Showing 183001 words to 186000 words out of 420383 words
Chapter 62 - SAI KA AURENI DOLE BY AYSHA A BAGUDU.txt
office dinsa hankalisa a tashe sbd yasan da dawowar abokinsa ranar dan shine ma zaije airport ya daukosu .
direct motarsa yashiga aguje yakama hanyar zuwa gidana dan baya son naga abinda ya faru sbd condition din danake ciki.
ya karaso daidai kofar dakina kenan yaji sautin ihuna cikin matsanancin tsoro take yashiga ihun kiran sunana yana murda handle din kofar ,sai dai kofar a rufe take kmr yadda taufeek yabani umarnin na dunga kulleta akoda yaushe .
ta window yazagayo ya hangoni a sume a kasa ya koma ya nemo jama'a aka tayasa balle kofar ,ya daukeni raina hannun Allah sai asibintinsa.. aka shiga bani taimakon gaugauwa sai danayi kwana biyu a sume sannan na farfado bakina dauke da kalmar inna lillahi wa inna ilaihi rajiun ,cikin matsancin kuka ina kiran sunan taufeek ....
sai lokacin nasan inda nake a she hospital din Doctor rak ne.
iya tashin hankali nashigeshi nayi kuka har na galabaita hawaye ne kawai ke zuba daga cikin kwarnin idanuna dan ko iya matso hawaye daga idanuwana ban iyawa sannan an daina jin sautin kukana.
tsawon sati daya ina kwance a hospital ana jinyata ,doctor rak ne tsaye akaina yana rarrashina da bani baki.
kallon bakinsa kawai nake amman zuwa wannan lokacin bansan me yake cewa ba, gani yayi da ala'mun bana cikin hankalina yasa ya kai hannunsa ya taba fuskata yaji wani irin zafi, tashi yayi yaje ya hado min ruwan zafi daidai yadda bazai kune min baki ba.
ya dawo yayi tsaye akaina ya miko min ko kallon inda yake banyi ba hawaye nacigaba tsiyaya.
muryarsa a sanyaye naji ya kira sunana saleemat... kmr yadda taufeek ke kirana dashi, still ban waigo na dubi inda yake tsaye ba.
"yace kiyi hkr da hukuncin da Allah ya zarta miki akan rashin abokina da kikayi.
"hakika nasan duk wanda zaiji zafin mutuwarsa byn ke da mahaifiyarsa ne sai km yar'uwarsa.
"amman ina son kiyiwa darajar Allah da darajar cikin masoyinki taufeek dake jikinki kici wani abu sbd kare lafiyar baby.
"ki duba kiga yau tsawon sati daya kenan bakisawa cikinki komai ba ,idan wani abu yasamu cikin jikinki me zaki kalla amatsayin taufeek dinki?
wannan mgnr da yayi shine ya dawo dani cikin haiyacina na waigo inda yake ina kallonsa.
sannan jikina na rawa na mika masa hannuna.
ya mika min kofin tea din, na amsa na kafa cup din abakina ban cire ba sai dana shanye tass, sannan na mika masa ina runtse idanuwana.
aiko gama shan tea na ke da wuya "yar" cikina tayi wani murdawa da karfi daman tun lokacin dana riski kaina cikin tashin hankali, ban sake jin motsinta ba sai a wannan lokaci dana gama shan tea .
bayana da marata ne suka rike alokaci daya , na dinga jin tmkr ana sara min bayana da gatari, ga wani azabar ciwo dana dinga ji from know where.
ahankali na sake runtse idanuwana gam gumi na karyo min ta koina ajikina, doctor rak naganin hk yashiga tmbyta .
ni kwata kwata na kasa mgn .
sai sake maimaita kalmar inna lillahi wa inna ilaihi rajiun nake jikina kuwa sai faman kirrrma yake wani tashin hankali ne ya sake ziyartata lokaci daya wanda yasa da kyar nake iya janyo numfashina .
bell din jikin bango naga doctor rak ya danna sai ga likitoci maxa da mata akaina ya bawa wata doctor damar ta duba masa lfyta.
cikin kwarewa likinta wacce tasan aikinta , ta gano na kudace ta kamani .
ai ko take batare da bata lokacin ba ,akayi dakin haihuwa dani.
byn uwar wahalar dana sha gurin nakudar haihuwarki sannan aka samu kikazo duniya .dan akalla sai dana shude sama da awa goma nasamu kaina .
aka fita dake domin agyaraki nima akimtsani.
wani dakin aka kaini domin hutu sannan aka kawo min ke, kina rike a hannuna na tsura miki ido ina kallon tsarin halitar da Allah yayi miki kyakkyawa ce tmkr mahaifinki yayi kaki komai irin nasa kika dauko babu abinda kika dauka nawa hatta yatsun kafafunki dana hannu irin nasa ne.
hkn yasa lokacin dana daura idanuna akanki na dauki son duniya na daura Mike, naji duk duniya babu me rabani dake soyayyar danakewa mahaifinki na tattara na daurata akanki. ranar da muka cika sati daya
Doctor rak ya tmbyeni wani suna za'a miki huduba dashi ?
zance mahaifinki ne yashiga yawo cikin 'kwalkwaluta idan yace mace na haifa sunan mahaifiyarsa zai sa idan km nmj ne sunan mahaifina.
,dan hk nayi kokarin cika masa burinsa " ahankali nacewa doctor rak yayi miki huduba da sunan mahaifiyar taufeek su'adullahi . ..
km a ranar ne doctor rak yake gaya min wai yaje gidansu taufeek ya iske mahaifiyarsa da yan'uwansa cikin halin damuwa .
nan docto rak yashiga bani labarin halin da mahaifiyar taufeek ta riski kanta lokacin da labarin mutuwar taufeek ta risketa .
kusan zaucewa tayi tana kuka .
inna lillahi wa inna ilaihi rajiun shine abinda hjy mahaifiyar taufeek ta dinga furtawa, jikinta sai faman rawa yake ,wani irin tashin hankali ne ya farmaki rayuwarta da kyar ta iya tashi zuwa inda tangameme hoton tilon d'anta yake ajikin bagon dakinta tashiga kallonsa.
" Muhammad taufeek dina na yafe maka duniya da lahira baka min komai ba sbd kai yaro ne na gari me biyyaya wanda baka taba sabawa umarnina ba .
a koda yaushe kana 'kokarin yi min biyayya,, "Allah ya gafarta maka yasa ka huta.
"Allah yasa aljana ce makomarka kai da iyalinka.
hk hjy tashiga yiwa taufeek addu'oi tare da yabawa da fadar kyawawan hallaiyansa. kwana biyu tsakani yayar taufeek din da suke uwa daya uba daya tazo nan fa kuka ya dawo sabo.
doctor rak " yace min yana zaune agurin byn ya baro gurin zaman makoki lokacin da yayar taufeek ke sanarwa hjy labarin ai muna tare dashi bamu rabu ba.
km har inda cikin wata bakwai .
nan hklinta ya sake tashi ta dinga kuka aje azo mata dani zata amshi cikin jikina wayyohhly Allah ..meyasa na hanashi auren muradin ransa..?
gashi yanzu na rasa d'ana da jikokina da diyata yanxu bani da komai sai cikin jikin yarinyar nan dana hanashi aurenta .
dan Allah kuje kuzo min daita ina son cikin jikinta "kuje ku amso min jinin d'ana taufeek hk ta dinga sabatu tana kuka ranar kwana sukayi a hospital sbd rikicewar datayi.
yace min yaso gaya musu inda nake amman yace sai ya nemi izinina kafin yasanar musu da komai .
yana kai wa karshen mgnrsa .
"nace kar ya kuskura yasanar musu da inda nake sbd su'ad diyace ni kaidai bata da wani dangin uwa balle uba nice komai nata a duniya da lahira.
"yace meyasa zan fadi hk?
"nace masa bisa abubuwa dayawa amman bari kaji kadan daga cikin dalilaina.
" duk mutumin dayace bai sonka baxai taba sonka ba har duniya ta nade , sannan yanzu rashin d'anta da jikokinta datayi ne yasa take bukatarmu arayuwarta .
lyace salema kiyi hkr ki tausaya rayuwar hjy kodan kada duniya ta sheganta min yarinya , ki bar yarinya ta taso cikin danginta.
"ni ko nace sam bazan taba mikaki ba duk runtse duk wuya ina tare dake.
babu yadda doctor rak bai so yayi comfuse dina ba amman naki yarda duk ta inda biyo nima sai na bullo masa da nawa dalilin, daga karshe yace na zauna nayi nazari sosai akan mgnr.
sannan yacigaba da bani labarin" salemat ki godewa Allah masoyinki yasamu sheidar arxiki takowani bangare mahaifiyarsa da danginsa har ma mutane gari abin sai yabaki mamaki .
wajen zaman makoki ma hk jama'a sukai ta zuwa wani mutun yazo yana kuka yace asirinsa ya tuno shekaru sama da biyar kenan taufeek ne ke dauke da cinsa dana ya'yansa da nauyin karatun ya'yansa.
hk ma wani mutun shima yazo ya kawo kudi kimanin dubu dari yace taufeek ne yabashi jari ya dinga juyawa yasamu abin ciyar da family dinsa.
koda aka duba diray dinsa aka ga sunan mutumin amman shi kyauta yabasa hk makarantu islamiya da masallatai suka dinga fadar irin taimakon dayake musu abin ni kaina sai da yabani mamaki sbd bai taba sanar min ba.
kuka nake sosai lokacin dayake sanar min amman km naji dadin aikin alkhari dayayi arayuwarsa.
watana daya cif a hospital din Doctor rak aka sallamomu muka dawo gida, duk a karkashin kulawar dr rak duk wani abun amfani dana bukata ya tsiya mana.
"sosai yake bamu kulawa tare da bata lokacinasa tare dake wani lokacin yayi kuka wani lokacin km naga yana kallonki yana murmushi.
airin tashin hankali da hjy ta riski kanta ciki, ciwon zuciya yayi nasarar kamata yayinda hawan jininta ya tashi zanga zanga sugar'nta ya hau sosai babu abinda take furtawa sai kuzo min da yarinyar da taufeek yayiwa ciki wallahi ina son cikin da yarinyar zata haifa .
ku taimaka ku kawo min ita tun ban mutu ba ,nan fa likitoci suka ce ayi mata abinda take so idan ba hk ba za'a iya rasata.
nan fa hankalin yan'uwa yayi mugun tashi aka baza nemana duk kasar da taufeek ya rubuta acikin diary dinsa muje tare dashi, babu wanda basu je nemana ba amman basu samu nasarar ganina ba .
daga karshe har kasata Cotonou sukaje da taimako address din gidanmu dake rubuce acikin diary dinsa .
nan ma sabon tashin hankali suka riska domin an tabbatar musu da banzo ba, hk suka dawo jiki a sanyaye.
ko lokacin sai da doctor rak ya tasani gaba da magiyar na taimakawa rayuwar hjy kar ta mutu nabari ya bayyana ni garesu ,na saka masa kuka wiwi "nace bai kaunata bai jin tausayina na sake tabbatar masa koda taufeek din ne zai dawo duniya bazan bashi diyata ya kaiwa hjy ba, ballantana baya raye, ka manta lokacin da nake kuka da idanuna ina tokonta akan ta tausaya min tabari d'anta ya aureni ,amman taki babu abinda taufeek baiyi ba dan ganin ta amince da aurenmu ta zubawa zuciyarta rashin imani amman shine yanzu zaka dinga son tillasa zuciyata akan nata muradin.
"wallahi wallahi doctor rak ko duk duniyar nan gatan hjy ne ko sama da kasa zasu hade ko mutuwa hjy zatayi sai da ta mutu amman ina tabbatar maka idanunta bazasu taba ganin diyata su'ad ba ,nasan su'ad jinin d'anta ce amman ta haramta gareta .
"banki idan su'ad din ce taso ganin danginta ba. shima ina tabbatar maka sai na kawar da tunaninta akansu.
jikin hjy yayi tsamari sosai zuwa lokacin zuciyar har tasoma kunbura idanunta sun kunbura sai an kwantar sai an tayar, hnklin yan'uwa dana diyarta data rage mata a duniya ,ya sake tashi babu abinda take iya cewa sai akawo min saleema da cikin jikinta .....
dan girman ku kawo min cikin jikin salema ina son..
wallahi matsawar banganta ba mutuwa zanyi, zan mutu, karku bari na mutu banga salema ba da cikin jikinta ba.
dr rak kuwa tunda ya damka min documents din gidajen da taufeek ya siya da sunana ,na gujeshi sbd lura danayi yana son tillastani akan kaiwa hjy ke, alhalin bazan iya ba dake ba .
dan hk na baro wancan tsohon gidan namu na dawo nan nacigaba da rayuwata ina baki kulawar data dace sauran gidajen na zuba yan haya da taimakon lawyer sa, domin amfanin da kudin gurin taimakawa rayuwarmu ni dake.
lokacin da taufeek ya kai shekara 4 cif da rasuwa itama hjy tace ga garinku byn doguwar jinyar datayi agida da hospital ,ta rasu batare da burinta na ganina da abinda na haifa ba .
lokacin da kika shekara biyar na hadu da hasan a kasuwar oshodi ,naje yi miki tsiyar kayan sallah, ban ganshi ba sai shi ne ya fara ganeni .
naji dadi sake ganinsa danayi, shine fa na kawosa gidana yaga inda nake ko alokacin sai daya tmbyi taufeek nagaya masa komai har labarina, yayi mugun tausaya min dan har kuka yayi, daga nan wannan lokacin mukashiga zumunci dashi .
har wata rana dayazo nake nace masa yayi aure man zama hk babu dadi .
"yace min ai yana da mata agarinsu har da yara guda biyu ,amman dai yana son yin aure anan amman tunanin kudin haya yake yi.
dan bashi da karfin kama haya.
take nace masa kar ya damu da gurin zama idan yasamu mata yayi aurensa ga flat nan abaya yazo ya tare da amaryarsa yaji dadi sosai yashiga yi min godiya .
nan fa yayi aurensa tun daman akwai wace yake so iyayenta sun dameshi da zance aure rashin gurin zama ne yasa yaki meida hankali.
da dabara na tura hasan zuwa garinmu domin binciko min yadda dangina suke rayuwa byn babu ni .
watansa biyu acikin kasar cotonou ya dawo min da labari iri iri wani naji dadin faruwarsa wani km kuka yasani sosai.
"mkr labarin mutuwar hjy babba dana dangina wayanda suka cigaba da rayuwarsu suka manta dani.
har number gaddafi yayana hasan yazo min dashi, wai ana yawan turosa Nigeria aiki a medical hospital din dake cikin sam .
abinda yasani jin dadi km labarin hjy harira da take tsaka da hauka tuburan acikin garin zugu har da tsince tsince abula tana tonawa kanta asirin abinda ta aikata , wanda hkn ne yayi sanadiyar yayyena duka ukun suka saki jikokinta, sannan dayawa daga cikin ya'yanta dake gidan miji aka sako mata su .
zaman mu lfy da hasan da matarsa wad'anda ke tsananin mu biyayya, "wani lokaci Hasan yake bani shawarar nayi aure, amman nace masa babu mgnr aure araina .
shi kuwa wani sabon auren ya kara ,tarewar amaryar bai fi da wata uku ba akayi wani mummunar hatsarin kwantaina akan bridge din oju elaigba.
kwntaina ta fado akan motocin dake kasan titi har da mutane yayinda hasan yakasance daya daga cikinsu .hk aka zomana da gawar hasan jina jina,domin ko wanka bayi masa ba sallah kawai akayi masa aka kaisa makwancinsa.
wayan nan matan guda biyu na cikin flat din baya duk matan hasan ne shiyasa duk lokacin da kikace a koresu daga gidan nan suna zaginki suna miki habaici nake sharewa da zance bawai dan zagin da suke miki bai damuna ba.
sbd suna cin darajar abu daya hasan ..sannan tun tasowarki kin bude ido kingansu ne acikin gidan nan, shi kasan hasan kun shaku dashi sosai fiyye da tunaninki yana sonki yana baki kulawa.
,kin taso cikin kulawa da farinciki, uwa uba natsuwa da hankali duk wanda yaganki yana sonki da son mu'amula dake, har lokacin dakika gama secondry school dinki.
shigarki jami'a da shekara daya komai naki yasoma dagulewa daga karshe naga kin dawo min wani iri.
tun daga wannan lokacin na riski rayuwarki cikin shaye shaye da fadace fadade da jama'a wanda ada bakya yi.
"km tun a wannan lokaci nayi bankwana da farinciki har zuwa yanxu danake baki labari....
lokacin da ummun su'ad takawo karshen labarinta ita kuka su'ad kuka aka rasa wanda zai rarrashi wani cikin uwa da "ya" su'ad ta mike tsaye jikinta a matukar sanyaye tana cigaba da kukanta har da shesheka.
kenan zargin mutane unguwarsu akanta ya tabbata gsky ne ita din shegiyace yar gaba da fatiha ....
abinda tafi tsana da kyamata kenan arayuwata ,shi akayi akasameni .
wayyohlly Allah nah... ta fadi hk a bayyane tare da daura hannuta duka bisa kanta wani irin kuka me taba zuciya ta saki. umma ta karaso gareta itama kuka take ta rungumeta kiyi hkr diyata karki dajeni dan kinji abinda muka aikata da mahaifinki, babanki mutumin kirki ne kaddara ce tasa muka same miki ta hanyar da batadace ba, ba dan zuciyarmu yaso hkn ba .
"ki tausayi min diyata karki juya min baya, kece duniyata, rungume umna su'ad tayi ajikinta sosai muryarta na rawa "tace ba zan taba gudunki ba umma ,duk duniya banida kmrki kice kika samar dani duk da bata hanyar dace ba amman bazan iya gudunki ba sbd kaddarar data fada miki ni kaina na tausaya miki ummana ,labarinki ya taba min zuciya sosai .
"da najin labarinki kafin zuwan wannan lokacin da banyi riskin din rayuwata ba.
umma da ban saka kaina cikin wannan mummunar rayuwar dana tsinci kaina ciki ba.
"naji taikaicin naji bakincikin ta hanyar danaxo duniya amman bai kai tsanar iyayenki dana mahaifina danake ahalin yanzu, ki bar kuka ummana ina tabbatar miki kukanki yazo karshe zan dawo miki su'ad dinki sak ta da abin alfaharinki , bazan gujeki ba ummana .
"na dauki kaddarar yadda kuka samar dani domin hk Allah yaso dani daman bata hanyar aure zanzo duniya ba.
bazan taba tsallake kaddarata ba ki daina kuka takarasa mgnr tana gogewa umma hawaye wasu na biyo kuncinta ,na daina kuka su'ad kema kiyi hkr ki yafe mana kuskuren damuka aikata wanda ayanzu ko wani naga zaiyi irin abinda na aikata abaya zan bashi shawara ..
tana karasa fadar hk tashige bayi tana wani irin kuka ta bar su'ad tsaye, itama kukan take har lokacin.
"umma tayi wanka tare da dauro alwala ta fito ta shinmfida pray mate ta tada sallah .
itama su'ad bayi tashiga tayi kmr yadda umma tayi sai dai ita kwanciya tayi akan gado dan kawai ta ragewa kanta xugin da zuciyar ke mata .
juyi kawai take akan gado ta kasa runtsawa ana cewa bacci barowa ne amman ya gagara daukarta har asuban fari bacci bai zo mata ba.
yayinda ita km umma har lokacin tana ta faman jera nafilfili.
mmn sudais ce
💗💗💗💗💗💗
SAI KA AURENI DOLE
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
~NA~
*AYSHA A BAGUDO*
~DEDICATED TO~
HAUWA A USMAN
JIDDARH
page 47
"lokacin da umma ta idar da sallah asuba ta dade zaune tana jero addu'ointa data saba kmr koda yaushe, sannan ta mike tsaye cike da sanyi jiki da niyyar tashin su'ad daga bacci domin yin sallah .
amman tana karasowa inda take kwance akan gado ta tsaya cak cike da matsanancin mamaki sbd ganin idanunta biyu tayi shr tana kallon saman ceiling
19, September 2025
Aisha Auwal
Wow