Showing 201001 words to 204000 words out of 420383 words
Chapter 68 - SAI KA AURENI DOLE BY AYSHA A BAGUDU.txt
rubuta number ajikin gida.
"akwai prison na kidnappe's ,akwai na masu satar yara ,da cin nama mutun ,419 tare da yan kungiyar haya killi's.
bakin wani tafkeken get aka nufa damu
wanda ake ajiye kananun yan fashi da makamin , ina kallo aka bude dan karamin get din , mu km akasa muka bi layi ana tmbyr sunanmu daya byn daya tare da mikawa kowanenmu dan karamin plet na cin abinci.
"ni kam kin amsa plet din nayi sbd tashin hankali danake ciki ya girmami wani abinci..
"basu wani damu da rashin amsar plet din da banyi ba, sai ma muryar daya daga cikin dan fashi danaji yace "damana kin amshi plet din wata kila zai miki amfani gaba.
" atake anan nasoma amsar sakamakon abinda na shukawa rayuwata, asanadin taimakawa abdulkabir danayi ,domin wata uwar ashariya na lailayo da yaren yarbanci na maka masa ina hargagi tmkr wata zankanya.
ana gama rubuta sunayenmu da kotu tabayar arubuce, naga an rabamu da yan fashi sunbi ta wata haya daban nima wata hanyar daban aka nuna min ashe ba guri daya za'a ajiyemu ba hkn na nufin gurin mata da ban hk ma maza.
a gidan yari kuwa "ihu nake ina kuka "ina cewa sun cuceni sunci amanata ban san su ba suka min sharin fashi da makamin, "sun yi sanadin saka rayuwata cikin ukuba da taskon rayuwa, tare da zama silar rabani da mahaifiyata .
cikin kuka "nace wallahi wallahi koda laifin da kuka aikata min kadai ya rage muku shiga aljanna bazan taba yafemuku ba. zan tabbata ina muku mummunar addua da jafa'i iri iri a iya tsawon rayuwata ..
can km na dawo nadamar abinda na aikatawa rayuwata .
kaina na dinga bugawa a bango dakin ina ihun meyasa na sadaukar da farincikina akan mutumin da bai san da zamana ba?
"meyasa kika aikata hk su'ad ...?
"me yasa baki dauki shawarar ore ba kika biyewa son zuciya kika aikata tsafi?
"tsafi fa kikayi da iliminki da koma byn kinsa yin hk shirka ne me girma.....
"wayyohhly Allah na "meyasa na aikata shirka ?
"hakika Allah (swa) yana cewa acikin idanuna littafinsa me sarki "hak'kin allah akan bayinsa shine, su bauta masa shi kadai kada su hadashi da komai a gurin bauta "to ni meyasa nabiyewa son zuciyata na aikata ?
"gashi nan ai tun yanzu nasoma amsar sakamakon abinda na aikatawa rayuwata ,yau zanyi bacci acikin gidan yari .
"na juya ina kallon mutane dakin ina wani irin ihun na cuci kaina na aikata shirka da ilimina, byn nasan Allah ya haramta, hada waninsa dashi agurin bauta.
"yanxu meye makomata da makomar abinda na aikata ...?
cikin hk naji an dafa kafadata ta bayana "kiyi hakuri kiyiwa kanki adduar samun mafuta arayuwarki ta yadda zakiyi ramuwar gayya ga wadan da kuka tsunduma rayuwarki cikin matsala.
ban kulata ba sai ma ihun danake tare da yarfa hannuna ina wani irin kuka ban ankara ba naji saukar hannu bisa kuncina ana share min hawaye tare da rungumeni ana dukan bayan.
fige fige nasoma yi ina kokarin raba jikina daita ina sake sakin wani sabon kuka kafin daga baya na tsulale kasa nasoma jan gashin kaina ina zuba sambatun iri iri ina furta "na aikata shirka da ilimi akan mutumin da bai san da zamana ba gashi zan bata shekara 3 agidan yari ....
rawan roba naga yarinyar ta dauko tashiga bulbulamin tundaga kaina har zuwa jikina sannan ta kafa min sauran abakina .
"kisha ko zaki ragewa kanki radadin da kike ji , dole na bude bakina nasoma sha sbd yadda ta rike kaina da hannunta ga robar ruwan abakina.. byn nagama sha na sauke naunauyen ajiyar zuciya batare da na shiryawa hkn ba.sannan nacigaba da kukana me ratsa zuciya..
sautin muryar yarinyar naji ta doki dodon kunnena wace agirme baxata girmeni ba zamu iya yin sa'anni daita "sunana ganiya ke fa?
nayi mata banza hawayen idanuna na sake gangarowa "a maganganunki na tsinci wasu abubuwan game da abinda ya faru dake.
"amman tunda kika tsinci kanki acikin gidan nan hakuri ya zamemeki dole.
"kiyi hkr ki cire wannan damuwar danake gani atattare dake.
"idanuna ne ya sake cikowa da wasu hawaye.
"ni nan da kika ganmu tayi mgnr tana nuna sauran mutanen dake zaune acikin daki "rikakkun yan fashi da makamin ne babu garuruwan da dama zuwa yin fashi...
" satar da mukayi last a murtala international airport last year January kenan itace sanadin zaman mu anan har tsawon shrkaru biyar kotu ta yanke mana yanxu munci 2 sauran 3..
"Kema yar fashi da makamin ce ko? ta jeho min tmbyr tana dubana "na dago da kumburarrun idanuna da kyar na saukesu bisa fuskarta sannan na girgiza mata kai ala'mun a'a.
"me kikayi aka kawo ki bangaren yan fashi "
"sharri aka min nayi mgnr hawaye na gangarowa bisa kuncinta ....duk yadda ganiya taso taji abinda yakawoni prison naki yarda na gaya mata komai , "na tsaya akan sharri akamin.
hk ta hakura ta barni tacigaba da rarrashina tana bani baki,akan na daina kuka na shiryawa daukar fansa ga wadan da suka min sharri.
ranar yadda naga dare hk naga rana na kasa runtsawa duk inda na juya fuskar mahaifiyata dana abdulkabir nake gani.
"zamana a prison zama ne wanda nayi shi cike da matsanancin kunci da bakinciki tare da tausayin mahaifiyata.
" sannan tun washegarin ranar da aka kawoni aka bani aiki byn bulala hamsi da aka mun, wanda kaidar prison din kenan kullun garin Allah ya waye sai an yiwa duk wanda ya kwana ya tashi agidan bulala 50 tare da aikin wahala..
watanmu uku a prison aka sake dibarmu zuwa Samuel illori court, kafin sharia tazo kanmu sai da akayi case yafi guda goma sannan aka kazo kanmu.
ko ranar ma naci kuka tmkr raina zai bar gangar jikina sai zare idanu nake naga ko zanga wanda nasani .
"bayanin case dinmu dai aka sake maimaitawa da sake jadda mana zamanmu gidan yari har na tsawon shrkaru 3.
kmr zuwanmu na farko tsakayar ganduroba muke, muna tafiya ahankali ,wannan karon a yadda nake kallon fuskokin yan fashin nan ya sake tsoratani na fidda rai da tsammanin kubuta daga tarkonsu .
"a hankali muke daga kafafunmu domin sauka kasa inda motar black mariya ke zaman jiranmu kawai naga daya daga cikin yan fashin nan
ya arta da matsayacin gudu yana sauka akan step, ai take ihu da kururuwa ya cika koina a koto yan'sanda dake kai kawo a sorrounding gurin suka mimike tsaye tare da rufe kowace hanya dake cikin kotu ,ai barawon nagama saukowa kasa yaga an kulle koina na sorronding gurin, bai tsaya wata wata ba kai tsaye ya nufi katangar company din guineas dake manne da katangar kotu ya haura. ai nan police suka bishi aguje wasu suka zagaya suka shiga cikin campany ...
cikin minti goma sai gashi sun kamoshi sai dai yaci uwar duka har bai iya daga kafafunsa ga jini daya rufe kanshi yana tsiyaya ...
cell din dake cikin koto aka wuce dasu ni km aka hadani da police sbd sai yamma zamu koma prison, anan zamu yini tun abinci daren jiya ne acikina gashi idan baka nan bakada abinci km ko ansan kana kotu baza'a ajiye maka ba, sannan a kotun ma ba abincin zakaci ba..
"akalla duk byn wata uku sai mun ziyarci kotu gashi har na kai tsawon shekara daya cikin ta biyu mahaifiyata batasan inda nake ba.
ana gobe zamu kotu muke zantawa atsakani yan dakinmu da makotan dakinmu inda akwai wadan da gobe inda munje kotu bazasu dawo cikinmu ba, kasancewar wa'adinsu yacika.
nan duk wani me sako tsakaninmu yabasu zuwa ga danginsa , ciki kuwa har dani danabawa bukky sakona zuwa ga ore aminiyata.
daren ranar kam nayi kuka sosai ina ji ina ma nice zanbar gidan yarin, su kuwa tsabar rashin jin mgn irin tasu da taurin kai "cewa sukayi dama an barsu sun cigaba da zamansu "menene babu acikin gidan yari"duk fa abinda muke so shi mukeyi babu matsi babu takura "muna waya muna shaye shayenmu yadda ranmu keso "to meye km yayi saura?
"ni kam cewa nayi har duniya ta nade bazan taba zabar zama cikin gidan yari ba ,kai ko abinda zai sa na sake dawowa gidan yari bazan aikata ba.
dry suka kwashe min dashi suna nuna da hannunsu, daren ranar kasa runtsawa nayi inaji kmr nice zan bar gidan.
munje kotu wannan karon har da su ganiya wanda shari'ar mu tazo daidai datasu ,byn angama gabatar da shari'arsu aka shiga tamu wace babu wani ci gaba acikin shari'a tamu , sai bakinciki tare da bada kwanan wata da zuwa kotu bisa gaida .
me shari'a ta mike byn tagama watsa mana tsadaddun turancinta muka fito daga cikin kotu zuwa harabarta kotu inda dandazon mutane suke .
"wasu a zaune wasu a tsaye kowa kagani agurin sha'ani gabansa yake ,yayinda wasu kana kallonsu kasan cikin tashin hankali suke dan zakaga har kuka suke sbd masefar tashin hankali dake cikin kotu .
muna zaune inda aka saba barinmu a duk sanda mukazo kotu. zaman dana saka masa suna da jiran tsammani ,muna kallon yan'uwansu bukky suka karaso garesu suka rungumesu suna murnar an sakosu ,.
"alokacin babu abinda yaxo raina kmr ummana ita kadai nake so da kwadayin sanyawa acikin kwayar idanuna dan gbdy tashin hankali danake ciki yasa na tattara soyayyar abdulkabir na ajiyeta agefe nafi jin tausayin mahaifiyata , domin nasan tana can cikin tashin hankali rashina har na tsawon lokaci.
ba'a cike wata biyu ba da tafiyar su bukky ina zaune naji ganduroba na kirana na mike cike da mamaki, domin lokacin shine karo na farko dana ji an anabi sunana da sunan anzo nemana .
ahankali jikina a sanyaye nabi bayansa har zuwa cikin wani office.
ore nagani zaune tana ganina ta mike tsaye jikinta na kirrma ni km sai hawaye sharrrrrr ta karaso gareni ta rungumeni ajikinta tana kuka "a she da gaske ne su'ad kina prison?
"cikin kuka nace gaske ne ore gani kuwa agabanki acikinsa.
"ya ummun su'ad take? nayi mata tmbyr ina kokarin barin gangar jikinta domin son sanin halin da mahaifiya take.
"tana lfy ko yanzu kafin nazo sai dana biya gurinta km na sanar mata da gurinki zanzo har tayi adduar Allah yasa bake din bace a prison kmr yadda sako yazo mana.
wasu zafafan hawaye suka sake zubo min.
na runtse idanuna domin rasa abinda zan ce "garin yaya su'ad ?
"garin yaya kika tsincin kanki cikin halin robboling?
"kaddara ore "kaddara ce silar meidani hk km kin gaya min gsky nakiji .
"a she shafuffukan rayuwata suna tattare da kaddarori bansani ba.
"danasan hk zan tsinci rayuwata dana dauki shawarki kingan ni nan cikin prison da sunan robbiling akan soyayyar abdulkabir.
minti 15 akabamu mu gana daita gasu har sun cika batare da hirarmu tayi tsawo ba domin har ganduroba yakaraso bisa kanmu ya tsaya yana bani umarnin komawa ciki ,itama yana bata umarnin wucewa.
ina kallonta taciro kudi akalla zasu kai dubu biyar ta miko min na girgiza mata kai "ki bar kudin ore basu da wani amfani gareni hannuna ta janyo ta tura kudin ciki ta rufe ki amsa zasu miki amfani, ta juya tana kuka kafin nayi hanzari har tabar gurin nan nima na fashe da wani gigitaccen kuka, ganduroba ya matso inda nake tsaye tare da miko min tafin hanunsa ala'mun na bashi kudin, take babu musu na mika masa nasoma daga kafufuna zuwa cikin dakunanmu.
tunda ore ta tabbarwa ummana Hali danake ciki ta tashi hankalinta, tayi kuka sosai har kukan ya janyo mata ciwo me tsananin a yadda ore tasanar min a wani zuwa datayi gurina .
zanga zanga ummana tashiga neman yadda zata fitar dani daga prinson, duk kudaden gidan hayar gadona wanda mahaifina ya barmin babu wanda bata amsa ba domin kubutar dani amman babu biyan bukata lawyer's sai dai su amshe mata kudi su dinga mata yawo da hankali tare da saka mata rana, ahaka a wani zuwa da ore tayi gurina take gayamin yadda abubuwa ke tafiya.
"nace tagaya mata tabar hasarar kudinta ta'ajiye watakila gaba suyi mana amfani ta min addua kawai domin shi nafi bukata daga gareta ahalin danake ciki.
"na kara dace mata ta duba jakar school dina akwai wani diary ciki duk randa zata sake zuwa tazo min dashi duk .
sati daya bata cika ba ta sake kawomin ziyara tazo min da littafin sirrin abdulkabir, cikin na duba naga cikakken address dinsa nataba nace ta binciko min komai akansa da halin dayake ciki .
kullun da tunanin mutun biyu nake kwana nake tashi arayuwta mahaifiyata da abdulkabir burin raina yayinda kullun kwanan duniya zazzafar kaunarsa ke sake wanzuwa acikin zuciyata.
duk sanda ore takawo min ziyara sai na tmbyeta lafiyar mutun 2 mahaifiytata da lafiyar abdulkabir dina tace min duk suna lafiya . hkn ne ke dan kwantar min da hnkli.
lokacina dana cike shekara biyu cif na gahurta acikin prison har nazama shugabansu ganinya gurinn shaye shaye da harakar dabanci babu wanda ke kawo min rainin wayo ,wani irin karfi nake ji ajikina kmr shara'A bana jin tsoro kowa duk girmanka sai natakaka, wanda lokacin har gasar fada muke yi atsakaninmu km nice nake lashewa, ni kaina idan ina yin wasu abubuwan mamaki kaina nakeyi nasha sigari na sha wiwi wanda duk acikin prison muke samu .
"wani lokacin ma ganiya kan bani shawarar me zai hana idan mun fito daga prison nayi join dinsu cikin harakar fashi.
sai dai na kalleta kawai nayi dry ,rayuwa cikin prison agurina babu dadi sabanin gurin su ganiya da gang dinta domin su sun meida gidan tmkr gidansu sbd yawon kawosu cikinsa da ake.
dan wannan zuwan nasu ba shine zuwansu na farko ba sun shasha zaman yari.
muna samun abinci amman ba ishashe ba ,dan wanda ake bamu baya wani isarmu abinci ne gashi nan kmr loma acikin plet gashi always Bean's ne.
sannan ana yawon kawo mana ziyara lokaci zuwa lokacin.
akwai wani malami daya taba zuwa kawo mana ziyara ya gani ina shan tabar wiwi hankalinsa yayu mugu mugun tashi yashiga min wa'azi tare da jamin ayoyin alqurni me girma abinda yabashi mamaki bai wuce yadda duk ayar daya ja ba, zan amshe na karashe ..
ya dade tsaye yana kallona sannan yashiga tmbyata dalilin xuwana gidan yari?
" kai tsaye nace masa kazafin sata akamin batare da nasan yadda ake yinta ba...
nan shima yace zaiyi iyakacin bakin kokarinsa gurin ya fitar dani daga prison .
da zai tafi nace masa "ya taimaka idan zai sake dawowa yaxo mana da kayan abinci sbd dayawa daga cikinmi suna son yin axumi amman rashin wadatacen abinci ke hanasu yi.
nagaya masa hkn ne sbd lokacin watan axumin ya karato km duk lokacin azumi ina ganin yadda suke wahala daga karshe ajiye azumin suke .
ya tabbar min da zai yi bakin kokarinsa da yarda allah .
" zance taimakon abinci kam ya tabbata domin tirala guda akayi na kayan abinci iri iri , ba prison din danake ba hatta na gefenmu sun cin albarkacina .
zance taimaka min da malamin yace zaiyi ne ya sha ruwa domin shi kansa babu irin shige da ficen da baiyi ba dan ganin na fito amman abu ya gagara.
dan hk na dauka shima rashin fitowar wata kaddarar sakamako ce gareni na sabawa umarnin mahalicina danayi..
akwana a tashi babu wuya har ka'idan da kotu tabani tacika na fito tare da su ganiya muna munar wanda ni duk nafisu murna.
akan hanyarmu daga kiriri zuwa oshodi muke bawa juna addrshin gidanjenmu sannan na tabbatar musu matsawar basu bar harkar fashi da makamin ba, kar suyi kuskuren tunkarar inda nake suma mance munsan juna .
ganiya ta tabbatar da sun daina bazasu sake aikata hkn ba , a daidai under bridge din oshodi muka rabu da junanmu nashiga motar me xuwa ikeja su km suka shiga motar me xuwa munshi ol'osha...
ina fitowa daga prison nasoma kokarin haduwa da abdulkabir dina kwasma ore take sanar min ai aure zaiyi abinda yasa bata sanar min ba tun ina prison ba bata son nashiga damuwa akan wanda nake ciki.
to tunda daga wannan ranar da ore tasanar min nasoma nemo hanyar da zanbi ganin ni kadai bazan iya ba, yasa na nemi taimakon ganiya nace ina son tabani goyon baya akwai aikin da zasu tayani .
dukkaninsu daga ita har ore babu wanda nagayawa abinda nayiwa AK ta wajen nemomasa lfyr jikinsa sbd sharadin alhj tapa daya gindaya min.
aiko ganiya ta tattaro min duk wasu gang din yan'iska dake munshi olosha muka shiga aiki neman yadda zan rabashi da zeey tare da karuwarsa onye.....
gama bada labarinta ke da wuya su'ad ta mike tsaye domin isa inda ummanta ke zaune tmkr an dasata agurin gbdy ta dawo mutun mutumi agurin azaune tana kuka tana al'ajabin abinda su'ad ta aikatawa rayuwarta ,aiko tafiya daya biyu tayi sai luuuuuu ta zube kasa tasoma rawar jiki irina masu cutar farfadiya tare da shure shure kunfa na fita daga cikin bakinta.
umma ta zabura ta mike tayi kanta zata kai hannunta ammi tayi saurin dakatar daita, da sauran mutane dake kokarin kai hannusu jikin su'ad sannan cikin rawar jiki ta nufi dakinta shima dady ya nufi cikin dakinsa.
maganin da suke yiwa abdulkabir amfani dashi suka dauka cikin sauri suka dawo parlour'n suka shiga rige rigen yi mata amfani da maganin lokacin AK ji yayi kmr kasa ya tsage ya nutse ciki ya huta da kunya tare da ganin wannan tashin hankali dake faruwa agabansa, wani irin ya dinga ajikinsa lokacin dayake kallon su'ad cikin yanayin cutar farfadiya.
" yanzu hk yake kasancewa a duk sanda wannan dan iskan ciwon ya tasamarsa? yayiwa kanshi tmbyr yana takaicin ciwon.
sauran mutane da suke gurin tsaye suke kan su'ad
19, September 2025
Aisha Auwal
Wow