Showing 93001 words to 96000 words out of 420383 words
Chapter 32 - SAI KA AURENI DOLE BY AYSHA A BAGUDU.txt
ina son kasan wani abu raba zuciyarta da sonka bakaramin tashin hankali bane, na fada sonka batare da nasan sanda hkn takasance dani ba.
wasu maruka ya sake zuba mata take bakinta ya balle da jini..... matsawar bazaki daina furta wannan banzar kalmar gareni ba .
zan rabaki da numfashinki ...zaki bar duniya batare kinyi nasarar cikar burinki ba. zan la'antaki na la'anta rayuwarki ...yana karasa fadar hk ya sake buga kanta da bago ginin...ta km sakin kara tana furta kalmar pls..
da kyar musty dake washe gefe guda yasamu ya mike tsaye ya tattaro dukkan wani karfi yasanyawa gangar jikinsa tare da shiga tsakaninsu yana kokarin kwatarta .
,da kyar musty yasamu ya kwace su'ad a hannunsa wace ta zube kasa tmkr wata sumammiya kafin daga baya tasoma fidda numfashi sama sama tana kallon cikin idanun ak hawayen tausayin kanta dana tsagwaron kaunar datake masa yashiga ganganrowa daga cikin kwarnin fareren idanunta.
ak yashiga nunata da dan yatsan hannushi wallahi matsawar baki rabudani ba kadan kikaga zan shayar dake guba da zata la'antaki ... hannusa dake rawa ya miko mata bani littafin sirrina..... tashiga girgiza masa kai bazaki bani ba?
ya tmbyeta nan ma sake girgiza masa kai tayi tana kokarin boye jakar hannuta.
motsota yayi sosai tare da saka kafarsa dake saye da takarmi ya take hannunta 1 yana mutsutsukawa.......
ta saki wata azababben kara .
ya fixge jakar ya bude.
idanunsa ne suka sauka akan littafin sirrinsa wanda ya nema yarasa tsawon lokaci.
yaciro yana turawa cikin aljijun wandonsa sannan ya maka mata jakar a fuskarta.
a matukar fusace yashiga janta yana marin fuskarta har sai daya kaita tsakiyar unguwar sannan yayi filinging daita yana tsare zan baki shawarar ki tsaya iyakarki........ kana
ya juya fuuuuuu yasoma takawa cike da izza zuwa gidansu .
rakiyar da baiwa musty ba kenan.
da sauri musty yakaraso gurinta tunaninsa ko ta suma ne amman sai isketa tana fidda numfashi hawaye na ganganrowa daga cikin idanunta .
nan yayita bata hkr da bata baki akan ta hakura ta rabu dashi tunda yace bai sonta .
nasan halin abokina tunda abdulkabir ya furta bai sonki bafa zai taba kaunarki ba har abada ..
ta mike da kyar tana shafa wunyata datake jinsa kmr ya dan soma tasawa alamun kunbura. wani irin radadin azabar ciwon gurin take ji sannan tace wannan karon zai yi abinda bai tabayi ba a tsawon rayuwarsa ..
sbd zai soni koda kuwa shine abu na karshe da zai aikata ya bar duniya... amman matsawar ina numfashi sai na mallaki zuciyarsa da gangar jikinsa ........
kallon tababbiya mara hankali musty yake mata tare da jinjinawa karfin halinta.
yarinya bazaki taba gane waye abdulkabir ba sai yayi miki illar da bazaki taba mantawa dashi ba yayi mgnr cikin ranshi.
da hannu musty yayi mata nuni tashiga mota. muje na kaiki hospital a dubaki... bata tsaya yin musu dashi ba sbd ita kanta tasan jikinta na bukatar hk .
duba da yanayin yadda goshinta da bakinta ke fidda jin .
shiga gaban motar tayi suka nufi wani karamin hospital .
byn an yi mata treatiment din gurin ya dauki hanyar gidansu a motarsa da kwatance data masa. tafiyar da suka yita suna tautaunawa. musty na sake sanar daita akan tsautsauran ra'ayin ak da rayuwarsa.
byn ya sauketa yabata kudi masu yawa ta kula da kanta.
" amman furrrr taki amsa sai ma godiya kawai data
masa tare da shigewa cikin gidansu dafe da goshinta.
ak nashiga gida kai tsaye part dinsa ya nufa yasoma balballe boturan gaban rigarsa, gumi ne ke tsatsafo masa takoina a ilahirin jikinsa surutu kawai yake tare da ciro litafin sirrinsa yana dubawa tabbas litafinsa ne..
to a ina tasamesa...? yayiwa kansa tmbyr.
ranar hk ya wuni yana juyi da tunaninta da gaske sonshi take ko tausayin abinda takaranta acikin litafin sirrinsa take.
Amman zai so ya zauna tare da musty domin zantawa dashi akanta akaro na farko.
hakika yana son sani wani abu game daita kafin ya sake daura idanunsa akanta .
wayarsa dake gefensa ne ta dauki karar sauti alamun ana kiransa runtse mayatattun idanunsa yayi sannan ya bude idanunsa ahankali ya kai dubasa ga inda wayar take .
ganin wace ke kiran ne yasa shi sakin dan gajeren tsaki yana furzar da iska kafin ya dauka.. Hello yayi mgnr a kasalance tare da sake runtse mayatattun idanunsa .
abangaren zeey kuwa sanyin dadi ne yakamata daga ina da take zaune akan gado ,ko babu komai taji muryarsa mai sakata jin kasala da samun natsuwa cikin ranta.
tunowa datayi da abinda yasa ta kirasa, yasa tayi saurin janye murmushin dake saman fuskarta.
a sanyaye tace an wuni lfy my life ?
lfy yabata amsa ataikace yana cixan lip's dinsa na kasa kadan, shr tayi cikin rashin jin dadin yadda ya amsa mata.
kusan tunda ta baro kasar Nigeria lamuranta suka sauya suke neman tabarbarewa ta kasa gane kasan.
wanda tasan ba komai bane ya haifar da hk illa aikinta dayayi sanyi yake bukatar tishi ,duk da hkn bai sa tafasa mgnr datayi niyya ba, dan hk muryarta ahankali tace yaya abdulkabir ........daman najika shr baka nemi ne ba tunda muka baro nigeria ,gashi ina son. mgn me mahimanci dakai shiyasa nakiraka yanzu.
"dan dakatawa tayi taji me zaice .
shiru yayi batare da yace komai ba a tunanin zeey ko bayajinta ne ko km layin ne ya tsinke ..
dan hk tasoma fadin hello ..hello.. hello ..my life kanajina.
dan numfashi yaja ya sauke da kyar.... kinga zeey ina wani abu ne yanzu ba km nason takura ko damuwa we will talk later ok.. batare da yajira abinda zatace ba yakashe wayar .
shiru yayi yana sake jin kirjinsa na rawa da bugawa akan tunanin su'ad da tunanin irin dukan da yayi mata .
sosai tunaninta yashiga yamutsa kwalkwaluwarsa.
ya matsu su kasance tare da musty yaji ina ya kaita sanda ya dauketa ,dan yaga lokacin datashiga cikin motarsa. wayarsa da sake daukar sauti ne ya dawo dashi daga duniyar tunanin daya lula amman yaki dauka.. duk da yaga kiran dady ne.
tunda ya katse kiran take rike da wayar a hannuta cike da matsanancin damuwa ta rafka uban tagumi allah yasani tana matukar kaunar abdulkabir so wanda bazata iya misaltashi ba. tun kafin tasan kanta take faman wahala da dako kaunarsa.
" sai gashi a daidai lokacin datafara murnar ya fara sonta da nuna kulawarsa gareta abu na neman tabarbare mata yazama dole da zaran sun dawo Nigeria tasan abinyi .
tana cikin wannan tunanin ne ammi da iman suka shigo dakin da sallamarsu shr bata amsa ba kasancewar tayi nesa cikin tunanin yadda zata mallakeshi dukansa batare da yana canza mata kmr hawainiya ba.
diyata lfy kuwa naganki hk..?
firgigib zeey ta dawo cikin haiyacinta tare da yin murmushin yake .
lfy ammi har kun dawo? um um zainab karki min karya mana tunani fa muka taddake kinayi. iman takarasa shigowa cikin dakin sosai ta ajiye farar laidar siyayar hannuta.
itama ta zauna kusa da zeey tana murmushi .
aunty kigayawa ammi gsky, tunanin yaya kike kawai dan hankalinta ya kwanta...da wannan firgicin datashiga.
ungo nan ammi tayiwa iman dakuwa na tmbyeki aku kuturu me bakin mgn kibarta tayi mgn man ..
ammi takaraso ta janyo wata karamar kujera da gabadaya jikinta kunshin ce ta zauna kusa da zeey tana fuskantarta.
ki fadamin gsky diyata meke faruwa dake ko tunanin biki ne...? ajiyar zuciya ta sauke tana rayawa aranta ina ma tunanin biki ne ai da sauki akan asirin datayiwa abdulkabir yakarye tana wata uwa duniya.
km wlh ko rantsuwa tayi bazatayi kaffara ba, tasan duk ammi ce ke ruguza mata shirin komai akansa.
tunda suka sauka a sakar saudiya bata zauna ta huta ba .
kullun tana harami ....ta km san gabadaya addu'ointa akansa zasu kare .
gashi ita yanzu komai na neman kwabe mata.. iman ma masowa tayi sosai ta kamo hannuta aunty zeey tunanin yaya abdulkabir ne ko ..?kallonta zeey tayi .sannan
tayi shr taki cewa komai hkn datayi ya tabbatarwa ammin da shi din ne sanadin shigarta cikin damuwa, Allah yasa bawani abun yayi mata ba.
ammi ta numfasa tana kallonta kana tace karki damu diyata zan san abin yi akan lamarin zankirasa zuwa anjima na lura tunda muka zo bai wani tsananta nemanki ba .
da sauri zeey ta zare hannuta dake cikin na iman ta meida cikin na ammi ta rike gam tana girgiza mata kai.
um um ammi bashi bane asali ma babu abinda yayi min lfy muke dashi yanzu ma muka gama waya dashi .
ammi ta sake numfasawa tana cigaba da kallonta .
sosai take jinjinawa kaunarta gareshi har tausayi take bata wani lokacin idan taga yadda yake mata wasu abubuwan.
ta dan bata lokaci zaune kafin daga baya ta mike tsaye tashigewarta bayi .
kinga aunty zeey namiji yanzu ko fa aurensa kikayi sai kina hadawa da hakuri da addua balle irin su yaya da mata ke rububibi.
sannan km tun farko kece kika fara nuna kaunarki da zakewarki akansa dan hk dole ki koyi juriya akan komai daga garesa .
nayi miki wannan mgnr ne amatsayinki na yar'uwata km aunty nah sannan nasan hk kawai ba wani abu ne ya haduku dashi ba .bazaki kasance cikin wannan yanayin ba.
aunty zeey ki tuna inda kike kina kasar saudiya kasar me tsarki .
wace ta wadatu da tarin ni'ima da albarka cikinta ki yawaita kaiwa allah kukanki kafin mubar kasar nan .
kai kawai ta iya dagawa iman nagode sosai iman Inshaallahuu zanyi kokarin yin hk.... mikewa zeey tayi ta nufi dakin baccinsu ta barta zuciyarta cike da sarkakiyar jin tsoron rasa abdulkabir dinta...
bangaren su'ad kuwa tana isa cikin compond dinsa ta iske makwabtansu ,su 4 zaune suna tautaunawa akanta da zaginta wanda daman halinsu kenan sai dai idan basu zauna ba.
suna ganinta kowace daga cikinsu tayi shr ta sha jinin jikinta suka shiga kamekame neman abunyi.
tsaki tayi dan tasan halin nasu suke yi na munafurcin da suka saba.
yau kam bata da lokacin kowace daga cikinsu.
damuwarta kadai ta isheta.
kai tsaye part dinsu ta nufa tana shiga ta iske ummanta zaune a parlour tana bare egusi idanunta na kan tv tana kallon tashar galaxy ko kallon inda uwar take zaune su'ad batayi ba.
balle wani abu shi sannu da gida.
tayi shigewarta uwar daka abinta.
uwar tabi bynta da kallo tana girgiza kai kawai dan taga raunin goshinta dana kafafunta.
amman yanzu ne ,tana mgn zata haiyayyako mata da fada.
ahankali ta maida dubanta ga kallon tv sannan tacigaba da abinda take..
tana shiga dakin kwalkwaluwarta tashiga caji domin nemawa kanta mafuta dan dole tasan abunyi kafin wata tazo tayi mata haye da shishigi cikin lamarinta da abdulkabir dinta. zagaye dakin tafara kafin tasoma zance zuci ita kadai .
su'ad dan dole ki tashi ki nemawa kanki mafuta tun lokaci bai kure miki ba .
akalla yanzu sauran watani biyu masu zuwa yarage wata ta mallekeshi bake ba.
me zanyi.... ..?
meye mafuta ni su'ad..tayiwa kanta tmbyr. ?
rashin samun mafuta yasa tayi shr tare da hawa kan dan karamin gadon ummanta ta kwanta lamo akan katifa. numfashi take saukewa ahankali tmkr wace tayi gudun famfalaki kanta dake daure da bandage tashiga jujjuyawa kafin tasoma sakin murmushin mugunta .
alokaci daya km ta sauke naunauyen ajiyar zuciya.
ta mike zumbur ta isa inda take ajiye kayan cajinta.
ta dauko kwalbar giya daga mabuyarta ta balle tare da tsiyayawa cikin glass cup tashiga kwankwadawa cikinta kafin kace me tunin har tasoma fita haiyacinta tana zuba surutai da sambatu iri iri akan soyayyar datakewa ak cike muryar maye i.....i..na sonka ba..ba.zan barwa kowa kai ba duk runtse .
duk wace tace zatashiga tsakaninmu sai na daddatsa shegiya da ada.. (masha o're enitowu meji.... )a hk umanta tashigo dakin ta isketa cikin mayen giya hannuta rike da tabawar wiwi tana zuka.
gbdy dakin ya turnuke da hayakin wiwi da warinta a zabure umman su'ad tayi kanta tare da rufeta da duka me zangani iskancin naki ya wuce kiyi shi waje.
yanzu tsinaniyar yarinyar adaki zaki zauna kina sha min giya da tabar wiwi...sbd lalacewa tasameki allah ya wadaran naka ya lalace allah wadaran wannan tsinan halin naki.
su'ad ta bude fararen idanunta wayanda suka gama canza kala zuwa jajja .
tasa hannuta ta tunkude ummanta gefe daya tare da mikewa tsaye tana tan gadi da nunata da yatsan hannuta ya ..ya isheki umman su'ad.
meye matsalarki da rayuwata ne. ..?
me kika tsamaci gani daga ya'ya iirinmu marasa gata da galihu ....?
na rokeki ki fita cikin rayuwata tun ban hadaki da hukuma ba ko na sassaraki da ada na raba kanki gida 4.....
ni zaki hada da hukuma su'ad ? sbd ke shegiyar yarinya ce ...umma tayi mgnr tana zubewa kasa kan gwiwowinta tana kuka me cin rai .
ni mahaifiyarki zaki hada da hukuma tare sara ? mahaifiyar banza ..... mahaifiyar wofi da iska gbdy tayi mgnr tana zubewa kan katifa sharaf wlh bazaki kwananmu a daki ba yau .
tashi maza ki koma parlour..wlh ni anan zan kwanta ...umma tashiga janta da karfin tsiya ta kaita parlour tare da ingizata tsakiyar parlour. tana kuka nadama tattare da danasani mara misaltuwa suka taru suka mata yawa.
hakika rayuwa na zuwa mata da abubuwa masu tsauri da azabtuwa.
wa zai taimakawa rayuwarta da rayuwar tilon diyarta ?
kuka take sosai har sanda taji ankira sallar magrib ta mike tashiga bayi ta daura alwala
tafito.
ta dan yaye labulan parlour warwass taganta kwance tana kwasar bacci kyakkyawar fuskarta ta sake fitowa sosai ta yi fiyat har yanzu tana nan da kyawunta sai dai farar fatarta data dan soma disashewa.
kallon su'ad umma ke yi tana kallon yadda tayi muguwar rama tare da canzawa ba wasu kayan kirki ne ajikinta ba nan take jikinta yayi wani irin sanyi tausayin ita da diyarta ya mamaye rurinta .
hawaye na sake ciccikowa a idanunta wace irin rayuwa ta sanya kanta ciki ?
kasa rike hawayen idanunta tayi hkn yasa suka samu nasarar saukowa cikin muryar sanyi tace ya Allah ka dubamin lama'rina dana yarinyata .
sannan ahankali ta saki labulen tazo ta shimfida abin sallah .
ta tayar da sallah .
byn ta idar ta dade zaune tana addu'ointa datasaba yi kullun tare da neman gafarar Allah da nemawar tilon diyarta shiriya agurin allah ..
sai wajen karfe dayan dare sannan su'ad ta tashi ta dawo cikin haiyacinta sharkaf da gumi.
gefe daya km ga radadin zafin ciwon jikinta .
hannuta na rawa tasa ta goge gumin daya rufe mata fuska kasancewar nepa basu kawo musu wuta ba ,tare da kallon agogon bangon dake manne da parlour da dan sauran hasken fitilar charge.
wasu zafaffan hawaye ne suka balle mata ta maida kanta jikin kujerar parlour 'n ta jinginar hawayen tausayin kanta na sake zubo mata idan abdulkabir ya auri wata macen baita ba batasan yadda rayuwarta zatakasance ba..
bata tunanin ruhinta da gangar jikinta zasu iya daukar wannan nauyi.
ya salam ta furta muryarta a sanyaye tana me mikewa tsaye ta kakkabe jikinta tare da shafa raunin dataji a goshinta ta koma cikin daki.
ta iske ummanta kwance a kasa tana bacci ,numfashinta na fita da karfi da jin yadda numfashinta ke fita tasan kuka tayi me tsanani .
karasawa tayi kusa daita ta sunbaci goshinta ummana ba nufina na kasance yar iska ba... naso na zamemeki sanyi idanunki ..
amman kiyi hkr ki cigaba da min addua .
im very sure wata rana i will change .
ta dago ta tsallaketa .
ta nufi bayi tayi wanka tare da dauro alwala sosai taji dadin jikinta sannan ta gabatar da sallolinta .
tana idarwa wucewa tayi makwancinta ta zauna tare da takure jikinta guri daya akan gadon ta tuno rayuwarta ada cike da farinciki da soyayyar ummanta, sabanin yanzu da komai na rayuwa ya sauya mata , ta zabi wannan rayuwar ne akan samun farincikinsa ....
amman duk da hk bai tausayawa rayuwarta ba. daita da banza duk daya ya daukesu .
ahankali ta zame ta kwanta tana tunani .....tare da sake takure jikinta guri daya atsakiyar gadon.
hb abdulkabir bai kamata ka wulakanta soyayyata ba sbd mahimmancinta gareka..
na zabi farincikinka akan komai dake cikin duniyar nan ,dan kawai na rayu dakai wa zan gayawa taskon rayuwar dana shiga akanka ya fahimceni?
wasu siraren hawaye ne masu zafi suka tsiyayo mata .
ranar da kyar tasamu ta runtsa wanda har da mafarkinsa tayi tana rokonsa yasota ya yantota daga shigin wasu..
amman furrrr yaki yace mata sam shi baya sonta baya kaunarta km bazai taba kaunarta ba......
washegari wani irin matsanancin zazzabi ne ya rufeta sakamakon raunukan jikinta.
gbdy ilahirin jikinta yayi mata tsami da kyar take iya bude kumburarrun idanunta dake like .
ga jikinta dake kirma, umman su'ad wace ta dade da tashi har tasoma aikace aikacenta na yau da kullun tashigo dakin ta duba ko su'ad din tashi ta cire kayan jikinta domin ta wanke. turus tayi sakamakon yadda taga idanunta da goshinta yayi .
kasa hakuri tayi takarasa zuwa kan gadon datake zaune hawaye na fita cikin idanunta ta rungume su'ad da sauri hawayen idanunwanta na saukowa cikin rawar muryar tace su'ad wace irin rayuwa kika zabawa kanki.?
wannan rayuwar sam bata dace dake ba kiyiwa girman Allah ki tausayawa rayuwar ummanki ki dawo ta kwarai .
duk duniya bani da kowa bani da komai sai ke kadai da Allah yabani....yanzu waye wanda bai da imani da tausayi yayi miki hk.?
wani irin sanyi jikin su'ad yayi idanunta suka sake cikowa da ruwan hawaye ita kanta batason takasance cikin wannan rayuwar me cike da sarkakiyar da kaskanci.
hakika wannan yanayin yakasance lokacin bakincikinta ne da rashin kwanciyar hankali gareta.
waye wanda keson kashe min ke..?
kiGaya min dan gidan ubawaye yayi miki wannan dukan?
ahankali su'ad tasanya duka hannuta ta rungume mahaifiyarta dake rungume daita tana kuka.
umma ta zare jikinta tana goge mata hawaye .kigaya min wanda yayi miki illa hk da ala'mun ma kasheki yake son yi...
hannuta takai kan fuskar mahaifiyarta tana goge mata hawaye muryar a raunane
19, September 2025
Aisha Auwal
Wow