Showing 378001 words to 381000 words out of 420383 words
Chapter 127 - SAI KA AURENI DOLE BY AYSHA A BAGUDU.txt
komai cikin rashin sani da taimakon sihirin data min, hankalina ya gushi ta sanadin macen dabanyi tsamanin haka daga gareta ba ,hakika zainab ta cutar dani ta ruguzamin rayuwa tayi nasarar rabani da muradin raina "ke kuma hajiya yau zaki ganewa idanunki mugun aikin da jikarki ke aikatawa ba sharri aka mata ba....
"a yau zakiga abinda d'an shege ya kasa aikatawa amman aka samu d'an halak dumu dumu da aikatashi ..
jikinsa na rawa cikin sauri ya fita bai fi minti biyu ba ya sake dawowa da SD da Akil yabashi "Dady ga plet din SD nan a kawo system d'in eiman eiman jikinta na rawa ta amsa tasa SD yasoma play kamar minti biyu sai gashi an soma nuno Zeey kwance Akil na ruwan cikinta yana zuba mata jijiya tana gurnanin ihun dadin haka aka dinga nuno tsiracin Zeey abu tamkar a bf gaba d'aya jikin mutane dake gurin babu wanda bai sanyi ba .
mutuwar tsaye sukayi har Daddy sai Ammi ce tayi karfin furta kalmar inna lillahi wa inna ilaihi da karfi "maza Abdul ka kashe wannan mugun abun da bai da dadin kallo, take ya kashe sannan ya fuskanci Dady "Dady ka karyatani akan Zeey bata min komai ba kana tinanin duk abinda na aikata ina cikin haiyacina shima wannan zan kawo maka shaida da idanunka da kunnuwanka zakaji abinda Zeey ta aika gareni.
"ke kuma Hajiya kinga zahirin wacece Zeey ko? "da aurena take bin maza har me gadin gidana yau be tsira ba agurinta "Alhamdullahi babu abinda zancewa Allah sai godiya dan tun a gidan duniya taga karshenta taga sakamakon abinda ta shuka, kiran waya yayi sai ga wasu kartan maza sun shigo daita tana fezge fizge tana son yin ihun babu baki gaba d'aya gashin kanta sun hargitse.
Ak yabasu umarnin su cire mata plast bakinta sannan su kwanceta aikata hakan keda wuya sai ga sautin muryarta a hargitse.
"yeeeeeeeeee hhhhhhhhhh nice nice ni........ ce naje gurin boka shugaban aljanun kan dutse ya sihirce min Abdulkabir tundaga lokaci dana ce ina son shi yace bai sona shine kawata bolaji ta kaini gurin boka yayi masa asirin daya dawo daga kasar spain batare da shiryawa hakan ba...
takarasa maganar tana kwashewa da wata mahaukaciyar dariya hhhhhhhhhh "nice nan na sashi ya saki matarsa su'ad har saki uku rassss...... "yeesssssssss tayi wani juyi tare da yin tsalle ta haye bayan kujerar da Ak ke tsaye tana cakulinsa nice nice nice shi kuwa mari ya dauketa dashi" karya kike ni bakisani na saki matata domin kuwa Allah ya tsareni a wannan lokacin ban saketa ba.
ita kuwa maman zeey wani irin kuka ta fashe dashi tare da furta "nashiga uku Zainab haukan gaske kike ko na karya Allah ba zai sa naga wannan ranar ba, naci wahalar ubanki wanda har yau ban fita aciki ba shine kema kika tsunduma kanki cikin wannan tashin hankali kuka take sosai har da shesheka sauran Jamar gurin kuwa cirkocirko sukyi har lokacin suna kallon sarautar Allah tunda suka zo duniya basu taba gani irin wannan tashin hankali ba Ammi kuwa banda kalmar "inna ilaihi wa inna ilaihi rajiun babu abinda take furtawa tana sake maimaitawa daga karshe tace "zainab ke...ke..
Zeey tayi saurin cewa ehhhhh "nice nayi komai tana tafa hannuwanta duka tana kokari kamo Ak yayi saurin janyota ya buga kanta da bango dakin ta zube kasa can kuma zaraf ta zabura mike tsaye tana sake kwashewa da dariya "nice nice nice nan na nemi Akil da kaina nace ya dinga saduwa dani yana rage min karfin shawarka dake damuna dan tunda naso na bude idanuna na daurasu akanka nake jin shawarka, ko lokacin dana balaga da shawarka nasoma balagata, william's yayi dani Sadik yayi dani Abbas yayi dani duk wanda yayi sex daita sai data furta mamanta tayi kanta takamota tana k'ok'ari rufe mata baki "Zeey ta d'auketa da wani gigitaccen mari tana kwashewa da mahaukaciyar dariya .
"kibarni na fadi abinda nayi nice eh nice ta dinga zagaye dakin tana tsalle tana kiran nice can ta kwasa da gudu zatayi waje mama tayi kanta tare da hjy kaka Ammi kam kasa motsi tayi daga zaunen datake duk da tasan zainab tayiwa d'anta asiri amman batun bin maza ya taba mata zuciyarta ,yau da wani ne yagaya mata zata karyarta hakan.
da taimakon dady aka samu aka kamo Zeey dake ihun"kubarni na fita shugaban bokaye da aljanun kan dutse na kirana "a a nazo zo, nazo mu tafi ko piiiiiiipppppp ganin nan zuwa "wayyo ku sakeni bokana nakirana tayi kukan kura ta kufce daga hannunsu bayan ta dauke hjy kaka da gigitaccen Mari har kuga biyu hjy tayi taga taga ta zube kasa warwas tana kuka maman zeey nayi..
zeey tayi waje aguje tana zunduma ihun "nice nice nayi komai "shugaban bokaye ganin nan zuwa.
maman zeey ta kurma ihu " wayyohhly Allah dan girman Allah yaya kutaimin karta fita "wayyo Allah mutuwa zanyi wani irin rayuwa ce haka zainba kikajefa kanki ciki ?
take securities suka shiga tara taran kamota a man kafin kace me tuni ta balle ta fice aguje tabar gidan tana tuki da hannunta kan titi unguwar securities suka bita abaya.
maman Zeey naganin ficewan zeey nan ta fadi k'asa sumammiya....
securities kasa kama Zeey sukayi har titi suka bita amman ina ta tsere musu d'an kafin kiftawa da bisimilla suka nemeta suka rasa..
Haka akaci gaba da gudanar da sha'anin biki bisa umarnin dady, sai dai kallo d'aya zakayi ma Ammi kagane tana cikin damuwa da tashin hankali matuk'a, domin batada walwala ko kad'an rashin su'ad wani babban gib'i ne a rayuwar ta.
Wai d'anma Umman su'ad ta tsaya kai da fata akan bikin domin Ammi birkice musu tayi ita sam baza ayi wani biki ba inba anga diyarta ba, gashi neman duniya anyi amma ba aga su'ad ba, duk inda akasan zata anje babu ita babu ala'mun kullum AK yana faman bulayi a gari neman su'ad tamkar mahaukaci gbdy duk yafita haiyacin sa yakoma tamkar sabon kamu, rabon shi da runtsawa tun randa abun ya faru ,kwana yake kuka da addua Allah yabayyana masa inda matarsa take.
maman zeey kuwa da tun lokacin da abun ya faru tana hospital da kyar likitoci suka samu ta dawo haiyacinta , numfashinta ya dawo ta farka tana kuka tare da yiwa diyarta adduar samun lafiya.
Ita kuwa Umman su'ad bata tab'a tsintar kanta cikin farin ciki, nishad'i da kwanciyar hankali ba irin na wannan lokacin, ita jikinta yana bata 'yarta tana wuri nagari wurin daya dace.
Hannu nagari aduk inda 'yar take to lallai tana cikin farin ciki da walwala wanda bata tab'a samu ba a rayuwar ta domin kullum sai tazo mata cikin barci tana mata murmushi me k'ayatarwa tace "Ummana ban tab'a samun kaina ciki jindadin rayuwa ba irin wanda nake ciki a yanzu.
"kema ina miki k'wad'ayin shigowa duniyar danake ciki Umma kid'and'ani dad'i da gardin dana ke d'an d'an.
Kullum haka Umman su'ad take fama kuma inta tashi zata dinga jinta cikin farin cikin .
Yau ake Mother's Day d'in eman da Musty hall yacika yayi mak'il da al'umman annabi inda Ado Gwanja yazage sai wake amarya da ango yake MC ne yadakatar da Gwanja domin gayyato amarya da angon a fili "Ado Gwanja yace "yana ison kayarta ma amarya da angonta da zafaffan wak'a saboda yanzu lokacin iyayen amarya ne sufito sunana farin cikin, dai dai Umman su'ad ta dok'a wurin Ammi tanace mata tasaki fuskanta dan Allah muryan MC sukaji yana fadin."
"Gaskiya amarya tamu 'yar gatace lallai wannan bikin na yar gata ce shugaban airvioce da kansa lallai babu mamaki dan an lika dollas.
dollas kawai ke zuba musu makad'an Gwanja anga dala sai k'ara sautin muryarsa suke da iyankan k'arfinsu Umman su'ad tace ammi "tashi muje muyi lik'i da kyar dai Ammi ta tashi.
Sir mahabub yana ta barin dala shida matarsa shemah su Ammi suka iso suka fara nasu zuba ruwan kudi juyowan da Sir mahabub yayi don gaisawa da Amim idanunsa ya fiddo waje gabanshi yafad'i da k'arfi kanshi yasara yasoma ganin juwa tare bakinshi dake rawa yace "
"Sali.......tun kafin ya kai ga rasa furtawa ya
zube k'asa wanwar................
mmn sudais ce
💗💗💗💗💗💗
SAI KA AURENI DOLE
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
~NA~
*AYSHA A BAGUDO*
Dedicated To
Hauwa A Usman
Jiddar
YA RAFI'U
THE EXALTER
page 82
.............tsoro da matsanancin firgici Ammi ta hango bayyane akan fuskar Umman Su'ad dake tsaye a gefenta jikinta na kirrrma, yayinda madam Shema ke tsugunne akan gangar jikin Taufeek tana girgizashi tana ihun kiran sunansa zuciyarta na tsananta bugawa kan abinda taga ya faru da mijinta.
cike da matsanancin tashin hankali Umman Su'ad tashiga nunashi da yatsan hannuta zuciyarta na wani irin bugawa da k'arfi bakinta na rawa da illahirin gangar jikinta ta furta complete name dinsa cikin wani irin sark'akk'iyar muryar da ita kanta batasan tana
da ita ba,
"Tau...Taufeeq Abubakar Tafeeda gulun ........
"sai kuma numfashinta ya tsaya cak,
yasoma barazanar d'aukewa cikin wani irin sanyin jiki tayi luuuuuuuu zata fad'i 'k'asa, cikin zafin nama Ammi tayi saurin tarota jikinta tana kiran sunanta Saleema Salema!!"
" ki tashi dan Allah karku sa zuciyata ta buga.. amman ina Umman Su'ad ko ala'mun motsi batayi ba..
Gaba d'aya mafi kusancin' 'yan uwa ne suka taru akansu suna kallon Sir Mahbub wanda sukaji Salema takira da Taufeek a yanzu,
da ita kanta Salemar dake zube jikin Ammi babu ala'mun numfashi atare da ita.
kafin kace me take gaba d'aya hall din ya hargitse da hayaniyyar mutane kowa da abinda yake fad'a akan abinda ya faru ahalin yanzu, Musty ne ya duba yaga itama Umman Su'ad din suma tayi,
dan haka cikin sauri ya fito da wayarsa cikin rawar jiki yashiga kiran number minister Mubarak wanda bai rigada yak'araso ba tukun.
Cikin tashin hankali ya sanar dashi komai daya faru "cewa Minister yayi a yayyafa musu ruwa yanzu, yana kan hanya k'arasowa babu musu Musty ya fad'a musu abinda Minister ya fad'a masa, aka kawo ruwan roba aka shiga tsiyaya musu an dai yi sa'ar Salema ta farfad'o amman shi Taufeek ko ala'mun farfad'owa bai yi ba.
Nan fa hankalin Shemah da Salema da ma Ammi gaba daya ya sake kololuwar tashi, inda Madam Shema ta d'aura hannuwanta duka bisa kanta tana kurma ihu da kururuwa kiran sunansa" dan Allah mahbub ka tashi,
ka tashi karka mutu kabarni kasan bani da kowa sai kai, "duk duniya kai kad'ai nake da,
" dan Allah ka tashi karka mutu kabarni .....
yadda Madam Shemah ke ihun kuka haka salema ke rike da hannunsa tana wani irin marayan kuka me tab'a zuciya tare da kiran sunansa "Taufeek d'ina,
ka tashi karka mutu karka sake barina a karo na biyu har sanda aka tattara gangar jikin Taufeek aka sakashi cikin mota direbansa ya fige motar aguje escort dinsa suka biyo bayan motar dayake ciki gudu kawai suke sharara kan titi.
Kai tsaye Shemah tace "ayi babban asibinti dashi fadar haka keda wuya taji saukar murya Ammi cikin kunnenta inda take bawa direban umarnin yawuce dashi gidanta,
haka kawai Shemah ta tsinci kanta da kasa mutsawa umarnin Ammi,
dan haka kawai take jin zuciyarta na rawa tun sanda ta d'aura idanunta akanta ta tabbatarwa kanta lallai akwai wata alak'a me k'arfi atsakaninsu dan kamartasu ya baci ..
"meyasa Mahbub ya firgita tare da suma akan yaga fuskar matar da batasan ko wacece ba, asalima yau ce rana ta farko data soma ganinta arayuwarta..?
"to ko Mahbub d'inta ya dawo cikin duniyar tuninsa ne sakamakon ganin fuskar matar ? tashiga yiwa kanta tambaya kirjinta na cigaba da bugawa da k'arfi.
"idan takasance ya dawo cikin tunaninsa kuma wannan, matar takasance matarsa ce alokacin ganinyar tunanisa, ya nata makomar rayuwar auren zai kasance..... ?
ta sake jehowa 'kwakwalwar ta tambaya zuciyarta na sake dokawa da sauri sauri,
"Allah kasa halakar yan'uwan takace kawai atsakaninsu ba aure ba ta tsinci kanta da fadar haka cikin k'asan ranta.
yadda Madam Shemah take tunani da zance zuci haka Umman Su'ad ke zurfafa tunaninta wanda ya zarta na madam shema sau ninkin ba ninkin tare da kisma matsayin Madam Shemah ga Taufeeq d'inta.
"yakayi Taufeek d'inta ya tsira daga mammunar hatsarin daya faru dasu har yayi aure a wata duniyar ya manta da ita arayuwarsa ?
"Ai kuwa idan haka ya kasance gaskiya data sake tafka babban kuskuren arayuwata, na 'bata tsawon rayuwarta datayi akan kaunarsa ....
cike da tashin hankali shemah ta juyo a firgice tana fuskantar gefen da Ammi ke zaune tana zubda hawaye tasoma magana cikin harshen turanci,
"dan Allah kiyi hak'uri akai shi hospital domin tsiratar da rayuwarsa banason na rasashi,
wallahi shine komai na rayuwata,
"rayuwar da babu Mahbub cikinta kango ne babu majingini...... takarasa maganar tana sake bawa direban umarnin zuwa hospital.
"Ammi dan Allah ki bari akaishi hoapital kar murasashi zuwa dashi gida bashi da wani amfani a wuce dashi hospital d'in Doctor rak "Ammi kinsa komai akaina kinsan halin k'angin rayuwar dana shiga akansa "dan Allah ammi karki bari na sake rasashi a karo na biyu arayuwata .. kuka suke sosai suna rokonta tamkar wasu yara k'anana,
wanda haka yasa Ammi kasa cewa komai
d'an kusan tafi kowa shiga tashin hankali sai dai murnar faruwar wannan alamari ya d'an natsar da zuciyarta, d'an batasan yadda zata misalta tarin farincikinta ba.
" yau tazo mata da abubuwa dayawa na rud'ani, farinciki da akasin haka ..
"abubuwan farinciki sun sha faruwa daita arayuwa amman wannan farincikin ya zarta kowani irin farinciki gareta ,ayanzu fatanta Allah ya farkar da d'an'uwanta ya dawo tamkar yadda take son ganinsa ..
"A she dai gaskiya Abdul ya fad'a mata lokacin baya a farkon had'uwarsa dashi har yazo mata da zance amman ta karyata yuwar haka ?
"ashe gaskay ne ba karya bane zata sake rayuwa da d'anuwanta mafi kusancin d'an uwa arayuwata, har su cigaba da rayuwarsu tamkar yadda suka ginata a can baya?
"wannan farincikin da me yayi kama?" idan aka barta da wannan farincikin kawai ya isheta karasa sauran rayuwarta datayi saura cikin salama da kwanciyar hankali mara misaltuwa .
da wannan tunanin suka k'araso hospital inda suka iske minister tare da wasu manya likitoci suna jiran karasowarsu suna gama karasowa batare da 'bata lokaci ba aka turo gadon marasa lfy aka daurashi aka nufi zuwa wani special room da minister yabada umarnin akwantar dashi sannan suka d'aura masa drip har lokacin bai farfado ba ransa na hannun Allah.
taimakon gaugauwa suka shiga bashi, da kyar suka samu nasarar dawo da numfashinsa daya d'auke sakamakon buguwar zuciyar daya samu.
bayan numfashinsa ya dawo daidai ,minister ya dawo kusa dashi ya tsaya akansa yana karewa amininsa kallo tsab "tabbas wannan shine mutumin da zuciyarsa take cike da kewa da mararin sake d'aura kwayar idanunsa akansa bayan wasu shekaru da suka shud'e, sosai ya tsurawa fuskar Taufeek ido tamkar ranar yasoma ganinsa kallonsa yacigaba da yi kafin daga baya ya fita ya bar d'akin tare da bawa Ammi kad'ai umarnin shiga taga yanayin jikinsa amman sai ga Salema da shema na rigerigen shiga d'akin kusan atare suka iso kansa kowanensu na kokarin taga ta kai hannunta jikinsa.
Salima ce tasamu nasarar rike laulausar tafin hannunsa cikin nata ita kuma Shema tayi k'ok'ari d'aga kansa ta d'aura saman cinyarta tana shafa sumar kanshi tana sauke naunauyen ajiyar zuciya.
wasu daga cikin tsirarru'yan uwana suka shigo d'akin suna tambayar yanayin jikin nasa" da sauki Ammi tace can bayan kamar minti goma doctor Rak ya sake dawowa d'akin cikin tsantsar farinciki yake taya Ammi da Salema murna sake ganin Taufeek a rayuwarsu daga karshe yace "su d'an barsa saboda yana buk'atar hutu dan kwakwalwarsa ta sake samun natsuwa .
zaune yake cikin motarsa kirar land cranch yana direving ahankali cike da matsanancin fargaba da tunani iri iri "ta inda zaiga Su'ad d'insa bugun zuciyarsa ,rayuwarsa yake "tunda abun nan ya faru bai sake samun natsuwar zuciya ba kullun fita yake bulayin nemanta cikin gari, "duk inda yasan zai ganta daman idan baiyi tunanin zai ganta ba yaje amman har zuwa wannan lokacin ko ci karo da me kama da ita zuciyarsa baiyi ba.
wani lokacin haka zai samu guri gefen titi yayi parking ya d'aura kansa saman sitiyarin mota yayita kukan xuci yana zance zuci yana hasko fuskar matarsa mafi soyuwa cikin ransa .
haka zai d'auki lokaci zaune yana tuna rayuwar da sukayi abaya tun kafin ya aureta da bayan aurensu, a halin yanzu kusan haushin kowa yake ji ganin yadda aketa sha'anin farinciki , alhalin an sa shi yana tattare da tashin hankali .
kiran wayarsa ake yafi sau goma sha amman da zarar ya duba screen din wayar yaga kiran daga Musty ne "sai yaja dogon tsaki tare da katse kiran a ganinsa kiran me zai masa?
"Lokacin daya rasa matarsa lokacin shi ya bude sabon shafin rayuwar farinciki ,wani kiran ne ya sake shigowa ya buga sitiyarin motar da k'arfi sannan ya d'auki wayar a fusace "lafiya malam zaka dameni?
"dan Allah kayi harkar gabanka nayi tawa ya ja tsaki yana k'ok'ari kashe kiran Musty yayi saurin dakatar dashi "please abokina karka d'auki zafi dani karka d'auka ban damu da damuwarka bane ko babu halakar komai tsakaninmu dole na tayaka jaje da jimamin tare da tayaka neman matarka.
"wallahi Ak na damu k'warai da rashin sanin inda Su'ad take kawai kafafuna ke tsaye amman ni kad'ai nasan irin tausayawar danake maka........
"dakata dan Allah malam banson long talk kiran me ka min yanzu bayan kun gama shan budurin
19, September 2025
Aisha Auwal
Wow