Showing 105001 words to 108000 words out of 420383 words

Chapter 36 - SAI KA AURENI DOLE BY AYSHA A BAGUDU.txt

Allah. sannan ki hango irin damuwar da nida ke zamu shiga agaba a sanadiyar tsiniwarki gareni, domin duk halin da zanshiga zai fi miki zafi da ciwo akan kowa.
amman karki damu zan bar miki gidan nan duk da kasancewarsa na mahaifina ne ,wlh zan bar miki gidan nan km a yanxu bazan jure bacin rai da damuwa irin hk .
da me zanji damuwar danake ciki ko km da kalaman tsinuwarki gareni, domin dana zauna ki dinga tsinemin na kara lalacewa gara nabar miki gidan na huta tana karasa fadar hk tajanyo akwatin kayanta ta bude wardrobe tasoma zuba kayanta tana gama xubawa ta zuge akwatin ta juyo tana kallon ummanta.
ina matukar kaunarki ummana ,kece jigon samar dani a duniya duk da bansa kotawace hanyar kika samar dani ba.
amman ina jinki cikin zuciyata, banida kowa bani da komai sai ke kadai.
ina rokon Allah ya sanyaya zuciyarki yabaki ikon yi min adduar shiriya da kariya gareni, ba hk na kasance abaya ba kece kika kawoni duniya kika tarbiyarta dani sannan daga baya kika tsince rayuwata hk, ni kaina banason wannan rayuwar danakeyi amman babu yadda zanyi dole na karbeta itace kaddarata .
tana gama fadar hk tasoma jan akwatinta har ta bude kofar ta fita allah sarki ai umma nagani fitar su'ad ta zube kasa tana kuka tmkr karamar yarinya uwa da "dal kenan sai Allah a zabure ta mike tana kuka da kiran sunanta su'ad ..su'ad dina dan Allah ki dawo karki tafi ki barni bazan iya rayuwa babu ke ba.
ke kadai gareni duk duniya banida kowa sai ke, a parlour ta risketa tana kokarin bude kofar ta rungumeta ajikinta karki tafi bazan iya rayuwa babu ke ba na hakura na dauki kaddara....dole ce tasani yanke wannan hukuncin kamota tayi ta zaunar daita umma kuka su'ad kuka babu me rarrashin wani.
ba dan dole ba mezai sa tayi tunanin yanke alaka da tausayawar dake tsakanin uwa da yarta ahankali cikin matsanancin damuwa ta daga hannuwanta sama cikin muryar kuka da rauni ta fara addua ya Allah ka shirya min yarinyata .Allah ka kawo mata natsuwar zuciya da kwanciyar hankali.
Allah ka canza mata rayuwa fiyye da wace tayi abaya .Allah kazama gatanta .
takarasa fadar hk ta janyo hannu yarinyata tana cigaba da kuka. ummana ki daina kuka dan girman allah zan canza ..ni dai ki cigaba da min addua hk suka kasance ranar cikin kunci da matsanancin damuwa, daga karshe umma ta janyo tablet din abinci tasoma bawa su'ad abinci abaki tana ci sosai ta dinga cin abincin kasancewar cikinta ya bude dan tabar wiwin datasha if not abinci bazai samu damar shiga cikinta ba. byn tagama ci umma ta dauko mata ruwa me sanyi ta mika mata.
ta karba ta sha har lokacin idanun umma bai bar zubar da hawaye ba, ahankali ta juya takoma daki ta kwanta a inda tasaba kwanciya tunanin rayuwarta ta baya tashigayi.
tunawa ta dingayi da abubuwan da suka faru idan ita batayi sa'ar uwa tagari ba wacce tayi sanadiyar ruguza rayuwarta, yarinyarta fa?
duk wata kulawa da tausayawa da tarbiya babu wace bata tsaya tsayin daka tabawa su'ad ba .
akarshe ga yadda takasance.. anya ba tarin zununbanta dana mahaifinta ne ya afka kan yarinyar dabata ji ba bata gani ba.
tashiga juya kai tana kuka tabbas ta tafka babban kuskuren arayuwarta wanda bazata taba gogewa kanta shi ba..

byn kwana wasu kwana su'ad na gida tana jinyar kanta dan idanunta sun dan dan sabe sai dai abinda baza'arasa ba. samun saukinta keda wuya ta fito neman ak amman gabadaya ta neshi tarasa ,duk inda tasan zata gashi ko taji duriyarsa taje babu shi babu alamunsa. dan hk ta yanke shawarar zuwa gidansu.
ta shirya cikin doguwar rigar material har kasa, wace ta lafe mata ajiki,ta fidda ainihin Shep din jikinta da kirjinta dan rigar ta kamata sosai daga sama daga kasa km flay ce ta yane kanta da dan karamin mayafi baki .kafafunta sanye cikin takalmi flat suma baki ,sosai tayi kyau kasancewarta fara sol doguwa , ta fashe ilahirin jikinta da turaren me sanyin kamshi da taba zuciya.
kai tsaye gidansu ak ta nufa.
kusan minti goma tana tsaye abakin karamin get din gidansu tana tunanin ta yadda zatayi nocking.
sai ta kai hannuta da niyyar nocking sai ta dauke.
, da kyar dai tasamu ta sanyawa jikinta jarumta tayi nocking kmr batasonyi...
me gadin gidan ne ya mike tsaye tare da budewa yana dubanta.
, ina wuni baba.
lfy lau yarinya ,ya amsa mata cikin sakin fuska, dan Allah baba ko abdulkabir na gida?
eh yana gida. idan da hali dan Allah baba
inason nashigo akwai abinda yakawoni gurinsa .
yasan da zuwan naki ne?
tayi Shiru tana tunanin abinda zatace ,har sai da baba ya sake maimaita tmbyrsa ,sannan tace eh yasan da zuwana .
baba me gadi yakarasa bude mata get tare da bata hanya shigowa.
kalle Kallen farfajiyar gidan take.
ahankali tasoma tunani ta inda zata soma ganinsa batasan inda zata dosa ba .
ganin yadda take zare idanuwa yasa baba me gadi yace ta biyo shi har bakin kofar part dinsa ya kaita yana nuna mata kofar shiga .
sannan ya juya zuwa bakin aikinsa.
ahankali ta kai hannu jikin kofar zatayi nocking sai km wani tunani yazo mata .
ta murda handle din kofar taji kofar ta bude sanyayyiyar ajiyar zuciya ta sauke, sannan
tasanya kanta ciki hadadden parlour'n wanda yakawatu da kayan more rayuwar duniya, wani irin kamashi airfreshiner ne yasoma kaiwa hancinta ziyara ,wanda kadan ya rage naumfashin bai tsaya ba.
, ga sanyi ac dake ratsa gbdy ilahirin jikinta .
komai na parlour me kyau ne kmr yadda mammalakin keda tsananin kyau. kallon parlour take kirjinta na dukan uku uku zuciyarta na harbawa da sauri sauri.
ahankali tasamu guri ta zauna akan kujera dake parlour tana fargaban haduwarta dashi.

kwance yake ruf da ciki acikin akan makeken bed dinsa , daga shi sai gajeren wando short niker iya cinya da whit singlet yana opereting system .
hk kawai ya tsinci kanshi da jin mummunar faduwar gaba...... sakamakon wani sauyi dayaji ajikinsa da hancinsa .
gbdy ji yayi cent din gidan ya sauya masa. wani irin kamshi yake ji wanda yakasa tantancewa. dan hk
, ahankali ya ture system din dake gabansa gefe tare da saukowa daga kan bed .yana mike hade da salati ala'mun gajiya.
ahankali ya bude kofar bedroom dinsa ..kmr a mafarki yaganta zaune ta daura kafarta daya kan daya tana jijigawa ahankali ahankali idanunta akan wani tangamemen hotonsa dake manne da bango parlour'n .
jikinta ne yabata duk inda akayi yana gurin ,dan hk ahankali tasoma jiyo da fuskarta har ta sauke fararen idanunta akan kyakkyawan fuskarsa, me dauke da annurin kyau.
, atare gabansu ya fadi suna kallon juna kafin daga bisani ta mike tsaye a firgice tana cigaba da kallonsa, tundaga sama har kasa.
kyakkwa ne ajin farko na bugawa ajarida, me tattare da siffar karfi ,duk inda ka kalla ajinsa kwance yake luf luf da kwantaccen gashi .
wanda ke sake bayyanar da tsansar kyawun surar jikin da Allah yayi masa.
hatta zara zaran yatsun kafarsa dana hannuwansa kwance suke luf da gashi .
shi din irin mazajan nan ne abin bukata da muradin kowace mace .
sannan samun irinsu ke da matukar wahala,gbdy shock ya hanasa motsawa daga inda yake tsaye, jiyake tmkr an shafe masa ganinsa ne abubuwanta sun daina daure masa kai, sun koma bashi tsoro yarinya tmkr aljana duk inda yayi tana like, ganin irin kallon kurrila datake masa ne yasanyashi saurin kallon jikinsa, sannan ya meida mayattun idanunsa akanta yana watsa mata wani matsiyacin kallo me hade da harara... muryarsa a matukar harzuke yace

me yakawoki km... ?meyasa jakanci da rashin zuciya yayi miki yawa ?

yama akayi kika shigo gidan nan .. ?

kayi hkr na kasa jure rashin ganinka ne akalla yau kwana biyu kenan bansaka cikin idanuna ba, duk hanyar dana san zanga ka kulleta abdulkabir ..
yaya kake son nayi da rayuwata ..?
Kayarda Dani wallahi ni masoyiyarkace .
wace yarda zanyi dake, yarda dake ko abin kunya Allah yakiyayeni da yarda da mace irinki ,yan kwanaki ne yarage a daura min aure da natsatsiya mata kamilalliya, wace tasan kima daraja da mutuncin kanta ba irinki ba taxi ......
ya janyo hannuta afusace yayi hanyar waje daita ,tare da ingizata harabar gidan ya juya da sauri yashige ciki part dinsa ya danno kofar da karfin grammmmmm kake ji yasanya key ,tare da jinginar da bayansa da jikin kofar yana sauke numfashi sama sama.
da mugun gudu su'ad takaraso jikin kofar tana bugawa da karfi hade ihun kiran sunansa abdulkabir..... abdulkabir...... Please open the door for me don't do this to me ... Nocking take da iyakacin karfinta tana ihun kiran sunansa Amman yayi mata banza.
wani irin juyi tayi tare da Tabaro jikin kofar tana surutai wallah
Banza yarda ba kajawota mata maseefa da bala'i me tsanani agurina .
sai na azabtar da ma kowacece zatayi gangancin aurenka da azaba mafi tsanani.
wlh baka isa ka aure wata kabarni ba matsawar ina numfashi.



mmn sudais ce

💗💗💗💗💗💗
SAI KA AURENI DOLE
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗



~NA~



*AYSHA A BAGUDO*



~DEDICATED TO~
HAUWA A USMAN
JIDDARH


*qala rasulillahi sallallahu alaihi wa sallam athur shaturul iman*

*best family forever and ever i really appreciate all your washi and the love you showed on me ,i truly feel happy to have such amazing family in my life Love you so much*💋

*hajarutul (mee'ad )da halimatu sadiya (e'man) Allah yaraya min ku cikin tafarkin sunnah ,Allah yasanyawa rayuwarku albarka*

page 28

a kalla ya kusan minti talatin jingine da jikin kofar ,dafe da saitin zuciyarsa, yana fidda numfashi sama sama.
runtse mayatattun idanunsa ya sake yi sosai tare da kiran sunan Allah, ya salam .. ..
karo na kusan goma kenan daya ja tsaki cike da matsanancin takaicinta .
bai san me ya kawota gidansu ba...
yanzu idan dady'nsa ya fito ya ganta agurin yace masa me ,akan yarinyar da tuni yace masa yakawo masa ita amman yaki ?
ahankali ya bude mayatattun idanunsa wayanda suka gama rikidewa sukayi jawur dasu sbd abinda yake jin yana masa yawo cikin rayuwarsa a game da lamarin yarinyar .
a fill yace, wannan wace irin maseefa da jaraba ke shirin kusantoni da rayuwata ?
ita bata barni na huta nayi rayuwarta yadda nasaba ba.
sannan ita bata bar kanta ta huta ba..
cikin wannan tunanin da yake wasu zafafan hawaye masu zafi da ciwo yaji suna sauko masa akan kyakkyawa fuskarsa..
cikin sauri yasanya hannusa ya sharesu tare da jan numfashi da kyar ya fitar ,lokacin ne yaji tsanyi ni'ima da wadataccen iska yana kursuwa ta kofofin window's din part dinsa da karfi .
cikin hanzari yasoma takowa ya isa ga window's yasoma kokarin kullewa kasancewar yadda iskan yake saukowa da karfi.
dan har feshin iskan yasoma shigowa.
tsaye yayi cike da sabon mamaki yana kallonta . tsaye take agurin tana kallon sararin samaniya yayinda ruwan sama oready yasoma saukowa da karfi ,yana sauka ajikinta.
,kusan minti goma ya dauka tsaye agurin yana kallon yadda ruwan sama ke sauka a sansar ajikinta batare da tayi yunkurin tsarewa ruwan ba.
,take kirjinsa yayi wani irin matsanacin bugu .. sosai ya zuba mata mayatattun idanunsa yana cigaba da dubanta tare da jin wani irin sauyi na daban agabadaya ilahirin sansar jikinsa.
takoina ajikinta jike yake sharkaf da ruwa tun daga samanta har zuwa kasanta tsiyaya take. wani irin sanyi ne Me tattare da tausayinta yasoma ratsa ilahiri jikinsa.
karo na farko kenan daya ji wani abu makamanci hk atare dashi a game daita.
,kmr ance ta juyo.. idanunsu suka
tsarke cikin juna.
a matukar firgice take kallonsa tare da narka da fuska ala'mun ya tausaya mata .
wani irin nagartaccen kwarjini taji ya sake yi mata me gauraye da tsagwaron sonshi.
yadda bai dauke idanunsa akanta ba.
hk itama bata fasa kallonsa ba, har sanda tasanya tafin hannuwanta duka bisa fuskarta tana goge ruwan dake kokarin rufe mata idanu ,domin hanata kallon cikin idanunsa.
,cike da mutuwar jiki ya saki labulen ya zuge glass din window, ya koma jikin kofar ya jingina yana jin yadda bugun zuciyarsa ke sake karuwa .
takun su'ad ta sake yi, ta dawo jikin kofar ta jingina bayanta tare da sake fashewa da wani irin kuka me cin rai da ban tausayi .. tana furta wayyohhly Allah Ni su'ad laifin me na aikata ma Allah da yasa nazo duniyar nan...?
ya Allahu laifin me nayi da rayuwata tadawo hk?
meye makusata da aibuna wanda yasa abdulkabir yakasa amsar soyayyata..?
Kowa yana sona a wannan duniyar, amman kai dana sha matsananciyar wahala akanka shekara da shekaru kana guduna.... babu wanda yake kina sai kai abdulkabir.. bakasona .......
bakason na rabeka ko rabar duk inda Kake ballantana na rage radadin da nake jin a zuciyata.
pls ...pls ...abdulkabir karka min hk NI masoyiyarka ce kamar yadda na sha gaya maka.
,wayyohhly Allah ya Allah ka dauki rayuwata na huta da wanan bak'ar ukubar akan na ga aurenka da wata ..
Allah ka kasheni kafin zuwan lokacin aurenka, na gwamaci mutuwata da wannan rayuwar... ahankali tasoma yin kasa kasa da jikinta tana risgar kuka har ta tsugunna tare da daura fuskarta akan gwiwowinta tana cigaba da kuka me cin rai da taba zuciyar ma'aboci sauraro.
iskan ruwan na sake dukanta inda take tsugune .
zuciyar AK ce tayi wani irin bugawa da karfin gaske sakamakon jiyo sautin muryarta cikin kuka ,har tagama sambatunta yana jingine yana jinta ,
wani irin sanyi ne ya dinga ratsa gangar jikinta.
take tasoma rawar sanyi da karkarwa har hakoranta na kirma.
ruwa ne aka tsugashi ba wasa ba .
domin kuwa duk wanda ya kwana ya tashi a garin Lagos yasan yadda ake tsuga ruwa barin ma farkon damuna.
km duk tsawon wannan lokaci tana nan a tsugunne ajikin kofar part dinsa tana cigaba da kukanta ahankali wanda ya hadasawa kanta sarawa da karfi.
gashi AK kwata kwata bashi da niyyar bude mata kofar balle tasamu mafaka domin tsira da lfyrta ...
hkn yasa tasoma dago kyakkyawa fuskarta dake zubar da ruwan hawaye ..tun kafin takarasa kai ga dagowa gbdy take jin wani irin azababben kamshin turaren wanda yasaba tsaya mata arai ..
km take ji ajikinta kmr tasan shi .
,tana karasa dago fararen idanunta da suka sauya daga fari zuwa ja ta saukesu akan fuskar wani dattijo dake tsaye can nesa kadan daita, yana dubanta .
hannunta tasa ta dan murza idanunta domin sake tabbarwa kanta mutumin dake tsaye agabanta ba abdulkabir dinta bane kama ce kawai, da dan bancanci tsakaninsu, shi wannan fuskarsa ta dan manyata sabanin ta abdulkabir dinta dake cike da tsantsar annuri da zati tattare da nagartacce kyau da kurciya.
kusan Mintuna talatin ta dauka tana kallonsa , kafin daga karshe ta zabura ta mike tsaye a firgice tana zare idanuwa cike da matsanancin tsoro..
bangaren dady kuwa tsaye yake cike da sarkakiya da mamaki ganin mace a kofar part din ak.
duk yadda yasan dan nasa na mu'amula da mata baiyi tunani zai iya kawo mace har cikin gidan dayake zaune ba, wani irin kallo yake bin yarinyar dashi zuciyarsa na kitsima masa wacece ita da kallon sani dayakewa fuskarta? her face is familiar to him .
sosai ya tsura mata idanu ahankali yashiga tunani Inda yasan fuskar ,gabansa ne yashiga dukan uku tabbas duk inda fuskar take yasanta sani km farin sani sai dai,ta ina hkn zata kasance, fuskar wayanda yake gani a fuskar yarinyar dake tsaye agabansa yanzu bata da halaka da fuskar dayasani, kama ce kawai ba wata halaka ko dangantaka ce ba. ahankali yacigaba da kallonta, kafin daga bisani ya numfasa tare da cewa .
yarinya daga ina hk ko wani kike nema..?
tunda dady yasoma mgn su'ad ta sunkuyar da kanta kasa gabanta na faduwa sbd kwarjinin da dattijon yayi mata, bakinta da jikinta rawa suke gurin cewa uhm ..uhm ina wuni sunana su'ad daman nazo wajen abdulkabir ne.. nazo gurin abdulkabir dady ya maimaita mgnrta cike da mamaki, take km zuciyarsa tasoma bashi haske akanta.
duk da bata gaya masa bayanin komai akanta ba ya gane yarinyar dake da halaka da tilon dansa ce tausayin yarinyar ne ya rufe shi ,ya dinga wani iri acikin ransa.

wannan wani irin so ne hk takewa abdulkabir dinsa ..?

yanzu duk ruwan nan
akanta yakare kome.?

to yanzu ina shi abdulkabir din yake. daya barta anan ruwa yayi mata duka? ajere
yayiwa kansa tmbyr acikin zuciyarsa.
wani irin sanyi yaji yana ratsashi ta koina, ko babu komai wannan abun alfahari ne ace mace tana maka irin wannan tsaftacencen soyayya ta gsky .
wanda duk wani uba na gari zai so ace dansa yasamu mace irin wannan me tsananin sonshi .
ita kanta soyayyar mace wani jigo ne da taimako a bangaren auratayya,rayuwar aure. sannan tunda yake
a rayuwarsa bai taba ji ko gani irin wannan soyayyar ba .
cikin sanyi jiki su'ad tashiga ware bakin mayafinta domin suturta jikinta , tana kokarin barin gurin dan gane kowaye agabanta.
dady yayi hanzarin dakatar daita da hannunsa yana takawo ahankali zuwa bakin kofar part din ak tare da yin noucking .
"ak wanda ke tsaye jikin kofar yayi shiru kirjinsa na bugawa da karfi, yaki motsawa balle yayi yunkurin bude kofar yayinda zuciyarsa tashiga shawagi tare da harbawa, jin bugun kofar yayi yawa ne yasa zuciyarsa dugunzuma tare bude bakinsa cike datakaici yace dan ubanki tsayuwar uwar wa kike da bazaki bar gidan nan ba ..
ko gidan ubanki ne ?
wlh idan kika sake na fito na sameki agurin zan miki dukan mutuwa na balbalki na aikawa ubanki da kasusuwanki stupid girl kawai ...wace

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login