Showing 45001 words to 48000 words out of 217237 words
a lokacin da be dace ba kuma da wacce ba ta dace ba”
Mikewa tsaye Abdallah yai yana jin wani abu na rashin jindadi yana kawo masa ziyara.
“Haka Allah ya kaddara”
“Haka Allah ya kaddara kuma da son ranta ba, idan ma wannan hukunci ne take tunanin ta yi to kuskure ne babba”
“Zan je gurin aikin Hajiyarmu ba wani abun ko?”
“Babu”
Sai da ya kalli yanayinta sannan ya sa kai ya fice ransa ya susuwa zuciyarta na konuwa.
HALIMATU POV.
Al-hamdulillah shine abunda na ke yawan maimaitawa tun daga lokacin da na saka kafata a gidan Abdulhamid, duk wani abun na jindadi rayuwa da mace zata nema a gidan miji Abdulhamid ya tanadar min shi, tun daga na ci har na sakawa a jikin har na kallo, kamar wata kwai haka yake tarairaiya ta a yadda yake nuna min kulawa da soyayya ban tsamanci samunta a gurinsa kamar haka ba. Yana yawan nanata min cewar ina da wani irin girma da daraja a idonsa saboda aurensa da nai alokacin da yake dauke da lulurar da ba ko wace mace ce za ta yarda ta aure shi a haka ba, wannan dalilin yasa yake da kara gwarjini a idonsa. Ya kara maida hankalinsa gurin neman magani fiye da da, ni ma kuma ina kokarin yi masa abubuwan da zasu taimaka duk dai bana ganin wani alamu na warkewar sai ban taba gajiyawa ba ko na fitar da rai domin na san babu cutar da bata da magani. Ina samun kwanciyar hankali a aurena da Abdulhamid fiye da wanda nai a baya da Aminu, ko ba komai zai nuna min kulawa zan kwanta a kirjinsa na farka a gefensa mu ci abinci tare mu yi fira mu yi hara mu yi nishadi, ba kamar a gidan Aminu ba da ba shi da lokaci na.
Bana da wani fargaba ko tunani a gidan aurena bayan ta mutum biyu yayana da kuma Hajiya wato mahaifiyarsa domin na lura a duk zuwan da muke gaishewa kamar bata na'am da ni, bayan a baya kuma ba haka na santa ba, duk dai ba wani zuwa muke sosai ba amman a duk lokacin da muka je gaisheta ko kuma muka fito daga wani gurin muka biya sai ta yi min tarba ba a baya da kai ba, ko kuma ta bar a nan a falon ba ita kadai ba har yayanta mata biyu na lura haka suke min basa son fira da ni balle kuma irin wasar nan ta matar yaya, namijin ne kawai babu ruwansa shi kan idan muka tarar da shi a gida mu yi ta fira abun kamar ba kanen mijina ba, amman bayan wannan bana da wata matsala da Abdulhamid idan ka cire na kyamar yayana da yake yi, domin na lura ko zancensu baya son ina yi idan aka kira waya da sunan za mu gaisa da su a lokacin da yake kusa da ni da a take yanayinsa zai canja, be taba siye ko da biscuit din maira goma ya mika min ko ya bawa wani yace a kai musu balle kuma har ya tambayi lafiyarsu ko karatunsu, sai dai ina masa uzuri da wannan ganin cewar shi din be taba aure ba sai yanzu kuma daman can ba mutum ne mai son yara ba, ballanta na san yadda wasu mazan suke basa son yayan wasu a kusa da su, musamman Abdulhamid da na lura da alamar yana ďan da kishi ba kamar wasu ba, tun daga lokacin da yai kokarin hana ni aikina na lura da hakan ga kuma ya hana yin ko. Wane irin social media saboda kar na hadu da maza, yana yawan fada min cewar na rike masa kaina na tsare masa kaina kar na bar shaidan ya rinjaye ni, wani lokacin na kan amsa masa da to ko nai masa alkawarin haka ba wani lokacin kuma sai dai na yi dariya, domin a tunani babu abunda zai kai ni na aikata wani alfama ko da bana da aure balle ina da shi, ba wai na fi karfin shaidan ba ne, kawai dai ina tuna baya ne a lokacin da Aminu zai iya shafe wata da watannani ba neme ni ba kuma babu kulawa da magana mai dadi ga shi ina zuwa aikin ina ganin mazan amman ban aikata ba, balle yanzu da nake auren mutumen da ya san darajar aure kuma bana ganin mazan ma, to mi kam Allah na tuba wace tsiyar ce zata saka ni aikata hakan.
A zaman aure da Abdulhamid wani abun da zai baka mamaki shine rashin iya girki, wanda ni kaina yake bani mamaki kuma ya ba ni tsoro, tun da na zo gida ban taba dora girki ko da ruwan zafi ne ya tafasa ba, idan na dora miya yadda na hada ta haka zan zo na tararda ita haka tuwo ma, shiyasa ban taba yin jalof ba lalle shimkafa da wake, indai har za mu sha tea sai dai Abdulhamid ya dora mana, indai har ni na dora ba zai tafasa ba ko da kuwa a gas ne ko electric kettle. Sai dai be taba sakawa Abdulhamid ya min fada ko nuna bacin ransa a hakan hakan ba, kullum safe shi zai dora mana ruwan da za mu amfani da su da rana kuma yai mana take away haka ma da dare, na kuma rasa gane dalilin haka bayan a can baya na iya girki na kamar ko wace mace, amman tun da na tsinci kaina a gidan Abdulhamid sai komai ya lalace.
Ranar wata labara da misalin sha daya da yan mintuna na ji an buga kofar falona, na yi tsamammi ko daya daga cikin yan matan gidan mu ne hakan yasa na tashi da kuzari na bude, abun mamaki sai nai arba da Suwaiba matar Abdallah kuma uwar yayansa mata guda biyu, na yi mamakin maganinta domin ta dade tana min waken zuwa amman bata zo ba sai yau, mun sha fira a ranar daman can Suwaiba mace ce mai son fira da far'a da haba haba da jama'a, ban yi zaton Abdallah ya kawo ta ba har da ta labarta min cewar shi ya kawo ta amman ya aje ta gurin gate wai yana sauri jaye gurin aiki.
Ta labarta min abubuwa da yawa a ciki har da na rashin son yara da Abdulhamid yake da shi, sannan ta dora min da cewar yawanci maza basa son yayan da ba na su ba, balle kuma Abdulhamid da yake saurayi, tana ta nanata min cewar sai na yi hakurin haka kamar ta san abunda ya fi damu na kenan, duk kuwa da kasancewar ban taba fadawa kowa ba.
Ganin na dauki waya na kira Abdulhamid na ce yai mana takeaway sai abun yai ta bata mamaki.
“Kar dai ace har yanzu baki fara girkin ba, ko kuwa amarcin ne ya motsa kike jin ba za ki iya dafawa ba?”
Dariya nai kamin na bata masa.
“Wallahi ba haka ba ne, idan na dora girkin baya dahuwa yadda na saka shi haka zan tararda shi kuma ga wuta ga komai amman ba ya yi”
“Too kar dai ace Abdulhamid ma yana da kohi kamar Abban Suhaima, ni ma idan nai masa wani laifin ko kuma na bata masa rai haka zan dafa abinci a ranar ba zai dafu ba sai na bashi hakuri”
Ta fada tana dariya... Ni ma dariyar nai sai dai ba irin ta ta domin ni wani tunanin ne ya zo min, kar dai ace Abdallah ne yai min kohi nake ta samun wannan matsalar?
“Ko da yake shi ma a tawaye ne dole za a samu dukansu suna yi, wata kila wani abun kika masa sai kin ba shi hakuri sannan za ki daidaita, amman fa ni kin san da na dauka ko Abdulhamid ba shi da kohi”
Zancenta ne ya dawo da ni daga duniyar tunani sai na sake yin murmushi a karo na biyu.
“Haka ne ai wani ba a iya ganewa sai idan wani abun ya faru”
“Haka ne”
Sai guraren karfi biyu ya kirata a waya yace ta fito bakin gate yana jiranta, a lokacin Abdulhamid be dawo ba, sai na saka Hijabina na rakata har gurin motarsa bayan na deba mata wasu abubuwan daga turaruka na da kayan kwaliya, gilashin motarsa a sauke yake amman ko da wasa Abdallah be dago ya kalleni ba da na gaishe ma sai ya amsa min a gajarce kamar be san ni ba, bayan sun wuce na dawo ciki gidan ina ta nazarin kalamanta. Daga karshe na yanke shawarar kiran Abdallah nai masa magana, haka kuwa akai bayan Abdulhamid ya dawo mun ci abinci mun yi fira ya fita sallah la'asar ni kuma na nemo number Abdallah ya aika masa kira, ringing tai kamar zata katse sannan ya daga, ban tsaya yi masa sallama ba balle gaisuwa kai tsaye na ce.
“Abdallah magana na ke son mu yi”
Sai na yi shiru bayan na fada masa hakan ina jiran na ji amsar da zai ba ni kamin na dora amman be ce min komai ba har sai da nai zaton ko wayar ta katse ne.
“Idan ka kullace ni da wani abun dan Allah ka kwance, tun da na zo gidan nan kullum nai girki ba ya yi”
“Babu hannuna a ciki”
Ya amsa da muryar da na jita kamar ba ta shi ba.
“Wata kila kana jin haushina ne, ko kuma kana jin bacin rai a kaina ne”
“Ban taba jin haushinki ba, kuma ba ki bata min rai ba, abunda kika aikata ne kawai idan na tuna ina jin babu dadi ne”
“To ka daina jin babu dadin, shiyasa bana iya girkin idan na yi ba yayi, dan Allah ka kwance Kohin da kai min”
Ina iya jiyo saukar numfashinsa kamin ya ce.
“Ban kullace ki da komai ba Halimatu, ke yanzu yar'uwata ce kawai kuma matar dan'uwana, yan'uwanta ta fi gaban wasa ko babu Abdulhamid babu abunda zai shiga tsakanin mu”
Yana fada min hakan ya kashe wayar, a take wani abun marar dadi ya kawo ma zuciyata ziyara. Har na gabatar da sallah la'asar ban daina jinsa ba, bayan sallah isha'i ina kwance saman kujera falo Abdulhamid ya fito daga bedroom ya nufo inda nake kwance, sumbatar kaina yai kamin ya daga ni na tashi zaune sai ya zauna sannan ya kwantar da kaina saman kijinsa yana shafa fuskata.
“Gobe fa ina tunanin zanje Abuja”
Dagowa nai na kalleshi sai na ga murmushi a fuskarsa.
“I know za ki yi mamaki ai, ni ma zuwan dole ya zame min kuma i think idan na samu yadda na ke so zan dawo ranar da na tafi”
A take na marairaice fuska kamar zan masa kuka.
“Mi zaka je yi Abuja?”
“Wallahi wasu takardu ne na ma'aikatar mu da ake son su jibi kuma dole sai an kai su Abuja an saka hannu shiyasa zan je, idan an saka hannu za a ba mu kudi masu dan dama sai mu juya su”
“Tare za mu je?”
“Na so haka amman be samu ba dole mi kadai zan je, amman a promise you idan ban dawo ranar ba washe gari zan dawo”
Har cikin raina na ji babu dadi sai na ji kamar tafiyar shekara zai yi, a ranar na kwanta a jikinsa sosai yadda kasan wata jaririya haka na zama.
Washe gari daga ni har shi mun tashi da wuri, shi ya hada mana abun karyawa ni kuma na shirya masa komai na tafiya, a tare muka karya ina ta narke masa a jiki tun yana daujar abun wasa har shi ma ya so ma jin babu dadi.
Na masa complaining din rashin mai gadin mu sai ya ba ni hakuri ya ce za a samu idan ya dawo bayan yayi min izinin zuwa gida na gaishesu ganin duk na bata rai ya san idan naje zan dan sake sosai, har gurin mota na rako shi nai masa addu'a sosai ta neman tsari da kuma alherin hanya, saboda na san yanayin kasar ana cikin halin fargaba balle tafiyar a mota zai je ba a jirgi ba.
Bayan tafiyarsa da awa daya na shirya na nufi gidanmu, yan gidan mu sun yi murnar ganina sai zolayata suke wai ina ta shining. A yanayin dana tararda Amal be min dadi ba, wai zawo take da amai yau kwana uku amman basu fada min ba ganin ba su gaza mata a komai ba, na san suna bata kulawa sosai ammn dai ai ya kamata ace sun sanar da ni a matsayinta na yata kuma karama, ko da yake na lura sukansu yanzu yaran idan suka gan ni sai su yi kamar ba su gan ni b babu ruwansu da nuna son zuwa ganina in banda Amal da ta kasa sabawa da kowa har yanzu. Wata kila Mama ta ki ta fada min ne ganin kamar zan iya daga hankalina ga shi kuma Abdulhamid ba son yara yake ba kamar yadda kowa ya lura da hakan.
A ranar Amal a jikina ta wuni lokaci zuwa lokaci sai ta kalleni ta sauke ajiyar zuciya abun har ya soma ba ni tsoro, na so na kaita asibiti duk kuwa da Mama ta fada min sun kai ta ga kuma da aka rubuto mata na gani amman hankalina zai fi kwanciya idan na kaita da kaina. A ranar nai deciding na dauko ta na dawo da ita gidan aurena tare da ni ba in yado washe gari sai na kira Abdulhamid na fada masa cewar na zo da ita saboda bata da jindadi kuma na nemi izininsa na kaita asibiti.
Bayan magariba na baron gidan da ita na debo wasu daga cikin tufafinta, har na iso gida babu komai a zuciyata sai tausayinsa, wata kila har da kewata ta sakata wannan ciwon saboda yadda ta saba da ni sosai. A gaskiya ranar na ji babu dadi marar misaltuwa, wani abun mamaki da muka dawo gida tare sai ta dan sake Allah ya kawo mata sauki har ta labari take ba ni wai Adnan ya dake ta ya zageta, sai dai idan an taba jikinta ina jin zafi a can gidan bata cin komai amman a nan da na bata abaya sai ta ci ta kwanta a jikinta ta tafe sosai kamar wata kyanwa.
Misalin tara da rabi na shiga kitchen na gwada dora indomie, wani abun Allah sai gashi ta dahu kamar yadda na saba dafata, ban san lokacin da na daka tsalle na dibe ba dan murna. Ta window kitchen na hango dorowar mutum ta gate, ta hanyar hasken fitulun da ke cikin gidan ne na iya gane wanda ya diron yana sanye da bakaken kaya fuskarsa ma a rufe da bakin fuska. A furgice n rugo da gudu na yo falo sai an samu Amal har ta yi bachi da sauri n rufi kofar falon na rufe zuciyata na bugawa kamar zata fado, abunda ban sani ba ashe na rufe falon da daya daga cikinsu ba, ban lura da hakan ba sai bayan an rufe kofar na yi baya sai na hango mutum ya fito bayan labule rufe da fuska kamar wacan yana nuna ni da bindigar da ke hannunsa.
*Khadija Abubakar Alkali*
7/20/21, 8:32 AM - Buhainat: *GOBE NA...*
By Khadeeja Candy
1️⃣7️⃣
Innalillahi wa'inna ilaihirraji'u, Innalillahi wa'inna ilaihirraji'u, Innalillahi wa'inna ilaihirraji'u.
Shine abunda nake ta maimaita a raina ina kallon bindigar da ake nuna ni da ita, zuciyata na wani irin zillo kamar zata tuma ta fado kasa. Ban ankaro da a filin na ke neman ceton Ubangijina ba har sai da mamalakin bindigar ya dora hannunsa a bakin da bana iya tantance saboda mask din da tai wa fuskarsa kawaya.
“Shiiiiiiiiiiiii, kwanta”
Kamar umarni nake jira a take na kwanta a guri kamar gawa, ina iya jiyo karar bude gate din gidan da akai kamin daga bisani a bude kofar falon sai shigowar mutane na ji ina kyautata zaton wanda ya diro ta gate ne ya bude musu suka shigo shi kuma na falon ya bude musu kofar.
“Ina mai gidan?”
Sautin muryarsa ba jina kadai ya razana ba har da ilahirin jikina da kwakwalwata, ban tana sanin haka tashin hankalin haduwa da mai makami yake ba sai yau, kamar wacce aka cewa ga mutuwa ta nan a gaba na haka na ke ji.
“Ina mai gidan yake...!”
Ya sake daka min tsawar da na ji ta kamar a mafarki, bana jin zan iya amsa musu domin numfashina ma rawa yake balle kuma muryar da na ke jin kamar ta kare a lokacin.
“Ke tashi zaune”
Ya sake daka min tsawa a karo na uku, sai na tashi ta sauri cikina har wani kuka yake saboda tsoro. Da dai-daya na bisu da kallo kamar zan ga wanda na sani ko ya san ni amman ban ga fuskar kowa ba a cikinsu sakamakon mask din da suka saka. Wanda ke kusa da ni ya saita bakin bingarsa a gafen kaina.
“Ina mijinki?”
“Baya nan....”
Na amsa idanuwa a rufe gam ina jimke hannayena, tashin hankalin da ke cikin kaina yana ta kara hauhauwa.
“Karya kike... Idan ba ki fada mana inda yake ba za mu kashe ki”
Wannan karon na tabbatar ba jikina kawai yake rawa ba har da kayan cikin da ke cikin cikina da kuma kaina.
“Wallahi baya nan ya tafi Abuja”
“Ina kudin da ya shigo da su jiya?”
“Be shigo da kudi ba takardar ce ya je ya kai Abuja a saka masa hannu”
“Idan baki ba mu kudi ba za mu kashe yarki”
Sai a lokacin na bude ido a take na nemi tsoro da gudun kar su kashe ni da na ke na rasa.
“Wallahi Wallahi babu kudi a cikin gidan nan, idan ba ku yarda ba ku duba ko'ina”
“Idan muka duba muka ga kudi za mu kashe ki”
Na gyada kai duk kuwa da kasancewar bana iya tantance mai maganar a cikinsu. A take ya bada umarnin a shiga a duba masa ko'ina na gidan, ba dakina kadai ba har falo sai da suka hankade komai sannan suka yarda da babu kudi a cikin gidan.
“To dauko mana zinari”
“Ba ni da zinari ba ni da komai”
Ina rufe baki na ji saukar mari gafen fuskata.
“Ki dauko mana zinari na ce”
“Ko kashe ni