Showing 102001 words to 105000 words out of 420383 words

Chapter 35 - SAI KA AURENI DOLE BY AYSHA A BAGUDU.txt

zan kebe maka kaina da kaina sai dai ina tabbatar maka zan sake dawowa gareka..mgnr kana sona ko akasin hk lokaci ne zai nuna.
da karfi police suka ja mota sukayi gaba ..

hankalinsa yayi mugu mugun tashi dajin lafazinta, me tataka dazata dinga gaya masa duk abinda yazo bakinta km alokaci tagama ?
wacece ita ..?
ya Allah wai meke shirin faruwa dani da rayuwata ne?
wannan wace irin matseefa ce ke shirin kusantoni?

ahankal shima ya juya ya koma cikin tafkeken gidansa cike da matsanancin tsanyi jiki da fargaba mara misaltuwa, yashiga motarsa ya tayar .
Williams na daga Masa hannu. amman ko kallon inda yake bai yi ba.

zaune kawai yake cikin motarsa yana diriving amman natsuwarsa da hankalinsa basa gangar jikinsa, ya dubi agogon diamond dake daure da tsintsiyar hannunsa wanda tsayawa fadar adadin kudinsa bata lokaci ne.
,karo na sau ba adadi kenan dayake ta jan dogon tsaki .
baisan me yashiga cikin tunaninsa ba akan yarinyar ..
da har yake kokarin hana police taba lafiyar jikinta, tare da hanasu daukar matakin laifin datayi ayanxu ,tabbas duk abinda ta lisafo akansa hk ne sun faru sai dai shi ba dan wata manufa ya hana securities dinsa da malik da wannan police din dukanta ko wani abu me kama da hukunci ba...hakika yasan bai sonta bai kaunarta asalima bai kaunar daura idanunsa akanta .
to meyasa meyasa take da tabbacin yasoma sonta...?
babu irin tunanin da baiyi ba akanta kafin yakarasa gida, da taimakon Allah ya iya kawo kanshi ikeja gra.
yana shiga farfajiyar gidansu kai tsaye parking space ya zarce yayi park din motarsa.
ya fito yana tan gadi tnkr wani mashayi ya nufi part dinsa .
tun daga barandar saman dady ya hango shigawarsa cikin wannan yanayin, take hankalinsa yayi mugun tashi da tsorata da ganin yanayinsa.
magzine din dake rike a hannunsa yasoma nadewa tare da mikewa tsaye ahankali yasoma tafiya zuwa part dinsa, wanda kusan atare suka shigo cikin parlour'n.
ak wanda ya zube a kan kujerar three star .
ya dago mayattun idanunsa dan jin motsin shigowa .
dady yagani yana kokarin sanyo kanshi cikin parlour'n ,har dady yakarasa shigowa ahankali ya nemi guri ya zauna yana fuskantarsa, idanun AK na kansa yakasa daukewa,sai numfashi daya furzar ahankali .
shima dady idanunsa ya tsura masa yana kallon yadda gabadaya yaron nasa ya dawo a dan tsakankanin wannan lokaci..
duk da kasancewarsa mara kiba amman zuwa yanzu ya sake ramewa fiyye da ko wani lokaci, kallo daya zaka masa kasan yana tattare da damuwa.
ahankali dady ya sauke naunauyen ajiyar zuciya still idanunsa na kan tilon dansa mafi soyuwa aranshi, sannan yakira sunansa ahankali abdulkabir..... AK ya gyara zamansa tare da amsawa muryarsa can kasa. meke damunka abdulkabir wanda yasa gbdy yanayinka ya sauya irin hk ..?
idan kana tare da wata damuwa ne ni mahaifinka ne ka fito kasanar min nasan abinyi akai.
, dady yaja yayi shiru dan son jin abinda zai ce amman yaji ak yayi masa Shiru yaki cewa komai sai dai mayatattun idanunsa daya zuba masa..
dady ya sake numfasawa cikin sanyin muryar yace ko kasoma shaye shaye ne abdulkabir?
da sauri AK ya mike zaune sosai yana duban cikin idanun mahaifinsa tare da girgiza masa kai.
ok kasanar min damuwarka ?
, ko shirye shiryen aurenka ne yasaka kasancewa hk? dady ya sake tmbyrsa.
nan ma ya girgiza masa kai yayi tare da sunkuyar da kanshi kasa .
pls my son if their is anything wrong let me know ?
ganin yanayin da mahaifinsa yashiga alokacin yasa shi
ahankali ya bude bakinsa yasoma bawa dady, labarin abinda ke faruwa tsakaninsa da su'ad, tun daga sanda tasoma bibiyarsa har sanda yasoma saninta zuwa yau din nan da yadda yasanya police sukayi arrest dinta.
dady yayi shr yana dubansa cike da matsanancin mamaki da tausayawa..
kusan minti talatin ya dauka yana kallon tilon "dan "nasa kafin daga baya ya sake numfasawa, sannan yace meyasa ka aikata hk abdulkabir......?
a tunina duk mutumin daya bude baki yace yana sonka koda kuwa mahaukacin dake yawo akan titi ne bai cancin wannan tuzarcin da wulakanci daga gareka ba.
, ballantana cikakkiyar me hankali .....
dady ni bana sonta ne ita km ta nace min dayawa.
data nace maka dayawa sai akace kamata wannan tuzarcin, ita din abar tausayi ce ,duk da banganta ba na tausaya Mata .
ita soyayya daga Allah NE ,babu wanda ya wuce ya tsinci kanshi cikinta sannan Allah yana jarabtan duk wanda yagadama daita .
Allah dady dan baka ganta bane shi yasa kake fadar hk, Amman wlh dady dazaka ganta zakaga kwata kwata bata dace dani ba.
duk fa abinda kasan mashayi nmj nasha babu wanda batasha, ta yaya zan tsaya sauraran mace irinta .
ai ajina ya zarta nata, taje can ta nemi mijinta gaba amman ba dai ni abdulkabir ba.. murmushi irin nasu na manya dady yayi tare da meida bayansa ya jingina akan kujerar dayake zaune. bance ka aureta dole ba ,amman bata cancanci wannan kaskancin ba.
zanso ka bada izinin sakinta a police station sannan ka gyara mu'amularka daita ta yadda zata samu natsuwa da salamar zuciya , duk macen datake cikin hali irin wanda take ciki tana bukatar rarrashi da kulawa tare da tausayawa, bakasani ba ko ta sanadiyarka zata shiryu tabar abinda take aikatawa, dan hk ina umartarka yanzu yanzu kakira a saketa.. shiru ak yayi yana sauraron dady tare da tsurawa Zara zaran yatsun kafafunsa ido yana kallo da tunani shi sam bai ga aibun abinda ya aikata mata ba.
balle yaji nadama ko wani abu shi tausayi .
shirun dayaji dady yayi ne sanyashi dago mayattun idanunsa yana dubansa, shima kallonsa yake tare da mikewa tsaye, ka tabbatar da kayi abinda nace if possible ma kazo min da yarinya ina son ganinta .. yanakarasa fadar hk yakama gabansa.
yana fita ak yashiga tunani sosai, so yake ya gano rashin dacewar abinda ya aikata amman duk ta inda ya duba bai ga aibun yin hk ba, ahankali yasanya hannunsa daya yasoma babbale botiran gaban rigarsa ya cire rigar yasoma cire wondan dake sanye ajikinsa ya saura tsirara ya mike rike da kayan zuwa bedroom dinsa ya bude dakin da washin machine dinsa yake ya zuba kayan ciki ,sannan ya fito yakarasa inda towel yake jikin kofa ya dauka ya daura yashiga bathroom ya dade tsaye cikin bathtub ruwa na tsiyaya a sansar jikinsa wanka yake son cikin dadin rai amman ,tunanin yarinyar yaki barinsa a gurguje yakarasa ya fito.
koda ya fito bai wani kira police station ba kmr yadda dady yace.
kawai sha'ani gabansa yasoma yi dan system dinsa ya dauko ya haye saman gado tare da jonata a charge ya jingina bayansa da pillow yasoma browsen .da tura sakowani.
kwana daya tsakani tafiyar gaugauwa takamashi zuwa abuja shida babban amininsa musty da wasu daga cikin manya ma'aikatan companies dinsa.
kwana biyu zasuyi cikin na 3 su dawo .tafiya ce datazama dole sai yaje if not babu inda zashi, sabon companies addas mali da toyos mother da zai bude ,ga intervew daza'awa sabbin works duk da wannan duty ya daura musty ,da bai san yadda zanyi ba dan abubuwa sunyi masa yawa,
hk ya wucewarsa batare da ya waiwayi police station ba.

yana zaune a dakin hotel din daya sauka, daga shi sai sai boxes iya cinyarsa da Whit singlet laptop ce agabansa sai tarin file file's dake zube akasa jibgib wasu zai sanya hannu , wasu km zai shigar da sakonni ne cikin system, kira ne yashigo wayarsa amman yaki daukaz har wayar tagaji da kara ta katse
sau ba adadi akayi ta kiran wayar kafin daga bisani yasoma lalubo wayar batare daya dauke idanunsa akan system ba ,ya dauka ya manna akuneshi yana cigaba da aikinsa ,jin sautin muryar data doki dodon kunensa ne yasashi dan gyara zamansa, still idanunsa na kan system, muryarsa ahankali yace an wuni lfy .
bangaren commission juyi yayi akan kujera dayake zaune tare da cewa lfy abdulkabir ykk ya aiki da shirye shiryen biki?
alhamdullahi dady.
commissionee yace kasa an yi arresting din yara har yanzu suna tsare batare da ka leko ba ,gashi ko waya baka kira ba har yau tsawon kwanaki 2 kenan kasan yanzu yanayin dokar garin ta bace, ba kmr lokacin baya ba, yanzu da mutun ya wuce kwana biyu zuwa uku koto ake wucewa dashi .
idan km aturasu zuwa koto ne kana iya zuwa kasa hannu, idan km a sakesu ne shima muna jiranka, tunda commission yasoma mgn ya dauke wuta ya daina gane sakonin dake shigowa ta cikin system dinsa da wanda yake turawa .
dan hk ya tsaya cak tare jifa babban dan yatsansa cikin bakinsa yana cizawa ahankali har commission ya dasa aya, km sai lokacin ya tuna da zance wasu yara dayasa aka kama dan kwata kwata shi ya mance da zance wasu yara.
ayyukan gabansa kawai yake aiwatarwa da shirye shiryen bikinsa .
dan hk ahankali ya sauke numfashin tare da sauke naunauyen ajiyar zuciya sannan yace nayi tafiya ne dady amman Inshaallahu gobe by this time ina office dinka nan sukayi sallama.
tunda commissioner ya katse kiran, ya kasa zaune ya kasa tsaye gbdy yakasa aiwatar da komai .
"tunanin yarinyar da kamaninta suka shiga zuwa masa daki daki , kenan duk iya kwanakin na tana tsare a cell...?yayiwa kanshi tmbyr yana shafa kwantaccen sumar kanshi kana ya runtse mayatattun idanunsa yana sake shafa kwantaccen sumar kanshi komawa yayi ya zauna ya janyo system gabansa amman yakasa aiwarta da komai banda fuskar yarinyar ayanzu babu abinda yake gani acikin system idanunsa ya tsurawa system din yana kallo wai gata tana kuka tana rokonsa ya so ta ,ya entoto daga shingin wasu ,kada ya wasar da soyayyarta, ganin yana kokarin manta komai sanadin tunaninta yasashi kashe laptop ya tattara files guri daya ya zuba uban tagumi.
da daddare yana kwance shiru a saman gado, sai juyi yake daga wannan bangaren zuwa wancan bangaren baki daya garin Abuja yayi masa zafi, ya manta yaushe rabon ya tsincin kanshi cikin damuwa irin hk, da kyar yasamu bacci barawo yasamu nasarar saceshi cike da tunanin yarinyar da mafarkinta.

washegari

3:00 daidai jirginsa ya sauka a murtala international airport motaci 5 ne jere suna jiran karasowarsa . ahankali yake saukowa daga matattakalar jirgin jikinsa sanye cikin wando da rigar suit ash colour sai yar cikinta Whit hannunsa daure da agogon relex kafafunsa sanye cikin wasu hadaddun shoe masu kyau da sheki.
ahankali yake takowa daga matattakalar jirgin yana gyara zaman tie din dake zagaye da wuyansa. sanyayyen kamshi turarensa gbdy yacika ilahirin gurin yana isar da sakon tahowarsa abdulkabir adam kennan kyakkyawa ne aji farko goggagen dan duniya ne me tsautsauran ra'ayi matashi me ji da kanshi. tun kafin su karaso inda motocinsu suke jere aka soma babbude musu motaoci , wace zai shiga ce atsakiya biyu baya 2 gaba suna gama shiga direboving suka tada mota.
ahankali ya kai mayatattun idanunsa kan agogon dake daure da tsintsiyar hannunsa ya jan tsaki sannan yayi mgn cikin sanyin murya dake nuna ala'mun gajiya yana bawa direban umarni.
ka wuce dani sac's office .
ok boos sannan yakira wayar musty kasancewar shi yana motar dake baya, ya sheda masa su wuce companies shi akwai inda zashi, suna kaiwa karshen brige din daya tawo daga airport ikeja inside suka rabo..

zaune yake a office din commission suna tautaunawa akan lamarin byn commissioner ya aika a tawo dasu su'ad. cikin minti goma aka shigo office din dasu.
,gabadaya sun fita haiyacinsu ,dan koda ak yagansu sai daya firgita da kyar ya ganesu sbd yanayin yadda kamaninsu ya sauya, barinma su'ad wace gbdy kanta ya kumbura, siririn hancin nan nata ya nitse ciki sosai fuskarta ta sauya ,wanda yasanta ne kawai zai iya tantanceta, sunyi bakinkirin kayan jikinsu tun na shekarajiya dayasa akayi arresting dinsu ne sanye ajikinsu.
da sauri ya dauke idanunsa akansu yana ambaton suna Allah , ya salam ya furta yana girgiza kai zuciyarsa na wani irin harbawa ,muryarsa ahankali ta fito ta yadda basu jishi ba.
sbd Allah dady waye yayi mata irin wannan dukan..? shi bai ma damu da irin raunukan jikin ore ba kmr nata.
commission yace mahukunta ,sbd an tabbatar min byn rashin kunya da cin mutuncin da suka yiwa ma'aikatantanmu ita waccen ya nuna inda su'ad take tsaye har da marin inspector kule tayi..... kasa cewa komai ak yayi ,ya dan juyo ya sake satar kallonta sannan yasoma mgn da commissioner sun dan dade suna zantawa inda daga karshe AK yace kmr yadda nayi maka bayanin komai dazu, so nake tarabu dani da rayuwata taje tayi nata rayuwar sbd ni daita sam bamu dace ba. kafin commission yayi mgn yaji sautin muryarta cikin kunenshi ba kada hankali abdulkabir ko nace hankalinka bai cika ba, a zabure ya juyo yana kallonta da mayattun idanunsa.
inda kasan wahalar dana sha akan soyayyarka bazaka fadi hk ba.
da wuya da azaba zai sa na barka da yanzu an wuce gurin ,ina sake tabbatar maka da *sai ka aureni dole* commission ya bude baki yana cewa bazai yiwu kice hk ba, tun da ba'ayin aure ta hanyar da kike biyo .
idan ma kina son ya aureki ne, kamata yayi ki natsu ki dawo haiyacinki ,domin a yadda kike din nan babu me ganinki hk yace zai aureki indai ba mahaukaci bane ...
wannan mahaukacin dakake mgn akai gashi nan zaune agabanka km ko yana yawo tsiyarara da hauka tubaran shi zuciyata tagani km takamu da sonshi .dan hk kagaya masa ya aureni kawai a wuce gurin, ko km ka tabbatar masa da yanzu aka soma wasan...musayar mgn suka dingayi da commissioner babu wata tsoro ko fargaba wanda daga karshe commission yace a sallami ore abar su'ad .
byn ore ta fita commission ya mike tsaye tare da zagayowa zuwa inda take tsaye yace ta zauna tare da nuna mata wata karamar kujera.
ta zauna tana cizan lip's dinta na kasa batare da takalli inda ak ke zaune ba yayinda shi kuwa AK duk motsinta akan idanunsa take.ya kasa dauke idanunsa akanta .
commissioner , yayi shiru kawai yana kare mata kallo.
naji duk abinda kikace kina son shi wannan yaron irin son da bantabajin irinsa ba ko atahiri. sai km kikayi rashin sa'a shi din ba sonki kmr yadda kike masa.
amman yanzu ina son kimin wani abu guda daya .
kiyi hkr ki hakura dashi tun da shi baya sonki idan kika natsu kikayi addua da hkr sai Allah yabaki wani wanda yafishi..
abinda bazai taba yiwu ba kenan ta fadi hk sbd ganowa datayi wayo kawai commissioner ke son yi mata.
, ina son kasan wani abu kai ma, abdulkabir kadai zuciyata ke so da muradi kasancewa tare dashi matsawar bai yanto zuciyata ba, damuwata zata kasance damuwarsa, matsalata zata addabeshi .
duk wannan bakar rayuwar da nakeyi akan shi ne fa.
sai kawai na hakura wata ta aur.....da sauri abdulkabir ya mike tsaye cikin tsananin fushi yake fadar baki isa ba... baki isa ki tursasani aurenki ba ..ko saka zuciyata abinda batayi niyya ba.
wuya da azaba tattare da matsin rayuwa yanzu kikafara sha koma nace baki ga komai ba .
kima soma kukan rasani.dan kuwa zaki rasani rashi na har abada dan bazan taba aurenki ba. dan hk ki tashi kibar office din nan yanzu tun kafin in zamo ajalinki ,ki bar duniya da huja.
, cikin tsananin firgici da faduwar gaba ta dago fuskarta wace take wanke da ruwan hawaye tana kallon cikin kwayar idanun masoyinta mafi soyuwa azuciyarta .
"ahankali ta mike tsaye zuciyarta tmkr zata buga .... still idanunta na cikin nashi batare da tace masa komai ba ,domin tasan matsawar batayi abinda yace ba ,bakaramin aikinsa bane yayi mata dukan mutuwa agurin ahkali cike da sanyi jiki da tausayin kanta ta mike tasoma tafiya tare da bude kofar ta fice daga office din.
komawa yayi zauna tare runtse mayatattun idanunsa ,hannusa yasa yana shafa fuskarsa dashi gbdy yarasa me zai sake cewa akan lamarin yarinyar.
commission ne yashiga bashi baki kafin daga baya ya bude baki da kyar yayi masa sallama.


koda su'ad takarasa gida da gudu ummanta taje ta rungumeta ,tana kukan da murna ganinta.
dan gbdy hankalita ba'a kwance yake ba ,babu inda bataje nemanta ba.
daga karshe ne aka tabbatar mata tana police station.
zamewa tayi daga jikin ummanta ta isa inda mirrow yake ta tsaya tana karewa kanta kallo, sannan tashiga bayin dake manne da parlour wanka take ahankali tana wanke kowani gaba dake gangar jikinta, ta dade bata fito ba, tana gasa jikinta da raunukan jikinta . tana fitowa ta iske ummanta ta shirya mata abinci ta daura mata akan dan karamin stood ,batabi ta kan abincin ba dan bashi ne agabanta .
tashige kuryar daki ta janyo jakarta ta ciro tabar wiwi tayi babban nade tare da kunawa tasoma busha hayaki tana lumshe fararen idanunta .
take hayaki ya bude dakin ,zariya take tana sambatu akan ak tana zukar tabarta har dai ta kai ga hayewa gado ta kwanta hawaye na gangaro mata .umma dake zaune cikin zullumi a parlour tasoma jiyo warin tabar wiwi da sautin kuka, da sauri ta banko kofar dakin cikin tsananin fushi take fadar bakiga komai ba yanzu kika soma kuka ba dai akan namiji kike neman kassara rayuwarki ba. maza maza ki tashi kibar min gida tun kafin na tsine miki ki karasa lalacewa kibi duniya da hujja tunda daman rayuwar kaskanci kika zabawa kanki.. cikin tsananin firgice da tashin hankali ta dago fuskarta daga kwanciyar datayi tana kallon fuskar mahaifiyarta mafi soyuwa gareta .
muryarta na rawa tace ki taimaka ...ki taimakeni ummana ki taimaki rayuwata ki sanyaya zuciyarki salama ki min addua ki cire kalmar tsinuwa agareni ki cigaba da nemammamin shiriya da sausauci wahalar da nake ciki agurin

Chapters

Related Ebooks
19, September 2025
Aisha Auwal

Wow

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login