin motar.
“Ki kula min da kanki”
Ya fada sannan yai ma motar key ya hau titi, ba ni da abunda ya wuce na bi motarsa da kallo har sai da na daina hangota.
7/21/21, 10:48 PM - Buhainat: *GOBE NA...*
By Khadeeja Candy
5️⃣3️⃣
ABDALLAH POV.
Misalin tara da yan mintuna ya shigo gurin Hajiyarsa kana kallonsa kasan yana cikin damuwa. Yayyen Hajiya ya tarar a falon wato Hajiya Altine da Hajiya Rukaiya, sai da ya gaishe su sannan ya wuce dakin mahaifiyarsa, yadda ya same ta zaune saman carpet rike da carbe fuskarta da damuwa sai ya kara jefashi a cikin nasa damuwar. Kusa da ita ya zauna bakin gado yana kallonta da Fuskarsa da ke bayyana damuwarsa karara.
“Hajiya barka da dare”
Ta dago ta kalleshi kana ganin idonta ka san ta sha kuka.
“Barka dai Husaini, ya aikin”
“Alhamdulillah, Hajiya ki rage saka kanki a damuwa, In-Sha-Allah za a ga Abdulhamid”
“To Allah yasa ni abun yanzu har tsoro yake ba ni, jikina yayi sanyi sosai, idan na duba sai na rasa abunda Abdulhamid zai yi wa wani da zai cutar da shi mutumen da magana ma bata sha masa kai ba, Allah yasa ba yan fillar kai ya hadu da su ba, domin na san masu neman kudi fansa da su suka kama shi da yanzu sun kira sun fadi abunda suke bukata”
Jimmmm Abdallah yai kamin ya kalleta a natse ya ce.
“Hajiya zaki iya tuna lokacin da akai yi Halima fyade?”
“Na sani”
“Mutumen da yai mata fyade wani kirista ne, kuma abokin Abdulhamid ne, ban san miya kai shi gidan ba har yai ma Halima fyade, a yanzu kuma ina kyautata zaton kamar da sa hannunsa gurin dauke Abdulhamid”
Cikin tashin hankali Hajiya ta kalleshi.
“Kamar kai ya akai ka sani?”
“Halima ta fada min mutumen ya dawo yana sonta, saboda cikin da tai shi kuma haihuwa yake nema, bata aminta da shi ba amman ya dage yana son ta aure shi, shiyasa na fada mata gaskiyar cewar shi yai mata fyade, sai dai ita bata san yana da alaka da Abdulhamid ba, ni kai dai na sani nima kuma saboda na taba ganinsu tare har hotuna sun yi tare, shi mutumen police”
“To me zai saka ya dauke Hassan?”
“Saboda ni na fadawa Abdulhamid gaskiyar daya kasa yarda da Halima a lokacin da abun ya same ta, ke da shi kuna ganin kamar ta aikata zina ne, yayi ta bakinciki yana fadar cewar shi Abraham zai ciwa amana, wata kila yai masa magana ko yai masa wata barazana shi kuma Abraham din ya dauke shi”
“Amman miyasa baka fadi wannan ba? Sai yan sanda su bincike shi mutunen?”
“Hajiya idan baka iya kama barawo ba, sai barawo ya kama ka, shi Abraham din police ne kuma da na bincika sai na samu labarin cewar baya cikin garin nan a office dinsa ma har an saka wani, amman mu saurara na kwana biyu tukuna tun da mun kai report din gurin Police kuma ana Addu'a, ko minene zai bayyana In-Sha-Allah”
“Amman irin wannan ai kama shi za ayi a bincike shi ko kuma ita Halimar, waya sani ko ma ita ta saka shi ya sace shi saboda ta dauki fansa balle ta ji zai yi aure, kuma ta ga shi Abraham din yan sonta”
“Haba Hajiya wane irin Halima kuma?”
“Zata iya yin komai wannan yarinyar da kake gani, ni sam ban yarda da ita ba ma”
“Babu hannunta a cikin nan, kuma na fada miki ki bari nan da kwana biyu idan ba mu ga wani abun ba, sai mu fada musu wanda muke zargi”
“To ko ma dai minene Allah ya bayyana shi”
“Amin”
Yayi kusan awa daya a dakin sannan yai mata sallama ya fice. Aiko kamar fitarsa take jira ta fito falo ta labartawa yan'uwanta abunda ya faru dukansu sun cika da mamaki.
“Wannan maganar ai ba abar a kyale ba ce”
Cewar Hajiya Altine, sai Hajiya ta amsa ta tana ware hannu.
“Ni ma shi na gani ban zafafa abun ba ne saboda a gabansa ne, na san zai iya shiga cikin lamarin tun da uwarsa ta shigo ciki, yadda kika san ta wanke gaba ta zuba masa ya shanye haka yake da ita, ko sunanta baya son a ambata a wani abu”
Hajiya Rukaiyah ta dora da.
“To waya sani, ko wani abun tai masa, amman duk yadda akai ta san inda Abdulhamid yake”
“Nima shi nake tunani, saboda bakinciki zai yi aure gashi ita ba tai ba zai iya sawa tace shi mutunen ya sace shi, ko kashe shi ma zasu iya yi, ko kuma su masa wani illar, kuma Allah kadai yasan gaskiyar lamarin nan wata kila ma daman can ta san abokinsa nw ta aure shi dan su kashe shi su ci dukiya Allah ba basu sa'a ba, Allah ya gani ko da akai auren nan ba zan ce miki yaron nan yana son Halimatu ba, be taba nuna min ba, kuma a lokacin ma ta neman lafiyarsa yake amman sai ya zo min da maganar aure daga sama, ban san yadda akai ta janyo hankalinsa ba ma, kamar abun magani, cikin kankanen lokaci akai komai”
“Kin san abunda za ayi? Ko yanzu ita ya kamata a kama, idan ta ji wuya dole ta fadi inda shi Abraham din yake da Abdulhamid din, wannan ai ba maganar bari ba ce”
Cewar Hajiya Altine tana tabe baki alamun mamaki ya gama cikata.
“To yanzu a kira Yusuf a fada masa, gobe tun da farar safiya a doka masu sammako a kamo yar iskar, yarinya ta same mana fitina a cikin dangi”
Hajiya ta fada tana kara yamutsa fuska. Hajiya Altine ta ce.
“Haka za ayi, daman Yusuf din ya fada min ai akwai inda suke saka mutum su saka masa wata hula duk iskancinsa sai ya fadi abunda yake gaskiya, bari na kira shi....”
Ta karasa tana danna number dan nata rai a bace, Hajiya kuma ta zauna saman cushion tana ta rawa da kafa tana kara kashe ido, babu komai a zuciyarta sai tsanar Halimatu.
HALIMATU POV.
Na iso gida cikin wani yanayi da ban taba samu kaina ba, ni dai ba zan ce ina son Ahmad ba, haka kuma bana kin shi, sai dai a yau kalamansa sun kashe min jiki sosai.
Mama ta yi mamakin ganin na dawo gida da wuri bayan a a lokacin na saba dawowa ba sai yamma, karya nai mata na ce mata yau babu aiki da yawa shiyasa aka tashemu. Har na yi kamar na labarta mata abunda ya faru da Abdulhamid sai kuma wata zuciyar ta hana ni, domin na san ita ma din zata zargi Ahmad da saka a ka masu kamar yadda nima zuciyata take zargi, kuma zata iya cewa zatai wa Hajiya jaje gudun kar ace bata ji ba idan taje kuma dole zata bada labarin abunda na fada mata ne, idan kuwa Hajiya ta ji haka zata zarge ni, so rufin asirina kawai nai shiru da bakina na bar abun a cikina, har sai ya bayyana.
Babu irin tunanin da ban yi ba a ranar har cikin daya ina abu daya, dan son gano abunda Abdulhamid da Abraham suke aikata marar kyau, idan na saka wannan na kwance wacan na kulla wannan, sata yake? Tare da Abraham din suke fashi? Ko kuma wata sana'ar ce dabam? Duk wani mugun aiki da zan kwatanta Abdulhamid da shi sai na ga kamar ba zai iya aikatawa ba, wata kila ma dai Abraham din shari yai masa saboda kar ya cutu shi kadai, domin ko a lokacin da na ke aurensa ban ga wata alama da ta nuna rashin gaskiya a tare da shi ba, duk da yake baka iya gane gaskiyar mutum mai boyo, Abdulhamid kuma yana daga ciki irin mutanen nan da suke boye abu, soyayyar da muka da shi ma a lokacin da nake budurwa a boye muka yi saboda baya son kowa ya sani.
Haka dai nai ta sakesake na har dare raba ban yi bachi ba, domin tun ina jin alamar bachi bachin a idona har ya fitar min gaba daya, tashi nai na fito bakin balcony na zauna ima ta kallon taurari kamar mai kidayarsu, babu komai a tare da ni sai tunani kala kala. Can ciki ciki na ji wayata dake kan drawer tana vibration alamar kira yana shigowa wayata. Sai na tashi na koma dakin, hannu na kai na cire carjin sannan na dauki wayar sai nai arba da number Ahmad, gabana ne ya fadi kamin mamaki ya rufe ni, miyasa ya kira ni yanzu? Abunda be tana ba, ko kirana a gida balle a wannan lokacin da agogon wayata ya nuna karfe biyu saura, to ko dai fada min zai yi an sako Abdulhamid? Ko kuma wani abun zai fada min dabam, kiran na daf da tsinkewa nai picking na kara a kunne sai dai ban yi magana ba sai da na fito balcony. Ina ta jiran yai magana be ce min komai ba, idan na duba wayar sai na ga kiran na tafiya har sai da na gaji da kaina na ce
“Hello”
“Lims, kema kin kasa bachi kamar ni kenan?”
“Eh”
“Kin san me? Dakina yai min ba dadi sai na fito na zauna harabar gida sai kidayar taurari nake, yanzu kuma haka nan kawai na ji ina bukatar jin muryarki, duk ban yi zaton za ki dauka ba”
Ya fada da murmushin da zan iya jiyowa, kana jin muryarsa ka san ransa kal yake fa farinciki. Na yi shiru ban ce masa komai ba.
“Fada min miya hanaki bachi?”
“Ni ma ban sani ba, na samu kaina da kasa bachin ne”
Murmushinsa mai sauti ne ya daki dodon kunnena.
“To je ki kwanta, so that's ki tashi da wuri i need to see early in the morning”
“Okay”
“Sweet dreams Lims, ki rufe idonki ki tuna duk wani beautiful memories we share together za ki yi bachi, kuma ina rokon ki yi mafarkina take good care of yourself for me pls”
Be jira abunda zan ce ba ya yanke wayar, for the first time na samu kaina da shiga calls list na kurawa number ido for no reason, before murmushi ya biyo fuskata, sai da na sake kallon taurarin sannan na tashi na koma daki na kwanta. Lumshe ido nai thinking all the good