Showing 177001 words to 180000 words out of 420383 words

Chapter 60 - SAI KA AURENI DOLE BY AYSHA A BAGUDU.txt

da karfi daga jin yanayin yadda yayi mgnr kasan atsorace yayita na amsa cikin kuka na'am taufeek ...ina ka'ajiye wayoyinka tun shekarajiya nake neman layinka da garari cikin gari ?
wayyohlly Allah nah.... kiyu hkr my louloooo.. yanzu kina ina ai tunda mutumin ya tabbatar min da macece takira wannan number jikina ya tabbatar wani abu .yace yanzu a ina kike?
muryarta cikin kuka nace bansa inda nake ba amman bari nabawa mutumin daya taimaka min .
nakarasa gurin mutumin na mika masa wayar nace dan Allah ka gaya masa sunan gurin nan. karba yayi tare da sanar masa inda muke kai tsaye ya katse kiran batare da ya sake dawowa min da wayar ba. muka tsaya zaman jiran isowarsa.
tun karfe 11 dana kira taufeek banga yazo ba.
hankalina ya tashi sosai yayinda mutumin yaki barina ya wuce sai ma sake neman layin taufeek din yayi ina jinsu suna waya yace ya hanzarta zuwa sbd area babu lafiya za'a yi (etutu) taufeek najin hk yace dan Allah ka taimakeni ka tsaysa min daita ina kan hanyar zuwa ne hoodup ne ya rike.
ni Allah ya yarda zan karaso kafin llokacin da zasu fara kasan woman develoment center? mutumin yace eh ok idan ma zaka wuce ne ka taimaka ka kaimin ita can tajirani yace to .

e'tutu wani tsafi ne da mutane lagos suka meidashi tmkr ibada ko al'ada kusan sunayinsa ne domin zaman lafiyar garinsu acewarsu tsafin yafi son ya'ya mata domin idan suka hadu da mace zasu mata tsirara haihuwar uwarta sannan su yankata yankan rago su tsiyaye jininta ,acikin kwaryar tsafinsu .
idan km namiji ne zasu masa dukan mutuwa da bulalar tsafi wani ya rayu wani km sai yayi doguwar jinya sannan ya dawo yasamu lfy .
suna fara wannan tsafin nasu ne da kmr misalin karfe daya saura .
ina jin mgnr da mutumin ke fada hankalina ya sake tashi jikina ya dauki rawa muka soma tafiya.
tafiya muke a kafa yana sake bani labarin yadda ake (e'tutun ho'ro) har muka kawo menegement yana cigaba da bani lbari wanda sai alokacin na tmbyi sunansa yace min hasan muna tsaye gaban get din woman development center muka tsaya daga gefe titi muna tsaye wani gang na yoroba people's suka zo suna hayaninya da iwace iwace daga karshe suka ja birki sai muka zage zage da tsine can km fada ya kaure tsakaninsu suka shiga bata kashi .
ban da fashe fashen kwallabe babu abinda suke sauran tsirarrun mutane dake bakin titin suka soma darewa lokacin da aka lumawa wani kwalba a gefen cikinsa ga hanjin mutun muraran kana gani ga jini na tsiyaya kmr ruwa ai nima bansan sanda na kwallara kara na kwasa da gudu nayi hanya me zuwa badagir shi km hasan bansa hanyar daya bi ba .

gudun nayi sosai kmr zan bar garin daga karshe na tsaya ina sauke numfashin ganin nayi nisa da gurin banda numfashi da haki hmmmmmmm hmmmm babu abinda nake nasamu wani jikin wani table na jingina kaina sbd kasa tsayuwar nayi yayinda naji marata tayi wani irin daurewa tare da murdawa ina nan tsaye agurin har daya tayi bansani ba matsafa har sun fito sun soma abubuwan tsafinsu a wasu wuraren motsi nasoma jiyowa na sautin muryoyi mutane daban daban suna fadar wasu abubuwa cikin harshen yarobanci wanda ni alokacin bansa me suke cewa ba sai daga baya nasan maa'anar su.
amman jin muryoyinsu kadai ya isa tsoratarwa tare da firgitar da zuciya, nayi saurin mikewa daga jinginar danayi nashige karkashin wani table na buya yayinda mutane suka cigaba da kusantowa inda nake sai alokacin naji hantar cikina ta sake kadawa fiyye da tsamaninki kowanensu tsirara haihuwar iyayensu daga mazan har matan kmr dai yadda hasan ya sanar min sannan hannuwansu rike da tukwanen kasa.
" jikina ya dauki kirrmm abinda ban taba gani ba kenan tun iya tasowata byn taufeek ban taba ganin tsirancin wani ba lokacin da suka zo kusa da inda nake boye naga sunja sun tsaya nayi saurin sake lullube ilahirin jikina da bakin hijabina ta yadda bazasu hangoni ba .
ahankali naji sautin daya daga cikinsu yace
(o'ju meji po'gbod'o fuju ko'nwa)ma'ana ido biyu bazai tabaganinmu ba dube dube yasoma sauran suna tsaye cak batare da sun waiga ba duk idon daya lekemu tsirara idon meshi zai fashe sauran suka ce (ashai)ma'ana ameen duk wanda yasan ya ganmu ya buya ya fito daga mabuyarsa ..
daidai tsaitin danake durkushe naga an haske da torchlight me shegen haske.
ganin tabbas dai sun ganni sannan na tuno da yadda hasan yabani labarinsu aiko na fallo aguje ni kaina bansa zan iya irin gudun danayi ba aiko suna ganin hk majiya karfin cikinsu suka biyo bayana aguje tmkr iska.
gudu nake suna bina ina kuka da kururuwar neman dauki suna bina da iyakacin karfinsu. aguje naga wata mota ta tsaya cak agabana na .
aka bude motar me shi ya fito na xube jikinsa sai km numfashina ya dauke kamshin turarensa ne yasani zabura na zauna da kyau shi km sai kokarin rivaerc yake sannan yaja motar ya kwasa da gudu. mukar gurin.
gudu kawai motar ke sharara akan titi .
bashi yarage gudun dayake ba sai da muka shigo cikin agege yasamu guri yayi parkin ya juyo gareni ya janyoni zuwa jikinsa ya rungumeni tsam yana furzar da numfashin yasoma mgn cikin kuka dana rasaki sanadin tsafin nan banza yadda zanyi ba .
kuka yake sosai har ds sheshekar kukansa bakaramin wahala naci ba lokacin danazo inda nace ku tsaya naga ala'mun fada akeyi dan har yansanda sunzo wajen shine nakira number mutumin shine yace min kinbi hanyar badagir na lumshe ido kawai dan bazan iya mgn ba daga nan gidan wani abokinsa ya zarce dani dake agege byn ya kirasa awaya .
koda mukaje nayi wanka mukayi shirin kwanciya sannam nasoma bashi labarin abinda ya faru madadin ya nuna bakincikinsa ko damuwa sai kawai naji ya rungumeni daman na tsamaci hkn daga gareki.
lokacin dana gaya masa abinda custom din nan yaso min ya firgita yace washegari sai na kai shi gurin nace bazan iya ganewa ba nan muka kwanta ranar kam nayi bacci har da munshari a saman fadadden kirjinsa wanda bazan iya tuna when last nayi bacci me dadin irin na ranar ba

byn kwana biyu ina kwance ajikinsa ya kira mahaifiyarsa akan zaizo gurinta ni kam dai bansa metace masa ba ya dai ce na shairiya cikin jallabiyar da siyomin muka nufi gidansu. babban gida ne dan yayi kusan namu sannan gini ne nazamani daganin gidan dai kasan namasu arziki ne.

muna isa gidan mahaifiyarsa muka isketa zaune akan kujerar one siter tana kallo tv hannuta rike da casbaha tana jawanda ya nuna ala'mun lazimi take da sallamar ya isa cikin parlour'n mahaifiyarsa ni km ina biye dashi abaya jikina na rawa .
yakarasa har inda take ya durkusa har kasa ya gaisheta hjy ya gida cikin fara'a hjy takarba tace a'a har kakaraso ?
inda kakirani kace min gaka nan zuwa ban tashi ba nan kazo kasameni.
yayi shr ahankali yayi min nuni dana karaso gurinta hk jikina na rawa na nakaraso na durkusa kmr yadda yayi muryata na rawa nace hjy ina yini.. da hausata da bata gama kwarewa ba.
wani irin kallo tamin wanda yasa hantar cikina kadawa batare da ta amsa ba ta waigo zuwa inda taufeek ke zaune tace wacece wannan km?
yayi shr yana kallonta kamin mgn man yakake kallona kmr wanda bashi da gasky?
ya sosai keya eh um hjy salema ce...... yana gama fadar hk ta sake hade ranta sosai sbd tasan kwanan zance. shiru ya dan ratsa parlour can hjy ta maida idanunta kan tv tana kallon shirin da'ake gabatarwa.
sannan tace ina fatan dai lfy ko akwai abinda ke tafe da kai naga ka tasota gaba kunxo ..?
ta jera masa tmbyr shafa keyarsa yayi sannan ya dago cikin sanyi da yanayin kunya ya fara mgn am... hjy.... daman.. sai km yayi shr ya fara in.. ina, ni kuwa duk inda tashin hankali yake ya kawomin ziyara tare da mamayr ilahirin jikina .
yayinda tsoro na neman farmakar rayuwata rawar da jikina yake yaki boyuwa hk kawai na dinga jin faduwar gaba maramisaltuwa.
sake hade rai hjy tayi tamau sannan tace ka kwantar da hnklinka kasanardani abinda ke tafe da kai ina sauraronka da kyar yasamu nasuwar zuciya ya fara mgn daman wannan ce saleema yarinyar danagaya miki na hadu daita a Cotonou........ ba wace mahaifinta yayi maka wulakacin karshe ba sannan ya hanaka aurenta yace wani zai bawa to yanxu me tazo nema gurinka ta katse masa hanzarin gurin fadar hk,
ko ba abinda kake son sanar min ba kenan? yayi shr ina jinka ko byn wannan akwai wani abu? mgnrta kawai take tmkr batasan da wata halita agurin ba.
sai daya numfasa sannan yace daman akwai matsala ne shiyasa tazo amman mushiga ciki muyi mgn babu inda zani kayi mgnrka anan duk abinda zamu tautauna tasan dashi bawani sabon abu bane .
hk kawai ya tsinci kanshi dakasa gaya mata zance cikin jikina sai naji yace tazo ne akan zance aurenmu daita... baka da hakali nace baka da hankali balle tunani taufeek yanxu yarinyar da kasha wulakacin ubanta dan kawai kace kana sonta..
ina ita yarinyar take ta juyo tana kallona ?
ni km nasake dukar da kaina kasa ince ga iya abinda kake haukan so da kokarin kashe kanka akanta ,wallahi idan ni keda irin matarka banga abin so anan ba dan hk ka dauketa kubar min gida tun ranka bai baci ba rawar jikina yake ya sake bayyana yayinda idanuna suka cicciko da ruwan hawaye tana gama fadar hk ta mike tashige cikin dakin .
ya mike tsaye da sauri yabi bayanta hyj karkice hk nagaya min komai akan yarinyar ne sbd kisan irin son danake mata bawai dan naji haushin abinda mahaifinta yayi min bane yasa nagaya miki abinda ya faru ....
ai bazakaji haushinsaba tunda ka makance akan diyarsa,
" dubeka sama da kasa "ya" kota shugaban kasa ce za'abaka aurenta balle wannan me kama da baroro.. ya matso gareta ya zauna tare da kamo hannuta ya dukar da kashi yakira sunata zuciyarsa na wani irin mahaukacin bugu hjy yarinyar, ciki gareta.. shine dalilin zuwanta mahaifinta ya koreta daga gidansa... daya koreta sai akayi yaya ?ta fada da sautin karfi har ina jiyota .
hjy kiyi hkr kisa fahimta narigada na miki bayanin komai tun dawowata da abinda yashiga tsakanina da yarinyar nan bisa kaddara ina ji ajikina cewa wani babban al'amari zai sameta ko bayyana ajikinta byn tahowata shine silar dayasa na sanar miki sbd banida wacce tafiki..
kai yanxu ka tabbatar da cikin jikinta naka ne?
yayi saurin girgiza mata kai ala'mun eh to ban yarda ba wallahi ,kawai sbd kana haukan sonta ne yasa kike kokarin amsar cikin jikinta duk macen data iya bawa nmj jikina tun a waje ina tabbatar maka zata iyabawa kowa ma kafin kai kasan maza nawa tyi mu'amula dasu?
yayi saurin durkushewa kasa wallahi yarinya ce wace batasan komai ba ni nan na fara .
tsawa da buga masa ne yasa yayi shr wanda yasa nima mikewa tsaye daga durkuson danayi na daura hannunwana duka bisa kaina sbd daga inda nake ina iya jiyo sautin muryoyinsu karka soma ce min wannan cikin na jikinta naka....sbd bazai taba yiwuwa ba ina raye a haifamin cikin shege acikin gidana wallahi tun yanzu karaba hanya da wannan yarinya tun kafin na tsine maka km muddin ina raye bazaka taba auren wannan yarinyar ba sai dai idan mutuwa zakayi kayi .
dan hk maza maza ka dauki wannan fasa gurbin ka bar min gida yanxu ...
"takarasa mgnr tana nuna masa hanyar fita ni kuwa zuwa lokacin hankalina yayi kololuwar tashi banda bugu babu abinda zuciyata da kirjina keyi yayinda ilahirin jikina yacigaba da rawa karrr karrr take naji wani abu ya tsarga min ta kasan marata sai km marar ta kulle gam wanda yasa tsayuwa ta gagareni ina daf da kaiwa kasa naji motsin fitowarsa yayi saurin karasowa gareni yana kiran suna salemat.. salemat.. meke damunki yasoma kokarin mikar dani jin hk yasa hjy fitowa tana mgn zaman me kuke min da har yanxu baku bar min gida ba turuss tayi sanda taga taufeek rungume dani duk ya birkice sai fama tmbyta yake abinda ke damuna ai ina daura idanuna akanta na nemi ciwon da marata yake narasa na kwace jikina daga nasa nasoma daga kafufuna da suka gama sagewa na isa inda take tsaye tana auno mana kallon wulakacin na durkusa bisa gwiwowina hawaye na gangarowa bisa kuncina tare da hade hannuwana duka na dukar da kaina kasa ina wani irin kuka me taba zuciyar ma'aboci sauraro kiyiwa Allah da manzonsa hjy karki dauki laifin mahaifina ki daura min da cikin dake jikina. nake kaunar taufeek dinki ba mahaifina ba... nike son rayuwa tare dashi ba babana.... iyayena sun sallamani akanshi idan bazaki duba soyayyar danakewa taufeek dinki ba ki duba darajar cikin dake jikina na gudan jiniki ..ki taimakeni ki taimaki rayuwata da cikin jikina wallahi taufeek sheida ne.. ban taba mu'amula da wani nmj ba byn shi yasani bankasance mazinaciya ba.. bansa yadda ake aikata ita kan zinar ba ,sai taufeek ya shigo cikin rayuwata na juyo inda taufeek yake tsaye ina kiran sunansa kayiwa hjyrka bayani ta gamsu ni bamazinaciya bace.
ka bata hkr ta bari ka amshi cikin jikina koda bazaka aureni ba ni yanxu na sadaukarwa duniya farincikina tunda iyayena suka kasa daukar kaddarata ko me mahaiifiyarka zatace min bazai dameni ba.
" amman zance cikin bazan lamunci rikeshi ba alhalin yana da ubansa ina karasa fadar hk nasoma kokarin karasawa gurin mahaifiyar taufeek ina kuka ina rokonta tabari danta ya aureni ,ni ba mazinaciya ba cikin jikina km na tilon danta ne.
amman matan tayi buruusss dani sai ma sake maimata kalmar data gaya masa a daki take .
muna cikin wannan halin matarsa ta shigo a haukace kmr an korota bansa yadda akayi tasan da zuwanmu ba .
" kawai ta tsura min ido tana kallona babu wani bata lokacin ta sheidani bata manta fuskata ba ina ganinta naji zuciyata ta buga da matsanacin karfi amnan na kudircewa raina, zan jure duk wata azabar rayuwa indai zasu amshi cikin jikina .
zuwan matarsa bai saka hjy fasa mgnrta ba taufeek.... takira sunansa a matukar fusace nace ka dauke min wannan yarinyar kabar min gidana daita wallahi zan iya tsine maka sanadin wannan yarinya wallahi wallahi kaji rantsuwar dan muslimi matsawar kenan ,kaga ka Auri yarinyar nan sai dai bana duniya.
gbdy na daburce narasa yadda zanyi jina ya dauke kwalkwaluwata ta tsaya cak ta Daina aiki Nasoma fige fige ina zare ido tmkr me cutar hauka ina kallon fuskar taufeek so nake ya tabbatar min maganganun mahaifiyarsa duka karya ne ba gaske ba....
na kamo hannunsa na rike gam cikin nawa muryata na rawa nace taufeek gaske ne abinda naji mahaifiyarka na fada wai bazaka aureni ba ..? kafin yace wani abu nasoma jan gwiwona zuwa inda matarsa ke tsaye tmkr andasata nace kiyiwa Allah da manzonsa kisa baki hjy ta amince kiyi hkr nasamu muhalli agidanki mijinki kawai nake da muradi auren zan kai hanuna jikinta tayi saurin ingizani zata daga hannunta ta sauke min mari taufeek ya rike hannun tare da cewa karki soma wannnan ganganci, nace dan Allah kabari ta mareni matukar zata bari na auri mijina bazan taba damuwa ba. gbdy na gigice ina ta basu hakuri sai alokaci nasan ba mahaifina kadai keda ra'ayin rekau ba..
nasake dawowa gurin taufeek na rike hannunsa kace karya ne wai bazaka aureni ba.
ya rike hanuna dake cikin nasa sosai sannan ya bude bakinsa yace min eh hk mahaifiyata tace amman ni ina sonki tare da cikina dake jikinki .
yadda na tabbatar miki a can baya ina sonki bazan gujeki ba har yanxu hakan ne acikin zuciyata.. ina sonki sale..... tsawar hjy ce ta katse shi ya kasa karasa mgnr .
dauketa nace..... ita matarsa kuwa cewa tayi muddin tana raye itama bazamuyi aure ba sannan takara da cewa taufeek ina sake tabbatar maka wannan ba matarka bace daduronka ce .
amman indai aureta ne sai dai kayi sa alahira idan anayi ,amman ba anan duniya ba. amman a duniyarmu sai dai wannan ta zauna matsayin karuwarka a tana gama fadar hk ta juya cikin matsanacin kuka tashige dakin hjy tace yanzu taufeek agaban matarka kake cewa kana son wata da nuna kulawa da tsantsar soyayya..?
ahankali yace hjy yazanyi kece mutun ta farko dazaki fahimceni amman kika juya min baya kamoni yayi zuwa jikinsa ya mikar dani idanun nan nasa sunyi jawur dasu bai taba tsammanin wannan ranar zatazo masa ba .
bai taba tunanin mahaifiyarsa zata kawo masa matsala a soyayyarsa da salema ba. yasan tayi hkn ne sbd farinciki mee'ad if not hjyrsa me matukar son farincikinsa ce .
"lokacin dana mike tsaye yasoma tafiya dani marata ta sake tsargawa ta rike gam nayi saurin dafe gurin sbd radadin azabar dana ji .
sai km ga jini ya shiga biyo fafuna na tsaya cak na kasa tafiya jikina na rawa .
ganin hk yasa taufeek ya daukeni agaban mahaifiyarsa wanda wannan abun dayayi min ya sake jefa zuciyata cikin tafkin kaunarsa ,km hkn ya sanyaya min raina ko babu komai ya nuna mata irin son dayake min.

kai tsaye hospital din wani amininsa ya nufa dani likitoci suka ce masa ina bukatar hutu ne idan ba hk cikin dake jikina zai iya zubewa dan har yafita daga cikin mahaifata ya koma byn mahaifa.
ina kuka wiwi cike da tashin hankali nakira sunansa muryarta a raunane taufeek....ya dago idanunsa da sukayi ja yana kallona tare da son jin abinda zance, kayi hakuri kabari a cire min cikin nan .......
sbd me?

sbd ingantuwar rayuwarmu data cikin domin shine first step

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login