Showing 330001 words to 333000 words out of 420383 words

Chapter 111 - SAI KA AURENI DOLE BY AYSHA A BAGUDU.txt

dan Allah tashi kije karki karasa zautar min da yaro yana ya kusan haukacewa takarasa mgnr tana murmushi .

"aikuwa yanzu muka fara wasan dan wallahi sai gidan nan sai yayi masa zafi ba dai takamarsa zafin kai ba sai na karya weekpoint dinsa sai na meidashi abin tausayi.

"idan baki meidashi abun tausayi ba shi ya meidake zeey ta bude bakinta zatayi mgn kenan mama ta katseta "ni jeki dan Allah magangunki sun fara sani jin ciwon kai.

zeey tashigo parlour'n tana yatsina fuska kamar taga kashi , shi kuwa yana ganinta ya sauke naunauyen ajiyar zuciya tare da mikewa tsaye ya nufiota yana kokarin rungumarta ta tokare kirjinsa da yatsunta tana furta "lafiyarka malam daga ganin mutun zakayi cikinsa?

ya marairaice murya " plz kiyi hkr karki hanani taba jikinki kefa matata ce.


"may be ka fara hauka ko kuma kasha wani abu wanda yake kokarin taba k'walk'kaunarka ,idan ka manta na tuna maka ka dade da sakina har nayi idda nagama dan haka ka matsa min a hanya in sha iskar duniya.

ta nufi kujera ta zauna tare da d'aura kafarta daya kan daya tana girgza jiki, shima yabiyo bayanta ya zauna kusa daita har cinyoyinsu na gugan juna ya riko tafin hannuta ciki nasa "dan Allah kiyi hakuri da abinda ya faru abaya yanzu ashirye nake danayi komai akanki ciki kuwa har meidake gidana.


" kai kai dan allah malam rabani da wad'an nan zantuttukan naka masu sakani jin wani iri, ko ka meidani gidanka ko karka meidani daman dole zan koma gidanka tunda har karigada ka dawo kasar.

ak yashiga girgiza mata kai sannan yace "what ever you want me to do i will do, gbdy ji nake idan bana tare dake kmr mutuwa zanyi, ki taimaka ki dawo gareni ayanzu .

ammi da eiman dake zaune suna dan tautaunawa akan lamarinsa sukayi sakatoto suna kallonsu tmkr TV cike da matsanancin mamakin abinda ke faruwa agabansu.

abun bai sake dagawa ammi hankali ba sai sanda taji yakamo hannun zeey "kinga tashi mu wuce gidanmu na meida aurenmu .

zeey ta fixege hannuta cikin nasa a fusace tana mikewa tsaye tare da cewa "kana hauka ne abdul a wani garin mahaukatan ka tab'a ganin an yi haka?

" kataba ganin idan miji ya sake matarsa har tsawon wata hudu ya meidata haka kai tsaye batare da an daura sabon aure ba?

yayi saurin girgiza mata kai tare da cewa "gaskiya ba'ayin haka .

"ok to idan ma ka soma hauka ne kayi saurin dawo da tinaninka ,sai an d'aura sabon auren zan iya komawa gidanka da sunan matarka ta juya tabarshi tsaye tana buga masa bombom dinta da suke baje a wa faratin batare da ta kalli inda ammi take zaune ba dan gabadaya yi tayi kmr batasan da wata halitta zaune agurin ba.

yayi sauri biyo bayanta yana kiran sunanta tare da kokarin kamo hannuta taja ta tsaya tare da dakatar dashi "ina km zaka bini?


"zan biki ciki ne mu kwana tare bazan iya kwana ni kadai batare da ke ba ,ta tabe baki "duk watanin nan da uwar wa kake kwana?


yayi shiru yana kallonta batare da yace mata komai ba sai idanunsa daya tsura mata ,
"kaje ga matarka can ku kwana tare .

"ina aibazan iya ba ko ra'bar inda take ma bazan yi ba asalima ni yanzu na tsani ganinta bana son d'aura idanuna akanta..


"wannan km matsalarka ce batawa ba idan ka gadama ka kasheta duk ba matsalata bace..


inna lillahi wa inna ilaihi rajiun shi ammi take furtawa acikin zuciyarta tana sake maimaitawa take km gefen kanta yayi wani irin mugun sara ta mike tsaye da kyar tashiga dakin dan eiman tuni ta rigata barin parlour'n bazata iya ganin takaici ba .

tana shiga dakin taji sound din kukan su'ad sama sama bata tsaya tambayarta dalilin kukanta ba dan ta lura akwai babbar matsala dake shirin kunno kai cikin rayuwarta da mijinta, tunda gashi idanunta sunga komai, abubuwan da abdul ya dingayi da yanayin yadda su'ad din tashigo mata gidan yashiga dawo mata, kai tsaye ammi ta nufi bayi ta dauro alwala ta fito ta shimfida katuwar sallayarta tare da feshe jikinta da turaruka masu sanyi kamshi ta tasoma sallah da niyyar kaiwa allah kukanta.

daren ranar kwana ammi tayi tana kaiwa allah kukanta batare da ta runtsa ba, haka ma su'ad ba'abarta abaya gurin yiwa mijinta addua saboda tasan haka kawai mijinta bazai canza ma farat daya ba batare da wani dalili ba .

kwana uku da dawowarsu ak ya addibi kowa acikin gidan da zance zeey duk wanda yazo masa sannu da zuwa zai dauko masa maganar zeey duk inda zeey tayi yana mane daita gbdy ya manta da wata su'ad a duniyarsa ballanatana rayuwar da sukayi.

gani babu wanda ya kula da lamarinsa yasa ya tashi hankali kowa shi dai a meida masa da matarsa ,matarsa yake bukata hauka ya dingayi sosai .

yayinda duk haukar dayake ko ajikin zeey sai ma wulakaci iri iri data dinga shuka masa su'ad kuwa tunda suka dawo bata zaman parlour ba tana daki ta kunshe kanta tana kuka da kaiwa Allah kukanta.

ganin wannan haukar da ak yakeyi tayi yawa akan zeey yasa dady tattara kan jamar gidan har hjy kakar ak.

zaune suke gbdy'su acikin parlour'n inda ak ya zabga uwar tagumi yana fuskatar zeey ko kifta ido bayason yi ita kuma sai wani shan kamshi take tana yatsina . su'ad kuwa tsurawa mijinta idanu tayi tana kallonsa tunda suka dawo bata sanya shi cikin idanunta ba gbdy duk sai taga kmr ya d'an fada .

dady ne yasoma magana kamar haka "na tattara dukanmu anan ne domin samun maslaha da cigabanmu, abdulkabir ya nemi a meida matarsa dakinta sucigaba da rayuwa byn dagon fushin da ya d'auka daita, dady yayi shiru kana ya numfasa sannan ya meida kallonsa ga ak yacigaba da magana "wannan shine damarka ta karshen agurina dazaka wulakanta matanka ka dawo na saka bakina ciki , ga matarka nan zaune kaje yanzu agabanmu kabata hkr idan ta hakura taji zata iya koma gidanka fine mun yan addua ne, idan kuma tace bazata koma ba babu me takurata . tunda dady yasoma mgn jikin su'ad ke rawa har sanda ya dasa aya jikinta bai bar rawa ba.

ai ak nagama jin haka ya miki zumbur jikinsa na kirma ya nufi inda zeey ke zaune tana ciccin magani ya zauna kusa daita yana bata hakuri tmkr wani zararre .

"bazan koma gidanka ba abdulkabir naga ma rayuwar aure da kai ,ka wukantani ka tozartani akan laifin da bani ce sanadi ba tursasani akayi dan h ...

jikinsa na rawa ya kai hannunsa ya toshe bakinta "plx my zeey dont say anything again i Realixe my mistake's, nasani ba halinki bane wacan yarinyar ce tajawo komai amman kiyi hkr ki dawo gareni zan rikeki amana, idan baki dawo ba zan rasa raina da komai na, dan Allah dady hjy ammi ku taimaka kusaka baki zeey ta dawo kar na mutu yakarasa mgnr yana jifan su'ad da mugun kallo .

A razane su'ad ta Mike tsaye a zaunen datake jikinta na sake daukar kirma tasoma daga Zara zaran yatsun kafafunta ta isa inda yake tsaye tana dubansa cike da tausayawa hawayen damuwa da tashin hankali na tsiyayowa bisa kuncita .

Tabbas hasashenta na son yazama gaske akwai abinda ke faruwa da mijinta ,koma tace abun ya faru yagama.

abdulkabir Dinta ne zaune yarasa sukuni yake rokon zeey takoma gidansa idan bata koma ba zai iya rasa rayuwarsa da komai nasa " Allah ta furta cikin zuciyarta kirjinta na wani zugin azabar radadi

ita ba bakincikin dawo war zeey gidansa take ba amman gadarar da xeey din ke nunawa Ahalin yanzu shine damuwarta kuma shine abinda yafi daga mata hankali .

Hankalimta bai tashi ba sai data taji zeey na sake maimaita kalmar bazan koma gidanka ba abdulkabir sai dai idan zaka durkusa agaban iyayenmu ka rokesu su meida makani sannan ka dawo gareni ka rokoni ta tsigar data dace sannan zan koma gidanka mucigaba da rayuwar aure .

Fadar hakan ke da wuya AK ya isa gaban dady da ammi dake zaune kujera guda ya durkusa har kasa " ammi dady dan girman Allah kuyi hakuri nayi nadama abinda nayi ku yafemin kubawa zeey hakuri ta dawo gareni idan narasa zan mutu .

Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun kalmar da ammi take furtawa kennan acikin xuciyarta tana sake mai maitawa ahankali ta runtse idanunta batare datace komai ba tana karato duk adduar datazo bakinta wannan wani irin tashin hankali ne ?

"wai meke shirin faruwa da gudan jinita hakika wannan ba abdulkabir dinta bane, abdulkabir dinta me dakakkiyar zuciya ne da izza da nuna isa ,shine yanzu durk'ushen yana marairaicewa akan Zainab da babu yadda bazuyi dashi ba ya dawo daita ya lashe takobin bashi ba sake rayuwa daita har abada.

Ita kuwa suad koma tayi ta jingina da bangon parlour'n tana dubansu ta dawo wata irin halitta gbdy ta dawo tamkar mutun mutumi atsaye .

Wai meke shirin faruwa daita ne?

ahankali ammi ta bude idanunta dake runtse ta daurasu akan suad batare da kalli inda ak yake durkushe agabansu yana faman rokonsu .

Karema mata kallo tayi cike da tsusayawa da mamakin wulakacin da abinda abdul yayiwa suad din a yanzu , babu abinda ya kai wannan zamowa wulakanci da tozarci mijinka ya dinga nuna son wata agabanka.


kowa dake zaune agurin da abinda yake ayyanawa aransa game da *sarkakkiya*
sabon novel dina me zuwa.

suna cikin haka ak ya mike zumbur tmkr wanda aka tsinkara ya isa gaban zeey su'ad batasan lokacin data isa garesa ba dan tasan durkusawa zaiyi agabanta da zumar bata hakuri yana kokarin durkusawa kmr yadda tayi tinani ta kai hannuta garesa ta dafa kafarsa ya juyo a fusace sbd jin wani kololon bakincikin tindaga tafin kafarsa har zuwa cikin zuciyarsa sakamakon jin hannuta ajikinsa hakan yasa ya buge hannunta cikin zafin nama yana hararata.

a matukar harzuke yace "idan kika sake yunkurin kai hannunki jikina zan yi pata pata da namanki dole ne nace banson ki sake tabani ke bana ko kaunar sake sanyaki cikin idanuna ki shafamin lafiya bana kaunar sake ganinki,a yanzu komai kikayi bakya birgeni duk abinda kikayi ahalin yanzu babu abinda yake karamun illa tsanarki dake ruruwa acikin zuciyata ,plz su'adullahi kishafa min lafiya da wannan nacin naki na tsanake na tsanake on-expecting taji dauuuuu ta dauke shi da wani gigitacen Mari .

Zaro idanunsa yayi wanda sai lokacin ya kalli kwayar idanunta dake cike da ruwan hawaye bashi da aka mara ba hatta jama'ar dake zaune agurin sai da suke mike tsaye suna duban su'ad.

kallonta yacigaba dayi cike da sabon tsanarta dayake fadan yana mata a halun yanzu, ganin yadda yake kollonta yasa jikinta na rawa tayi kokarin sanya kwayar idanunta cikin nasa tana me fashewa da wani irin marayar kuku tana kallon tafin hannuta data mareshi dashi daga karshe tayi saurin durkushewa kasa agabansa tana yarfe hannuta tana jin nadamar abinda ta aikata yau itace ta mari mijin aurenta bata ta'ba tinani zuwan wannan ranar ba jikinta na rawa ta kamo kafafunsa cikin rawar murya tasoma magana "kayi hakuri mijina koda tsanar da kake mun zata zamo ajalina dan Allah ka kalleni ka sake furta min kalmar so ,zuciyar su'ad baxata iya daukar wannan tashin hankalin ba, bance karka dawo da zeey ba amman dan girman Allah ka fuskancin halin damuwar da zanshiga .

Janye kafafunsa yayi yana mata wani mugun kallo" har abada bazaki sake samun wannan kalmar daga bakin abdulkabir ba ,marina da kikayi zaki san kin mareni wallahi sai kinyi nadamar marin da kika min yakarasa ya isa gaban zeey data cika tayi taff tana kokarin fashewa har ya karyar gwiwarsa xuwa kasa ammi tace kul!

"Kar naji kar nagani ka durkusa min ka durkusawa wata, bance karka meida zeey gidanka ba matsawar kana bukatar hakan sabo da itama kmr ya' ce agurina amman batun durkusu shine bazan dauka ba ....
Ammi takara mgnr tana takaicin ak cikin ranta

Cike da sanyi jiki ya sake xuwa gurin ammi ya riko hannuta "karki ce haka ammi meye acikin dan na durkusuwa zainab matsawar zata dawo gareni zan iya durkusuwa agabanta na kuma roketa ..

A fusace ammi ta fixge hannuta "tabbas ka haukace ,haukar da zainab takira dashi ta tabbata domin kuwa baka cikin hankalinka da natsuwarka gaban zeey yabada rassss sakamakon jin furucin ammi.



ammi tacigaba da mgn "wallahi nasan da kana cikin hankalinka abdul bazaka taba yunkurin durkusuwa kowace irin mace bace aduniya bayan ni dana kawoka duniya amman duk abinda mutun yayi shi da Allah.


hjy kaka ta amshe zance da cewa " me kike nufi da wannan maganar taki baraka ?

"Kina nufin zainab tayi masa wani abu ne ya dawo haka ko me maganarki take nufi ?

Ammi tayi shiru taki cewa komai sai girgiza kafa take tana kallon su'ad dake wani irin kuka .


"Ince a gidan wani irin hauka ne abdul bai yi akan su'ad ba amman ko sau daya naji kince anyi masa wani abu oho ashe fa ita diyar d'anuwanki ce .


"hjy ki fahimci zance na...



"Dakata baraka babu abinda zan fahimta kai abdul kayi duk abinda zakayi ka dawo da matarka matukar hakan shine kwanciyar hankalinka .

Cikin kuka su'ad takaraso gurin tace "ammi ki duba da kyau wallahi abdul baya cikin hankalinsa wani abu na damun tininsa, watannin baya da suka gabata babu yadda banyi dashi ba akan zance meida zeey yace sam bazai meidata ba sai km yanxu da rana saka ya dawo yana hauka akanta takarasa tana 'barkewa da sabon kuka me ta'ba zuciya ..

ran hjy kaka ya sake 'baci sosai tace "Kinga yakike da suna ma ni manta su'ad ko me sai fa kiyi hakuri ,km tun farko kinsa bake kadai abdulkabir yake so ba, asalima zainab ce burin ransa kika yi wa rayuwarsu katsalandan dan haka addua zakayi akan zamanku dan zama da kishiya dole ,ni nasan komawar jikata gidansa baza'a samu wata matsala ba tunda tana da hakuri da hangen nesa muradinmu idan ta koma ku zauna lfy da junanku shine magana amman wannan kukan naki bazai hana komai .


Jin maganganun hjy yabashi kwarin gwiwar tashi ya nufi inda zeey take zaune batare daya Kalli su'ad ,Yana gama isa ya kamo tafin hannun zeey cikin nasa ya zauna gefenta yana mata magana kasa kasa ta yadda babu me jin abinda yake cewa sai ita kadai.
"Kiyi hakuri kinji my zeey kiyi yafemin nayi nadamar abinda na aikata miki kibani damar na gyara kuskurena .

Ahankali itama tayi mgana "abdul takira sunansa ya amsa da" ina jinki my zeey.

"Bakayi nadama ba tunda har yanzu banganka durkushe agabana ba .

"Dan wannan ai me sauki ne wallahi zan durkusa har birgima idan kina so zanyi miki nifa yanzu ko cewa kikayi na rabu da kowa akanki zanyi ,ya Mike tsaye hannunsa cikin nata yana murzawa daidai lokacin da su'ad takaraso dan ita taji duk abinda suke tautaunawa kasancewar gbdy hankalinta na garesu sabanin jama'ar parlour'n da hankalinsu ya tafi akan tautaunawa .

Ak yasoma kokarin zai durkusa su'ad ta katse masa hanzari ta hanyar raba tsakaninsu ya Mike tsaye tare da dagowa yana dubanta ta kai hannunta garesa ta dafa kadarsa wannan Karon taji wani irin zirrrrrrrr tundaga kanta har zuwa babban d'an yatsanta ga wani irin kallo dayake jifanta dashi wanda ke bugar mata da zuciya amman haka ta daure tace "bazan taba yarda ka durkusa mata ba Abdul in har sai ka durkusa mata sai dai karta koma gidanka .

"Abdul ka dubi cikin idanuna nice su'ad din da kayiwa alkawarirruka dayawa arayuwa tare da alkwarin zaka rikeni amana gashi tun ba'aje koina ba kana neman juya min baya dan Allah mijina ka dawo cikin tinaninka bancancaci irin wannan tsanar daga gareka ba .


dayarasa yasa abinda yakama yayi kawai yashiga yaryarfa mata mari tare da ingizata tayi baya taga taga zata fadi sannan ta tsaya yakarso har inda take tsaye tana dubansa ya rufeta da duka ta saki wata uwar razananniyar kara wanda ya hankalta da ammi a haukace ta mike tayi kansa bata tsaya wata wata ba ta kafa masa hakori "sakita dan ubanka zaka kashe min ita ne ?

"da me kake son taji da wananan maseefar ko kuma da wulakanci daka tsiro mata dashi yana dukan su'ad ammi na dukansa da cizo da yakushi dady da maman zeey suka yakarso atare banda hjy dake zaune dan ita dadin dukan da ak yayiwa su'ad taji haba ina dalili wannan jaraba ta fada aranta da kyar dady ya amshi su'ad ahannun ak .

ammi ta rungumeta ajikinta tana kuka ganin har kamanin fuskarta ta sauya "abdul baka da imani abdul baka da tausayi kasamu yar mutane kana duka haka kamar kasamu jakar ubanka ,wallahi sai Allah yasakamata , ta sake rungume su'ad ajikinta tana kuka tana shafa bayanta ,"yi shiru mamana sai Allah yasaka miki matsawar akwai zalinci acikin wannan lamarin ,bakida kowa kuma baki dogara da kowa sai Allah km shi zai tsaya miki yabi miki hakin zalintarki da'akayi .

"kai kuma idan namaka baki sai yabika, wallahi kaji na rantse akan su'ad zan iya 'batawa da kowa ciki har da mahaifinka dan haka idan ma akwai abinda ke cikin 'kwal'kwartaka ka ciresa tun wuri tun raina baiga karasa baci ba takarasa maganar tana duban fusakar su'ad mamana ,
"Ki masa Allah ya isa ko kiyi karasa gurin Allah akan tozarcin da yayi miki ...

take Su'ad tashiga girgiza mata kai alamun baxata iya abinda tasata ba .

"Ni saki nace ki gayawa Allah ta hanyar kai karasa gareshi ,ki kalli sama ki gayawa Allah, Allah na amsar adduar wanda aka zalinta shi

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login