Showing 210001 words to 213000 words out of 217237 words
yi mamaki na san indai Hafiza ce zata fadi fiye da haka ma, da dai ace Aisha ce ko Husna take maganar da ce ina kunyarsu amman Hafiza sai gyaran Allah ba kunya ba tsoro kuma bata jiran sai an mata.
Ko ba a fada na ni an san wasu dan gulma da neman ganin gidan da za a kaini yasa sun bin motocin daukar amarya tun da a budurwa nake ba balle ace dole sai kowa yaje, amman Al-hamdulillah shi ma farinciki ne kuma na san ba za su je su tarardar wani abin tsegumi ba, sai dai kowa ya bawa idonsa abinci.
Ni kaina da na already na ga gidan kamin a kawo ni amman hakan be hana ni zama bakauya ba a birnin, wata kila kuma dan yana dare ne sai ko'ina da gidan ya dauki haske ga shuke shuken da suka kara kawata gidan gwanin sha'awa.
Bangaren mahaifiyarsa aka fara shiga da ni Gwaggota na rike da hannuna kaina na cikin gyale jikina sanye da shadda lace mai ruwa kwai, sai kamshin turare nake kamar yadda muka shiga muka tarardar falon Hajiya ma yana kamshin turaren wuta. Muna shiga matan dake cikin falon suka fara guda kamar an aurowa dansu burduwa, sai saka min albarka suke yan matan na daukata hoto, har cikin dakin Hajiya aka shiga da ni tai min nasiha sannan na taso tare da mutanen da muke tare aka nufi bangare na da ni.
Mutane da yawa sun yaba da yadda aka samu part dina so Ma-sha-Allah, ciki har da masu fadin mai hakuri mawadaci, basu dade ba suka fita har su Hafiza aka bar ni kadai a dakin ta cikin a nan na yaye gyalena ina kara kallon yadda kalle da aka min ja yake ta haiba.
Few people ne suka raso Ahnad zuwa dakina, a yadda suke zolayarsa yai musu shiru yana murmushi sai ka rantse da Allah ba shi ba ne, sai wani sun sun yake da kai kamar mai kunyar gaske.
Suma sun mana nasiha irin tasu sannan sukai mana addu'a, sai da ya raka su ya dawo, sai ya zauna kusa da ni ya cire min mayafin yana murmushi kamar yadda nima nake tsakanin fuskata da tasa sai na rasa wacce ta fi wata annuri, hannuna ya kama ta sumbata sannan yaja ni jikinsa ya rumgume.
“Al-hamdulillah, a yau Allah ya tabbatar mana da abunda ba mu taba mafarki ba, abunda ba mu taba kawowa a rai cewar zai faru ba a tsarim rayuwarmu, nesa ta zame mana kusa kunci da bakinciki ya zame mana farinciki da nishadi, ina rokon Allah yasa mutuwa ce zata raba mu kuma ya bamu zuri'ar mai kyau mai albarka, kuma ya bamu ikon kula da su da dauke sauke nauyinsu da yake kan mu”
“Amin”
Na fada ina wasa da zanen shaddar dake jikinsa, ji yai kamar rumgumar da yai min ba tai ba sai ya kara matseni sosai ya kirjinsa.
“Wallahi gani nake kamar ba gaske ne ba, Al-hamdulillah Allah”
Ya sake fada cike da nishadin, sallah godiya ga Ubangijince farkon abunda muka fara gabatarwa sannan neman tsarin Allah da kuma ni'imarsa ya biyo baya, muka ci daga abunda ya shigo min da shi, kana ya zuba min madara na sha sannan muka sake dabbaka wata sunnar.
Washe gari tun kamin mu tashi bachi Siyama da kwankwaso mana kofa, ina jin lokacin da ya daga ni a hankali saman kirjinsa ya kwantar da ni, ya gyara min duvet din sannan ya sumbace ni ya tashi ya fita. Be dade ba ya dawo ya sake jana kirjinsa ya rungume ba mu tashi ba sai kusan tara har da wani abu, shi ma dan Hafiza ta kira ni ta fada min cewar akwai yan'uwan Inna da za su zo yanzu.
A lokacin ne na tashi nai wanka na fito na tafi gaban madubi na shirya ina kokarin mikewa tsaye na hango shi ta cikin madubin yana kallon jikinsa ba riga sai tawul din daya daura shima iya kwankwasonsa. Murmushi nai na juyo ina kallonsa.
“Kawai gani nake kamar ba gaske ba ne”
Na sake yin murmushin sannan na nufi wardrobe a zatona kayan da nace Hafiza ta dauko min yana ciki sai nai arba da wasu tufafin dabam a ciki juyowa nai na kalleshi.
“Nawa ne?”
“Eh mana, daman ai ba zan kai miki gida ki yi kwalliya wani ya gani ba, ni da na siya ni za ayi wa kwalliya da su”
Bayan ya fadi haka ya karaso kusa da ni ya dafa ni yana min inda aka jera takalmin, akwai kayan da ba a dinke ba sai dai dikaken yafi yawa kuma kowane kaya da kalar hijabinsa babu gyale ko daya, gyale kan sai na abayar da aka saka a ciki amman bayan shi ban san wani mayafi mai suna veil a cikin kayan ba. Ko ba a fada min ba ni kaina a fahimci Ahmad mutum ne mai kishi hijabin kuma zai taimaka min na kara kare martabata da kuma mutuncin aure da kuma abunda Ahmad yake cewa na boye masa wai na sa shi kadai.
Sati daya Hajiya ta dauka tana mana girki na safe na rana na dare bata taba gajiyawa ba, sai da akai satin daya sannan ta sa aka kirani ita da kanta ta zaunar da ni falonta ta fada min cewar daga gobe zan fara girkawa mijina abinci da kaina.
“A ka'ida kwana uku ake, amman saboda ki huta yasa na dauki sati daya ina miki, yawancin duk abunda kika ga ina girka muku shine favorite din mijinki, dan haka sai ki haddace wani abun kuma za ki iya karawa dan kanki ko kuma ki saffara masa wani abun irin naku na yan zamani”
“In-Sha-Allah Hajiya na gode sosai Allah ya saka da alheri ya kara miki lafiya”
“Amin Allah ya muku albarka ku ma”
A nan na amsa da Amin, sannan na tashi na dawo part dina raina fes. Zaunawa nai saman kujerar da yake zaune sai ya dago ya kalleni sannan yasa hannunsa ya zagaye mazaunena.
“Hajiya tace zan fara maka girki daga gobe”
Na fada ina jan hancinsa dayan hannuna kuma a kunnensa ina wasa da shi. Lumshe ido yai ya bude yana tsutsar lips dinsa.
“Kin iya?”
Na dan yi fuskar shagwaba.
“Haba shi girkin?”
“Eh mana wasu yara irinki ba a koya musu girki a gida saboda son jiki”
Dariya nai sai ya kamo kaina ya hade goshinsa da nawa, ya sumbanci hancina yana isar min da numfashinsa.
“Idan baka kiya ba zan iya saka ki catering school ki koya mana”
“No ni din eh to ban hana ko dan koyan wadansu abubuwan ba na zamani amman indan girki ne irin na mu na hausa ai na saba yi na iya daidai gwargwado”
Mikewa tai tsaye ya ja hannuna muka nufi kitchen, gaban gas ya fara tsayar da ni sai ya koma bayana ya rumgume ni, da dayan hannuna ya rika nuna min yadda zan yi amfani da gas din.
“Na fa iya”
Bakinsa ya kai saitin kunnen yana cizona a hankali yace.
“Ki dauka baki taba aure ba sai yanzu, ki dauka wannan auren shi ne aurenki na fari, ki dauka komai sai a yanzu ne za ki koya sai a yanzu zaki iya, ki dauka Ahmad ne mijinki na farko kuma na karshe har abada”
Na gyada kai a hankali ina dan matse fuska domin maganar yake yana cizon kunne a hankali kamshin turarensa duk ya cika ni sai tayar min da zuciya yake.
“Okay”
“That's my Lims”
A dolen dole na biye masa ya rika nuna komai na kitchen din da yadda ake amfani da shi, wani abu kan ban san shi ba sai da ya fada min sauran kam duk na sansu kuma na saba amfani da su, domin ko a gidan Aminu da gas nake aiki balle kuma Abdulhamid.
Bayan mun gama muka fito daga kitchen din sai ya sake ni ya shiga ciki yai alwala, ina zaune ya fito yana sake hannayen rigarsa dake nade.
“Tashi ki yi alwala zanje masallaci”
Ya fada yana kissing dina, a kokarin yi masa addu'ar Allah ya tsare na ji lemun da na sha dazun ya dawo min a baki, saurin mikewa nai tsaye sai ya rike ni.
“Lafiya?”
Karnin turarensa yasa na fara sheka amai a gurin kamar wacce ta fi wani abu, sakina yai sai yai baya baya yana kallona baki sake kamar mai mamaki sai kuma ya rugo a guje yazo ya rumgume yana murmushi sai kuma ya sake ni.
“No wait....”
Sai kuma ya sake rumgume ni ya sake sakin ya sake rumgume ni yayi min haka yafi a kirga sai dariya yake. Can ya cire hular kansa ya jefar ya fara zagaya falon yana kallona kamar mai mafarki, sai kuma ya nufo ni ya daga fuskata yana kallona
“I can't believe this”
Ya fada kamin ya sake ni ya fadi a gurin yana ma Allah Sujada. Ni kan a raina nace daga ganin na yi amai idan kuma ya kasance malaria ce fa? Domin ni ban saba ciki da amai tun yana yaro ba sai ya fara girma hasalima ko irin laulayin nan na masu yaron ciki ban saba yi a ba sai ya fara fitowa na ke cin wuya har sai na raina kaina.
7/28/21, 8:33 PM - Buhainat: *GOBE NA...*
By Khadeeja Candy
6️⃣4️⃣
Iyakar kokarin da nai na danne dariya ta ne domin har ga Allah ya bani dariya matuka, daga ganin amai sai ya sa rai da ciki, ko da yake idan ance ina da cikin ba mamaki tunda mahaifa a bude take kamar yadda Aminu ya fada wai ina ta haihuwa zan tsufar da shi, yau kuma gashi Allah ya kawo ni inda ake kaunar yaya ake son haihuwa.
Ganin abun nasa ba mai karewa ba ne yasa na nufi gurin da nake aje tsintsiya na dauka na dawo gurin da zimmar gyara gurin sai ya kai hannu ya rike hannuna.
“That's my condition idan mace tana da ciki bata aikin komai sai cikin ya tsufa”
Kallon mamaki nai masa.
“Wani irin ciki dan Allah what if malaria ce?”
Dan murmushi yai murmushin dake nuna alamar be jidadin kalmar ba, ya karbe tsintsiyar ya aje ya matsa kusa da ni ya rike hannayensa yana min kyakkyawan murmushinsa cikin sanyi murya yace.
“Kin fatar ciki ne mana, da ko ya ko kuma duka biyun Allah ya hada ban ki ba, ina son haihuwa lims ina son yaya, yaya rahama ne sanyin idaniya ne i need my own family too, Hajiya ma tana son na haihu Siyama ni kaina ina son naga yayana na ciki, ko yayana nawa zaki haifa min ina so ni dai fatana su zama masu albarka kuma masu tausayinmu”
Sai kuma ya zaunar da ni ya kara jimke hannuna yana kallona cikin idona da idanuwansa da suka koma kalar tausayi.
“Ba zan iya fada miki yadda na ji a lokacin dana rasa Baby, idan har wannan aman da kikai ya tabbata ciki ne zan fi kowa farinciki Lims, and idan kika duba rayuwar nan bata da wani tsayo wata kila zamu dade wata kila ba zamu dade ba akalla ya kamata ace kamin mu bar duniya mu yi sadakatul jariya, sannan mu haifi yayan da zasu rika mana addu'a bakya fatar ki ga jinina za su yi kyau idan sun biyo ki look at your nose”
Ya fada yana jan hancina yana murmushi, nima hancin nasa naja.
“Ko kuma idan sun biyoka ba, Allah ya bamu masu albarka”
Kiss ya mannna min a goshi ya tashi yana fadin.
“Shiga ciki ki gyara jikinki zanje nai sallah na dawo sai na gyara gurin”
Ba musu na tashi na nufi hanyar dakin, bina yai da kallo sai da shiga sannan na ji ya bude kofar falon na fita. Da na shiga bandakin sai na tsaya haban madubi ina kallon kaina.
“Ba dai wani cikin ba ne? Ke dai Mahaifarki a bude take da anyi abu kadan sai ciki, da gangan dai kike yi so kike ki tara min yaya na rasa yadda zan yi nai saurin tsufa, ki hana ni jindadin rayuwa, yaushe kika haye Aiman da har za a ce kin dauki wani cikin? Mtchssss”
Abun dariya wai abunda Aminu yai min a lokacin dana samun cikin Amal ne ya rika dawo min, lallai na yarda bayan wuya sai dadi kuma komai yai farko dole ne yai karshe gashi a yau na aurin wanda jiran haihuwar ma yake ba kyama ba.
Tufafina gaba daya na cire tufafi na sake wanka nai alwala na fito daure tawul a kirjina sai na same shi gefen gadona a zauna yana ta kallon kofar bandakin kamar mai jiran fitowata.
Gaban madubi naje na tsaya sai ya mike tsaye ya tsaya a bayana yana kallona ta cikin madubi wani irin kallon ne da a zan iya fadar ma'anarsa ba.
“Da sannu ina ta maye gurbin abubuwan da na rasa”
Na yi murmushi sai ya rumgume ta baya yana sumbantar kafadata dayan hannunsa kuma a kaina yana shafa kananan tsorayen da ke kaina. Juyowa nai ina kallonsa, sai ya sa hannunsa ya lakaci kumatuna.
“Ya akai?”
Kasa ce masa komai nai sai kallonsa nake ina murmushi a raina ina ayyana irin kyau da Allah ya hore masa ga sura da cikar zati irin na da'namiji.
“Kin yi sallah?”
Ya tambaya yana had goshina da nashi, hakan yasa nai saurin sakinsa na nufi wardrobe na dauko wasu tufafin na saka ya shimfida min pray mat na saka Hijabi, har na yi sallah na gama banda kallona babu abunda Ahmad yake.
“Zan samo wacce zata rika dan share share da mopping girki kuma sai na karbo gurin Hajiya”
“Zan iya komai bama bukatar mai aiki, salon wata ta zo ta karbe min kai”
Na fada da iyakar gaskiyata. Ya dan wara ido ya dawo kusa da ni ya zauna.
“Kina tunani akwai wacce zata kwace place dinki? No one i mean no one”
“To idan kuma tai creating nata place din fa”
“Ai ba dadin zama za ta ji ba, kin riga kin karbe Hajiya Siyama ni da duk Family na”
“Ni dai ban yarda ba”
“Dole ma ki yarda wannan ka'idata ce indai macce nada ciki zan barta ta ji da dawainiyar cikin ne kawai sai na dauke mata na gida amman banda kaina”
Ya fada da murmushin.
“To yanzu shikenan sai ka cewa Hajiya ina da ciki Fisabilillahi sati daya da kawo ni?”
“A a ba fada mata zan yi ba, sai sai tace ba mu da hakuri mun yi ciki tun a waje, abun ai da kunya, amman kuma idan kika yi wata 8 kika haihuwa ganewa za yi fa?”
Magana yake da ni yana zaro ido kamar mai magana da wata karamar yarinya har da bude baki. Ni ban sansan lokacin da na fashe da dariyar ba na buge masa bakin sai ya rumgume ni yana kissing dina.
Kamar wasa, abu ya zama na gaske ko kofina Ahmad baya barin na dauke, idan ya bar ni na yi wani aikin sai idan baya nan, wata tsohuwa aka dauko tana mana aiki wanke wanke da shara sai mopping da karbo mana abincin gurin Hajiya, ban san abunda ya fadawa Hajiyarsa ba kullum sai ta kawo min abincin rana da dare wani lokacin kuma idan bana sha'awar abincin sai ya siyo min. Sai dai tun wacan aman da nai ban sake yin wani ba, kuma a kullum sai Ahmad ya tambaye ni me kike ji me kike so ina ke maki ciwo idan kin ji wani abu ki fada, haka yake kula da ni kamar wacce mai cikin fari, idan ya fita kuma ya ga wani abun kwadayi sai ya siyo min wai be sani ba ko ina so.
Be barni naje gida ba sai da nai wata uku da kuwa da irin kewar da nayi da ganin su Inna da Mama, suna Namra kam ko wane weekend sai ya dauko su sun zo mana hutu. Kowa fadi yake na canja wai fuskata ta kara cika fari na ya fito kamar ba ni ba, ni kaina na san na canja domin ina jin nauyin jikina a yanzu sabanin da. A gidan na wuni sai dare yaje da kansa ya dauko ni bayan ya shiga ya gaisa da su Mama yai musu alheri sannan muka kamo hanya.
“Zaki ci tsire?”
Yana tambaya na hade yawu dan na hango mai tsiren yana gasawa gefen hanya. Sai ya faka motarsa ya fita ya siyo min ya dawo.
“Sauran ice cream”
“A a ba ki san sanyi yana effecting abunda ke ciki ba? Na lura da ke kullun sai kin sha ruwan sanyi fa sai ma na cire makulin fridge din nan ai”
“Ai kadan nake sha”
Be ce min komai ba ya faka gefen titi ya sake fita ya siyo min ice cream sannan ya dawo motar a lokacin ni kam har na yi nisa da fara cin tsiren.
Ko da muka isa gida na cinye rabi sai dai ba ni kadai ba har da shi dake tukin miko min bakinsa yake na saka masa. A part dinsa yai bakin motar ya zagayo ya bude min kamar yadda ya saba na fito rike da kedar sai ya rufe motar sannan ya karba ledar hannuna.
“Jira ni a nan na fito Hajiya na da bako zaki je ki gaishe shi”
A gurin na tsaya har ya shiga ciki ya fito, sannan ya bude motarsa ya dauko tissue ya gyara min bakina kamar wata karamar yarinya ya jefar sannan ya rika hannuna muka nufi part din Hajiya. Sai muna daf da shiga sannan ya saki hannun nawa ya bude min kofar falon na shiga bakin kumshe da sallama Hajiya ce kadai a falon sai mai aikinta sam ban lura da su Kabir ba da wata mai zaman mahaifiyarsa wace suka tafi waje tare da ita da matarsa da wasu mutanen da suke tare da su ba sai da naje zan zauna. Aiko ba shiri na gwalo ido baki saki ina kallonshi shi ko sai dariya yake min.
“Kabir.....?”
“Na'am..... ”
Kara zaro ido nai jin muryarsa ce da gaske kuma gashi har ya amsa min ga shigarsa tsaftsaf cikin kamala, aiko na nufi cikin wani irin mamaki da bazata sai jin nai an rike ni an dawo da ni baya.
“Ke”
Sai na juyo na kalli Ahmad baki saki farinciki