Showing 387001 words to 390000 words out of 420383 words
Chapter 130 - SAI KA AURENI DOLE BY AYSHA A BAGUDU.txt
bai wuce wannan bawar Allah dake tsaye a gabanki ba.
soyayyarsu ta wuce na tsaya misalta miki, nan Ammi tashiga bawa shemah labarin Salema tundaga farko haduwarsu da Taufeeq har karshe da haihuwar d'iya macen datayi masa da yadda d'an cikinta ya aureta abu d'aya ne bata sanar mata ba shine batan su'ad shima dan kar kara masa dumuwa ne.
wani irin kuka Shemah ta fashe dashi me tsuma zuciya "lallai ta cancanta yasota fiyye da komai a arayuwarsa "amman dan Allah ni dai sumin alfarmar cigaba da rayuwa dasu, na kasance a cikin inuwarsu, bazan shiga rayuwarsu ba burina nakasance tare da Taufeek araye, saboda bani da kowa a yanzu daya ragemin sai shi....... kuka take sosai har tabawa Salema tausayi ta isa gareta ta rungumeta suka rungume juna suna kuka.
"ki bar kuka shemah zaki rayu da Taufeeq oredy ma taufeek naki ne" daman ni tuni na cire rai da rayuwa dashi ,zuciyata ta dade da hak'ura dashi kucigaba da rayuwarku kawaki kamar yadda kukayi a can baya nabar miki shi muddin rai.... shema ta rungumeta sosai "nagode nagode har bansa da wace kalma zan gode miki ba amman ki aureshi mu zauna tare..
shi kuwa Taufeek jin abinda Salima ta fad'a yasa komai ya tsaya masa tunani kala kala zuwar masa yake acikin zuciya har yaji gefen kansa yayi mugun sarawa "me salima take nufi da kalmar tabarwa shemah shi? abinda ma bazai ta'ba yiwuwa ba kenan yana raye tana raye yayi rayuwa dawata ba ita ba yayi mgnr cikin ranshi.
daga can wani b'angare na zuciyarsa ke tambayarsa " anya ma kuwa zaka iya cigaba da rayuwa da shemah?
"idan nace zan yacigaba da rayuwa da ita bazai iya yin adalci atsakaninta da Salima ba,domin kuwa Salimarsa dabance da sauran mata, bazai tab'a iya raba soyayyarta da wata ba ballantana a yanzu daya ji furuncinta me gauraye da tsagwaron kishi daga bakin Salima "wai ta barma Shema shi, kallo d'aya yayi mata yagane maganar ba daga zuciyar ta takeba iya baki ne kawai .
tsawon lokacin ya d'auka tsaye yana kallonsu har sanda Doctor Rak yak'araso garesa ya dafa kafad'arsa yasoma masa magana cikin rad'a "ka zauna kasan baka gama wastsakewa ba tukun "kabi komai ahankali ta hakan ne kawai zamu samu sauk'in alamarin..
"Rak... Taufeeq yakira sunansa ahankali kamar yadda yasaba a tun farko wanda shine mutumin daya rad'a masa sunan tun a ganinyar kurciya.
"kasa a sallameni ina buk'atar barin hospital d'in nan ayanzu gida nake buk'ata domin ina bukatar natsuwar zuciyar tunkaran mahaifin Salema ...
."an gama inji cewar minister lafiya wanda ya kamo hannunsa ya zaunar dashi akan gefen gado shi kuwa taufeeq da idanu kawai yake bin Salima dashi hankalinsa a matukar tashe gani yake tamkar ba Salimar sabace , me sonshi kalamanta sun tsaya masa arai matuka ya matsu ba'a zo an sallamesu ba ..
misalin k'arfe takwas na daren ranar aka sallamo Prof Taufeek daga gadon asibiti, kai tsaye gidan Ammi sukayo dashi, akayi masa masauki a part d'in dake kallon na Ammi zaune yake abakin gadon ya nad'e hannu wansa duka a kirjinsa tare da d'aura kafarsa d'aya kan d'aya yana d'an girgizawa ahankali ahankali ya bala'in tsurawa Umman Su'ad kyakkyawa idanunsa batare da yace mata komai ba ,yayi shr yana nazarinta so yake ya gano gaskiya abinda ta fad'a a hospital "na ta dad'e da cire ran zasu sake rayuwa tabarwa shemah shi sucigaba da rayuwarsu, kallonta yacigaba dayi itama shi din take kallo har yanzu wannan sihirtaccen kyauwun nasa na nan babu inda yaje ta d'auke idanunta akansa cikin sanyi jiki take yiwa Ammi magana k'asa k'asa daga inda yake kacokan hankalinsa da natsuwarsa na kansu.
" Amman baya jin abinda suke cewa atsakaninsu har sanda yaga ta juya ta bar d'akin cikin sauri da idanunsa yayiwa Ammi magana "ina zata?
itama Ammi nuni tayi masa da ya kwantar da hankalinsa zata dawo, d'akin yacigaba da d'aukar shiru kusan minti goma har shemah tashigo d'akin hannunta rike da d'an karamin tire me d'auke da flask da kananan glass Cup's ta iso gabansa ta tsiyaya masa coffe cikin cup ta mika masa cike da sanyin jiki ya amsa ya kai bakinsa ita kuma ta zauna kusa dashi tana tambayar Ammi ina Umman Su'ad ."
Aunty Umman Su'ad taje ? daidai ya kai cup din bakinsa da zumar shan coffee din Ammi taba ta amsa da"
"ta wuce gidanta "
Ai bai san sanda ya furzar da coffen din daya soma k'urb'a ba yana duban Ammi a matukar tsorace "ta wuce gidanta... ya sake maimaita abinda Ammi ta fad'a....
Ammi tace "eh ta wuce gidanta amman zata dawo gobe ,dan Allah ka natsu ka kwantar da hankalinka cikin satin nan da an kai eiman gidanta zamu shirya zuwa garinsu..
"Aunty.... kinji fa abinda tace tabawar shemah ni, "nafiki sanin wacece Salema nasan yadda nake cikin zuciyarta barina dazatayi ,shine babban tashin hankalina gara ina tare daita karta gudu tabarni kan wani dalilita
"wannan kuma gaskiya ne inji cewar Madam Shema "ina ne gidan nata yaka mata muje yanzu ..?
ya mik'e tsaye da kyar yana dafe daidai saitin kansa dayaji ya cigaba da sara masa wanda hakan yasa Ammi saurin mik'ewa tsaye suka nufo harabar gidan inda motacinsa ke jire ,escort dinsa naganinsa suka mimik'e tsaye tare da k'ok'ari bud'e masa gidan baya tare da Ammi suka shiga cikin hadaddiyar Land cranchis suka zauna .
Madam Shema tashiga dayar motar tunda suka shiga motar yayi shiru yana tunani iri iri gaba d'aya ya kasa manta maganganunta, ita ta hak'ura dashi yaci gaba da rayuwa tare da matarsa wannan kalmar bai san amizanin dazai ajiyeta ba aciki zuciyarsa .
gefe d'aya kuma Ammi magana take masa akan Shema cikin tsigar rarashi ya hakura yayiwa shema adalci yacigaba da zama daita har suka karya kwanar unguwar zance shemah take masa wanda shi kwata kwata bashi ne agabansa ba..
suna gama shigowa unguwar take ya gane d'aya daga cikin gidajen sirrinsa ne daya mallaka mata take zaune aciki, ajiyar zuciya ya sauke da karfi daidai sun iso k'ofar gidan bai tsaya jiran escort dinsa sun fito sub bude masa k'ofar motar ba ya fito ,sai bangaren k'ofar Ammi da take suka samu damar bud'ewa .
tashiga gaba yana biye da ita ahankali har bakin k'ofar part din Umman su'ad inda yashige gaban Ammi yasoma knocking can yaji sauti muryarta tace "waye?
"mu..mune suka had'a baki gurin fad'ar haka, yadda suka had'a bakin yasa bata tancace muryoyinsu ba, ta danyi shiru kamar minti biyu sannan ta bada umarnin shigowa.
yasanya kai cikin parlour'n d'akin tana ganinsu tasha jinin jikinta tare da nuna musu kujera da hannunta suka zauna har Madam Shema Ammi "tace sai kuma kika ganmu daga sama?
"shine ai fatan Allah yasa lafiya dai?
"ina fa lafiya Taufeek ne ya matsa wallahi lallai sai munzo.
shiru tayi tare da tsaida zuciyarta shigewarta cikin uwar d'akinta dan batasan abinda zatace ba yana ganin shigewarta , yabi bayanta gaba d'aya kallon d'akin yake koina a hargitse ga katuwar jakarta akan bed cike da rabin kaya ,ta isa inda kayanta ke zube tacigaba da d'aukarsu tana shiryawa cikin jakar.
ya iso gareta ya d'aura hannunsa kan katuwar jakar "mekike shirin yi haka Salima?
"ina zaki kike shirya kaya?
"zan koma mahaifata tabashi amsa tana cigaba da d'ibar kayanta tana sawa cikin jakar.
"a yaushe kenan zaki tafi ?
"a yanzu "tabashi amsa atakaice..
shiru yayi na wasu mintuna sannan yace "kibar tafitar nan zuwa nan da byn daurin aure eiman ,ki bar komai anan yanzu kibini mu koma gidan Ammi har zuwa lokacin da zamu tafi tare..
"bazan iya ba ..."karka damu kanka akaina sannan karka tillasta kanka akan zuwa gurin d'angina, oredy nace na hak'ura da kai lni matar bariki ce agurinka, kana da mata a halin yanzu kayi hak'uri kacigaba da rayuwa da matarka tana sonka fiyye da son da nake maka...
"karki sake kuskuren kira min kanki da matar bariki"kin kuwa san ma'anar matar bariki da kika kirawa kanki?
"nasan kin dai fada ne amman bakisan ma'anarsa ba ....
"ina tabbatar miki ke ba matar bariki bace ...
"kadara ce me girma da kima a idanuna wace bazan iya bazatar da lamuranta ba "ke din kadarace da million kudi basu kai a fansheki dasu ba ..
"ada can baya musu ko jayya bai ta'ba shiga tsakanina dake ba banason ayanzu da muka kara sanin ciwon kanmu muyi jayayya akan cigaban rayuwarmu" kiyi abinda nabaki umarni, ko da kin daina sona Salima ni har abada bazan ta'ba daina sonki ba saboda sonki ajinina yake , da soyayyarki akan halacin zuciyata ko kin fasa aurena ni bazan fasa aurinki ba "ta yaya kike tunanin zan iya barinki nacigaba da rayuwa da wata ?
ya kamo tafin hannuta cikin nashi yana murzawa "muje yanzu agabanki na sauwake ma shemah aurena dake kanta tunda saboda ita kike k'ok'ari gujewa aurena.....
yasoma tafiya da ita tayi saurin ja da baya "sakar min hannu ni ba saboda da ita bane kawai dai zuciyata zata fi samun natsuwa ne idan nabarku kucigaba da rayuwarku tare.
labulen d'akin ya d'an d'aga ya kira Ammi tana shigowa ya nuna mata jakar kayanta "kalli kigani Aunty shirin guduwa take tabarni saboda ta daina sona kiyi mata bayanin "ita zuciyata take so ba Shemah ba, "meye amfanin soyayyar da mukayi da ita abaya matsawar bazamu kasance cikin inuwa d'aya ba?
" idan tayi kuskuren barina wannan karon ba juyewar 'kwa'kwalwa ba mutuwa zanyi gaba d'aya yakarasa maganar kamar zaiyi kuka sannan yasaki hannunta ya koma ya jingina bayansa da bangon d'akin yana kallonta Ammi tasoma mata magana cikin sanyi murya da rarrashi domin fahimtar da ita illa rashin aurensa" yanzu fa ke ba yarinya bace karki manta d'iya gareki har kina shirin samun jika arayuwarki "me kike tunani akan yarinyarki da jikokinki?
"me kike tunanin mutane zasu ce akansa dake kanki idan baku auri junanku ba?
"Shema bata da matsala da dukkanin ala'mun, ta nuna zata iya zama daku bai kamata ki nuna kin aurensa akanta ba.. "matsawar kika gujewa aurensa kenan kinyi bak'inciki da sake dawowarsa cikin duniyar mu ke nan.
"na d'auka kece mutun ta farko dazata soma bada gudumuwarta gurin aurenku dashi .
"duk da nasan wannan maganar da kika fad'a nasan bata kai zuci ba, wallahi ko rantsuwa nayi bazanyi kaffara ba nasan bata kai zuciyarki ba domin kuwa har yanzu kina tattare da soyayyarsa kuma nasan bazaki iya barinsa ba, ni ma bazan bar wannan damar tayi tasiri ba muddin ina raye sai kin aureshi dole.. Ammi ta dad'e tana nuna mata faidar aurensu koda kuwa babu soyayya atsakaninsu ballantana da tsansar so atsakaninsu.
tana kuka tace "shikenan Ammi na amince.. jin haka yasa ya sauke naunauyen ajiyar zuciya ,take suka ajiye maganar akan zuwa jibi zasu tafi kasar haihuwarta.
Taufeeq yace "ki bar shirya kayan mu wuce gidan Ammi yanzu daga can sai mu wuce.
"kuyi tafiyarku idan kun shirya kubiyo ta nan ku daukeni, "bazai yiwu ba d'an bazan iya barinki ke kad'ai anan ba.
"Anan nayi rayuwa tsawon shekaru meyasa meni ? "ko kaga wani sauyi ne tattare dani?
"wannan zance da ne, ke kinsan da muna tare bazan ta'ba yarda da hakan ba ,kiyi abinda nace kawai mu samu zaman lafiya "har yanzu yana nan da ikonsa babu abinda ya sauya a halaiyensa, ba d'an taso ba haka tabisu..
daren ranar kasa runtsawa tayi banda juyi babu abinda take akan gadon Ammi ,tunani kala kala ke zuwan mata zata koma kasarta "ko yaya iyayenta zasu kar'bi lamarinta ?
zasu amince da lamarinta su amincewa aurenta da Taufeek a karo na biyu ko kuma har yanzu suna akan ra'ayinsu ?
zuciyarta tace "wannan karon karki soma bujirewa umarnin iyayenki duk abinda suka zartar hakinki ne kiyi musu biyayya, domin rashin bin umarni iyaye babu abinda yake haifarwa face nadamar rayuwa..
yadda ta kasa runtsawa haka shima Prof bai runtsa ba sai dai shi kwana yayi yana gayawa Allah..
washegari byn an d'aura auren eiman Ammi tasa aka kira mata kanin mahaifinsu dazo daurin aure ,shi kadai yayi musu saura araye tayi masa zancen taufeek tunda daman can yasan da komai daya faru ya tabbatar mata babu matsala in Allah ya yarda dashi za'a yi tafiyar .
daren ranar eiman ta tare a gidan mijinta dake omole estate cike da kewar su'ad, gidan ya tsaru sosai babu abinda babu Ammi da Dady sunyi k'ok'ari sosai d'an bakaramin kudi suka kashe ba Hajiya kaka da kuka tabaro gidan sakamakon tuno jikarta zeey.
haka 'yan kai amarya suka watse aka bar amarya da kawayenta zaman jiran angwane.
Allah sarki Ak yayinda abubuwa keta faruwa, shi yana can neman matarsa kamar zai yi hauka zuwa lokacin yayi baki ya rame yagama fita haiyansa baya zuwa office kullun yana kan titi daga wannan unguwar zuwa wancan unguwar har gurin gang dinta na da yaje yayiwa ore magiyar duniya da ganiya da su taimaka idan sun san inda take .
agurin ore ne ma ya samu sausauci inda tace masa suna waya sai dai da privete number take kiranta dan haka kullun da zarar yashirya gurin ore yake fara zuwa yaji ko takira..
bayan kwana uku
da misalin karfe 7:00 na safiyar ranar
suka escort dinsa suka d'auki hanyar zuwa kasar Cotonou zasu jirasu a aiport, Dady Ammi Umman Su'ad da Taufeek minister Rak da k'anin mahaifinsu Ammi banda Shemah suka bi jirgi .
12 :00 daidai a k'asar Cotonou tayi musu batare da bata lokaci ba escort dinsa suka shiga bubude kofar motocin, suka shiga direbobin suka ja, lokacin da taga motacin sun karya kwanar unguwarsu taji bugun zuciyarta ya tsananta, "ta yaya zata fuskanci iyayenta ?
"da wani ido zata dubesu bayan shekaru sama da ashirin datayi batare dasu ba ?
har motocin suka ja suka tsaya a k'ofar tafkaken get din gidansu bata da kuzari , jikinta yayi mugun sanyi .
ahankali mutanen dake cikin mototocin suka soma firfitowa d'aya bayan d'aya har suka gama fitowa banda ita dake zaune har lokacin abayan motar.
Ammi ta sake lek'owa cikin motar "fito mana Salema kisanyawa zuciyarki natsuwa babu wani abinda zai faru sai alkhairi, takarasa maganar tare da kamo hannuta cikin nata, ta fito
kafafunta dake rawa.
idanunta ta d'ago ahankali ta tsurawa gidansu , tana kallon gidan ,tsarin ginin na nan kamar da can baya sai d'an karin kyale kyalen zamani da gidan yasamu wanda hakan ya nuna mata ahlin gidan suna nan kan samun abun duniya, koma tace arzikin yaci uban na da .
me gadin gidan wani mutun ne daban ba wanda tasani ba ahankali take bin bayan Ammi dayake sauran mutane sunyi gaba har sun nemi iso zuwa cikin gidan bayan kamar minti biyu ta d'ago idanunta saka makon jin sautin muryar wanda ya fito bayan shigar me gadi, gama d'agowarta ke da wuya ta sauke idanunta akan k'aramin kaninta autansu Sulaiman ,wanda yanzu ya kara girma ko tace yazama babban mutun kamar a mafarki ya ganta ,mutuwar tsaye yayi agurin yana dubanta kana yashiga nuna ta" yaya salem............. kece ko kuwa idanuna ne ke min gizo?
Dady ne ya bashi amsa da "itace me gidan na nan?
kai kawai yashiga girgizawa sannan ya juya cikin sauri ya koma cikin gidan yana kiran sunan "mamma mamma mamma !!! "ga Salimarki mamma daga inda take zaune jikinta ya d'auki rawa duk tasan tabbas wata rana wannan ranar zatakasance..
Tashi take son yi daga inda take zaune amman ta kasa yunkurawa har sanda Ammi da Salima suka k'arasa shigowa had'ad'd'en parlour'n gidan tana zaune idanunta sanye da farin medical glass ta tsurawa k'ofar shigowar idanuta tana kallon d'iyarta data zama cikakkiyar mace.
kallon kallo ne aka shiga yi tsakanin uwa da 'ya wasu hawaye ne shrrrrrr suka shiga bin kuncin Salima da ta k'asa cigaba da d'aga kafafunta, tsawon rayuwata bata tab'a jin farinciki irin na yau ba.
sakamakon d'aura kwayar idanunta datayi akan mahaifiyarta, take anan duk wata ga'ba ta jikinta tashiga aiki fiyye da lokutan baya, yadda ta zuba mata ido tana kallonta tana zubda hawaye haka mamma ta zuba mata ido "mamma ta tsufa sai dai ba can ba wanda tasan tsabar jin dadi ne ya hana tsufanta bayyana.
Mahaifiyar Salima tsaye ta zuba ma 'yarta ido tana tasbihi ga Allah daya dubeta da idon rahama ya amsa mata rok'on ta,
Ya dawo mata da tilon 'yarta mafi soyuwa a gare ta lfy.
zance zuci tashiga yi "Allah nagode ma daka dawo min da Salima cikin duniya ta naganta tun ban mutu ba, Salima k'araso gareni Salima inji dumin jikinki,
"hmmmmm tabbas Salima jikina yana bani daman kobajima ko ba dad'e watan wata rana zaki dawo garemu.
Duk zantuttukan nan da mahaifiyar Salima keyi a zuciyar ta take yin shi azahiri kuwa zuba ma gud'an jinin nata ido tayi babu ko kiftawa.
salema dake tsaye tmkr an dasata ahankali sautin murya Ammi taji ta doki cikin kunnuwanta "ki k'arasa ga mahaifiyarki Salima taji dumin jikinki kiji nata yau ranar farinciki ce gareku gaba d'aya, ki god'ewa Allah da kika sameta araye cikin koshin lafiya.
tasoma k'okarin d'aga kafafunta da Suka soma sagewa tana k'ok'ari zuwa ga mahaifiyarta wace zuwa lokacin ta yunkura da kyar ta tsaya bisa kafafunta tare da ware hannuwan ta duka ala'mun tazo gareta tak'arasa da hanzarinta tashige jikinta suka rungume juna.
Salima na wani irin kuka me ta'ba zuciya babu abinda yafi iyaye dadi arayuwa barin ma uwa... ..."uwa dabance uwace kawai zata iya sanin radadin da ciwon ya'yanta, uwa jigon rayuwa itace komai itace jin dadin rayuwar ya'yanta babu kamar uwa a duniya .
farinciki da bakinciki da zai same mutun uwa bazata tab'a gudunka ba wani irin sanyin dad'i ne ke ratsa zukatansu sosai Salima ke kuka mamma na shafa bayanta dan farin ciki yasa taka sa furta dai dai da kalmar
19, September 2025
Aisha Auwal
Wow