Showing 66001 words to 69000 words out of 217237 words

Chapter 23 - GOBE NA Compelet Book by Khadijah Candy.txt

24 Sep 2025

173

ne, duk wani buri da nake da shi akan ki ne, na san kin yi jihadin aurena bayan kin san bana iya komai, wannan kadai ya isa ya nuna cewar kina kaunata, amman be isa ya wadatar da cewar za ki iya tsare kanki ba, wannan abun da ya faru laifina ne na cutar da ke, taya son rai yasa na cilasta miki aurena bayan na san ba zan iya sauke hakokinki ba, komai kika aikata ba ki yi laifi ba Halima saboda ni ne ba mutum ba, da ace ni din namiji ne kamar kowa da duk hakan be faru ba da baki rasa komai ba”

Hannayensa ya kai ya riko fuskata ya matso da tasa fuskar daf da tawa yana hawaye kamar yadda ni ma nake.

“Wannan sirrinmu ne, babu wanda zai ji? Karki fadawa kowa mu bar wannan a tsakaninmu, na miki alkawari ba zan ta a fadawa kowa ba, babu wanda zai ji wannan abun daga gareni, kuma zan cigaba da zama da ke kamar yadda muka saba, na sani ni ma wannan jarabawata ce, and i think this is the only way da zan iya repay na aurena da kika a yadda na ke marar lafiya, saboda Allah ya kaddaro min haka a rayuwata, na yafe miki har Allah na yafe miki kuma ina fatar Allah ya yafe miki....!”

Yana kaiwa nan ya hade yawun bakinsa ya dauke hannayensa daga fuskata ya juya yana cigaba da hawaye ya fice. Ban yi zaton akwai wani sauran karfi a jikina ba, a take kafafuwana suka fara rawa sai gani a kasa zaune jikina na ta rawa kamar wacce ta fito daga cikin kankara.!




ABDALLAH POV.


Cikin wani irin bachin rai ya shigo gidan, tun daga yanayin parking dinsa ma ya isa a gane hakan balle kuma idan a kai arba da fuskarsa, zuciyarsa har wani bugawa take da karfi kamar zata fito.

Dukan yaransa suna falo kasancewar yau Thursday babu islamiya school, suna masa sannu da zuwa amman be amsa musu ba kai tsaye ya nufi dakin Mahaifiyarsu. Tana zaune saman gado tana waya ganinsa da kuma yanayinsa yasa ta katse wayar tana kallonsa.

“Me yake damunki Suwaiba?”

Da karfi ya aika mata da tambaya sai da hantar cikinta ta kada.

“Me na aikata?”

“Ba ki san abunda kika aikata ba? Ba a nan muka gama maganar Halimatu ba? Akan me za ki dauki wannan maganar ki kaita social media a page irin wannan?”

“Ba ni bace ni ban kai komai a page ba.. ”

“Ba ke bace wacece? Taya za asan da labarin idan ba ki fada ba? Har da sunan Namra? Da maganar School fees? Haka kawai ki dauki maganar da an riga an yi ta ki saka a media? Wace irin shawara kike nema? Kin san mutane sai zagina suke, a ina za su sama miki mafitar? Kina tunanin idan Halima ko Abdulhamid suka ga wannan ya za su ji? And look at the way da kika fadi labarin is like zargina kike ma? Kin ja ana ta tsina mana alrbaka ni da ita”

“Maganar kenan Halima Halima....”

Ya kara matsowa kusa da ita yana nuna mata wayarsa da ke hannunsa.

“Yes Halima Halima, Halima yar uwata ce, kuma ni ba mazina ce ba ne, ban nemai matan waje ba ma babu yadda za ayi na nemi yar'uwata yar'uwar ma matar dan'uwana, ko a lokacin da Halima take gidan Aminu ban neme ta ba balle yanzu da take auren dan'uwana, ni ba mahaukaci ba ne kuma na jahili ba ne ba zan taba neman aikata Zina da Halima ba har abada! no matter how much I love her, ki shiga hankalinki karna sake jin sirrin gidan nan a media”

Yana fadar hakan ya juyawa ya fice daga dakin cikin bacin rai. Second to last sentence na sa ya fi komai rudata ya yanke mata hanzari kuma ya jefata a duniyar tunani.

‘No matter how much I love her....’

Those that means Abdallah yana son Halimatu? Zargin da yan comments suke ya zama gaskiya kenan? Cewar da suke yana son ta ne wasu kuma na fadar cewar yana tarayya da ita ne ya zama gaskiya kenan? Ada kam sam ita bata kawo ma kanta wannan tunanin ba, ta fi zargin ko Abdallah yana son kanenta ne, amman yanzu kam gaskiyarta fito. Da sauri ta kunna data ta shiga page din da ta tura neman shawara ta shiga kara duba Comments din followers.



_Al-hamdulillah, mun dawo fatar dai Yan Team Halimatu da Abdullah da Abdulhamid da Ahmad har ma da Aminu ba su yi fushi ba 😊_
7/21/21, 10:44 PM - Buhainat: https://chat.whatsapp.com/C40KoSeXq9l35nIiFXS1Rz

*GOBE NA...*

By Khadeeja Candy


2️⃣3️⃣

Na kan dora komai a mizanin kaddara, na yarda dukan abunda ya same ni ko zai same ni rubuttacen al'amari ne daga gurin mahaliccina, wani be isa ya goge min ba kamat yadda ban iya na yayewa kaina ba.

Wannan ma yana cikin kaddararki Halimatu, haka zuciyata take yawan fada min kuma ina samun natsuwa sosai idan na tuna cewa ko wane abu da izinin Ubangijina yake samu na. Iyakar kokarin da nai na danne zuciyata ne daga kokarin aikata wani abu marar kyau wanda wani bangare nata yake hararo na ke ganin kamar mafita a gareni. Tun daga lokacin ba mu sake hada shimfida da Abdulhamid zai ba, ma'ana dai be sake leko dakina ba kamar yadda ni ma ban sake taka kafata dakinsa ba matukar yana a cikin gidan, ban fasa masa girki ba be fasa ci ba, ban kasa mika masa ko wace irin gaisuwa ba, sannu da dawowa, Allah ya tsare daman halina ne. Sai dai ban sake ganin walwalar fuskarsa ba kamar yadda walwalarsa ta hana tawa walwalar.
Idan ina zaune a falo baya zama, idan kuma yana zaune na zauna sai yai kamar ya tsargu a take zai tashi ya shige dakinsa.

Ban taba ganin laifin Abdulhamid min akan wannan ba, idan na saka kaina a matsayinsa ni kaina na san kwatankwacin abunda zan yi kenan, ba lallai ne ya gasgata ni ba, kamar yadda ba kowa zan fada haka ya yarda ba, sai dai abunda yafi min ciwo kallon da yake min na cewar na ci amanarsa.
Ina ji ina gani zaman gidan yaki yai min dadi, na kasa sakewa, kwanciyar hankali yai min kwara walwala ta yi min bankwana, kuka da damuwa suka kwankwaso min kofa.

Har ta kai bana iya bachi idan lokacin bachin yai, sai dai na raya dare da sallah ko kuma na zauna nai ta kallon sillin ko da kuwa bana tunanin komai bachin ba zai dauke ni, da rana kuma sai na tsargu ina ganin kamar ni ce kadai nake cikin matsala. Da kaina na fita chemist din dake unguwar na siyo maganin mura na ruwa a duk lokacin da na ji ina bukatar bachi sai na sha, wani abun mamaki a take bachi zai dauke ni kuma sai na manta da duk wata damuwa dake tare da ni.
Da dare kawai ba, da rana ma idan na ji damuwar ta matsa min na dan kan sha sai kuma na samu salama da natsuwa, na sani akwai illa abunda nakr sha, kuma na san ba abu ne mai kyau ba, mace kamar ni mai yaya hudu ace na buge da shan kayan maye domin na samu bachi, wannan ma yana saka ni damuwa sai dai babu yadda na iya idan ban yi hakan ba ban san abunda rashin bachin zai janyo min ba. Gaba daya yanayi na ya canja ni kaina na sani, bana sakewa kamar da ga ciwon ido ya saka ni a gaba har ta kai bana iya daga idon sosai.
Tun lokacin da abun ya faru ban sake fita da sunan zuwa unguwa ba ko wani gurin, Hajara ma ban sake labarta mata komai ba, a ganina duk wanda zan fadawa ba zai sama min mafita ba dan haka babu amfanin fallasa sirrin nawa.

Yau ma kamar jiya ta kama weekend sai dai yau Sunday ba Saturday ba, Abdulhamid tun safe ya fita kamar yadda ya sabawar kansa yanzu da fita ranar weekend ya wuni a wani gurin sai dare zai dawo, bayan da can ba haka ya saba ba. Lamarinsa na ya bani tausayi ta wani bangaren kuma sai ya bani tsoro na kan yi tunani anya ko wace mace zata iya sadaukarwar da nai? Auren mutum kamar Abdulhamid a lokacin da tawa kaddarar ta same ni sai ya juya min baya? No be kamata nai wannan tunanin ba, shi ai ba shi da lafiya rashin lafiyarsa babbar damuwarsa ce sai kuma ni na kara masa wata, ya fa kamata na gane wani abu a duk lokacin da wani ya rabe ni sai wani abu marar kyau ko kuma na bakinciki ya same shi, misali kamar Kabir ko yana ina ma yanzu?
Ni kadai nake zaune a falona ina ta sake sake da tunani kala kala wasu masu amfani wasu kuma marar amfanin. A tsorace na kalli kofar falon saboda knocked din da akai, haka nake yawan tsorata ko iska ya kada sai gabana ya yanke ya fadi. Sai da na sake jin an kwankwasa kuma na ji kamar hayani a waje sannan na tashi na nufi kofar na bude. Kanwata ce Hafiza tare da Namra da Aiman da Adnan da Amal da kuma wata yarinyar da ban waye ta sosai ba. Da gudu suka rumgume ni su dukansu wani kalar farinciki na ji wanda na dade ban ji irinsa ba, lallai ya'ya rahama ne, a take idona ya cika da kwalla ni kaina na san na yi kewar ya'yana, dukawa nai na dauki Amal muka shigo falon tare da su.
Bayan sun huta na dauko musu abincinmu, sannan na shiga dora wani domin ban san da zuwansu ba kuma nasan wanda za su cin ma ba isarsu zai yi ba, ina cikin kitchen din Hafiza ta same ni da zancen siyayyar da Aminu yake ta musu Namra a kwanakin nan, daman kuma Mama ta fada min a waya a duk lokacin da ya zo sai ta fada min domin ita ma mamaki abun yake bata kamar ni. Daga ni har sun mun rasa dalilinsa na nunawa yarana kulawa a yanzu, bayan siyayya ma duk bayan kwana biyu sai ya zo ya fita da su ko kuma ya duba lafiyarsu.

“Ni kaina Hafiza na rasa ganene dalilin Aminu na yin haka, mutumen da can ma be kula da yaran ba, har cewa yake na tara masa yara har hudu da kurciyarsa, yanzu kuma shine yake nuna musu kulawa abun yana bani tsoro”

“Ko ma minene nufinsa ba zai samu nasara ba, matukar dan ya cutar ke ko su zai yi”

“In-Sha-Allah, ba zai samu wata dama ta yin wani abu ba”

“Amman Anty miyasa kika daina zuwa gida? Baba ma kwana biyu ciwon kafafuwansa sai tashi suke?”

A take gabana ya fadi hankali kuma ya tashi abunka y'a da uba.

“Subhanallahi amman shine ba a fada min ko a waya ba?”

“Ba ke kadai ba ko su Anty Murja da suke nesa ya hana a fada musu wai za a daga musu hankali kawai, kin san ciwon nasa idan ya tashi yau ciwo gobe lafiya haka yake masa shiyasa”


“Allah ya bashi lafiya”

“Amin, Mama da Inna sai zancen ki suke su suka ce na zo da su Namra ma mu duba ki lafiya kike? Kuma gaskiya na ga alamar ba lafiya ba”

“Kamar ya?”

Na tambaya ina kokarin kirkiro murmushi.

“Haba Anty kalle ki fa, duk kin rame kin koma kamar ba ke ba, ke da kika da jikinki mulmul ma sha Allah amman yanzu ko ki na fi ki ki ba, duk kin yi baki kin lalace Gaskiya akwai abunda yake damunki”

“Babu abunda yake damuna Hafiza”

Ina fadar hakan na juyo na fito daga kitchen din domin bana son ta cika ni da tambayoyi. Ina fitowa Namra ta fara bani labarin Daddynsu yana zuwa gurinsu yanzu har ma siyayyar da yai musu, tana cikin lissafa abubuwan da ya siyo musu sai Adnan ya karbe daga nan sai Aiman har da Amal ma labarta min take abubuwan da Daddy yake musu, wani irin farinciki da annushuwa nake ganin a fuskar yayana, da alama hakan da yake musu a yanzu yana musu dadi, ko ni da nake babban na so mahaifina a kusa da ni balle su da suke kanana kuma babu ni a kusa da su. A nan Namra take nuna min new friend dinta mai irin sunanta.

“Momi kin tuna lokacin dana bata a gidansu aka kai ni, kin suna ita ce yarinyar gidan”

Sai a lokacin na tuna har na wayi fuskarka.

“Momi Daddynta yana sonta sosai komai siya mata yake, kuma har shi yake zuwa daukarta idan zata koma gida”

“A ina kika hadu da ita?”

“A school din mu take ita ce tana so na friend tace ita bata da friends kuma Momi ita ma sunan Mominta Halima, amman ta rasu.... ”

Hannu na mika mata alamar ta zo, sai ta taso daga inda take zaune a kan Center tebur ta nufo inda nake sanye da English Wears dinta kanta babu dankwali balle ayi maganar hijabi.

“Kin ganeni?”

Na tambaya bayan na rike hannunta, sai ta gyada min kai tana murmushi irin murmushin nan na yara masu kiriniya.

“Momi na fada mata yau za mu zo gidanki shine tace tana son ta ganki, tace daddynta ya kawota kuma ya kawo ta”

Namra ta fada da mamaki a fuskarta, domin ita bata tashi cikin irin wannan gatan ba, da mahaifinta zai mata abu ko kuma ya nuna mata kula balle har ya dauketa ya fita da ita.

“Daddynta yana sonta sosai Momi har da waya ya siya mata, yana bata chocolate komai siya mata yake, kuma gidansu har da motar wasan yara ya siya mata da lilo irin an scul dinmu”

Ta sake fada, ni kuma sai nai murmushi na shafa kanta domin na san abunda yata take ji, kwatankwacin abunda nake ji idan na ga wata mace ta yi dacen mijin aure.

“Kin yi dacen uba, Allah yai miki albarka ya jikan mahaifiyarki”

Da kanta ta amsa min da Ameen kamin ta saki hannuna ta nufi gurin su Adnan, da alama dai ta sake sosai da su kamar wasu yan'uwanta.

A gidan suka wuni tare da Hafiza sai dare suka tafi, duk yadda ta so na labarta mata damuwa ban yarda na bude mata cikina ba. Tafiyarsu da minti ashirin Abdulhamid ya dawo a lokacin ina zaune falo, bai yi knocked ba daman yanzu ya gane sai dai ya saka key ya bude kofar falon ya shigo. Na masa sannu da zuwa ya amsa min irin amsawar nan kamar an masa dole, a yadda na lura Abdulhamid yana zaune da ni ne irin zaman nan kamar na dole domin ba zaka ga zamantakewar aurenmu ka ce zaman ne na masoya ba. Na so na gabatar masa da zancen zuwa gida duba Abbah a wannan lokacin sai kuma wata zuciyar ta hana ni, na yanke shawarar da safe zan fada masa idan ya gama karyawa.
Ashe abunda ban sani ba Abdulhamid tafiya zai yi a garin da ban san ina ba ne, sai da safiyar ta waye bayan na gama hada masa abun karyawar na yi ta jiran ya fito shiru be fito ba, har tara da rabi ganin be saba kai wa hakan ba yasa na shiga dakinsa sai na samu dakin wayam babu kowa a ciki sai wata farar takardar a saman gadonsa, karasa nai na dauki takardar wacce ke saman kudin da ban san na minene ba har sai dana karanta takardar.

“Tafiya ta kamani zuwa Kaduna, zan dawo on Tuesday ko Wednesday ga kudi nan ki yi amfani da su.....”

Ina gama karanta takardar hawaye ya wanke min fuska, a yanzu bana da martabar da Abdulhamid zai kalli ya fada min cewar zai yi tafiya? Zauna nai bakin gadon ina tuna irin rayuwar da nai a gidan Aminu, a da na yi tunanin komai ya wuce, ashe abubuwan da zan fuskatanta suna da yawa, ko wace mace da irin jarrabawar da take tsintar kanta a cikin a gidan mijinta, wata mijinta neman mata yake, wata ya hana ta ci da sha, wata ya hana ta lokacinsa, wata ya hana ta kudin kashewa. ni kuma irin tawa kaddarar kenan.

“Al-hamdulillah”

Na furta sannan na share hawayena na taso na fito daga dakin, dakina na dawo na bude drawer ta na dauko maganin bachi na kurba kadan na kwanta, da niyar nai bachin kadan sai ga shi na zarce da dogon bachi ban farka ba sai la'asar. Azahar ma sai da na ramata sannan na dora da la'asar din, haka kuma be min dadi ba domin ban saba ramuwar sallah ba, idan ba da wani dalili mai karfi ba. Ganin ni kadai ce a gidan yasa ban wahalar da kaina wajen girka komai ba, daman can ba ci nake ba saboda shi nake girkawa kuma yanzu baya ma garin.
Wayarta na dauko na kira layin Baba, ringing biyu ya dauka na gaishe shi cikin girmama da kauna ya amsa min da kuzarinsa.

“Baba ya jikin?”

“Al-hamdulillah jiki da sauki sosai sai da suka fada miki ko?”

“Hafiza ta zo jiya ta fada min, Baba ciwo ba abun boyu ba ne, musamman irin naka da idan kafafuwan suka tashi baka iya takasu, ya kamata aje asibiti a sake dubawa”

“Kafafuwan da sauki fa, yanzu nan ma Abdullahi ya dawo da ni gurin gashi, shi ke kaini aka gasa kafafuwan kullum, da sauki sosai ki kwantar da hankalinki”

“To Baba na so na shigo sai Abdulhamid yai tafiya, amman idan ya dawo ko kuma na yi waya da shi na nemi izininsa zan zo na dubaka”

“Allah ya miki albarka Halimatu, karki zoba da izininsa ba, ayi ta hakuri”

“To Baba Allah ya kara maka lafiya”

Da amin ya amsa na sauke wayar ina hawaye, duk yadda na so na daga waya na kira Abdulhamid na tambayi izininsa na zuwa gida sai na kasa, daga karshe na yanke shawarar tura masa sako. Ko minti biyu ba ayi ba ya dawo min da reply har da kalmar da nake zaton zolayace kawai ko kuma ya rubutu min ne saboda ya saba rubuto haka a karshen ko wane

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login