Showing 414001 words to 417000 words out of 420383 words
Chapter 139 - SAI KA AURENI DOLE BY AYSHA A BAGUDU.txt
kizo mu zauna guri daya ba.
muryarta cike da matsanancin kuka tace "Allah bazan iya cigaba da zama da mutumin da bai san darajar iyayena ba.. take umma ta fahimci inda zanceta ya dosa "karki ce min akan abinda ya faru last week kikayo yaji.?
su'ad ta d'aga kanta ala'mun eh, umma tayi shiru tana dubanta duk da matakin data d'auka ya sanyaya ranta ,amman bata so ya jin datayo ba ,saboda gudun abinda zai faru gaba ,"wannan zuciyarta ta mijinta komai zai iyayi.
hawaye suka ciciko idanunta tayi saurin meidasu dan kar su'ad tagani hankalinta ya sake tashi. ganin yadda hankalinta yake a tashe yasa umma kyaleta tacigaba da kukanta har zuciyarta tayi sanyi , rarashinta tayi sosai byn tayi shiru tace.
"yanzu ina kika baro yaran?
"suna gurinsa "
"bari naje na kawo miki abinci amman bai kamata ki baro yaranki ba sunyi kanana dayawa uwa kad'ai ce tasan yadda zata kula da ya'yanta ,da ko karamin ki riko takarasa mgnr tana ficewa daga d'akin .
kasa cin abinci da umman takawo mata tayi illa kashe wayarta datayi tasamu guri tayi kwanciyarta a saman gado, sai lokacin tunani barin yaranta datayi yazo mata datasani ta taho da ko karamin d'anta ne.
kusan awa biyu da tafiyarta yana nan zaune agurin bai san abinda yakamata yayi ba har yaran sukayi bacci ajikinsa. ahankali ya mike ya kaisu bayan motarsa wanda hkn yasa suka farka daga bacci dan daman bawani dadewa sukeyi a bacci, yana kokarin shiga mota escort dinsa suka taso da sauri , d'aga musu hannu yayi ala'mun suyi zamansu sannan yashiga motar yabar gidan.
kai tsaye gidan musty ya nufa tun a mota yakirasa "yace gashi nan zuwa yana isowa kofar gidan yakirashi ,can kmr minti biyu musty ya fito rungume da diyarsa fadela ya mika masa hannu suka gaisa "lafiyar nagan kayi wani sukusuku dai kai?
"ina fa lafiya wannan shagwababbiyar yarinyar ce ke nan caja min kwakwalluwa da daru. ya fito daga cikin motar tare da yaransa suka shiga cikin gidan.
a parlour baki suka zauna byn yasanarwa eiman da xuwansu, eiman tashigo parlour'n sanye cikin bakar doguwar riga har k'asa hannunta rike da tire tana murmushi ta karaso ta ajiye akan center tabble idanunta na sauka akan yaran tace "kai kai marahabun da manya baki yau ya'yana ne agidan..?
sannuku da zuwa ,"zo nan mamana yanaga duk ranki a'bace me yasameki a baki takoma hannun yarinyar tare da zama gefen mijinta tana sake fad'ad'a murmushinta sannan tace "yaya ina wuni ya su'ad take?
"tana lfy ya amsa mata atakai ta mike tsaye byn sun gaisa ta amshi emran ta sanya yaran gaba sukayi ciki domin basu guri sun zanta.
byan fitar eiman musty ya gyara zama "uhm abokina ina sauraronka me ya had'aka gimbiyar taka ?
"ak ya zayyano masa abinda ya faru tun last week zuwa yau din nan shiru musty yayi ya k'asa cewa komai ya tsura masa ido dan lamarin ak yafi karfinsa "gsaky aboki baka kyauta ba "maza tashi muje biko tun abun bai girmama ba.
"kabarta kawai friend yanzu haushina take ji ko muje ma ba sauraranmu zatayi ba mubari zuwa wani sati ,zuciyarsa kuwa fad'ar hk yayi ba dan yana jin zai je wani biko ba.
nan suka cigaba da tautauna yadda lamarin zai kasance da zai tafi eima tace yabarsu farhan tunda hutu ake ranshi bai so ba amman babu yadda ya iya hk yabarsu ya wuce .
koda prof taufeek ya dawo umman su'ad ta sanar dashi abinda ya faru "yace su'ad tayi daidai hk ake son d'a me kishin iyayensa wannan mataki data d'auka zai sa shi mijin yagane iyayenta na da mutunci agurinta ,dan haka bazan takuramata ba, idan taji tana iya cigaba da zama dashi fine, babu ruwana idan kuma bazata iya ba ni me tsaya mata ne ta amshi yanacinta agurinsa .
"bai dace kace hk ba kodan darajar aunty.
"shi abinda yayi ya dace ?
"idan bai duba darajarki na sirikarsa data bashi auren diyarta har da yara guda uku tsakani, yakamata ya duba darajata amatsayana na kanin mahaifiyarsa .
"idan shi akayiwa tashi uwar zai ji dadi?
umman su'ad ta bud'e bakinta kennan zata sake yin mgn ya d'aura hannunsa akan bakinta "banason na sake jin komai daga bakinki ki xuba idanu kmr yadda nima zanyi "shikena idan ka gama abinci ya kammala "bar zancen abincin nan ki matso kusa dani akwai abu me mahimmanci danazo muki dashi..
ta hararesa" kai haba yallabai wai bakasan ka tsufa ba "wani tsufa ki matso bakisani ba ko adduarmu ta kar'bu muyi d'an kanmu yau kinga shikenan mun huta da... "dan Allah kayi shiru kar wani kunne yajika "haihuwa yanzu gotai gotai dani, ina haihuwa diyata na haihuwa" haba yanzu fa mun Tsufa da wata haihuwa, duk abinda zan haifa nabarwa su'ad," bazan iya da wannan kayan kunyar ba "kece kike ganin kmr mun tsufa da haihuwa.
"ina gani fa yar yarinya karama zan bari asamomin na aure abata tayita haihuwa tunda keda shemah har yanxu shiru "wallahi ni nama fijin shemah adduar danake mata kenan kullun ko guda daya ne Allah yabata tasamu abokin shawara..
musty yaji shiru shiru ak bai sake masa zance zuwa gurin su'ad ba, ya same shi zaune acikin office dinsa yana operating system "aboki najika shiru baka sake yi min zance ummul ihsan ba alhalin nasan abin yana damunka.?
"wallahi kamar kasani lamarin na mugun ta'ba min zuciya banyi expecting hrt beat zata iya sharewa da lamarina ba, duk ba ma shareni datayi yafi damuna ba kamar yadda iyayenta sukayi burus dani ko zaman daduro nake da diyarsu ai yakamata su nemi ni..
"kai da kake da mata baka nemesu ba ta yaya kake tunani sun nemaka?
kawai malam kaajiye girman kai muje yanzu ayi maslaha ka ba kowa na gidansu hakuri a wuce gurin musty yakarasa mgnr yana kwashewa da dry.
a cikin mota ma fad'a musty yake masa akan ya canza hali dan wannan halin nasa baiyi ba..
"ka kasa fahimatata ne kawai bakasan yadda nake ji in dawo gida banga yarana ba most especial ihsan yarinyar ta ba'lain shiga raina "hakuri zakayi kamar yadda kowa yake yi, dole ka d'auke zuciyarka akansu, kasancewa jikokin diya mace a zuciyar iyaye suke ballanata wad'an nan jikoki daban suke agurinsu duba ga mahaifiyarsu ita kad'ai ce agurin iyayenta.
"sannan ka dinga respecting iyayenta aboki a maganganunka babu respect ciki "yanzu irin abinda kakewa mahaifiyar yarinyar nan, idan nawa ammi zakaji dadi?
"ka yi tinani kagani dan Allah daga yau komai ya wuce katayata kyautatawa iyayenta kmr yadda take wa ammi. har suka kusan karaso unguwar fad'a musty ke masa shi kuma yayi shr kmar da gaske d'aukar nasihar yake.
cikin kankani lokaci suka iso unguwarsu , agaban makeken get din gidan sukaja birki tare da yin hon me gadi dake zaune yaji karar hon ya mike da sauri ya isa jikin hujin karamin get din gidan yana dubawa wad'an daya Gani ne yasashi fitowa batare da ya bude get ba ,ya isa jikin motar yana me rankwafowa ala'mun girmamawa .
musty yayi kasa da glass din motar , yinka ya sake risinawa "sannuku da zuwa.
"ykk yinka ya aiki inji cewar musty.
"lafiya sir"
"yinka bude mana get mushigo "
yinka yayi shiru yana tunanin abinda zai fad'a musu har sai da musty ya sake maimaita abinda yace ,sannan yinka ya dawo cikin haiyacinsa yace "dan Allah kuyi hkr small madam tace idan kukazo kar na sake mabarku ku shigo.
matukar firgice musty da ak suka kalli juna hankalin ak yayi maseefar tashi da jin hk take jikinsa yasoma tsuma a harzuke "yace kunci kutumar ubanku kai da small madam din wawa kawai ,jibeshi katun banza kawai ya wani 'bare baki yana mgana kmr jaki dan allah malam bude mana get mushigo kafin nafito na tattaka agurin "kasan kuwa ko ni waye dakake isar min da wannan banza sakon "cool down fried ka natsu ka dawo hankalinka "kabari mubi komai ahankali "akan aikinsa yake abinda aka gaya masa shi ya aiwatar "kai yinka jeka kace mata tayi baki ne. .
yinka ya juya da sauri yayi cikin gidan, cikin mintina da basu wuce biyar ba, sai gashi ya dawo cikin sauri "wai tace baza ta samu damar fitowa ba, jin hk yasa zuciyar ak tsananta bugawa da sauri sauri, musty ya dan juyo ya saci kallon inda yake zaune akallon da yake masa zuciyarsa kmr zata basa kirjinsa ta fito .
sannan ya juyo ga yinka dake tsaye cikin tashin hankali "koma kace mata musty ne yake son ganinta .
"sir dan allah kuyi hkr wallahi tace kar na sake dawo mata da any excuse idan na dawo abakacin aikina.
ak yayi saurin juyar da kanshi gefe , yashiga kokuwa da numfashinsa dake barazanar d'aukewa, ji yake kmr ya fita ya shako wuyan yinka yayita dukansa har sai yaga baya numfashi.
jiki a sanyaye musty yace "ok yi tafiyarka, muje kawai Allah ya kyauta duk kai janyo wannan matsalar , "matsalar uwar me najayo daga kar'bo ya'yana sai abu yazama masefa kar Allah yasa ta bada izinin ganinta tacigaba da zama a gidansu har mahdi ya bayyana aikin banza kawai ,so take ta meidani mijin tace abinda bazai yiwu ba kenan yaja tsaki yana furzar da iska me zafi.
tuki kawai yake yana tunani "shi su'ad zata wulakanta saboda taga yana haukan sonta "aiko zai nuna mata iyakarta ,ba dai takamarta son dayake mata ba, zai fizge dan iskan sonta ya hutawa rayuwarsa ....
Mmn sudais ce
💗💗💗💗💗💗
SAI KA AURENI DOLE
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
~NA~
*AYSHA A BAGUDO*
~DEDICATED TO~
HAUWA A USMAN
JIDDARH
YA GHAFUR
THE ALL FORGIVING
page 90
🔚🔚🔚🔚🔚
....... motar ta d'auki shiru kowanensu da abinda yake tunani acikin zuciyarsa, musty na tsananin mamakin halaiyan abokinsa na rashin da'a "to ko dan an haifeshi cikin turawa ne ya girma cikinsu yasa yake da ikidar rashin girmama mutane matukar ba iyayensa ba.?
"shi gbdy lamarinsa na d'aure masa kai bai ta'ba ganin bahagon mutun irinsa ba ,komai cikin zafin rai .
shi kuwa ak ji yake kmr ana diga masa ruwan dalma ne a cikin zuciyarsa ,wani irin tuttukin bakinciki ne ke tasomasa from know where yana mamaye ilahirin sansar jikinsa ,a yanxu dayake zaune kokarin cireta daga cikin zuciyarsa yake amman zuciyarsa taki aminta da haka, dan duk inda ya motsa yana jinta acikin tsokar dake makale akirjinsa tana tafiya da bugun zuciyarsa, har suka iso gidan ak bai daina tunanita ba.
tun daga harabar gidan yasoma jiyo sautin kukan fitinanun yaransa ,da hanzarisa yashigo parlour'n farhan ne ke jibgar emran kmr Allah ya aikosa akan ball, shi kuma emran sai ihu yake tsallarawa tamkar ana zaran ransa, da sauri ak yakarasa yashiga tsakaninsu tare da kwace ball din da suke kokarin kashe kansu akai ya d'auki emran ,a daidai lokacin da eiman ta fito parlour'n wace fitowarta kenan daga wanka ko kimtsa kanta bata tsaya yi ba ta zira hajibi saboda hayaniyarsu, tsayawa kawai tayi dafe da goshinta ganin uwar gumi da suka had'a duk da sanyi AC parlour'n aranta tace "yaran nan ba dai fitina ba, ita kanta tunda sukazo gidan tarasa sukuni ga barna, da jarabar fad'a barin ma kar farhan yaji labari ,duk yafisu jarabar maseefa da zuciya, gsky uwarsu na kokari .
muryarsa a kasalance yace "haba babana meyasa kake cin zalin kanika ?"kai fa big brother ne daga yau kar na sake ganin kayi fad'a da emran ko ihsan, kuka farhan ya fashe dashi tare da cewa "ni ba big brother bane sai dai ko emran.
gbdy suka kwashe da dry har eiman shi kuwa ak haushin dake tattare dashi bai barsa ya dara ba yace " shikenan tun da bakason zama big brother babu ruwana da kai, mamana ita tazama big sis ko?
da sauri ihsan tashiga girgiza masa kai "allah nima dady banason big sis ni sunana baraka.. wata dryr suka sakeyi sannan suka nemi gurin zama daga musty har ak byn mkr minti talatin eiman tagama shirya dining taxo tagayawa musty "aboki muje muci abinci table ya kammala "kaje kaci kawai babu muhalin abinci acikina, ya karasa fadar hk yana runtse mayatattun idanunsa "dan girman allah ka sausautawa kanka abdul ya fad'a mgnr muryarta a sanyaye "karkayi abinda zaka dawo kana dakasani "wannan fad'an rashin gsky kake kokarin yi.
ak ya bude mayatattun idanunsa ya xuba masa "eh man fad'an rashin gsky kakeyi ya zaka daketa sannan ka hanata kuka "musty... ak ya kira sunansa a sayaye "ina jinka "stop tell me all this nonsense.
"ni ne nake gaya maka nonsense akan ina fad'a maka gsky to kajira ranar da zan sake maka mgn akan matarka "better yace atakaice sannan ya mike tsaye ransa a bace yana kiran sunan eiman "ke eiman ta fito da sauri "gani yaya "had'o min kayan yaran nan "lfy yaya zaka wuce dasu na d'auka sai sun gama hutu damu?
"uhm da nayi tunanin hk amman yanzu na fasa.
jikinta a sanyaye ta juya takoma ciki tana tunanin abinda ke damunsa duk kwanakin hk take ganinsa "yanzu dan wannan mganr dana maka shine zaka tafi dasu wai meyasa kake irin hk ne ?
"dakata dan Allah malam nace maka akan maganar daka min ne ?
"dan Allah karka k'ara min damuwa akan wancce nake ciki .
eiman ta sake dawo parlour'n hannunta janye da karamar turolly dinsu, ya tasa yaransa gaba suka bar gidan batare da yayi musu sallama .
eiman takaraso kusa da musty da d'an hanzarinta "honey lfy naga yanayin yaya hk? "ina fa lfy tun last week suka samu sa'bani da matarsa nan yashiga koro mata komai daya faru, "ni dai nayi iya bakin kokarina akan lamarin amman abun ya cutura dan itama su'ad din ta hau dokin fushi yakarasa maganar yana soma cin abinci shiru tayi tan tunani "to ko shiyasa take neman layinta shiru . ?
tunda ya koma gida ya k'asa zaune ya k'asa tsaye acikin d'akinsa, ya kai gwaro ya kai mari babu abinda ke cin zuciyarsa kmr irin wulakacin da su'ad tayi masa , ranar baiyi isashen bacci ba, ga tsananin ciwon abinda tayi masa ga kuma jarabar kewarta daya addabi ruhinsa,juyi kawai yake akan gado rungume da yaransa ,gbdy tunani yashigayi akan lamarinsa daita , wanda har yake neman tarwatsa masa kwalkwaluwa "wai har shi zata sa a wulakanka ta hanyar kin bada izinin shigowarsa gidansu .. ?
"me yasa bazan iya barin rayuwata ba kmr yadda ta bukata ?
ya fad'a yana kallon cilling d'akin da mayattun idanunsa wad'an da suka gama kad'awa suka soye tsabar baccin dake cinkinsu .
"kana sonta shine dalilin dayasa ka k'asa rabuwa daita"
"ina sonta amman bashi zai sa nabarta tayi yadda tagadama ni nake aurenta baita take aurena ba, yaran da ake tashin hankali akansu ya'yana ne why da za'a takurani akansu ya tambayar kansa yana cinza lip's dinsa can ahankali ya motsa labbansa "oh my God.. Allah narokeka ka ciremin son yarinyar nan araina," ka mantar dani lamarinta duk abinda ya dangancita ,kasanya min hakurin rashinta har karfe biyun dare ak na kwance yakasa runtsawa gbdy ki burbushin bacci yaki zuwan masa, wani tunani yazo masa ya yunkura ya tashi ya sauko daga gadonsa ya gyarawa yaransa kwanciya yashiga bathroom ya d'auro alwala yazo ya tayar da sallah nafilfili ya dinga jerawa wanda bazai ce ga adadin wanda yayi ba daga karshe bacci ya d'aukeshi anan inda ya idar da sallah.
washegari tun gurin kula da yara yasoma raina kansa da kyar yasamu yayi musu wanka yashiryasu ya kwashesu sukaje gidan abinci sukaci daga nan ya kaisu shopping sannan suka dawo gida, ya k'asa barinsu yaje aiki gashi gbdy sun hargitsa gidan da kayan ciye ciyen daya siyo musu hk wuni ranar zurr yayisa a bautar yaya har dayasani d'auko su yayi daga gidan eiman. dare yayi tunanin uwarsu ya addabi ruhinsa duk yadda yaso yakiceta abun ya tura dan hk ya yarda ya sallama tagama da zuciyarsa, daga safiya har daren duniya a kiran layinta yake karewa amman bai shiga yanxu haka kiran layinta yake akaro na sau ba adadi amman kalma daya ake gaya masa is not respond ya dafe goshinsa dayan hannunsa na saman ruwan cikinsa ahankali ya zamo daga kan kujerar dayake zaune, yaransa gbdy suka zagayeshi suna kuka "dady momy'nmu "ka kai mu gurin momy gbdy abun duniya ya taru yayi masa yawa ya janyosu ya rungumesu gbdy ajikinsa, duk ta inda ya juya babu dadi acikin kwanaki goman da bar gidansa, komai ya tsaya masa cak hatta iskar duniya daya yake shaka baya jinta yadda yake bukata kallo daya zaka masa kasan yana cikin damuwa da tashin hankali . tuni yasoma nadamar abinda ya aikata ,banci hk da yanzu yana tare da matarsa uwar ya'yansa me son farincikinsa, daya yanzu suna tare ko suna hira ko suna kwance acikin bargo daya, ya matse pillow dake rungume akirjinsa "i love you my beautiful wife plz come back to me don't live me, i can't do without you "yanzu na gane sai dake zan iya cigaba da rayuwa amman zuciyarsa na kwabarsa kar yayi saurin zuwa zata dawo da kanta idan tagama fushinta .
ammi bata tashi jin abinda ya faru ba sai da lamarin ya kara girmama, dan kimani wata biyu kenan ak bai taka inda su'ad take ba da sunan biko ,haka itama tabangarenta babu wanda yayi kokarin nemansa.
eiman tasanarwa ammi dan musty yayi rantsuwar bazai sake tuntu'brsa da zance ba matsawar ba shine yayi masa ba ,ammi nagama jin abinda yayi ,take ta rufeshi da fad'a, ta inda take shiga bata nan take fito ba, "ta yaya zaka hana yara zuwa gurin kakaninsu ?
"ni kaina ina bukatar yaran nan su dinga zuwanmana ko da week end amman kabi ka kanai naye komai ,kmr kai kad'ai kayi silar zuwansu duniya
19, September 2025
Aisha Auwal
Wow