Showing 273001 words to 276000 words out of 420383 words

Chapter 92 - SAI KA AURENI DOLE BY AYSHA A BAGUDU.txt

tuttukin bakinciki "hk zamuyi da yarinyar nan? ya mike tsaye.

"ni zata jama aji?

Ya fadi hk yana sake kira layin yaji wayar a kashe.

bangarenta kuwa hirarsu suka cigaba dayi daga karshe sukayi kwanciyar su ,da kyar su'ad ta samu barci ya sace ta byn juye juyen data dingayi tana takure jikinta guri daya .

washegari da Zullumin haduwarta dashi ta tashi .

salon soyayyar AK da tsarin yanayin takurawarsa da nuna ikonsa yana matukar bata tsoro gaskiya.

Shi kuwa tunda ya tashi yake faman zarya apart din ammi, ammi na lura dashi tayi kamar bata san yanayi ba ko breakfast yaki zama yayi gashi sai faman kiransa ake daga office da ala'mun kiran is very important amman yaki tafiya.
Ransa yayi mugu mugun baci matuka, ya zauna tare da dafe goshinsa yayi shiru yana tunani ..

sai wajen 11 saura ta shigo parlour yana ganin ta ,ya sauke naunauyen ajiyar zuciya batare da yace mata komai ba sai tsura mata mayatattu idanunsa dayayi kawai yana kallonta duk ransa a matukar harzuke yake amman duk da hk yaji dadin ganinta .
sai dai idan ka kalli yanayin yadda ya nuna afuskarsa kaza dauka baiji dadin ganinta ba. ahankali ya mike tsaye ya bar parlour 'n.

" Ta gaida da ammi tana sunkuyar da kai dan bakaramin kunya taji ba lokacin da ak ya kafeta da mayun idanunsa yana kallonta kmr zai cinyeta, hk kawai ta tsinci kanta da kasa zama a parlour ta wuce kitchen ammi Ta bita ta ido tana 'yar dariya Wannan zafaffar soyayya ta abdul ai sai ya tashi gari.

can kmr minti goma Ya sake shigowa yana daure fuskarsa me nuna ala'mun yana fushi.

"ammi na wuce sai na dawo.....

ammi ta kalleshi a kaikace "breakfast din fa ko zaka aiko ne?

"no abarshi kawai na koshi yayi mgnr yana tafiya ,ammi tabi bynsa da kallo tana mamakin halinsa ,yacika zafin rai tsiya da son ikon mallaka ita duk bataga wani abun fushi anan ba .

Koda ta gama hada abinda take son ci tayi dakin eiman.

Da daddare taci kwaliyarta cikin dinkin riga da siket na atamfar super exclusive me zanen fulawa kalar ja da ruwan dorawa ,dinki yayi matukar amsar surar jikinta barin ma siket din wanda ya zauna das a kungunta ya fidda ainihi Hip's dinta, ta fashe ilahirin jikinta da daddaden kamshi turarenta, tazo parlour ta hakince tana zaman jira shigowarsa amma taji shiru gbby ta kasa samun sukuni dan hk ta mike ta fito waje ta nufi gurin motacin gidan duk suna jere a ma'ajinsu tafi kusan awa daya agurin tarasa gane da wace motar ya fita balle tasan ko yashigo gidan.
tacigaba da tsayuwa agurin amma shr bashi ba alamunsa .

Duk km sai ta shiga damuwa takasa tsukuni ta dawo daki dan kar ammi ta farga tana cikin damuwa ta kwanta lamo akan gado tana jin kmr taje part dinsu ta dubosa ko ya dawo gidan.

Washe gari tunda sanyi safiya yabar gidan, nan hankalinta ya sake kololuwar tashi ta kasa tsaye ta kasa zaune cikin hk ammi ta rutsata adaki ta soma dan janta da labari har ta dan saki jikinta.

abu fa kmr wasa ak ya lashi sati uku yana fitar sassafe km baya dawo gidan sai cikin dare ta sake shiga damuwa kmr wancen lokacin, wanda ita kanta ammi ta lura da hkn har ta kai ga tmbyrta
" Ni kuwa mamana kwanakin nan duk bana jin dadin yadda nake ganinki ko bakijin dadin
jikinki ne?

"babu komai fa ammi lfyta lau ta fada tana yar murmushi wanda ya bayyana wushiyarta amman kallo daya zaka mata kasan murshin iya baki ne bai kai zuciya ba.
"ni kuwa sai nake gane kamar kina tare da damuwa ko wani gurin na miki ciwo .

"wallahi ammi babu komai "idan ba haka bane to ki saki jikin kibkoma kamar farko .

" toh, tana sake fadada murmushinta.

ammi ta danyi shiru tana nazarinta , sannan ta murmushi irin nasu na manya kana tace "mamana na daukeki tamkar 'yar da na haifa acikina, in takaice miki ko ya'yan dana haifa bana jinsu kmr yadda nake jinki kasancewar su din suna da komai na rayuwar duniya basu rasa soyayyar uba..
"ke kuwa tun kina cikin ciki mahaifinki ya rasu ya barki, a kullun na tuna dan uwana da abubuwan da suka faru abaya na kan zubda hawaye ,ahalin yanzu ke kadai ke maye min gurbin uwa uba dan'uwa har ma da dangi gbdy. dan haka ina rokon ki saki jikin ki kada kibari damuwar matsalolin abdul ya taba min farincikinki da lfyrki, wanda shine kwanciyar hankalina kinji.

su'ad "Ta ce toh ammi nima ina sonki sosai a halin yanzu banajin cewa ni din maraniya km mara galihun, " ke kadai da kika rage min yar uwar mahaifina araye yafin komai yi min dadi a duniya ..
ammi ta rungumeta ajikinta.


" kinga wannan yanayin na abdul bakomai bane face tsagwaron bacin rai. duk sanda kika ga yana bata rai irin hk bakaramin tashin hankali yake ciki ba ,mijikin ne mamana yakamata ki fuskanci yanayinsa nasan kin masa wani laifi ,tunda naga ya dauke mana wuta, kada kiyi girman kai ki bashi hakuri kinji?

muryarta a raunane Ta ce" toh ammi zan bashi hakuri.
ammi tayi murmushi jin dadi
" Lallai ammi ta cika uwa ta gama gano cewar danta fushi yakeyi daita Duk da bata san dalilin Fushin ba.

zaman falo dai ya gagari su'ad yanzu saboda fargaba , ammi na zaune ta hango shigowarsa da sauri yashiga part din dake kallon nasu , ammi tayi saurin kwadawa su'ad kira ta fito da sauri saboda yanayin kiran.
Ta ce maza shiga part din can ki dauko mun kwalin ruwan nestly . tayi mamakin jin hk kasancewar bata taba aikenta part din ba amman ta
juya ahankali ta nufi inda ammi ta aiketa
Ta na shiga tasoma jiyo kamshin turarensa tafiya yake yana duba document din dake hannunsa wanda shine dalilin dawowarsa gidan a daidai wannan lokacin saura kadan su hade cikin junsu ,yayi saurin ja baya da sauri yana kaucewa hkn har zaiyi magana sai kuma ya fasa kawai ya raba ta gefenta ya wuce.

" wayyohlly allah meye hk ni su'adullahi ta fadi hk tana dafe kirjinta tare da
bin bynsa da wani firgitaccen kallo kar da fushi yakeyi dani ?

to Me na masa ? kawai taji jikinta yayi wani irin sanyi banda bugawa babu abinda kirjinta da zuciyarta keyi ,gbdy ta kasa aiwatarwa da abinda akace mata , kwata kwata ma ta manta abinda ammi ta aikota.

ammi na nan zaune ta hangoshi ya fito cikin sauri tasan bai kula su'ad ba.
Gaban ta yayi wani irin mahaukacin bugu ko ya hakura da soyayyar su'ad din ne .? tai wa kanta tmyr tana dafe goshinta.

jiki a matukar sanyaye su'ad ta shigo parlour 'n ranta a dagule kmr zatayi kuka, ta ajiye mata ruwan ta shige ciki daki, Ikon Allah ammi ta furta tana kama baki.. kiransa ammi tayi tana tmbyrsa abinda ke faruwa yace babu komai "to ka daina son su'ad din ne ka kawo min takardar sakinta?
"a fusace yace ina son matata... "to meida wukar mara kunya kawai . ta katse kiran tana jin dadi.

gbdy su'ad ta rasa me ke mata dadi, duniya ta tsaya mata cak ta daina jin dadin iskar dake shawagi acikin sararin duniyar, banda zumbure zumburen baki babu abinda take kusan haushin kowa takeji .

ammi tashigo dakin ta shige bathroom tana dariyarsu sbd duk suna son junansu .
Har bayan magriba su'ad taki fitowa .

ganin hk yasa ammi yin kusa daita ta yadda zata sani damuwarta. ta isketa zaune adaki ta zabga uban tagumi tana kallon ceiling dakin
ammi takaraso gareta ta zauna tana tmbyrta lafiyarta kuwa "cikina ne bana jin dadinsa tabawa ammi amsa tana kokarin kawar da damuwarta , ammi ta kunshe dariyarta, kai kai ciwon cikin km yau ?

su'ad ta girgiza mata kai kawai ammi batayi wani yunkurin bata magani ba dan tasan babu wani ciwon ciki dake damunta ,kar aje ma ko tana da shigar ciki ba'a sani ba, dan hk tace Allah ya sauwake ta dauki hijab dinta tasanya ta wuce part din dady .

ammi na fita daga dakin ta kwanta flat akan gado tana juyi ahankali daga farkon gado har karshensa kewar mijinta ke damunta batason ganinsa cikin damuwa most especial ace itace sila.

yadda take cikin damuwa da tashin hankali ,hk shima AK dan kusan har ya zartata shiga damuwa dan har gara ita tana iya runtsawa da danne damuwarta akansa, shi kuwa yadda yake ganin rana hk yake ganin dare.

ganin idan bai yi wani abu akan lamarin ba, shi zai kwana cikin matsala ,duk inda ka'aje aka dawo shi za'abari cikin taskon rayuwa yasa ya xubda makaman yakinsa ,ya rigada yasan tayi wining dinsa takoina bakaramin sonta yake ba.
soyayyarta tayi masa muguwar kamu ta yadda bazai iya jure yin dagon fushi daita ba. dan hk yayi tunani ya tura mata da sakon ban hkr duk da itace tai masa laifi..

jikinsa a matukar sanyaye ya lalubo wayarsa dake gefen bed side ya tsurawa wayar idanu yana kallon screen din wayar, yana tunani irin sakon da zai tura ma ahankali cike matsamancin shaukinta kwalkwaluwarsa tasoma hasko masa abinda zai rubuta mata

_slm my hrt beat love is always having to say I'm sorry it seems i did not do anything to you still i can apology its love_

tana kwance taji shigowar message ta dauki wayarta tana dubawa sunan wanda tagani ne yasa ta mike ta tashi zumbur jikinta har rawa yake.

ahankali takarance text din a tsanake tana sake maimaita kenan kasoma fahimtar lallai sai dani zaka yi rayuwa ,duk nice me laifi amman dole zan sakaka jin kaine da alhakin laifin, daga karshe kayi bleming kanka da kanka.


can Wani sabon text yasake shigowa.

_am really Sorry what i did was foolish _

ta koma ta jingine bayanta tare da yiwa bynta makari da pillow tana sake bi wayar da kallo tana murmushi jin dadi ..

aranta tace naka wasa ne Mr man, ai sai naga karshen girman kai da nuna kai wani ne, kana son mutun km bazaka kwantar da kai ba komai cikin iko dagadara zakayi .

yafi mintuna talatin zaune rike da wayar amma batayi kokarin meida masa reply ba ya kara tura mata

_you hurt me but i didn't take it anything ur angry that breaks my Hrt but my hrt will never stop to love you, I know whatever happened, Should nt happened the way it did, But, am really sorry My intention was not this from the start, So please forgive me_

Tsalle ta buga tana wani irin ihu ita kadai a daki har da rawa wayyohlly allah gayen nan fa yazo hannu sosai .


ta koma ta kwanta tana kamkame jikinta guri tana jin wani irin yanayi a gbdy ilahiri gangar jikinta tana jujjuya wayar a hannuta ban da shaukinsa babu abinda ke dawainiya daita a yadda take jinsa dazasu hadu yanzu zata iya mallaka masa kanta.. .

yayi shiru yana kallon wayar wannan shine Karo na farko arayuwarsa daya turawa wata mace sako ta wayarsa da zumar ban hakuri alhalin shi akawa laifin ,kai jama'a wannan maseefae da me tayi kama nifa bana son dogon fushi....

kmr yayi bacci ya manta daita shima amman ya kasa aiwatar da hkn yacigaba da kallon wayar yana jin yadda kirjinsa ke tafarfasa yana bugawa hade da tsalle yana kokuwa da numfashinsa dayayi saura ajikinsa "ka manta daita kawai tunda so take taga karshenka ga mata nan a duniya birjik sai zaba ka dirje take yayi saurin dafe daidai saitin zuciyarsa duniya akwai macen da zataba samun matsayi da shiga raina tare da tsaya min arai kmr ta babu yabawa kansa amsa
ya kara rubuta wani sakon ya tura mata

_Please forgive me for what I did, My intention was pure I admit seems you can hurt me but , I did not want to hurt you a bit, I am really sorry for reaction_

ta sake tashi zaune tana sake karanta sakon tare da kamkame wayar akirjinta tana lumshe fararen idanunta kafin ta ankare
Wani sakon ya sake shigowa har kyarma jikinta ke yi.


_su'adullah Things are not the same without your company, I am missing you a lot, and I told you sorry, Please forgive me and forget This won't ever happen again_

Ai sai tayi mutuwar zaune, motsin kirki ta kasayi duk illahirin jikinta ya mutu murus banda kasala da son ganinsa babu abinda take awannan lokacin data kasance .

jin shiru bata meida masa da amsar sakoninsa ba yayi tagumi sai ga kwalla sun soma zubo masa, jiki a sanyaye ya kashe wayar gbdy tare da dafe daidai saitin zuciyarsa dayake jin yana harbawa da karfi karfi .

Lokacin daya tura mata da sakonsa na karshe hankalinta yayi mugun tashi gbdy ta birkice adaki banda kwadayin son jin muryarsa da ganinsa babu abinda take a halin datake ciki batare da bata lokaci ba tasoma nemi layinsa amman taji a kashe
ta dora hannuwanta duka saman kanta tana jin kmr ta kurma ihu neman dauki ....ta zabura ta doro daga kan gadon kamar wata mahaukaciya ta fito, tana zuwa parlour agogo na bugawa karfe sha biyun dare, ta koma ta jingine bayanta da bango falon tana me runtse fararen idanunta cikin wani irin radadin son ganinsa .
Dukkansu babu Wanda ya samu damar runtsawa kusan kwanan zaune sukayi

tunda ta idar da sallah asuba take zaune kan salayarta cike da matsanancin rudani da son ganinsa koda kuwa bazasucewa juna komai ba.
shi kuwa tun biyar ya gama shirinsa ya tafi masjid, ko da ya dawo sallar asubah bai shiga part dinsa ba ya zarce part din ammi ya zauna bisa daya daga cikin kujerun falon .

haka kawai ta tsinci kanta da son fitowa parlour a daidai wannan lokacin
ta hangoshi zaune, Sam baiyi tsammanin ganinta ba yasan zata iya kaiwa 10 zuwa 11 kafin ta fito ,tsayawa tayi kal tana kare masa kallo, kansa a duke ,sanye da jallabiya brown color hannunsa rike da casbaha yana lazimi ...

jin alamun tsayuwar mutum akansa yasa ya dago da dan sauri , Ta rike kugu da hannuta daya idanunta akansa ta tsura masa fararen idanunta tana kallonsa ,
shima mayattun idanunsa ya tsura mata da suke daf da kawo ruwa hawaye muryasa a kasalance yasoma motsa labbansa " me na miki hrt beat da kike kokarin kasheni?
Saura kadan dariya ta kufce mata sbd yayi mgnr kmr bashi bane wannan me dakakkiyar zuciyar, amma ta sha mur sosai tana rausayar da idanunta cikin nasa batare da tace masa komai ba.

"kece kika fara min laifi ban duba hkn ba na kaskantar da kaina nabaki hakuri amman narasa dalilinki na son nuna min iyakata...

ta dan dukar da akanta kasa dan gaf take da kwashewa da dry .

yayi shiru yana kokarin maida damuwarsa dan baya so hawayen dake makale da idanunsa samun nasarar zubowa yacigaba " jiya na miki text zakice baki gani bane ko km so kike sai damuwarki ta min illar da zan bar miki duniyar ..?

ta tabe bakinta tana wasa da yatsun hannuwanta, sannan tace" ni ban ga wani text ba.

"Me ka ce a text din? tayi masa tmbyr tana tsura masa fararen idanunta kirjinta na dokawa .

ya ciro wayarsa a matukar hasale yashiga bude page Duk gashi duba gashi ki duba kuma duka yaje na tabbatar yana faman scrolling din nuna mata .

ta kyalkale da dariya tana binshi da wani irin kallo, nan da nan ya tsargu kunya duk ta baibayesa, ya wasa mata wata uwar harara wanda yasa taji kayan cikinta yamutsewa ransa a bace "wai ke wani irin kafurar zuciya ce dake dabaya yafiya?

"wallahi wallahi dana san yadda zanyi na cire soyayyarki da tuni nayi tun kafin mukawo wanann tsage din..
ya mike tsaye yana nufo inda take tsaye yana cigaba da dubanta.

"zaka iya cire wannan is normal thing ne zuciyata km kmr ta sauran bil'adam ce "kai ba'a ce maka wata irin zuciya gareka ba sai kaine zaka cewa mutun hk, koda yake kai fa me son kanka ne dayawa ne ,"wato kai har ka manta sanda nake binka guri guri ina hauka kasoni ko.... takarasa mgnr tana jan tsaki ta juya zata wuce yasanya hannunwasa duka ya janyo ta ta fado fadadden kirjinsa.


"Lallai ana daf da mutuwa acikin gidan nan matsawar bazaki fuskanci lamarina ba ,na tuba bisa kuskurena na baya, ki gaya min abinda kike son nayi miki ki dawo da kaunata kmr da ina sonki su'ad bazan iya rayuwa babu ke ba plz plz ki taimaki zuciyar abdulkabir kar mahaifiyarsa tarasashi.
Ta fara kokarin zamewa daga cikin jikinsa "kai meyasa lokacin danake binki ina rokonka ka taimaki tawa rayuwar kar tawa mahaifiyar tarasani kaki?
sai ma wulakacin iri iri daka dinga shuka min dan hk kabi ahankali dan zuciyar su'ad ta kekashe ahalin yanzu ta daina sonka ...

yashiga yawo da hannunsa

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login