Showing 210001 words to 213000 words out of 420383 words

Chapter 71 - SAI KA AURENI DOLE BY AYSHA A BAGUDU.txt

sonta dole na aureta sbd bin umarnin iyayena ko kina son iyayena su tsine min akan rashin aurenta ?

ta sake jifansa da wata muguwar harara, ai dole ka fakaice da fadar hk man byn ni nasan kana sonta kana son aurenta amman kazo kana yaudarata.
"nidai nace na fasa aurenka na bar mata kai idan ma cinyeka zatayi karewar so taje tayi ta kaya ni kam gara mutuwa ta akan na zauna da kishiya ..

ya fahimci zallar kishi ne ke dawainiya daita dan hk ya rikota zuwa jikinsa yana rarrashita tare da fada mata wasu sanyayyun kalamai amman a maimakon taji dadin kalamain sai ma taji tmkr yana watsa mata garwashin wuta ne ajikinta tayi kokarin kwacewa daga jikinsa amman takasa domin yayi mata kwakkwarar rikon da bata isa ta iya kwatar kanta daga gareshi ba.

kuka me sauti ta sakar masa, kan kace me zeey ta haukace masa dukansa take da yakushi amman yaki sakinta "karabu dani mana , ak ya girgaza mata kansa tare da cewa bazan iya rabuwa dake ba, kema kinsani dan hk kiyi hkr wallahi tun iya tsawon rayuwata banta furtawa wata mace ina sonta ba ko son aurenta sai ke.

kiyi hkr ki dauki kaddara domin babu yadda banyi dasu dady ba akan a fasa auren tun kafin mgnr tazo gurinki amman sun tsaya tsayin daka dole na hadaku tare.

"bazai yiwu ba na hakura da kai na bar mata Allah bazan iya sharing dinka ba dan hk na bar mata kai.

kada muyi hk dake mana ta zabga masa harara cikin kankanin lokaci ta rikita masa kwalkwaluwa jinsa yake tmkr ya rutsa ihu.

ita kanta tasha mamaki yadda ya sukurkuce mata yana rarrashi, amman ba abin mamaki bane tunda tasan har lokacin akwai miyagun ayyuka akansa wanda tasirinsu ya wuce yadda take tunani, amman banci hk abdulkabir zata dinga wannan salon iskanci bai mata dukan mutuwa ba, ko yace shima ya fasa auren.
"amman ji yadda ya wani rude ya gigice akanta yana fama bata hkr gsky ta jinjinawa aikin boka na kan dutse.

rungumeta yayi tsam ajikinsa sannan ya lalubo kunnenta yana rada mata wasu sirri kalamai game da yi mata alkwarin zai riketa amana km bazai taba hada gado da su'ad da sunan auratayya ba dan hk itama ta taimaka masa yayiwa iyayensa biyayya ya auri su'ad ba dan yana sonta ba.

da irin wadan kalaman AK yasamu ya shawo kan zeey ta amince da bukatarsa duk da tasan ko ya kusanci su'ad hkn bazai taba karya asirin data masa ba domin daita da su'ad din duk sammakar ne babu cikakkiyar budurwa acikinsu.
"muryata ahankali tace na amince ,sbd murnar abinda tayi masa AK yayi mata alkwarin zai mallaka mata zukekiyar motarsa dayasa aka turo masa daga span domin yin angonci daita .
tayi matukar yin murna da wannan kyauta .
*********
ammi tashirya taje gurin islamic malamin dake bada maganin farfadiya, byn ammi tagama koro masa bayani yanayin ciwon su'ad da yadda akayi ciwon ya dawo kanta mlmin yace azo su'ad.


jiniyace ta cika gbdy ilahiri unguwarsu su'ad har zuwa kofar tafkeken bakin get din gidansu inda tarin motocin minister lafiya suka ja birki suka tsaya ,aka bude masa bayan mota ya fito ammi dake zaune cikin daya daga cikin motocinsa ta fito suka nufin cikin gidan.
shigarsu yayi daidai da fitowar umman su'ad a firgice tana ganinsu tayi mugun bata rai sannan ta juya zuwa cikin daki inda ta bar su'ad zaune gabanta na dukan tara.

bakinsu dauke da sallama suka sanya kansu cikin parlour gidan jin sautin muryar yasa su'ad saurin dagowa da kanta idanunta ya sauka akansu ta mike da sauri gabanta na cigaba da faduwa yayinda ummanta takoma ta jingina bayanta da jikin bango tare da daura hannuta kan TV tana dan bubbugawa ahankali .
idanunta na sama tana kallon ceiling din dakin batare da tace dasu komai ba .
ammi da minister sukayi kansu gurin zama dan ganin ko kallon kirki basu samu daga umman su'ad ba balle su samu arxikin gurin zama.

"muryar ammi a sanyaye tace diyata zo gareni na sake jin duminki ajikina, ko naji sanyi tare da rage radadin dake cin zuciyata.
" yau tsawon shekaru shirin da yan kai ina bulayin nemanki cikin duniya.
"diyata da... a matukar hassale umman su'ad ta katse ammi ta hanyar cewa " wace diyarki anan ina ganin kmr kina cikin rudu amman anan babu wata datayi kama da diyarki.

"wannan "ya"tace ni kadai....

"karki yi hk salema karki yi yunkurin sake raba yarinyar nan da danginta alhalin suna tsananin sonta?

"karka gaya min hk doctor ince agabanka komai ya faru.. dan haka babu wani zance "ya" anan su'ad diyatace dana haifa cikin ganiyar kunci rayuwa da rashin wadataccen soyayyar dangi .

"bari nagaya maka ko taufeek ne zai dawo duniya bazan taba mika su'ad ga danginsa ba balle babu shi araye takarasa mgnr tana goge hawayen daya zo mata.

"kenan kin yar da kice salemar taufeek ?

" tabbas nice salemar da kasani, kmr yadda nida kai mukasan su'ad diyar taufeek ce sai dai duk duniya babu wanda ya isa ya rabani daita.

duk maganganunsu suna shiga cikin kunnen su'ad daya byn daya idan zata fahimci inda zantattukansu ya dosa kenan zarginta ya tabbata ,har yana shirin zamowa gsky ,wadan nan bayin Allah suna da halaka me karfi daita ..
"to su din su waye gareta ?
tayi kanta tmby.

a matukar tsorace take bin umman da mutanen dake zaune a parlour 'n.


sautin muryar mutumin ta sake ji cikin kunnuwanta "tun wancen lokacin naso na bayyana komai amman kika hana wanda sanadiyar hk akayi rashin hjy ,dangi suka shiga halin ha'ulai amman a wannan karon wallahi wallahi baki isa ki rabamu da jinin taufeek ba.

"na isa Doctor sbd nice nan na kawota duniya ko lokacin danake shan wahalar nakudar haihuwarta akwai daya daga cikinku daya tayani?

"tmbyrku nake kun tayani shan zafin nakuda haihuwarta ne?

"bamu tayaki nakuda ba amman ke kinsa ba diyarki bace ke kadai tunda bake kikawa kanki cikin ba.

"har wani abun takoho ne akan cikin da aka nunawa duniya ba'a so sai dai a haifa byn rai "kasani doctor ina mugun jin kunyarka wallahi if not da idan nagaya muku wata mgnr har ku mutu ba zaku mantani ba.

zaiyi mgn ammi ta dakatar dashi mubarak bawannan long talk din ya kawo mu ba yanxu saleema kin zauna muyi mgn ta fahimtar juna.

umman su'ad ta zauna tana jiran jin abinda ammi zata ce "atsanake ammi tasoma mgn saleema bamunzo gurinki dan murabaki da diyarki bane, nan tayi mata bayani me maganin da sukaje gurinsa ne , wanda ya tabbatar musu da dole sai an zo masa su'ad yaganta.

umman su'ad bata amince ba alokaci daya sai da aka kai ruwa rana sanan ta amince .

cikin sanyi murya ammi tacigaba da mgn atsanake kmr farko kiyi hakuri saleema ki sake rungumar kaddararki kmr yadda kika fada a wancan ranar cewa kaddara acikin jiniki take.

"wallahi wallahi ko ki yarda ko karki yarda muna sonki ke da diyarki, nasan ko lokacin baya taufeek bai taba gaya miki ina daga cikin wadan da basu son aurenki dashi ba,bangaki ba alokacin amman naji araina ina sonki kasancewar dan'uwana na mugun kaunarki.

ammi ta tsaya ta numfasa sannan tacigaba "an dai samun matsalar ne daga gurin hjyrmu wace itama daga baya tayi datasani dan ina tabbatar miki datasan daga baya hk abubuwa zasu kwabe da bata hana aureku da taufeek ba.

"asanadiyar rashinki da cikin jikinki hjy tarasa rayuwarta har ta mutu bakinta bai daina ambarta sunanki ba.
ina rokon alfarma da arziki kiyafe mana darajar allah da km darajar soyayyar dake tsakanki da taufeek sannan ayanzu ki lamunce min na wuce da mamana...

"saleema ammi takira sunanta cikin sanyi murya "kin cika yar halak kin tabbatar mana da ke din me amana ce da rike alkwari ce tunda kika cika burin taufeek byn kinsa baya raye .
"kika iya hakuri da juriyar da kika sakawa diyarki sunan mahaifiyarmu wannan abun kadai da kika mana ya isa a jinjina miki..

tun lokacin da ammi tasoma mgn kuka saleemat take wanda tasa minister goge hawayensa dan mganrsu na tuno masa da aminisa..

"kiyi hkr kiyi hkr ki manta komai daya gabata mu maida hankulanmu akan lafiyar diyrmu ..

cike da matsancin sanyi jiki su'ad takaraso ga ummanta ta riko hannuwanta duka cikin kuka muryarta na wani irin rawa tace "umma wai su din su waye dan Allah ki gaya min halakarsu da mahaifina ina son sani me ye dangantakarmu dasu?

muryar umma cike da matsanancin kuka tace "yayar mahaifinki ce uwa daya uba daya shi km wannan aminin mahaifinki ne wanda Allah kadai yasan tsakaninsu..
a zabure su'ad ta juyo tana kallon ammi da minister da ke zaune dukkaninsu hawaye suke gbdy su'ad ta gigice tsoronta ya sake bayyana da hannuta take nuna ammi takasa mgn yayinda ammi tashiga girgiza mata kanta tana nuna mata kirjinta ala'mun itace yar' uwa mahaifinta..
wani irin sanyayye murmushi ya bayyana saman fuskarta me cike da tsantsar farincikin. sai km hawayen murna yashiga gangaro mata bisa kuncinta.
"ayau bata san da me zata misalta farincikinta ba mahaifiyar ak itace yayar mahaifinta km uwa daya uba daya wannan wani irin alamari ne me ban mamaki.

ammi ta warewa su'ad hannuwanta gbdy ala'mun tazo gareta aiko bata tsaya bata lokaci ba ta isa jikin ammi ta rungumeta tana kukan farinciki itama ammi rungumeta tayi sosai ajikinta tana kuka tare da tunawa da dan'uwanta.

ammi kuka minster kuka umman su'ad da su'ad kuka aka rasa wanda zai rarrashi wani karar jiniyace ta hankalta dasu.

kafin kace me aka soma bubbuga kofar part din su su'ad minister ya mike y fito tarin police yagani kusan guda goma sha biyar kowanne hannunsa rike da bindigar suna mazura.

"gabansa na faduwa ya tmbyesu wa suke nema?

kai tsaye daya daga cikin police yace "munzo arresting din su'ad ne.

"kunzo arresting dinta minister ya maimaita sannan yace "akan wani laifi?

"akan laifin yunkurin yin kisa ta hanyar fayde yabashi amsa da fadar hk.

minister ya ciro wayarsa ya kira number commission yana dauka yayi masa bayani kmr yadda police yayi masa commission yace abawa police din waya minister ya mikawa police kmr yadda commission ya bukata.

shi dai bai san abinda commission yace musu ba shi gani yayi sun miko masa waya tare da juyawa suka bar gidan shi km ya koma ciki yanawa ammi bayanin zuwan polisawa naunayen ajiyar zuciya ammi ta sauke tare da cewa "yanzu kam wallahi babu me sake saka min ita cikin tashin hankali byn wanda tagani.

tare da su'ad ammi ta wuce gida.
*******
tsaye yake jingine da jin kofar hannuwansa duka akirji mayatattun idanunsa akanta ya tsurawa fuskarta ido yana karewa mata kallon tsab cike da matsanancin mamaki ganinta kan gadon amminsa kwance ta dungule jikinta guri daya tmkr me jin zazzabi.

su'ad dake kwance hk kawai ta tsinci kanta da jin faduwar gaba dan hk ta bude idanunta ahanakali suka sauka akanshi har lokacin kallonta yake , yunkura tayi ta juya masa bayanta zuciyarta na wani irin harbawa . gabansa ne yayi mugun faduwa sbd baiyi tunani zata iya ganinsa ta juya masa baya, cikin wannan yanayin ammi ta fito daga bayi taganshi tsaye yana kallon bayan su'ad "a'a ya km ka tsaya anan ka karaso ciki man ?

ahankali yasoma daga kafafunsa daidai lokacin da su'ad ta mike bata ko kalleshi ba tashigewarta bayi ,abinda yayi matukar bakanta ranshi kenan.
" me hkn yake nufi ?

"da gaske ta tsane shi bata son ganinsa ko me ?

tabe bakinsa yayi tare da jan dan gutun tsaki yana shafa kwantaccen sumar kanshi wanda yasa ammi tayi saurin dagowa ta dubeshi "meye abin tsaki daga ganin yarinya?
"to ni ammi nace dan na ganta ne?
"dan ka ganta ne man halinka ne bansani ba kome?

runtse mayatattun idanunsa yana ciza lip's dinsa na kasa sannan muryarsa a sanyaye yace "ni ba daita nake ba.

"gara yazamo bada ita kake ba dan wallahi kaji na rantse akan yarinyar zan iya bata maka rai .
"ni banga abin ki a yarinyar ba .

",yanzu ba kika san halakarki daita ba amman da ai goyon baya kike bani akan zaafafa kinta, yayi mgnr cikin ranshi sannan ya mike ya bar dakin.

da daddare commission ya bugo wayar dady yake gaya dady cikakken laifin da su'ad din tayi na yunkurin yin kisa ta hanyar fayde ga karuwar abdulkabir wanda yasa police suka shiga cikin lamarin ,dady naji hk ya saka wayar a hands-free ta ammi zataji komai a commission yacigaba a yadda nasamu labarin police sun dade suna nemanta basu samu nasarar kamata ba sai a wannan lokaci amman karku damu komai yazo cikin sauki tunda nashiga cikin lamari godiya dady yayi masa sosai sannan sukayi sallama.

ammi takira AK ta waya
aiko ak yasha fada kmr babu gobe ta inda dady da ammi suke shiga bata nan suke fita ba.
wallahi kabani kunya abdul da girmanka da iliminka da komai ka dinga bin matan banza, tun yaushe ake binka kayi aure ,kake yiwa mutane yawo da hnkli ashe kasan barnar da kake yi aboye .
"wallahi tun wuri ka tuba ka daina aikata zina ka koma neman istigari gurin Allah sbd zina tana da matukar illa da yiwa dan adam tabo ajiki .

"kai kana da wannan meyagun halin amman kake gudun auren me irin halin sbd tsbabar mugunta irin naka, kana ganin idan Allah bai jarabceka da auren mace me irin halinka ba ya'yanka fa abdul ?
"baka jin tsoron wannan maseefa ta shafi ya'yanka...

cikin sanyi murya yace Allah ammi ban... da hannunta ta dakatar da shi ta hanyar cewa karka gaya min komai "wannan yarinyar da kake gudu itace matar da take maka soyayya tsakani da Allah.
"wallahi azim idan nice ita nasan kana mu'amula da wata katuwar arniya me zanyi da kai?
"meza'ayi da me hali irin naka abdul ?
"ni bansan me mamana tagani jikinka ba wanda yasa ta nece maka?

shi kam dady kasa cewa komai yayi tun fadan farko dayayi masa dan abin ya zarta tsammaninsa shifa duk tunaninsa ak ya daina hulda da matan banza a she yana kan halinsa bai daina ba.
Allah ya Kyauta ya shiryeka ya furta hkn cikin bacin rai itama ammi adduar shiriya tayi masa.

tundaga ranar ammi ta canzawa AK dan ko murmushi baya gani a fuskarta gbdy ta ttarashi ta watsar ,ta meida hankalinta kan kula da su'ad .

itama su'ad kuwa duk inda tasan zata hadu da AK bata zama idan yana parlour 'n ammi tana daki kwata kwata bata yarda su kasance guri daya ,duk yadda AK ya dauki lamarin yarinyar ya zarta hk kmr baita bace ke binsa da ihun duk inda yayi akan sai ya aureta dole amman yanzu gbdy ta sauya ko kallon inda yake bata son yi.

ammi ta koma tare da su'ad gurin malamin da zai bawa su'ad magani farfadiya amman rashin sa'a basu sameshi ba wai anyi masa kiran gaugauwa zuwa ghana amman zaiyi wata daya kafin ya dawo hk suka dawo ammi suka dawo gida da zumar zasu sake komawa .

AK yashirya yaje hospital inda onye ke jinyar kanta har lokacin .
tana ganinsa taji kmr duk damuwar ta yaye ,banda murna da farinciki babu abinda take yakarasa har bakin gadonta tare da janyo kujera ya zauna yana dubanta sannan yasoma da bata hakurin abinda su'ad tasa aka mata a sanadiyarsa nan suka shiga hira atsaninsu inda cikin hirarsu "take ce masa ak ya mgnr aurenmu da kai ne ?
"nifa har yanzu ina kan bakana nason aurenka.. murmushin takaicinta yayi sannan yace"haba onye ko mutun goma basu miki fayde ba ai bazan taba aurenki ba onye, ba tun yau ba nasha gaya miki bazan iya aurnki ba.

hawaye ne suka soma gangaro mata sbd a iya zamanta dashi ta karanci yana da tsananin kishin maseefa .. muryarta cike da kuka tace karka min hk ak akanka na rabu da duk abokan harakata sbd tsananin kaunar danake ma...

"kar ki kisoma fadar hk ada na amince dake amman ayanzu babu wannan amincewar atsakaninmu ,ina mu'amula dake cike yarda kefa maci amana ce onye dake kwance ta zabura ta mike zaune tana masa wani duba zuciyarta cike da fargaba ahankali yacigaba ba sai nace miki komai ba amman abinda nasani wannan haduwar tamu itace haduwa ta karshe da zamu sake yi.. ai bata san sanda ta duro daga kan gadon ba ta durkusa kasa kayi hakuri kasancewata karuwa ba yin kaina bane yin mahaifiyata ne ni kaina danasan zan hadu da kai arayuwata da ban zunduma kaina cikin harakar karuwanci ba... "sake of God abdulkabir karka gujeni "

"onye bazan iya aurenki ba ko kina son nayi miki karyar zan aureki nazo ban aureki ba?
kanta tashiga girgiza masa yanzu sbd kasancewata karuwa ne bazaka aureni ba yace kwarai kuwa. ya juya zai wuce ta riko hannunsa ya tsaya cak batare da ya juyo ba. ahankali tace ka tsaya nabaka takaitacen labarina .

kmr yadda kasani sunana
onye ni yar asalin jahar akwaibon ce ,acikin wani kauye me suna ugun dake kusa da kauyen eket ,mahaifina ya hadu da mahaifiyarta ne alokacin da yayi wani zuwa ganin gida kasancewar shi a acikin enugu yake aiki tare da ya'yansa ya auri mahaifiyata suka dawo enugu da zama .

babu laifi mahaifina yana da rufin asiri, sai dai ba'a dauki wani dagon lokaci ba byn rabuwarsa da ya'yansa sai kariyar arziki tasamesa ahankali komai nasa yayi kasa dan shagonsa dayake tun kaho dashi ya fara karewa a hk mukacigaba da manejin rayuwa lokacin da wannan iftilain yasamu mahaifina duka alokacin ban wuce aji uku na matakin karatun secondry ba.
kasancewar ina da halitar jiki me kyau da maseefar kyau, hakan ya janyo min tarin samari duk inda nashiga sai na samu samari irin shigar danake shi ke kara janyo samari suna kai min hari, hkn ke sanyawa a

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login