Showing 333001 words to 336000 words out of 420383 words
Chapter 112 - SAI KA AURENI DOLE BY AYSHA A BAGUDU.txt
kadai ne zai saka miki .
a fusace ak ya duban ammi kafin daga baya yace "Wai meye haka ne ammi ?
"Me kike kokarin yi ?
"Ubanka nake kokarin yi mara imani wallahi yau ace ni ba uwa bace sai na maka mummunar addua akan wannan wulakanci daka mata, amman akwai Allah kuma zamu gaya masa zamu kai kukanmu gareshi ..
Ya furzar da iska ta bakinsa me zafi yana duban su'ad dake kwance ajikin ammi tana numfashi sama sama.
a fusace ak ya nunata da yatsansa "kika sake yunkurin hanani abinda nayi niyya abakacin aurena dake.............
zuuuuuuuuuu su'ad ta zame ajikin ammi tashiga fixgo numfashi da kyar tana fitarwa ammi tabita ta rungumota jikinta tana kiran sunanta idan ka saketa mutuwa zatayi bazata ta mutu saima tasamu wanda yafika ta aura shasha wanda bai san ciwon kansa ba .
Shi kuwa ak juyawa yayi ya nufi gurin zeey ya durkusa har kasa bisa gwiwowinsa yashiga rokonta yana bata hakuri wannan al'amarin ya tabbatarwa su'ad tabbas zainab tayi wani abu akan mijinta sbd mijinta ba lusarin namijj bane mijinta ba irin nmj dazai durkusuwa mace bane, mijinta ba mijin tace ba tsayayyen namiji ne wanda baya daukar iskanci sai gashi yau ana fama dashi akan abinda tasan inda yana cikin hankalinsa bazai taba aikatawa ba .
"wannan abu ya gigitata ya girgiza zuciyrta wanda take taji numfashinta yasoma kokarin barin gangar jikinta ammi bata ankara ba tana can ga zagin ak " taji numfashinta ya fara tsarkewa tmkr me shakuwa ,can km ta hau tari ba 'kau'kautawa lokaci daya ta hau aman jini jikinta ya soma sakewa take numfashinta ya tsaya cak kmr ance ammi ta meida idanunta kanta taga jini nan fa hankalinta ya tashi tashiga jijigata shiru aiko ta saki ihu.
"shikenan Abdul kayi nasarar kashe min ita wallahi idan su'ad ta mutu kaima kasan dasanin mutuwa zakayi dan wallahi bazan barka araye ba, da hannuna zan kasheka kowa ya huta tana kuka soma kokarin daukarta dady yakarso agigice ya amsheta daga hannun yana kallonta tabbas bata numfashi .
"ta mutu ko inji cewar ammi?
"haba baraka ki natsu mana bata mutu ba, shi dai dady bashi da tabbas din ta mutu ne ko tana raye ,shi dai ya fadi haka ne dan kawai ya kwantar mata da hankali.
wannan al'amari yasa jikin ak yayi magu mugun sanyi ,take zuciyarsa tashiga bugawa da karfi karfi ya juyo cike da mutuwar jiki zai isa garesu zeey tayi saurin kamo tafin hannunsa cikin nata "my life ina kuma zaka?
ya tsotsa keyarsa domin rasa abinda zai ce mata
suna tsaye suna kallo dady yayi hanyar waje da su'ad ammi tabi bayansa tana kuka mama ce tayi karfin halin binsu hjy kam ko ajikinta .
zeey ta d'an saci kallonsa taga kamar reaction dinsa ya canza muryarta a sarke tace "sai naga kamar hankalinka ya tashi ko zaka busu ne?
ya girgiza mata kai ala'mun aa " yauwa ka rabudasu kawai su karata yanxu kaje kasan yadda za'ayi a meida aurenmu .
"ok ok my zeey duk abinda kika ce shi za'a yi.
shine zance inji cewar hjy, zeey tayi murmushin jin dadi tare da cewa "da ala'mun fa hjy kema bakiyi da wannan yariya.
"ko daya zainab amman kinsa so sone amman sonkai yafi bakiga itama baraka goyon bayan diyar dan'uwanta takeyi ba . nan suka zauna sukayita zagin mami agaban AK amman ko ajikinsa asalima ji yayi kansa na jujjuyawa dan haka ya zame ya kwanta flat tare da d'aura hannusa ya dafe goshinsa dayan hannunsa kuma ya d'aura saman ruwan cikinsa.
Kai tsaye mota aka nufa da su'ad.
general hospital din dake kusa dasu suka nufa daita . suna parking a harbar hospital ammi ta fito aguje tayi cikin hospital tana dictor wani matashin likita tacikaro dashi tashiga karo masa bayanin matsalar da suke ciki "ku taimaka min zata mutu yarinyar tace zata mutu aman jini take..
take doctor saifullahi wanda mutane suka saninsa da dr saif yabada umarni turo gadon marasa lfy aka daurata aka nufi dakin doctor daita
likitoci suka soma aiki akanta da kyar likitoci suka samu aman jinin ya tsaya numfashinta ya dawo daidai kowa yafita aka bar doctor saif shi kadai yana kallon kyakkyawar fuskarta me d'auke da annurin kyau gsky yarinyar nan tashiga ransa matuka wani abu ya dinga ji akanta har tsakiyar kansa haka kawai tunda d'aura idanunsa akanta yaji zuciyarsa ta amsa ya dade zaune yana kallonnta kafin daga bisani ya fita.
ammi da dady zaune a office din Doctor saif yana musu bayani a game da rashin lafiyar su'ad "damuwa ce ta haifar mata da buguwar zuciya wanda ya haddasawa jinita hawa sosai fiyye da yadda ake bukata ,yakamata a dinga kiyaye bacin ranta idan ba haka za'a iya rasata zata tashi amman sai zuwa la'asar godiya suka masa suka fito zuwa dakin da aka kwantar da su'ad .
ammi taci kuka sosai har ta godewa Allah gabadaya ta zabge alokaci daya tayi wata irin rama, sako ta tura umman su'ad tazo suna asibiti da su'ad, tura sakon baifi da minti goma ba sai gata ta iso ammi bata boye mata komai ba domin ta taya diyarta da addua .
muryarta a sanyaye umman su'ad tace "yanzu wani hali take ciki?
"likita yace sai zuwa la'asar zata farfado, shiru tayi tare da karasawa jikin gadon ta dubata, yaushe rabon data d'aura idanunta akan diyarta mafi soyuwa cikin ranta.
kusan minti goma ta dauka tsaye akanta tana kallonta har yanzu kamaninta da mahaifinta na nan, abubuwan data nata basu dayawa tana maseefar kaunar fiyye da kaunar data nuna wa mahaifinta bata kaunar ganinta cikin tashin hankali ta gwamaci maseefa ta fad'a mata akan diyarta kuka ne ya subuce mata aiko tashiga rare kuka abubuwa dayawa suka shiga dawo mata batasan yaushe ne zasu samu hutun rayuwa ita da diyarta, duk fa wannan maseefar dake bibiyarsu itace silar komai datayi hakuri bata biyewa sharrin soyayya ba yanxu tana tare da dangita cikin gatatan .
ammi takaraso ta dafa kafadarta tace "dan Allah salema kibar kuka haka kiyi mata addua samun lafiya jinki.
la'asar har ta wuce amman su'ad bata farfado ba doctor saif ya sake shigowa dakin lokacin ammi kadai ce umman su'ad taje gida ta dawo ,ammi nagani shigowarsa tace" yauwa likita tunda kashigo bari naje nayi sallah kafin kagama dubata.
"badamuwa kawai yace kasancewarsa shi mutun ne miskili bai fiyye son hayaniya ba. ya koma ya jingina bynsa da bango daki ya tsura mata idanunsa yana kallonta yana jin wani irin sanyi dadi ajikinsa burinsa a halin yanzu ya mallaketa matsayin matar aurensa, hannuwansa duka ya rungume akirjisa yana cigaba da dubanta .
fitar ammi da minti biyu ta fara motsi har ta farfado sai dai ta farka ne cikin matukar razana nan ta hau kuka tana cewa ...abdulkabir karka min haka ka dawo gareni ban cancaci wannan wulakancin daga gareka ba idan kabarni mutuwa zanyi ,kadawo ka dawo gareni dan Allah kayi min alqawari zaka rayu dani babu cin amanar soyayya tsakaninmu.
bance karka dawo da zeey ba amman kajidani kabani kulawa ina sonka dayawa bazan iya rayuwa babu kai ka koyardani soyayyarka fiyye da lokacin dana tsinci kaina cikin saukinka .
take gaban doctor saif yabada rasssss yashiga faduwa,
Tari ne ya tsarketa sai km tashiga aman jini daidai lokacin da doctor saif yakaraso gareta cikin sauri yashiga bata taimakon gaugauwa da kyar aman ya tsaya yayi mata allurar bacci wanda a kalla zata kai har zuwa washegari tana bacci .
koda yakoma gida kasa zaune yayi ya kai gwaro ya kai mari acikin tafkaken dakinsa ya dade yana tinani akan sambatun da yarinya ta dingayi , wanda hakan ke nuni da tana cikin shauki soyayya ne da wani har ya kaita ga kwanciya .to idan haka ne meyakamata shi yayi?
"shi dai gasky yana sonta idan ya rasa zai iya mutuwa da kyar bacci barawo yasamu nasarar daukasa amman har lokacin jikinsa bai bar tsuma ba akan yarinyar da bai san kowacece ba...
washrgari har gurin la'asar bata farka daga bacci ba , doctor saif dake kula daita ya tashi aiki amman sam ya kasa tafiya ya barta sai dai yana office dinsa zaune tinaninta yana fixgarsa byn kmr mint talati ya sake shigowa dakin da take kwance har lokacin bacci take ya gaida ammi da mahaifiyar su'ad cikin girmamawa dan duk yadda akayi su din jininta kodaga yanayin yadda yarinyar ke din ban kamani dasu.
sai lokacin ammi tasamu damar tmbyrsa abinda yasa su'ad yin bata farka ba kamar yadda yace "ta farka wani allura na sake yi mata sbd damuwa tayi mata yawa tana bukatar hutu sosai idan ba'a dauki matakin daya dace komai zai iya faruwa daita
ammi ta jinjina kai ita kuwa umman su'ad tagumi tayi tana yiwa diyarta adduar samun sauki
doctor yacigaba da magana "amman ina
ga zarar ta farka komai zaizo da sauki.
atare ammi da umman su'ad suka amsa "allah yasa
karasawa yayi gadon da su'ad ke kwance tmkr matacciya ya dubata ruwan dake daure da hannuta ma ya kusan karewa ya zubawa fuskarta ido take gabansa yashiga faduwa aransa yace "Allah yayi halitta kyau anan .
tunda yake bai taba cin karo da fuskar data tsaya masa azuciya ba kmr fuskar dayake kallo yanzu agabansa .
ya dan tsaya yana jiran ruwan yakarasa karewa ya zare mata gbdy sannan ya wuce kusan minti goma ya kai tsaye sannan ya kai hannunsa da niyar zare abun ruwan yaji wani irin zirrrrrrr ajikinsa tundaga taf karfarsa abinda yaji yashiga yawo ajikinsa da sauri yakarasa cirewa ya yi musu sallama ya fita .
Kwananta uku kwance ba tasan a wani halin take ciki ba, ammi da mahaifiyarta da eiman ke faman dawainiyya daita wanda zuwa lokacin duk wanda yaganta sai ya xubar mata da hawayen tausayi ,ta zabge ta rame tayi fari sosai ta d'ashe .
ta farka a bacci datake taga mahaifiyarta zaune agabanta ta dukar da kanta jikin karfen gadon ahankali takai hannunta ta daura bisa kanta tana furta "ummana ......
da sauri mahaifiyarta ta dago idanunta cike da ruwan hawaye dan ba bacci take ba tunanin duniya kawai ne ya addabi rayuwarta. mikewa tayi cikin sauri zata fita su'ad ta riko hannuta cikin nata "ina zaki tafi kibarni?
"Zanje na kirawo doctor ne yace idan kin tashi azo akirasa, ta runtse idanunta gam tana me zame hannunta .
Tare umman su'ad suka dawo da doctor har ammi dataje siyan magani suka shiga jero mata sannu bata amsa ba sai idanuwa data dinga binsu dashi, shi km likita yashiga aikinsa tare da duba lafiyar bp dinta daya hau sosai sannan yayi mata allura yaso ya tsaya amman ya kasa hakan adalilin tsayuwarsa zata iya fallasa sirrin dake boye a zuciyarsa dan kallonta na ta'ba masa zuciyarsa duk sanda yakusanci indatake yana jin wani iri ajikinsa gashi bai sani ba ko matar aure ce ko budurwa shi dai fatansa takasance budurwa ce jikinsa a sanyaye ya fita .
byn fitar likita ta bude bakinta da kyar takira sunan ammi "Ammi ina Abdul dina ?
"Bai xo ya dubani ba ko ?
Ammi ta sake matsowa sosai ta rike hannuta cike da tsigar rarrashi tasoma magana "kiyi hakuri mamana da wannan iftilain daya samemu amman abinda nake so dake ki cire zance abdul azuciyarki har ki samu lafiya.
Zare hannuta tayi cikin na ammi tare da kawar da fuskarta gefe tana kallon bangon daki hawaye na gangarowa akan pillow da kanta ke kwance .
Ta yaya ammi zatace taciresa cikin xuciyarta alhalin tasan hakan ba abu ne me yiwu ba a gareta .
yadda bazata iya cire numfashinta daga gangar jikinta ba haka bazata iya cire abdulkabir cikin xuciyarta dama rayuwarta gbdy , tasan lokacin mutuwar ce tayi kusa tunda tarasa abdul arayuwarta.
ahankali tashiga kuka sosai dan ita kadai tasan yadda take jin zuciyarta akan mijinta ummantace takaraso daidai kanta su'ad yanzu ba lokacin kuka bane, ba kuka zakiyi Ba abinda ya faru yaridaga ya faru ta lafityarki zakiyi Allah kiyaye gaba.
duk da maganar da mahaifiyarta keyi yana shiga cikin kunnenta amman ko gezo batayi ba kuka take sosai har da shesheka.., idanunta ya sauka akan zoben silver dake makale da yatsan hannunta take tinanin abubuwan da suka faru kafin tafiyarsu zuwa koria har zuwa sanda ya saceta batareda saninta ba ,da yadda ya dinga bata kulawar ta hanyar tsumata da tsumammiyar soyayyarsa me tsayawa arai ,ta tuna wani yammanci ana sauran kwana uku da faruwar komai garesu, ya sata ta tsuke cikin wasu hadaddun kananan kaya tayi rolling kanta da bakin mayafi shima kusan irin shigar jikinta yayi sunyi kyau sosai ya dauketa zuwa wani hadadden shopping mall dake spain ahankali suka jera hannunsu cikin juna ,da kansa ya dinga daukar mata abubuwan amafaninta batare daya d'aukarwa kansa komai ba ,ita km ganin haka yasa ta daukar masa wani zoben silver me shegen kyau me d'auke da harafin sunanta *S*
ta kamo tsinsiyar hannusa tana kallon cikin kwayar idanunsa ta saka masa tare da kissing din hannu atake ya janyota jikinsa ya rungumeta tsam ajikinsa yayi kissing din goshinta yana jin dadin wannan kyautar tayi masa cikin kunnenta ya rada mata" dole nabada tukuicin wannan kyautar idan muje gida.
tayi murmushi tana dukan kirjinsa tare da cewa "Allah banason wannan tukuicin.
ya sake janyota jikinsa sosai shima ya d'auki zobe irin wanda tasaka masa, me harafin sunansa *A*
ya saka mata yayi kising din hannuta har da kari dan sai da yayi kissing din lip's dinta sannan yajanyo hannuta suka sake jerowa hannunsu makale cikin juna ya zagayo ya bude mata kofar mota ita km ta tsaya rungume da hannuwanta duka akirji tana dubansa tana murmushi cike da jikin dadi .
da hannusa yayi mata ala'mun tashiga ta koma ta tsaya bakin kofar motar taki shiga sai ma ta tsaya tacigaba da kallonsa cike da matsanancin kaunarsa.
tsura mata mayatattu idanunsa yayi sosai sannan yace " kallon fa?
"ina kallonka ne sbd tsabar son da nake maka sai km zance na gaba wannnan soyayyar da kake nuna min batayi yawa ba kuwa?
"sbd me kika ce haka? yayi mgnr yana kashe mata idonsa daya hannunsa rike da murfin mota.
ta ciza lips dinta na kasa tana me narkar da fuska ala'mun son yin shagwaba sannan tace "ni dai soyayarce ta min yawa ina jin tsoron fa.
"tsoro fa kikace ..... ya furta hkn yana narkar da idanunsa cikin kwayar idanunta tare da kamo lip's dinsa na kasa yayita tsotsa yana kallonta .
ta daga masa kai ala'mun haka take nufi, itama tana kallon cikin kwayar idanunsa a wannan lokaci tace "ina jin tsoro da fargaba sosai kada wata rana kazo ka juya min baya bansan yadda zanyi ba idan hakan ya faru...
"bazan taba juya miki baya ba arayuwata , yanzu saboda kulawa da soyayyar danake baki ce ta sakijin haka? ta girgiza masa kai tare da kashe masa idanta daya .
" to meye ne aciki kece fa sauraniyar zuciyata , ni km tmkr bawa ne gareki kinga kuwa dole bawa yabawa sarauniyarsa duk wata kulawar data dace duk abinda nasan zai sakaki farinciki zan miki shi matukar bai fi karfina ba sai abu naga bana son kina min zance juya baya .. ....
Ammi ce ta katse mata tinaninta ta hanyar kira sunanta" mamana ki daure nasan abun da kamar wuya ki iya ciresa aranki ,amman ki daure kisawa zuciyarki hakuri duk girman alamari baifi karfin Allah ba kuma muna kan gaya masa .
Tasoma yunkurin mikewa zaune ammi tayi saurin kamota ta zaunar daita hade da sanya mata pillow ta bayanta , hawaye ne suka shiga turereniyar fitowa daga kwarnin idanunta mgn take son yi amman ta kasa bude bakinta wanda koda ta bude bakin ma bai zama lallai maganar ta fito ba.
dan haka ta jingina bayanta tashiga jan numfashi da kyar tana fitawar tana cigaba da zubda hawayen tausayin kanta.
Ummanta ta hado mata tea me kwari ta karaso tare d mika mata cup din tea su'ad ta girgiza kai alamun bazata sha ba.
Ammi ta amsa cup din daga hannunta ta kai daidai saitin bakinta "ki bude baki ki sha mamana tunda aka kawoki asibiti bakisa komai acikinki ba, dan Allah ki tausayamana ki duba kiga yadda nida mahaifiyarki muka dawo akan rashin lafiyarki, ki tausayamana muna bukatarki araye idan kika bari wata cutar takamaki akan abdul mu kika cuta sbd shi bai da hasara rayuwarsa zaicigaba yi ..
Da kyar da rarrashi ammi tasamu tasha kadan ta kawar da kanta tana jin yadda zuciyarta tayi mata nauyi kmr an dora mata dotse ,zamewa tayi takoma ta kwanta tana cigaba da tinanin mijinta tare da tsurawa zoben hannuta ido tana ji kmr alokacin yasanya mata shi .
Acikin satin mutane kawai ke turereniyar zuwa duba jikin su'ad takowani bangare ciki kuwa har da musty wanda ya dawo kasar loakacin dayasamu labarin abinda ya faru yasha mamakin sosai dashi akacigaba da jinyarta.
babu laifi su'ad ta ji sauki sosai sai dai har lokacin doctor saif yaki basu sallama kasancewar baya son rabuwa daita duk da zuwa wannan lokacin yasan matsalar soyayya ce ke d'awainiyya daita amman yana ji aransa zai iya cire soyayya kowaye ya dasa nashi.
sam abdulkabir baiyi yunkuri zuwa duba jikinta ba duk da yadda jama'a sukayi ta zuwa ta bangarensa, wannan abu yayi matukar taba zuciyarta dan haka su'ad ta masa a sallameta ita tagaji da zaman hospital doctor saif yashigo ya iske ana fama daita akan ta tsaya ta kara samun sauki sai shagwaba takeyiwa ammi tana ganin shigowar doctor tayi dif da bakinta .
muryarsa a kasalance yace "ammi kmr yadda yaji ana kiranta dashi "akwai damuwa ne?
"babu wata damuwa likita mamana ce dai ta takura dole gida take
19, September 2025
Aisha Auwal
Wow