Showing 216001 words to 219000 words out of 420383 words
Chapter 73 - SAI KA AURENI DOLE BY AYSHA A BAGUDU.txt
ba auren aka daura ba.
bangaren zeey kuwa jin ammi kawai take dan ita aganinta kmr yanzu ta daina sonta tunda tasamu diyar dan'uwanta .
hatta kulawar da ammi take bata ada ana tunanin yanzu ta daina, idan ba hk ba saunawa suke kebancewa da AK a dakinsa bata taba ce mata hk ba ko nuna mata illar abun sai yanzu, duk bayanin ammi suna shiga kunneta suna fita ne dan bata tsinci komai ba.
duk wani abu da'ake wanda ya danganci event zeey taki yarda tayi ko daya baya ga gyara kasanta datake yi koda yaushe cikin tsarki da ruwan zafi take dan har Stiche kawarta bolaji tayi mata domin kasanta ya hade sosai ta dawo tmkr wace ba'a taba yin sex daita ba.
shima bangaren ak yadda Zeey ta nuna batada ra'ayin sake yin wani event shima yace babu abinda za yi .
balle km baiwar Allah su'ad wace gbdy fargabar aurensa ya sakata gaba ko kwakwarar motsin kirki batayi idan yana guri .
babu wani banbacin duk abinda ammi take bawa su'ad tabangaren kayan mata shi take bawa zeey, a rashin ba tasan ita zeey tana karawa kanta da wasu ingantattun kayan mata na musamman wanda take siya a boyewa...
mmn sudais ce
💗💗💗💗💗💗
SAI KA AURENI DOLE
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
~NA~
*AYSHA A BAGUDO*
~DEDICATED TO~
HAUWA A USMAN
JIDDARH
*Allah messenger saw said seeking knowledge is compulsory*
page 54
umman su'ad tazo gurin ammi akan zance kayan dakin su'ad ,domin itama tayi nata tanadin na musamman akan tilon diyarta, amman lokacin datake gayawa ammi dalilin zuwanta dan tagama komai na kayan daki inda za'a zubasu kawai ya rage .
ran ammi yayi matukar baci har ta nunawa umman su'ad bacin ranta inda tace "haba saleema ko ban hada komai da su'ad ba ai ni me mata kayan daki ce ballanata su'ad diyata ce halak malak dole nace.
" wannan abinda ya rataye ne akaina ba sai kin wahalar da kanki ba duk abinda ya dace uwa tayi diyarta ni zanwa su'ad shi sannan babu wanda yake da halakin daukar nauyin sama dani.
"duk da hk dai zanyi nawa iya bakin kokarin kiyi naki daban nawa daba inji cewar umman su'ad.
"yin duniya ammi tayi da umman su'ad akan ta hutar da kanta amman furrrrr taki "tace sai dai a ware mata daki daya itama ta zubawa diyarta abinda Allah ya hore mata ,hk ammi ta hakura ba dan tason faruwar hkn ba tare da cewa mata "zatawa abdulkabir mgnr .
ammi ta mike tashege uwar daka tare da turo mata su'ad, a shagwabe su'ad takaraso inda ummanta ke zaune ta zauna kusa daita tare da gaisheta umma ta amsa tana murmushi hade da tsura mata ido kawai tana kallonta .
tayi wani irin kyau na fitina farinta ya sake fitowa sosai sai dai ta rame sosai fiyye da tunanin me karatu muryar umma cike da matsanancin rauni tace "meke damunki su'ad?
"idan akwai damuwa a zamanki cikin gidan nan ki sanarmin na wuce dake?
su'ad tayi narainarai da fararen idanunta tmkr zatayi kuka kana "tace ba komai umma, "kin tabbata da babu komai?
"Allah bana tare da damuwar komai duk abinda nake so shi ake yi km duk abinda nake so shi nake ci.
"idan ma akwai matsalar bata wuce rashin jin duriyar su ore ba, suna raina kullun "nice silar komai gashi ni yanzu ina kebance guri guda, su km bansan halin da suke ciki ba takarasa mgnr tana me daura kanta bisa cinyar umma.
"karki damu kiyiwa hjy mgn nasan zatasa baki commission yasa asakesu dan gsky idan aka barsu can karshe prison za'a wuce dasu kinga abu baiyi dadi ba ..
"shine abinda yafi damuna wlh wanda kusan shi ke hanani runtsawa.
nan suka shiga tautaunawa tsakanin uwa da "ya" inda su'ad take cewa umma yakamata muje su mu nemi Uncle gaddafi a sam ethemic hospital.
"abinda ke raina kenan kullun da tunin son zuwa nemansa amman babu inda zanje gbdy sun tattara sun cireni acikin duniyarsu ko daidai da rana daya basu taba yunkurin nemana inda nake ba ina raye ko ina mace wanda hkn bakaramin taba zuciyata yake ba.
"kiyi hkr umma kiyi musu uziri ta ina zasu fara nemanki?
" nigeria ba karamin kasa bace da kawai zaxo neman mutun kai tsaye batare da wani cikakken address dinsa ba.
zantawa suke atsakaninsu akan abinda yashafi rayuwarsu inda umma ke bawa su'ad shawarar da hanyar da zatabi gurin ja hankalin AK zuwa gareta, yayinda ahankali take daukar duk wani lacar ummanta da mahimmanci "umman su'ad...... "na'am sanyin idaniyana "zanyi missing dinki.
"kmr yadda nima zanyi missimg dinki yanxu hk dauriya kawai nake akan rashinki kusa dani, gani nake kmr ana son rabani da rayuwata ne.
"akwai abubuwa dayawa da fuskarki ke debemin kewarsu amman babu yadda zanyi auren shine mutuncinki da na wa .
"ni kasance babu aure sannan kema naki aurar dake,ai idan nayi hk ban yiwa kaina adalci ba, takarasa fadar hk tare da daura hannuta bisa kan su'ad tana shafawa ahankali tana jin wani irin kewar diyarta cikin zuciyarta.
tun yanzu kenan tasoma jin rashin jin dadi rabuwa da diyarta da zata sake yi kwata kwata bata kaunar abinda zai sake nisatata daita ,sun dade tare har sanda AK yashigo part din kallo daya yayi musu ya dauke kanshi tmkr bai gansu ba ya shige dakin ammi .
********
yau sauran sati daya a daura auren su'ad da ak hankalinta yayi bala'i tashi sbd tsabar fargaba, a duk sanda ta daura idanunta akanshi sai taji gabanta na wani irin mahaukacin bugu da karfi, wanda hkn yasa ramar datayi ta sake fitowa sosai dan kallo daya zaka mta kasan tana cikin tashin hankali .
yayinda gefe guda iskanci da ak keyi da zeey agabanta ke tafarfasa mata zuciya.
" yanzu hk zaune take a dakin ammi ta zabga uwar tagumi sai tunanin take "me ak ya gani ajikin zeey daya nace yake rawar jiki akainta ga mata nan zube masu aji da Class amman ya makale mata sai wani nan nan yake daita yana rawar jiki wanda kusan iskancinsa baya tashi sai yaga tana gurin.
" ahalin yanzu da take ciki datasanin take data lalata rayuwarta a sadiyyarsa ,ahankali ta mike tsaye daga zaunen datake zuciyarta na wani irin tsalle .
numfashinta na kokarin barin jikinta sbd hasko abdulkabir dinta tare da zeey ,tana da maseefaffen kishi akansa wanda ita kanta bazata iya cewa ga inda limit din kishinta ya kai ba ,amman rashin son dayake nuna mata shi ya hana wannan kishin tasiri agangar jikinta.
zariya tasoma yi acikin dakin hawaye sun ciciko a idanunta "me tarasa arayuwa da AK bai dauketa abakin komai ba?
"kyau ne ko me ? tayiwa kanta tmbyr duk abinda da namiji zai bukata ajikin cikakkiyar mace Allah ya mallaka shi.
"idan km abinda ta aikata a baya ne yasa ya tsaneta ai shine silar faruwar komai da sanadiyar tabarbarewar rayuwaata.
gbdy abubuwa da yakewa zeey ya hanata zuciyarta sukuni duk inda ta motsa ganin hkn take azahirance acikin idanunta yana mata yawo acikin kwalkwaluwarta wanda tasan dayawa abubuwan da yakewa zeey yana yi ne kawai dan ya kullar da zuciyarta.
taja numfashi da ajiyar zuciya atare ta sauke tana dafe goshinta cikin datasani mara amfani .
duk wannan iskankanci nasa bai daga mata hankali ba kmr yadda taji
yana ikirarin gidansa na green hill estate na zeey ita kadai sannan har da kyautar dalliyar motar.. cike da sanyin jiki tasa hannunta ta goge hawayen daya gangaro mata daga cikin kwarnin idanunta ...
"meyasa ni bazaka soni ba abdulkabir ?
"daman ashe wanda yace yana sonka zai iya zama makiyinka ?
"bana bukatar komai naka ,bana bukarta komai daga gareka baya ga soyayyarka tare da kulawarka gareni ,amman ina tabbatarwa kaina matsawar ba kai ka kawo kanka gareni ba bazan sake yunkurin nufar inda kake da sunan
soyayata ba, takarasa mgnr zuci wasu hawaye masu zafi suka shiga gangarowa bisa kuncinta tana gogewa wasu na biyowa .
cikin wannan yanayin ammi da ak suka shigo dakin suka risketa cikin wannan tashin hankali tana cigaba da zariya adakin tana mgn ita kadai kwata kwata bata ji motsin shigowarsu ba hatta sallamar da sukayi bai sa ta hankalta da shigowarsu ba.
da wani irin saurin ammi takira sunanta mamana..... daidai lokacin da su'ad ta juya musu bayanta cak taja ta tsaya jikinta na wai irin rawa tare da saurin goge hawayenta dake tsiyaya da hannunwanta duka sai dai takasa juyowa ta fuskanci ammi.
ahankali ammi takaraso zuwa inda take tsaye tmkr wace aka dasa ta kai hannunta ta rikota zuwa kan gado ta zaunar daita kana itama ta zauna .
"meke faruwa dake naganki hk?
"me ke damunki hk?
"ko wani abu aka miki acikin gidan nan?
hk ammi tayi mata tmbyr ajere tana kallon fuskarta cike da matsanancin firgici.
ta bude bakinta zatayi mgn kenan taji anja wani dogon tsaki wanda yasa tayi saurin dago fararen idanunta 4eyes sukayi dashi tsaye ya jingina da bango dakin ya tsura mata mayatattun idanunsa masu neman tarwatsa mata kwalkwaluwa yana kallonta dan sosai yanayinta yake bashi mugun haushi tare da takaicinta arayuwarsa baya jin akwai halittar dakeji ya tsana kmr ta arayuwarsa ya tsaneta har baya kaunar ganinta idan yace halakarsu daita bai dagula masa lissafi ba yayiwa kansa karya .
da sauri ta dauke idanunta akanshi tana sake jin wani irin faduwar gaba ,dan hk ta dukar da kanta kasa takasa cigaba da kallonsa dan tunda alkadarin komai ya karye , ciwonsa ya dawo jikinta ta nemi tsiwa da rashin kunyarta tarasa. "
"ahalin yanzu babu abinda ke karyar mata da zuciya da fargaba kmr kwayar idanunsa akanta kusan minti goma ammi na jiran su'ad tace wani abu amman tayi mata dif takasa cewa komai dan hk ta sake maimaita tmbyrta akan abinda ke damunta .
rashin abinda zata gayawa ammi ne yasa muryarta a raunace "tace ammi friends dina na tuna ..da sauri" ammi tace kina son ganinsu ne?
"eh ammi sai dai suna cell tun lokacin da aka kamamu tare km nasan zuwa yanzu killa an wuce dasu jail ...."banason sanadiyata su sake koma rayuwar prison most especial ore data sadaukar da farincikinta akaina .
"ok karki damu zanyi waya da commission naji halin da suke ciki .
tunda su'ad tasoma mgn yake kallon yadda take motsawa dan karamin bakinta ahankali wanda ko lokacin da take tsaka da ganinyar bibiyarsa hka yanayin mgnrta take cike tsayin da dadin sauraro amman yanzu dayake kallonta agabansa cikin natsuwa ji yayi sanyin mgnr har ya zarta na baya dadi .
"ki kwantar da hankalin bana son ganinki cikin damuwa duk abinda kike so ki gaya min zan miki shi matsawar bai fi karfina ba ,sannan duk wanda ya nemi ya takura miki agidan ki sanar dani koda kuwa wannan da dake tsaye ne takarasa mgnr tana nuna inda AK yake..
tabe baki yayi kawai batare da yace komai ba ya karaso ya zauna gefen ammi inda su'ad ke dayan gefenta na dama suka sata atsakiya .
"ammi.. ya kira sunanta cikin sanyi muryarsa me maseefar kashewa mutun sansar jiki ,
har zai soma mgn sai km ya fasa tare da dago mayattun idanunsa ya dubi inda su'ad take zaune "ke tashi ki bawa mutane gurin zanyi mgn da uwata yayi mgnr kmr bai so fitowarta ba.
"ban son rainin hankali fa abdul baka san sunanta bane dazaka wani kirata da ke .
"to bazata koina ba kayi mgnr dazakayi ,idan km mgnr bata da mahimmanci kana iya barinta amman baxata koina ba.
murmushin takaici yayi yana me cizan gefen lip's dinsa da karfi sannan ya lumshe mayattun idanunsa tare da cewa haba ammi wai meyasa gbdy yanzu kika canzamin ne?
"halinka ne yaja hk ammi tabashi amsa atakaice tana sake meida hankalinta kan su'ad .
" to ai na canza na dawo yadda kike so "Allah yasa ai nafi kowa bukatar naga ka canza .
sai da ta numfasa ta sauke ajiyar zuciya sannan tace "wai da gske ne zance danaji zeey tazo min dashi kabata kyauta motar da aka turo maka daga spain?
ya girgiza kanshi ala'mun eh tare bude idanunsa ya tsurawa zara zaran yatsun kafafunsa ido yana kallonsu, "to ina na su'ad?
"wace hk km ammi.
"abdulkabir kashiga hankalinka dani ,wlh kafita idona fa idan ba kana bukatar rainka yabaci ba .
" wace irin banza tmby ce wannan?
" matar datake shirin zama mallakinka kake cewa wace hk?
ganin yadda ammi tashiga balbaleshi da fada da masifa yasa su'ad saurin mikewa jikinta a matukar sanyaye zuciyar na harbawa ta nufi bathroom ba dan akwai abinda zakiyi aciki ba tayi hk ne kawai dan ta gujewa zuciyarta bacin rai .
"kiyi hkr ammi amman dan Allah na rokeki ki daina min fada agaban yarinyar nan zata rainani ni km kinsa ba daukar raini zanyi ba dan zan iya karya yarinya wallahi .
"idan ka fasa karyarta ban gode maka ba, km wallahi naga tata motar acikin gidan nan kafin ka hadu da fushina , runtse mayatattun idanunsa ya sake yi sosai tare da gyara zamansa ya kamo hannuwan ammi cikin nasa ,"kiyi hkr amminah banason ganin bacin ranki ,tunda kika furta akawo mata tata motar angama ai duk abinda kikace kina so shi zanyi .
ta jinjina kai tare da cewa " sauran zance inda zata zauna shima naji kamin shiru sbd kayan daki tunda ita zainab nata sun dade acan gidan ka.
shiru yayi na dan wani lokaci daga bisani muryarsa a kasalance yasoma motsa labbansa ahankali "me zai hana ta zauna a part dina na nan gidan ,sbd can gidan mutun daya ne .
"kace dai baka son hadasu guri daya wannan tsarin naka ya daidai agurina gara zamanta kusadani , idan ba'a kwatanta adalci ba a hadu da bacin raina.
shi dai duk abinda tace da eh ko a'a yake binta dan su rabu lfy dan yaga yanzu gbdy ammi ta maseefar sauya masa akan su'ad, da yayi mgn zata sauya masa .
ahankali ya mike tsaye yana dubanta "ni zai wuce gida addur a sauka lfy tayi masa.
********
ammi takira commission akan zancesu ore "yace mata ai tun shekarajiya yasa aka sakesu godiya tayi masa sosai sbd yana matukar yimasu karamci da mutunci ,dan byn shi da yanzu su'ad na gurin police kasancewar tana da sanya hannu dumu dumu gurin bada gudumuwar yiwa onye fayde.
*********
a yammacin yau ne ore taki kira su'ad inda take sanar mata zasu shigo gurinta zuwa anjima, tayi murna sosai da jin zasu kawo mata ziyara, duk da tarin damuwar datake ciki hkn bai hana wannan farincikin tasiri afuskata ba.
taje da murnarta ta sanarwa ammi xuwan su ore sbd abinda zaije ya koma .
ammi kanta bataji dadin wannan zuwan nasu ba ,dan tafi son kowa yakamata gabansa amman yadda taga su'ad din cikin tsantsar farinciki maramisaltuwa yasa tace mata babu matsala Allah ya kawosu lafiya bari zan yiwa hannutu mgn asa abinci dare dasu.
da misalin karfe 7:00 daidai suka karaso gidan kusan su goma har da ganiya lokacin da suka iso bakin get din gidan securities din bakin get suka hanasu shigowa sai da suka kira wayar su'ad ita km ta gayawa ammi.
eiman ammi ta tura tashigo dasu kai tsaye falon baki ta nufa dasu ita km juya.
kafin su'ad takaraso har abinci da abin sha sun karaso kalolin abinci birjiki agabansu tare da kayan marmari, cike da natsuwa su'ad tasanyo kanta cikin parlour 'n
suna ganinta suka mike tsaye suna ihu da kururuwa ganinta ol'orin o'won agba, gba tiya suka shiga bawa juna hannu suna tafawa daga bisa suka rungume juna da matan .
ganinsu ore bakaramin sake faranta rain su'ad yayi ba kasancewar tagansu suma cikin natsuwa da kwanciyar hankali kmr yadda itama yanzu tasamu natsuwar zuciya ,kowanensu cikin shiga ta mutunci duk da shigar kananun kaya ne amman yafi na da da suke sakawa wanda alokacin sau tari gajeren wando ne iya gwiwa sai banzayen riguna na yan iska.
yadda shigar matan take a mutunce hk ma maxan shigar take.
sun ci abinci sunyi nak sai hirar yaushe gamo suke atsakaninsu suna kwashewa da dry inda ganiya da ore suke tmbyrta cigaban da aka samu a tsakaninta da AK.
uhm numfashi da ajiyar zuciya su'ad ta sauke atare , take km yanayinta ya sauya sannan muryarta a sanyaye tace "babu wani sauyi jiya iya yau muna nan kmr yadda kuka sani, sannan ta kara da basu labarina halakar dake tsakaninta da AK dukkaninsu sun sha mamaki da jin hk .
inda baba laye yace "ki bari zan yiwa wani mutumi mgn a unguwarsu,malami ne sosai ko zai taimaka miki ki mallakeshi.
a matukar zabura su'ad ta zaro fararen idanunta waje tana dubansa kafin daga bisani tasoma girgiza masa kai "karka soma baba laye ,ai ni arayuwa na dauki darasi iri iri "bari ingaya maka malami kona addinin muslinci ne bazan sake kai kaina gareshi da sunan taimako ba, matsawar sai na kaiwa wani malami ziyara sai dai kar na mallake abdulkabir arayuwata.
" wlh gara muyita zama hk nidashi zan cigaba da kaiwa allah kukana Allah yasan yadda zaiyi da lamarina, amman zance zuwa gurin wani malami sam karma ka sake kawo min zance shi.
su ore suka hada baki gurin cewa kina da gsky wlh yaushe zaki tsaya ki karar da arayuwarki akan nmj, ni da zakiji shawarata wallahi da rabuwa kikayi dashi akwai maza dayawa a office inji cewar ore.
"gaki da kalar yan birni one time kina rabuwa dashi zaki samu wanda yafishi .
murmshi su'ad tayi kana tace "akwai matsala ne idan na rabu dashi , nan
19, September 2025
Aisha Auwal
Wow