Showing 51001 words to 54000 words out of 217237 words
sai ya saka hallabiyarsa ya dauko makullinsa ya bude mana mota muka shiga ni da ita, abun ka da yaro sai ta kara lafewa a jikina har da saka hannayenta ta rumgume ni ta bata fuska sosai kamar zata fasa kuka. Ban ce masa komai ba har muka isa gida duk kuwa da kasancewar shi din yana ta min fira sama sama. Wani abun mamaki tun da na shiga gidan Namra ba ta yi na'am da ganina ba, kallo na ma sau daya tai ta dauke kanta bata sake kallon inda na ke ba, Aiman dai na tarar yayi bachi Adnan ne kawai ke kwance tsakar gida rike da karamar wayar Haulat yana kallo. A lokacin da na aje Amal sai ta fara kuka alamar bata son rabuwa da ni da sauri Namra ta zo ta dauke ta ta nufi dakin Inna da ita ba tare da tace min komai ba. Raina ya sosu ba kadan ba, kar dai ace yayana sun fara tunani ko na zabi wani ne na bar su? Babu ubansu a kusa da su kuma ni na na tafi na bar su. Har muka dawo gidan ban sake na yi walwala yadda ya kamata ba, sai dai ko kadan hakan be damu Abdulhamid ba saboda a tunaninsa ina son saka damuwar yara a raina ne.
A haka muka kwashe wata uku na saka sakewa da shi kamar yadda muke a da, har ya fara zargi yana tambayar ko dai na fara kosawa da zama da shi ne haka ne saboda baya iya komai, na fada masa ba haka ba ne amman be yarda ba har ta kai ya fara kokarin gamsar da ni da hannunsa, hakan kuma be kara min komai ba sai damuwa na fada masa bana jindadin yadda nake zaune dabam da yayana ne.
“Ai aure ya gaji haka, yaran ba daya ba ne Halimatu balle a ce a dauko su mu zauna da su, kuma tsakani da Allah ba zan biye miki ba idan har aka dauko yaranta zan takura kuma zan cutu ba dan bana son su ba sai dan irin tsarina kuma na ra'ayina bana son yanayi kin san ni, kuma any how ina iya rumgumarki ko nai kissing dinki idan akwai yara ba zan iya ba”
Ban ce masa komai ba, iya kar kokarin da nai na fahimtarsa ne da kuma yi masa uzuri sai na danna nawa damuwar da kyautata masa zato tun da shi be taba yin yayan ba kuma be saba da su ba na sani shi ba kamar Abdallah ne ba.
“Na san kina hakuri Halimatu na zama da namiji irina mai kamar fanko, shiyasa matsayinki yake da girma azuciya saboda kin yi jihadin da ba ko wace mace ce zata iya ba, ko da kuma kin bukaci rabuwa da ni a yanzu ba zan ga laifinki ba....”
“Na aureka ne saboda ina son ka Abdulhamid, ba aureka dan saboda nai sadaukarwar kawai ba, sai dai son ka ne ya fara gina zuciyata tun farkon fari da soyayyarka ka fara sanin miye so”
Na fada ina kallon cikin idonsa da dukan gaskiyata, murmushi yai ya kai hannu ya shafa fuskata.
“Ina ta saurare ina ta jira.... ina ta tsammani yaushe zan samu lafiya na nuna miki irin son da nake miki? Wata kila nan kusa ne wata kila kuma nesa ne, ban sani ba, ba a sanar min ba, fata kawai na ke yi, sai dai ba zan gushe ina neman taimakonki na addu'a ba da kuma rokon ki kara hakuri da ni har zuwa lokacin da zan samu lafiya, idan kuma lafiyar ta gagara samuwa zan sawwake miki kije ki auri mai lafiya saboda kar na tauye miki hakki, ba burina ne nai ta kallonki a haka ba Halima”
Tausayinsa ne ya nemi gurbi a zuciyata yai kwance, kalamansa suka rasa ni kaunarsa ta kara samu muhallin a zuciyata, murmushin na sakar masa sai ya kama hannuna ya kai saitin zuciyarsa.
“Ina jinki sosai a zuciyata, ina jin kaunarki fiye da yadda kike tunani, dan Allah ki tsare min mutunci, kuma ki rika kula min da kanki ba fata na ke ba amman ina fargabar ranar da wani abu zai faru ace za ki bar ni”
“Ba zan taba barinka ba ban aureka dan na rabu da kai ba”
“Thank you”
Ya fada yana kissing din hannuna. Ni kaina na san Abdulhamid na so na, na san mijina yana kaunarta kuma ina kaunarsa amman na rasa dalilin rashin sakewa da samun farinciki da bana yi a yanzu wanda hakan ke saka shi cikin damuwa.
“Gobe zamu je mu gaishe da Hajiya,ya kamata muje cikin daren nan mu siya abunda za mu rika mata domin da safe zan aje ki can idan zan wuce gurin aiki kuma ba lallai ace lokacin masu super market sun bude ba”
Tashi nai na shiga dakina na canja tufafi jikina a tsakanin shiryawa da na shi be wuce minti ashiri ba ya yan kai sannan mu ka fito, da kansa ya bude min motar na shiga sannan ya shiga mazauninsa ya tashi motar, da mu kai bakin gate sai ya fita ya bude mana gate din ya fita da motar sai kuma ya rufe ta muka kama hanyar jifatu.
Har muka isa zuciyata raya min take na fada masa gaskiya, ko ba komai ai shi mijina ne be kamata na boye masa ba, abunda ban sani ba ashe shi fira yake ta min ban lura ba sai da ya kira sunana.
“Na'am”
Na amsa da sauri a daidai lokacin da kiransa ya dawo da ni hayyacina.
“Me kike tunani?”
“Komai bana na tunanin komai”
Da hannu ya nuna min alamar na bude motar na fita yana ta kallon yanayi kamar mai tuhumar wani abu, a hankali na bude motar na fito kamar wata marar lafiya, a tare muka jera muna tafiya daf da za mu shiga cikin gurin wani mutume mai kama da mahaukaci ya miko mana hannu alamar mu ba shi, da na kalleshi da kyau sai na nemi damuwata ta da tunani na rasa, hankalina ya tashi har na kusan rikicewa. Kabir ne Kabir abokin aikina Kabir din da ya kamu da lalurar saboda ni ashe da gaske abun ya taba kwakwalwarsa, da gaske ya haukace. Ni yake mikowa hannuna yana ta kallona sai kuma ya juya yana kallon Abdulhamid ya mika masa hannu, Abdulhamid ya saka hannunsa aljihu ya ciro dari biyu ya mika masa, sai ya juya ya fara tafiya yana dingishi alamar kafar tasa akwai ciwo ko rauni a gurin.
“Haima kuka kike yi?”
A rikice na kalli Abdulhamid ba dan na san abunda ya fada ba sai dan sunana da na ji ya ambata.
“Kabirr...... ”
Na ambaci sunansa ina maida numfashi.
“Kin san shi ne?”
Wannan karo na ji abunda ya fada hakan yasa nai saurin gyada masa kai na juya da sauri fuskanci kofar shiga Jifatu din.
“Kuka fa kike”
Da na taba fuskata sai na ji hawaye masu zafi suna sauko min, da sauri na share hawayena na karasa ciki sai ya biyo bayana, har na yi zaben abunda za mu siyawa Hajiya ban daina hawaye ba, babu yadda ban yi ba dan na tsaida hawayena amman abu ya ci tura. Na riga shi dawowa cikin motar na zauna kamin ya biya kudin siyayyar, a front na zauna ina ta kallon Kabir da ke mikawa masu zuwa gurin hannu idan aka ba shi sai ya koma ya zauna, idan ya hango wani ya sake tasowa, kallonsa be haifa min da komai ba sai bakinciki da kuka mai tsanani? Rayuwarsa da baya ta dawo min, ina ta ganin murmushinsa da kulawarsa a kaina. Mutumen da ke da son kwaliya ga tsafta yau shine a wannan halin? Ina matarsa? Ina mahaifiyarsa? Ina danginsa? Miyasa suka bar shi haka babu kulawa?
Hango Abdulhamid tafe yasa na share hawayena na yi saurin gyara fuskata, gidan baya ya bude ya saka ledar sannan ya dawo mazauninsa ya tashi motar, har muka isa gida be ce min komai ba yana farkin na bude motar na fita ina shiga falo wani sabon kuka yai min lale marhabun hakan yasa na nufi kitchen da sauri na wanke fuskata.
“Ba zan hana zuciyarki tausayin wani ba, amman yana da kyau idan za ki ji tausayinsa ki yi a bayan idona ba gaban idona ba, na ji zafi sosai Halima ace hawayen nan saboda wani namijin kike zubar da su ba ni ba, abunda ba ki taba sani ba shine ina da tsananin kishi, ina kishin ace matata ta kula wani ba ni ba, I'm sorry to say yaran nan ma idan na tuna ba da ni kika haife su ba ina jin babu dadi, saboda ina tsananin sonki kuma ina kishinki, na san idan nai shiru zan cutu ne kuma na kwari kaina ke kuma kin kasa gane haka....”
Magana yake min a yayinda yake tsaye a kofar kitchen din yana kallon bayana ni kuma ina kallon windows din kitchen wasu sabbin hawayena na sauko min. Ban yarda na jiyo ba har sai da na ji motsi ficewarsa daga kitchen din, sannan na dawo dakina na shiga bandaki nai kuka mai isa har sai da na ji amai ya taso min sannan na sassautawa kaina, sai dai ban samu salama ba har sai da nai aman sannan na hada ruwan nai wanka na shirya cikin kayan bachi na hau gadona na kwanta, a yanayin yadda ya nuna min bacin ransa ban yi zaton zai zo dakina ba, domin haka Aminu yake min a duk lokacin da muka samu tsabani, sai dai a mamakina sai ga Abdulhamid ya shigo dakina ya kwanta bayana yana sumbatata ya saka ni a kirjinsa ya rumgume ni sosai.
“I Love you”
Shine abunda na san ya rada min a kunne kamin bachi yai gaba da shi, ni kan har kusan biyu saura na dare ban yi bachi ba, babu komai a duniyata sai tunani da damuwa. Kiran sallah farko muka farka shi ya tafi masallaci ni kuma na nai sallah a gida, Misalin takwas muka karya sannan na shiga nai wanka shi ma ya shirya muka fito da zimmar zai aje ni gidan Hajiya ya wuce gurin aiki, ya lura da yadda na saka sakewa tun jiya damuwa karara a fuskata sai dai be min magana ba har muka isa. Tare muka shiga cikin falon sai muka same Hajiya zaune a kujera daya ita da Abdallah, tun da na kalleshi sau daya ban sake kallon inda yake ba har na zauna sai dai jikina yana ta ba ni cewar idonsa na kaina, ni kam na manta when last na saka Abdallah a idona ma dan ni har na manta da shi a duniyata.
“Hajiya ina kwana”
Ya mika mata gaisuwa ina dan risinawa, sai tai kamar bata ji ba ta maida hankalinta gurin Abdulhamid da ke magana da Abdallah.
“Lafiya kake karyawa a nan”
“As you know ko Madam tana nan ina karyawa a nan ai balle yanzu da tai tafiya”
Yadda Abdallah ya amsawa dan'uwansa sai da abun ya ban mamaki domin babu alamar shauki ko wani far'a a tare da shi.
“Matarsa bata nan taje Kaduna gurin biki”
Hajiya ta amsawa Abdulhamid, sannan ta kalli inda nake ta dauke kai kamar ta ga wata makiyiyarta.
“Hajiya ina kwana”
Na sake miki mata gaisuwa,wannan karon ta amsa amman sai da ta dauki lokaci, ban damu ba daman tun da na auri Abdulhamid na lura da Hajiya kamar bata na'am da ni, ledar siyayyar da muka mata na tura mata gabanta sai kawai ta kalli ledar ta mike tsaye ta nufi dakinta tana fadin.
“Kai ma ka karya ko na kawo maka abun kari”
“A a ni kam sai da muka ci abinci muka fito gida”
Ya fada yana kallona da murmushi a fuskarsa, ni ma murmushi nai masa kamin na maida dubana gurin roben da ke saman glass table din da Abdallah ya aje mug din hannunsa. Farin zobe ne mai kamar na silver da alphabet din A a ciki, alphabet din baka kamar na wacan zoben da na gani a daren bakinciki.
“Kin ji sai na dawo zan zo na dauke ki”
Abdulhamid ya fada min haka bayan ya mike tsaye, kai na gyada masa sai ya shiga dakin Hajiya yai mata sallama ya fice, kamar fitarsa na ke jira nai saurin kai hannu na dauki zoben da ke aje, da sauri Abdallah ya miko hannunsa fuska a hade ya rike hannuna.
“Ba ni zobena”
“A ina ka same shi?”
Nima na tambaya rai a hade cike da tsananin mamaki, a maimakon ya amsa min sai kawai ya watsa min wani kallo da ban san ma'anarsa ba, tunani be tunatar da ni cewar a falon Hajiya muke ba, ban kawo a raina cewar Abdulhamid zai iya dawowa ba, ban damuwa da rikon hannu da karfi da Abdallah yai ba saboda hankalina ya dauku akan zoben da son sanin dalilinsa, daman ya san za mu zo da har yasa ya cire zoben ya aje a inda zan gani ko dai na yi gamda da katar din ganin ne? Motsi muka ji daga bakin kofar shigowa falon alamar za a shigo hakan yasa yai saurin sakin hannuna ya sake miko min dayan hannunsa.
“Ba ni na ce”
Ya fada a tsawace wanda hakan yai daidai da shigowar Abdulhamid a falon.
“Minene?”
Ya fada yana kallon yanayi da nasa. Da sauri na saki zoben ya fadi kasa shi kuma ya mike tsaye ya kai hannu ya dauka ya fice zuwa dakin Hajiya, a sannan Abdulhamid ya karasa kusa da ni ya miko min wayata yana kallon fuskata.
“Ga wayarki”
Ya miko min yana aje mumfashi a hankali sannan ya juya ba tare da ya sake ce min komai ba ya fice, dafe kaina nai gabana na mugun faduwa, faduwar da ba ban san ta Minenen ta fargabar kar ya zargi wani abu ko kuwa ta fargabar ganinmu ko kuma ta fargabar zoben da na gani a hannun Abdallah?
AHMAD POV.
Kansa a kasa yake sauraren Momy, idonsa sun rikide gaba daya saboda bacin rai, ta ya yanzu Momy za ta zo masa da wannan maganar? Wani irin magana ce wannan wacce hankali ba zai dauka ba, taya zata hana shi auren wannan saboda kawai ita Shuwa ce?
“Wallahi ance mallake miji suke ni sam ban yarda ka aureta ba ka nemo mata”
Dagowa yai ya kalleta cikin tsananin bacin rai da damuwa.
“Amman tun farko da na fada miki family yarinyar na fada miki wacece ita ya kamata ki hana ni ba sai yanzu da yar mutane ya kamu da so na ba, har na gaisa da mahaifita sun yi magana sun ce na turo magabata sannan ki kawo wannan maganar haba Momy wannan na reason ba ne.... ”
Zare masa ido tai ta wurgarda remote din tv a kujera.
“Idan a gurinka ba komai ba ne, ni a gurina komai ne, ba zan bari ka auri yarinyar da zata mallake min Kai ba, ka juya min baya ni da Baby Namra ba zai yiyu ba”
Tana kai wa nan ta mike tsaye ta nufi upstairs tana fadin.
“Ai dole ne idan za ayi aure ayi bincike ba zan yarda ka auro min yarinyar da zata canja ka ba, ko wacce zata zo ta kashe ka ta kwashe dukiyarka ba, mata ba abun yarda ba ne musamman na yanzu.... ”
Tana shigewa dakinta, kanwarsa ta taso ta dawo kusa da shi ta zauna tana masa rada.
“Wallahi ka kai je ka kaita gurin wani boka ayi mata asiri ta yarda ka auri wannan yarinyar... ”
Duk yadda yake cikin bacin rai sai da ta saka shi murmushin dole saboda wautarta, sannan ya mike tsaye yasa hannuns aljihu ya fice daga falon harabar gidan ya fito ya jingina da motar yana cikawa bakinss iska ya san halin mahaifiyarsa idan ta ce bata yarda da abu ba, babu yadda za ayi ta yarda da shi har abada, idan kuma bata son abu babu mai cilasta ta so shi, shi yanzu ya zai yi da matsalarsa a duk lokacin da ya taso da maganar aure sai ta nuna bata so, ya kasa fahimta wace irin uwa ce ita? Miyasa ko da yaushe take kishin ganin yayi aure? Ko take kishin duk matar da ya aura? Forget about the past shi yanzu ya zai yi da yar mutane idan ya barta za a ce ya yaudareta daman can ba auren yai niya ba, after that idan ya nemo wata ita ba Momy zata iya cewa tana da wata matsalar. Kansa ya daga yana kallon katon gidan mai cike da kayan alatu, mi mahaifiyarsa ta nema ta rasa? Then miyasa shi ba zata bar shi ya samu nasa farincikin ba? Miyasa ba zata bar shi ya gina rayuwarsa ba? Kara wayar da ke hannunsa tai alamar sako number Momy ce.
_Ka dawo karfe 8pm_
Yana karanta sakon ya shafa kansa yana busar da iskar bakinsa.
“Ohhh Momy ni fa ba yaro ba ne why all these rules?”
Bude motarsa yai shiga ransa babu dadi yai ma motar key ya danna horn aka bude masa gate ya hau titi ba tare da sani inda zai je ba, gari yake ta zagawa a titi, maganganun Hajiya ne suke ta masa yawo a kai shi ya rasa gane abunda yake damun mahaifiyarsa. Har ya daga wayarsa ya kira abokinsa wanda ya saba labarta masa damuwarsa sai kuma wata zuciyar ta hana shi, he decided ya faka motarsa gefen titi yai relaxing cikin motar for a while sannan ya koma gida, after ya faka motarsa gefen titi ya sauke gilashin motar ya kwantar da kujerar motar tare da cire hular kansa.
Wata yarinya ya hango gefen titi tana kuka, sai da ya kalli ko'ina yaga babu kowa a tare da ita sannan ya bude motar ya fita ya nufi inda take.
“Ke lafiya? Me kike yi ma kuka?”
“Bacewa nai”
Ta amsa masa cikin kuka.
“Garin ya?”
“Muna tare da Mama Hafiza mun zo biki shine kuma yanzu ban ganta ba, tace na zo bakin titi na same ta mu wuce na zo ban ganta ba kuma na koma ban gane gidan da na fito ba”
“Ina Mamanki?”
“Tana can gidanta”
“Babanki fa”
“Ban san inda yake ba”
“Rasuwa yai?”
“Aa tunda ya saki Momy mu ban sake ganinsa ba, ita kuma Momy mu ta auri wani...”
The way da tai masa maganar sai