Showing 294001 words to 297000 words out of 420383 words
Chapter 99 - SAI KA AURENI DOLE BY AYSHA A BAGUDU.txt
zauna daidai lokacin da kamal ya karaso daf dasu yana murmushin yake .
cikin dakiyar zuciya ya shiga tare da rufe murfin motan yana bawa driva umarni yaja suka tafi kallonta yayi a fusace yana zaro ido kmr mayunwacin zaki yayi kasa kasa da muryarsa kmr zai mata mgnr azirki cikin rada yace "kalli dan iskar shigar da kikayi wanda hkn yabawa wani banza kallemeki, "duk tarin siturinki ki rasa kayan dazaki saka sai wadan banzayen kaya yaja tsaki yana kawar da fuakarsa jikinta tabi da kallo dan ta gano illar shigarta , koina ajikinta a lullube yake baya ga fuskasta da tafin hannuwanta idanunta ne suka cicciko da ruwan hawaye tare sa kawar fuskarta gefen hawaye na gangarowa ta gefen idanuta .
Tun daga hanya take karewa garin kallo tare da mutane garin masu fasali da aljanu har suka isa kawataccen hotel din da zasu sauka.
wanda ya amsa sunansa hotel ne wanda manya attajirai, ko kusoshin gwanati wad'anda suka ci suka koshi ne zasu iya zama cikinsa.
hotel ne mai kyau da tsari,duk wanda kaga yakama hotel din to shahararen me hannu da shuni ne ,zamanka cikin hoter din tmkr kana rayuwa ne a muhalinka duk wani abun bukata akwai shi acikin wannan hadadden hotel din, daya amsa sunansa a duniya gbdy babu abinda zaka bukata ka nema ka rasa.
ahankali motarsu ta tsaya cikin farfajiyar hotel din shine yasoma fitowa ya barta zaune cikin mota.
shi da nustymusty ne tsaye suna mgn yayinda babban yaron sir mahbub ke kai kawo amsar musu daki kusan minti goma tsakani komai ya kammala ya budewa su'ad kofa ta fiti tafiya yasoma yi ahankali tana manne a gefensa yana rike da hannuta.
ta kowani bangare ta kalla ma'aikatan hotel din ke kai kawo daga maza har mata sanye da wasu haddadun suit
har suka karaso dakinsu hannuta na rike cikin nashi bai yarda yayi ganganci sakinta ba .
suna shiga dakin sanyi Ac ya ratsa ilahiri jikinta Komai a gyare yake tsab a dakin.
ahankali ya saki tafin hannunta zuciyarsa na harbawa har yanzu ya kasa hakurin iskanci da kamal yayi masa, yane shi da bai taba kusantar kowace mace da suna zina arayuwarsa ba byn matansa na sunnah ,bai taba tsayuwa da wata matar aure wace ba yar uwarsa bace ,shima tsayuwar baya wuce gaisuwa," ta yane wani kato zai dinga kalle masa mata har da lasar lip's wannan abu ya maseefar tsaya masa arai anya kuwa zai iya hakuri wannan iskanci wayoyinsa ya ciro gbdy ya watsar a saman gado .
ma'aikatan hotel din suka biyosu da manya hakunkunansu .
tsaye take har lokacin a gefesa tana dan kalle kalle a dakin kallo daya zaka mata kasan wannan shine Karonta na farko data sanya kafa zuwa wata kasa.
takaicinta bai sa saurareta ba ya matsa kadan daga gefenta yayi tsaye gaban gado yana k'ok'arin sassauta tie din wuyansa,yana son rage daya daga cikin rigunan dake sanye a jikinkinsa .
daya daga cikin wayoyinsa daya watsar a saman gadon ta dauki karar sauti me dadi sai da kiran ya katse bayan ya gama sassauta tie din wuyansa sannan ya dauki wayar yana dubawa,hannunshi daya riqe a kugunshi yana takawa ahankali zuwa bakin window hotel din,ya zuge labuyen yana kallon harabar hotel din , yana mgn atsanake ta dan saci kallon yanayinsa taga har lokacin fuskarsa a hade take kmr wanda aka aikowa da sakon mutuwa duk km sai taji babu dadi zuciyarta tashiga damuwa da halin dayake ciki kmr takarasa gareshi ta runguneshi tabashi hkr sannan tace ya dan saki ransa, ammam fargaba abinda zai mata ya hanata ta manna jikinta da bangon dakin tacigaba da kallonsa tana sauke jiyar zuciya .oh Allah ko ta ya ne zansoma rayuwa dagani sai shi
,ta fada hk cikin zuciyarta tana runtse idanunta Tare da dunkule hannaye.
tsawon lokaci ya dauka yana waya da wanda taji yana kira sunansa da sir mahbub sannan ya katse kiran yashiga wanka cikin sauri sauri ya fito yace tashiga wanka shi km yasoma shirin fita tana tsaye tana kallonsa ya sake kaya zuwa wasu kananun kaya masu matukar kyau da daukar hankali kayan su amshi jikinsa matuka sosai suka sake fito da ainihin surar jikinsa ahankali muryarsa ta fito "ina zuwa zanje mu hadu da sir mahbub bazan dade ba zan dawo ya nufi kofar fita .
"Allah ya tsare ya dawo da kai lfy ....
da sauri ya dan dawo yana zaro idanu waje yana dubanta cike da mamakin jin furucinta ya lumshe mayattun idanunsa tare da furta "woww tun yanzu yarinya karki min hk man plz banason kiyi saurin yin ladaf tun yanzu ba gsky. yakarasa mgnr yana fice daga dakin ya kulleta ta baya.
numfashi taja ta sauke da kyar tare da cewa masefaffe kawai , da ba'a ayi masa gwaninta , idan bakayi ba yace bakayi ba idan kayi ya gwasaleka.
zakaye dakin tashiga yi tana karewa yanayin gurin kallo , dakuna ne guda biyu wannan datake ciki babba ne sosai dauke da makeken gado brow colour wanda aka shimfidesa da laulausar zanin gado fari sol sai bargo daga gefe ,sai doguwa kujera guda daya, can gefe km guda wordrob ne da mirrow bedside duk set ne da gadon dakin .
sai wanda suka baro kafin shigowarsu shima babba ne sosai dan kusan yafi wannan datake tsaye acikinsa girma zagaye yake kujeru masu kama da italy bed da frigde daga gefe .
ahankali ta sake fitowa parlour inda idanunta suka sauka ta gefen damanta tasoma takowa ahankali cike da matsanancin farinciki har takarasa ta yaye labulen datagani wani madaidacin bancoly tagani wani irin tsalle tayi hade juyi tana rungume hannuwanta duka a kirjinta tana shakar iskar garin .
"guri me kyau"
jikin karfen takarasa tana kallon tsirarrun mutane dake kai kawo cikin hotel tare da sake bayyana farincikinta ahankali ta sake furta "gsky gurin nan ya tsaru sosai "gurin abun sha'awa zanji dadina .
ta dauki tsawon lokaci tana tsaye a bancoly har sai data duba taga lokacin sallar azahar tayi sannan ta dawo dakin ta shiga toilet .
bathroom din tsab yake yana bada wani cent din kamshi me dadi tayi wanka tare da dauro alwala ta fito ,sai data kammala sallar sannan hankali ta mike takarasa inda taga jakunkuna guda biyu ta janyo daya tare da zuge zip din ,kayansa tasoma cin karo dashi ajere gwanin sha'awa suna fidda kamshi turarensa me sanyi dadi da taba zuciya haka ta dinga fitar da su tana jerawa a tsanake ta sake janyo dayar jakar abinda yabata mamaki bai wuce ganin kayanta shake da jakar ba tayi shiru tana zare idanu tana kallon kayan kafin daga baya ta fara cirosu daya byn daya hatta kayayyanki amfaninta suna ciki hkn ya tabbatar mata zuwanta kasar ba'a shekaranjiya yasamo asali ba an dade da shiryawa hkn ,km tasan komai ya faru ne da hadin bakin eiman.
dayan bangaren wardrobe din tajera nata kayan ,komai ta ajiyeshi a muhallinsa.
zuwa lokacin sallar la'asar yayi,ta soma jin wata azabbbiyar yunwa ta fitar hankali sai dai babu komai acikin dakin na ci,hatta freezer dake dakin babu komai ciki,bayi tashiga
ta sake dauro alwala ta dawo ta gabatar da sallar la'asar ta koma lamo ta kwanta saman gadon tana mukurkusun yunwa , rabonta da abinci tun jiya.
lokacin da suka tsaya a Thailand taso taci abinci amman ganin yadda yake ciccin magani yasa ta kasa tmbyrsa shi km yaki taya mata.
Wasa wasa lokaci ya tafi sosai duhu ya fara yashigowa ,har lokacin sallar yayi ishai tayi,a daddafe ta tashi tayi sallar magariba da ishai ta dawo ta sake dawowa ta lafewa ta kwanta,a haka har tara tayi ,zuwa wannan lokacin ta fara raina kanta,tuni ta fara fidda ruwan hawaye,tunaninta kawai mugunta yasa AK yayi mata haka ,ya barta babu abinda zataci gashi tana jin sautin kararrawa jikin dakin, wanda tunaninta yabata ma'aikatan hotel din ne . amman babu daman bude musu kofar kasancewar ya kulleta ta waje,gbdy takaici ya cika zuciyarta,tana daga kwance amma jiri takeji yana dawainiyya daita saboda tsabagen yunwa.
ahankali lokaci zuwa lokacin zata duba agogo tana share hawaye dake tsiyayowa daga ciki kwarnin idanunta tana juyi saman gadon, tuni idanunta suka sauya launi zuwa wani kalar daban saboda kukan yunwa.
Tunda ya fita yana tare da sir mahbub da wasu daga cikin manya kasar suna tautaunawa akan yadda ,bude kafaninsa zai kasance duk wannn dogon lokacin daya dauka hankalinsa na kan sarauniyar zuciyarsa
basu gama abinda yaje yi ba amman hk ya katse meeting din ya baro guest house din sir mahbub shida musty da wasu daga cikin yarasa tun a hanya suka rabu shi km direban sir mahbub ya nufo hanyar hotel .
tafiyar minti arba'in cif tsakanin guest house din sir mahbub da hotel din da suka isa ,ficewa yayi daga cikin motar dauke yana bawa direban daya daukasa umarni cikin harshen turanci yazo gobe da wuri ya daukeshi.
Tana kwancen taji ana kokarin bude kofar,sai ta sake tsurewa ta zaro ido tana duban bakin kofar,a nutse ya turo kofar dakin ya shigo ya maidata kofar ya rufe.
ahankali mayatattun idanunsa suka fara sauka,akanta tana murkususu da ciki da sauri ya tako zuwa inda take kwance wanda tuni ta runtse fararen idanunta da suka raina fata hawaye masu zafi ke bin gefen idanunta ,cikin wani irin yanayi na zallar kaunarta ya durkusa a gabanta ganin bata motsa ba yasa ya haura saman gadon ya tarairayota zuwa jikinsa ya rugumeta, cikin sauri yakira repction yana bada umarnin akawo masa abinci sannan yasoma cire suit din sama rigarsa daga zaune dayake ahankali ya kai bakinsa daidai saitin kunneta yana rada mata kalmar ban hkr
"Am so sorry hrt " ya furta yana janyota jikinsa ya kai hannunsa kasanta mararta yana shafawa sanyayyiyar muryarsa tasa ta bude idanuunta dake runtse ta zuba masa cikin zallar shaukinsa . cikin minti goma yaji bell din dakin na kara.
bai tsaya kallonta ba ya kwantar daita ya sauko cikin sauri ya bude kofar ya amshi tiren abinci da ya dawo inda take kwance ya sake hawowa gadon soyayyar shinkafa da gasashshiyar kaza,bayan ya ajiye robar fresh milk plate abinci ya dauko mata ya sanya cokali sannan ya dagota yana dubanta
"Tashi kici abinci am sorry karki dauka na mantaki ne kina tare da ruhina " shr tai taki duban inda yake kusan minti goma kafin ta mike cikin rashin kakkiyar kuzari tana goge hawaye ya kasa dauke idanunsa daga kanta,sbd yana ji acikin zuciyarsa kmr yazalincene murayasa a kasalance byn ya riko tafin hannuta cikin nasa yace
"Stop crying hrt kukanki na bugar min da zuciya taba kiji ya kai hannuta daidai saitin zuciyarsa tabbas taji bugun da zuciyarsa ke yi amman ai bai kai nata ba .
"am really sorry tai shr taki amsawa illa zare hannuta data cikin nasa taja plate din abinci ta soma tsakuran abinci shi km yashiga bayi bawani cin abinci dayawa tayi ba ta ture plet kasancewar cikinta yagama kullewa.
tsahon 30 mint ya dauka acikin bayi yana durza jikinsa sannan ya fito daure da towel wanda da kadan ya zarta gwiwarsa,hakan ya sanya kwantaccen sumar gashin dake kwance ajikinsa data sha ruwa kwanciya luf luf,idanu suka hada sanda yake fitowa,tayi saurin dauke idanunta daga kansa ta maida idonunta ta rufe gam dan tasan halinsa kmr yunwar cikinta sai dai tabawa wani labarinsa, a yadda take jin sanin halinsa ko ammi data kawo shi duniya bazata fita sani ba ,tana kwance zuciyarta na tsananta harbawa dan batasan yadda zasu kare ba yau daga ita sai shi a daki daya .
kai tsaye wardrobe ya nufa dan bai ga jakar kayansu ba yana budewa yacikaro da kayansa ajere .
ya fito da whit shirt me budaden gaba wanda daga kasanta akwai botira daga samanta km a dan bude take hkn ne ya bawa wani sashi na gashin dake kwance a kirjinsa bayyana, gajeren wando da fari sol kmr yadda rigar take.
inda take su'ad kwance ya sake dawowa ya kai hannunsa ya shafa tuming dinta ta bude idanunta ahankali ta sauke akansa ya janyota jikinsa abincin ya sake mika mata,ganin bataci abun arxiki ba da idanusa yayi mata nuni data ci,fuskarta ta yatsina ala'mun baxata ci ba ,ya tsura mata idanunsa wanda hakan ya tilastata yin yadda yake so din.
,baki daya cin abincin kawai take saboda yadda ya rutsata da idanunshi yana bibiyar motsinta,.
karar wayarshi ce kawai ya ceceta,mikewa yayi daga gun ya koma gefan gado bayan ya janyo center table ya dora,abinci akai gbdy abincin chips ne da hadin cowslow kamar ko yaushe da ruwan cocumber ,sai da ya zauna sosai sannan ya fara amsa wayar yana tsakurar abinci .
Ya jima yana wayar wanda har batasan sanda ya kammala ba sakamakon gyangyadi data soma a wajen data gama cin abincin saboda mutuwar jiki da kasala data rufeta,wutar dakin ya kashe mata ya barmata hasken dum Light dan tasamu damar yin bacci shi km koma parlour.
tana jin motsin fitarsa ta mike ta kunna haske wayarta ta fidda doguwar rigar baccinta ta'ajiye saman gado , tashige bayi wani wanka tayi ta fito byn ta goge jikinta tun cikin bayi, ta saka rigar bacci tare da bin ilahirin jikinta da turarenta oud touch.
A hankali taye saman gado ta kwanta tana juyi akan gado tsawon 30 minti da kwanciyar amman ta kasa runtsawa juyi kawai take akan gadon tana mika tare da mammatse jiki sbd wani irin yanayi data tsinci kanta .
ak dake zaune a parlour yana aiki akan system ya ture daga gabansa ya Mike yashigo dakin ya dubota ,idanunshi fesssss suka sauka a kanta kwance bisa gado tana mika me tattare da gajiya ya tsura mata idanunsa yana kallonta,haske farar rigar bacci ne ya haske dakin ,binta yacigaba dayi da mayatattu idanunsa .
ahankali ya runtse mayatattun idanunshi yana sauke numfashi da ajiyar zuciya atare hadi da ambatar sunan Allah.
wani irin yanayi yasoma ji ajikinsa
yaso kwarai ya tilastawa kansa yin bacci ya barta yau kawai ta huta batare da yayi wani abu daita ba sai dai baya jin zai iya wannan hakuri, yakarasa inda take ya kwanta agefenta ya motso gareta ya hadeta da kirjinsa yashiga shashshafa sansar jikinta, ahankali yake binta yana massaging din sansar jikinta domin tasamu sausaucin gajiyar data kwaso kafin daga baya ya zarce da mammtsa mata kafafunta kungunta da bayanta yana mata massaging ahankali, sosai take jin dadin yadda yake mata hkn km ya kwantar mata da hankali tasan babu abinda zai mata dan da zai yi da yanzu an wuce gurin bashi ya barta ba sai daya ga ala'mun bacci me karfi yayi nasarar daukarta sannan ya barta .
ya sauko daga kan gadon ya nufi parlour ya dauko system dinsa ya dawo dakin, ya jona a charger yashiga opereting yana tura sakowani da duba sakonni da'aka tura masa har tsakiyar dare yana kan system yayinda su'ad ke sharar baccinta hankali kwance.
misalin karfe 2:00 dot ta farkar sakamakon fitsarin da ya cika mata mara ahankali tasoma bude idanunta ganin saman gadon wayam babu shi babu alamusa ta mike ta sauko ta nufi parlour 'n nan ma batagansa ba yasa taji gabanta ya bada wani irin rassss da sauri ta dawo a dakin a tsorace tunanita ko ya sake fita yayi acikin tsakiyar daren amman sai tajiyo saukar ruwa a bandaki hkn yasa ta zauna tana sauke numfashi ,minti biyar tsakani ya turo kofar ya fito tsirara kmr koda yaushe jikinsa ajike da ruwa ala'mun wanka yayi ,tai saurin runtse idanunta ya tsura mata mayatattu idanunsa yana kallonta baiyi tsammanin farkawarta a daidai wannan lokacin ganin yadda take baccin hannusa yasa ya janyo whit towel ajikin kofar bayin ya daura a kugunsa yana cigaba da kallonta.
yanayinsa datagani yasa kirjinta da zuciyarta bugawa da sauri dan tasan me karbarta a hannunsa yau sai Allah ,a sikwane ya dauke idanunsa akanta byn hatsabibin kallo da ya dinga jifanta dashi me cike da tarin abubuwa da dayawa sannan cike dakewa da daure fuska ya dawo mata tamkar asalin abdulkabir din datasani ada can baya , hkn ya haddsawa jikinta daukar kirrma yakarasa bude ma'ajiyar kaya.
ta mike da kyar ta fada bathroom sbd matsinta da fitsarin yayi ,ganinshi haka babu kaya sanye ajikinsa yai matukar tsaya mata rai duk da ba wannan ne karonta na farko data fara ganinsa babu kaya sanye ajikinsa ba, amman tarasa dalilin da yasa yanzu abun ya dameta km ya tsaya mata arai, ko dan daga ita sai shine a dakin batasani ba.
bata fito ba sai data dauki wasu lokuta sannan ta fito ta haye saman gado ta kudundune jikinta bayan ta duba agogo bangon dake manne a dakin ta tabbatar da tsakiyar dare suke, ya bata akalla awa daya kafin ya koma saman gadon ya kwanta tare da janyota zuwa
19, September 2025
Aisha Auwal
Wow