Showing 171001 words to 174000 words out of 420383 words
Chapter 58 - SAI KA AURENI DOLE BY AYSHA A BAGUDU.txt
karfi numfashina ya soma barazanar daukewa ina cigaba da kallonsa .
"wani irin ubane shi dai bai son farincikin ya'yansa ban taba tunanin mahaifina zai iya hanani abincin ruhina ba.
lokacin danake zaune gabansa nayi danasanin kasancewarsa uba gareni domin ya aikata abunda iyaye dayawa bazasu iya yiwa ya'yansu na cikinsu ba ,na dauka ya'ya sune sanyi idanun iyaye a she ba hk bane .... ina cikin wannan tunanin ne muryarsa ta daki dodon kunnena lokacin dayake cewa taso mamana mushiga ciki ya miko min hanunsa.
,alamun nazo kallon tafin hannunsa nake ina tsiyayar hawaye batare da nayi yukunri mikewa tsaye ba,hawayen bakin ciki kawai ke gangaro min bisa kuncina .
xuciyata shiga tunanin me yake son fada min km byn yayi nasarar rabani da sanyin idaniyana.
" banda uba uba ne alokacin ina jin kmr na canza nawa uban..
"kusan minti goma ina zaune ina kallon tafin hannusa , sannan na mike a zabure ina kallonsa mgn nake son yi masa alokacin amman na kasa furta komai kawai na juya da gudu zan bar gurin ya sake kiran sunana muryarsa na rawa mamana ki tsaya ki saurareni.......
na tsaya cak tare da juyowa idanuna akan fuskar mahaifina me zakace min baba ..?atahiri rayuwa ma iyaye kan sadaukar da farincikinsu ne wa ya'yansu domin samun kwanciyar hankalinsu .
amman ni na kasa samun wannan farincikin daga gareka .
"ina son taufeek tmkr raina.. ina son rayuwa tare dashi amman kayi sanadin yanke wannan soyayya me girma da sadaukarwa .
taufeek na sona har yafi sona da bukatata fiyye da wanda kake kokarin hadani dashi .
"amman babu komai Baba nagode......nagode
ina kaiwa nan na haye matattakala da gudu suka biyo byna suna ihun kiran sunana tare da rige rigen kamoni.
ban juyo balle na tsaya har sai dana dangana da dakina nashiga da sauri na rufo kofar tare da murda key .
na jingina bayana da jikin kofar ina kuka ina sambatu irir ina kiran sunan taufeek da iyakacin karfina ......
bugun kofar suke da iyakacin karfinsu kowane nakiran sunana da kalar rarrashinsu gareni akan na bude musu kofar su shigo amman naki hk suka gaji da bugu kofar suka hakura .
ranar gidanmu dawowa yayi tmkr gidan mutuwa kowa kagani fuskarsa babu annuri yayi jugun tare da zabga uban tagumi har matan yayyena.
"mahaifiyata kuwa tunda tashige dakinta ta kulle kainta bata sake yunkurin fitowa ba...
ni kuwa duk wannan lokacin ina jingine jikin kofar dakina ina kuka me taba rai ....
jikina a matukar sanyaye na daga kafafuna da kyar na nufi gadona na fada ina sake barkewa da wani sabon kukan ina jin yau idan ban sake daura idanuna akan taufeek ba mutuwa zanyi..
ina son na sake ganshi koda kuwa hkn zai zama ganina dashi na karshe arayuwata wayyohhhly Allah babana kana son kashe saleemarka ne da hannunka..
meyasa baxaka gane halin dazan shiga arashin taufeek ba?
meyasa bazaka zama jigon tallafawa tilon diyarka ba akan abinda zuciyarta ke matsananci so ba?
ina son taufeek tmkr raina ida narashi zanshiga wani hali .
sannan zaka iya rasani sanadin hanani aurenshi.
meyasa bazaka fahimceni ba babana.......
bani na sanyawa kaina son taufeek ba ?
hk na dinga sambatu ina kuka ina birgima acikin dakina na dawo tmkr wata mahauciya,
mahaifiyata tazo yafi sau goma tana min mgn na bude mata kofa naki .
hk yayyena maza babu wanda bai yi iya kokarinsa ba ,har babana da kanshi sai daya zo yagama tsayuwarsa ya tafi.
ina kwance lamo a kan makeken gadona tare da runtse idanuna hawaye na tsiyaya byn shudewar awa uku ina kwance kiran sallah ne kawai ke tayar dani.
ranar kwana nayi kuka ina neman layin taufeek domin son jin muryarsa da sanin halin dayake ciki ,amman number'sa taki shiga ,abinda ya sake daga min hankalina kenan.
na sake shiga rudani da tashin hankali fiyye da wanda nake ciki .
"nayi kukan nayi hauka adakina tare da sabatu iri iri , idanuna bude suka kwana dan ko bacci barawo bai yi nasarar daukata ba yadda naga rana hk naga dare .
hankalin mahaifina yayi mugun mugun tashi ganin har asuba naki bude kofar dakina.
shi kansa ba'ason ranshi zai min auren da bana so ba ayyadda naji sautin muryarsa amman babu yadda ya iya da rayuwarsa domin bazai iya kin aiwatar da kudirin hjy harira ba .
dan hk gari nagama wayewa tun da sassafe ya bar Cotonou zuwa xugu.
zaune yake gaban hjy harira byn sun gaisa yace daman naxo ne kan zance auren salema da yakub .. nan yashiga koro mata komai dake faruwa tun daga farko da wanda tasani da wanda bata da masaniyarsa har ya dasa aya .
tana gama ji komai tace uhm daka kwaso jiki kaxo me kake son ayi ..?
daman nace ko za'a bar zance auren inyaso kowannensu ya auri wanda yake ra'ayi.
" domin samun zaman lafiya kar azo garin karfafa zumunci,zumunci yazo ya lalace dan.... atsawace ta katse shi da hannuta tayi tsalle ta dire agabansa tana huci tmkr yar bori tare da cewa daga kai uban nata har ita salemar baku isa ba....nace baku isa ba .
"ina tabbatar maka wannan auren kamar anyisa angama koda kuwa zata mutu tabar duniya ne byn anyishi . amman wallahi sai yakub jikana ya mallaki salema diyarka matsayin matarsa.
sannan ga sako kabawa salemar idan ka koma gida, tasani yadda bata son auren yakub shima yakub bai sonta bai son aurenta nice nan nake son auren km tillas ayisa koda kuwa duk duniyar nan gatan ne .
kai gaka me "ya" kawani kwaso jiki kaxo min da zantuttuka banza marasa ma'ana .
dan hk nabaka nan da wata 3 kagama duk wani shirinka akan lamarin aure..lokacin yinsa yayi. hk ya mike jikinsa a sanyaye yabaro zugu.
.... .koda ya dawo daga zugu bai yi gigin sanarwa mahaifiyata komai ba dan yasan idan yasanar mata yadda sukayi da hjy harira rigama kawai za'a yi agidan .
sai dai ya tmbyeta ko na bude dakina tace masa a'a....
washegarin ranar ta biyu da faruwar abun na gwada kiran layin taufeek cikin sa'a number'sa tashiga yana dauka na sakar masa kuka yayi shiri N wani lokaci sannan yace isa! ya isa!! my louloooo dan Allah salema kibar kukan nan hk .
kukanki bashine mafita ba idan kina irin wannan kukan ya kike son ni nayi da tarin damuwata.. ? nafiki shiga damuwa kasancewar soyayyata tafi taki karfi .
kuka nake sosai har da shesheka nace taufeek ina cikin bakincikin rashinka dole nayi kuka wanda nasan har karshen rayuwata da kukan rashinka zanyi .
kiyi hkr nima ina cikin bakinciki kwarai da gaske akan cewa bazaki zamo matata ba.
nasan km zan kasance cikinsa har abadan duniya, kenan har aranar da rayuwata zata zamo the end salemat ina sonki ..ina sonki so na tsakani da Allah amman gashi ina ji ina gani babu yadda zanyi na mallakeki yakarasa mgnr yana jan numfashi kana yayi shr amman ina ki san wani abu bazan taba son wata diya mace kmr yadda nake matsanancin kaunarki ba.
da mahaifinki zai yarda yabani auranki da zan zame masa tmkr bawa garesa .
ko matsayin me gadin gidansa yabani zan amsa matsawar zai bani aurenki .. kece farincikina....zan bar kasar da tarin tunaninki da kewarki.. kece muradina samun mace irinki a wannan lokacin yana da matukar wuya kece sarauniyar zuciyata. hk ya dinga gaya min word' world masu dadi da taba zuciya ni km ina kuka tmkr raina zai fita har daga karshe ya kashe wayarsa tare da yi min sallama .
******
tsawon sati daya kenan da faruwar tashin hankali dana tsinci kaina ciki gari zai waye dare yayi ina cikin dakina kwance kusan kwanaki 4 kenan da suka wuce wanda lisafina taufeek ya dade da barin kasar sbd duk kwanakin cikin kiransa nake number'sa batashiga.
yayinda kwanciya ya zamemin abinda nafi so da bugata alokacin ,idan na kwanta har bana son tashi ko kwakwarar motsi nayi zuciyata manne take da tunani taufeek tare da tuna momment din da mukayi spend tare da shi. hk zan dinga jin hannunsa na yawo ajikina duk inda na motsa.
kiran sallah ne kawai ke tadani dan ta abinci ma na manta rabona daya shiga cikina .
rabona da abinci tun wanda naci ana gobe taufeek zai zo gidanmu .
dan randa zai zo ma kasa cin komai nayi sbd fargabar abinda zai faru.
hjy harira ganin yadda mahaifina yasameta da zance fasa aurena da yakub yasa ta sake tashin hankalinta .
"ta km bazama gurin bokayenta da malaman tsubu sannan ta bawa yakub din umarnin yasoma zuwa gurina zance byn sake jaddamasa kudinrata akan aurena datake son yi tunda tun farko tasanar Masa kasancewar shima makiri ne irinta bai nuna mata kin abin ba sai murna dayayi .wanda shi daman ya dade da kamuwa da matsanancin kaunata.
ranar farko dayazo gidanmu gurina bai samu ganina ba, sbd ina dakina a kulle mamma ta tareshi cike da karramawa da mutuntawa sai dai fuskarta babu yabo babu fallasa.
ya tmbye ni mamma bata boye masa komai ba tace yayi hkr bazai samu damar ganina ba sbd kwanana bakwai kenan adaki a kwance na kulle kaina na hana kowa ya ganni .
yayi shr yana sauraronta can km tace tana xuwa bari ta gwada tagani ko zan bude.
byn kmr minti 5 sai gata ta dawo tace yayi hkr naki budewa .
wani bakin ciki ne ya kama kahon zuciyarsa ya tokareshi tagumin bakinciki yayi sbd yaxo da maitar son ganina dan ko abinci da mamma takawo masa ma bai ci ba ya bar gidan ransa abace.
akwana na goma ne iyayena suka sa aka balla musu kofar dakina wanda zuwa lokacin na galaibaya iya galabaita na fita haiyacina numfashi ma da kyar nake iya janyowa .
ai Suna ganin halin danake ciki kuka suka saka ina kallonsu da idanuna dake lumshe .
"duk kawaici irin na mamma sai data kalli tsabar idanun babana tana kuka tace idan kabari wani abu yasamu yarinyata bazan yarda ba..
dawood ...zan cire zumunci da auren dake tsakanina da kai nayi kararka xuwa court dan bazan zauna ina kallo ka nemi kashe min yarinya ba sbd farinciki wasu ...
ban taba ganin bacin ran mamma ba sai s ranar ta inda take shiga ba ta nan take fita ba .gama mgnrta ke da wuya ta juyo kaina tana tabani cikin muka take kiran sunana sai gani tayi jikina ya sake na sume... hankalita ya tashi ta juyo ahargitse ta cakumi wuyar rigar babana tana ihun tana kukan ya kashe mata ni .
da kyar wata yayar babana datazo duba jikin hjy babba tashiga tsakaninsu .
aka kira likita yazo gida ya bani taimakon gaugauwa tare da daura min drip .
a dan tsakankanin wannan lokacin mahaifiyarta da yan'uwana basa nesa dani kullun cikin rarrashina suke da bani baki .
"abinci ne agabana mamma tana rarrashina naci amman naki sai dan ruwan shayi dana soma sha .
tun daga ranar da mamma tace min yakub yazo gurina bai sake takowa gidanmu ba. ni km kuwa nayi kudirin koda ya dawo bazan bari yaganin ba.
yayinda hjy harir ta sake banko wani sabon tasiri me zafi ajikin mahaifina dan hk wata rana mamma na zaune a parlour ya dawo gida a hargitse yake sanar mata da za'akawo kayan aurena tace yanzu bazaka bar zance auren nan ba?
Kai tsaye yace mata eh idan an daura auren na mutu.
kwasam ina parlour akwance naji sautin muryar mutane nashigo cikin babban parlour gidanmu wanda duk wancin yan'uwanmu ne dan na dauki muryoyinsu wai sunzo kawo kayan aurena da yakub . ina kallon lokacin da mamma take musu alama da suyi shr amman ina
nagama sauraronsu na mike tsaye ina layi kawai sai gani sukayi na zube kasa na sume .
hankali kowa ya tashi akayi hospital dani wanda likitoci sukayi tsaye akaina domin dawo dani haiyacina amman numfashina yaki dawowa sai da aka manna min isar oxygen domin taimakawa numfashina yayinda mamma da ssuran dagin ke gefena cikin fita haiyacinsu da shiga tashin hankali lokacin dana dawo haiyacina aka canza min daki.
satina biyu a hospital aka sallameni muka dawo gida wanda har lokacin bangama dawowa daidai ba.
kwance nake adakina cikin matsanancin tashin hankali tun danake atsawon rayuwa ban taba fuskatar irin tashin hankali danake ba alokacin .
idanuna sukayi luhu luhu suka zurma daman ga uwar rama dana sakeyi dan gbdy na zabge na dawo wata irin dani sai kashi nayi kuka har nagaji.
itama mamma tayi kuka har ciwon idanu sukayi nasarar kama idanunta tana zaune tana kallona tmkr matacciya .
surutai take ahankali zuwa lokacin tace batasan me taufeek yayiwa tilon diyarta kwaya dal a duniya ba wanda yasa ta shiga wannan halin .
ina sauraronta har tagama sambatunta amman hankalina bai gareta bare nace mata wani abu .
har zuwa sanda yayyena suka shigo dakin jikinta har rawa yake gurin ce masu anya kuwa yaron nan da salema ke mutuwar so bawani abu yayi mata ba? soyayyar datake masa yasoma bani tsoro.
yaya yusif ne yayi karfin halin cewa babu abinda yayi mata kawai dai tata kalar soyayyace tazo mata da zafi.
ahankali naji mamma tace ban yarda wannan soyayyar ta wuce ace babu abinda yayi mata takarasa mgnrta tare matsowa sosai inda nake kwance tmkr matacciya ta kamo hanuna cikin nata tare da kiran sunana mamana ki sanar min ko taufeek yabaki wani abu ne alokacin da kuke soyayya musan yadda zamu bullowa lamarin? nayi shr naki cewa komai. tacigaba
ko km kunsha jinin juna ne kedashi ki gaya min ni mahaifiyarki ce ko kowa yakiki ni ina tare dake ki gaya min inda akayi aikin muje akarya ki dawo haiyacinki .
na ma shr duk da bakina nason tanka mata amman na kasa bude labbana da suke a bushe.
ahankali nasoma samun sauki kadan sbd kulawar danake samu daga mamma .
dan gbdy kauracewa mahaifina tayi.
" ta dawo dakina tare muke bacci daita tana kula da yanayin , wani lokacin idan taga nashiga damuwa sai tasanyani ajikinta wai naji tumin jikinta ko zan dawo daidai.
alokaci su'ad idan akace miki nice wannan matashiyar salemar me cikar halitta da kyau zakice karya ne sbd muguwar ramar danayi kirjina har wasu mugayen katsutsuwa ne suka bayyana step by step.. kallo daya zaka min kasan ina cikin alhini da tashin hankali.
ciwona bai hana mahaifina soma shirye shiryen bikina da yakub ba dan har ankawo komai daza'a bukata agurin biki .
hatta kayan daki ya kammala anje anyi jere anyi komai wanda kusan duk dagin mahaifina ne ke tsaye akan komai dan mamma na tare dani taki yarda tashiga cikin sha'anin bikin.
yadda bani son auren da yakub hk itama take nunawa dangin mahaifina bata so har rigama yaso shiga tsakaninta da mahaifiyar yakub. sai da manya suka shiga tsakani.
yayinda ni km hankalina ya sake tashi nashiga tashin hankali mara misaltuwa fiyye da lokutan by na kara ramewa sai dai nayi wani irin fari na dashe kmr wace bata da jini jiki sannan sai alokacin nake sake tabbarwar kaina da gaske dai narasa taufeek har abada.
take ciwon sonshi ya motsa min ya dawo min sabo fil .
barin lokacin da magangagunsa suka dinga dawo min daki daki kibini mutafi kasata muyi aurenmu acan zan zame miki komai zan soki zan baki kulawar data dace bazan taba cin amanarki ina kawowa nan jikina yasoma rawa rawa kafin kace me wani zazzzafan zazzabi yayi nasarar rufeni na dunkule kaina adaki na lullube cikin bargo duk hayaniyar da'ake acikin gidan ina ji wanda hkn ke karawa zazzabin jikina tsamari ranar dai sai da muka dangana hospital naga likita. byn mun dawo daga hospital nashiga tunanin mafuta nakarasa inda jakata dana saka diary da taufeek yabani ya dauko har na juyo da niyyar fito da diray nakaranta abinda yake ciki . najiyo takun shigowar mamma dan hk na nade jakar da sauri ta turata cikin wata yar karamar akwatina nakaraso na zauna gefen gado.
itama guri tasamu ta zauna gefen gadon kusadani tana me taba wuyana taji ko har lokacin jikina da zafi.
zafin daya ratsa tafin hanunta kmr garwashin wuta yasa ta kamoni ta kwantar dani .
mike tashiga bayina taje ta dibo ruwa acikin yar karamar robo da towel ciki wanda ni har ina gadona kwance lamo makale da tunanin taufeek tasoma matse towel din byn taciremin yar rigar shimin dake jikina ta dinga goge min towel din tana meida shi cikin ruwan tsayi kafin kace min har zafin jikina ya ragu.
*******
ranar daurin aurena tashi nayi jikina a sanyaye ji nake kmr narasa komai na rayuwata ne.
yayinda hklina gbdy baya gangar jikina banda kuka babu abinda nake .
bakaramin tashin hankali mamma tashiga ba ita da sauran yan'uwana taki yarda tayi nisa dani tana dakina takasa barina sai da wasu daga cikin daginta suka zo sannan taje gurinsu .
ni kuwa tattare da kololon bakin ciki wanda ya hanani walwala da sakin fuska balle na damar fitowa tsakar gidanmu.
" yayinda gbdy dagina na nesa dana kusa sun hallara . duk da ansa bana son auren amman hkn bai hana wasu daga cikin dagina bayyana farincikinsu ba. ina zaune cikin matsanancin tashin hankali mamma takirani a waya tace nazo dakinta alokacin tana son ganina.
na mike da kyar jikina na rawa na fito daga dakina ina fitowa babban parlour gidanmu ina da iske mutane makil suna ganina gurin ya kaure da ihun ga amarya..ga amarya ..take zuciyata tashiga tsalle tasoma harbawa da sauri sauri kenan da gaske ne aurena za'a daura.. take jikina ya sake daukar kirrma sbd hango yakub danayi cikin wando da riga da yar samanta komai na dake sanye ajikinsa fari ne ga annuri bayyane akan fuskarsa yana gyara malunlun rigarsa wani irin kyau yayi wanda bai taba yin
19, September 2025
Aisha Auwal
Wow