Showing 390001 words to 393000 words out of 420383 words
Chapter 131 - SAI KA AURENI DOLE BY AYSHA A BAGUDU.txt
d'aya.
cikin muryar kuka Umman Su'ad tasoma magana "mamma ki yafe ni....... kiya femin abinda nayi nasan nayi kuskure abaya wanda bazan sake kwatanta abinda nayi ba tsawon minti goma suna rungume da juna sannan Umman Su'ad ta zare jikinta suka tsurawa juna idanun ahankali ta karya gwiwarta zata tsuguna gaban mahaifiyarta wanda sai lokacin mamma tayi mata magana cewar"
"karki zauna a k'asa mana mamana "mamman kibarni haka ina babana yake ina son sake d'aura idanuna akansa ?
"mahaifinki na nan salema yana d'ayan b'angare can ya koma da zama tun bayan barinki gida ,"ga Sulaiman can yayi bangarensa na sanan zuwa yanzu yasan da zuwanki takarasa maganar tare da duban inda Ammi ke tsaye tana dubansu"
"bawar Allah sannuku da zuwa kiyi hak'uri dan Allah ga gurin ki zauna.
kafin kace me tuni dawowar Salema ya isa kunnen yan'uwanta gaddafi da Yasif Ibrahim Sulaiman gaba d'aya sun zagayeta kowanensu na murnar dawowar ta ..
can kuwa an yiwa su Dady masauki a b'angaren baki inda mahaifin Salema ya isa d'akin cike da matsanancin mamaki bak'in da akace yayi ahankali yashigo parlour'n bakinsa dauke da sallama "Assalamu Alaikum....
gaba d'ayansu suka amsa masa Taufeek dake zaune ya d'ago idanunsa domin sake kallon fuskar dattijon daya hanashi abinda ya so mallaka tun ganiyar kuruciya ,idanunwansu suka tsarke cikin juna tsawon rayuwarsa bai tab'a shiga tashin hankali da rudu irin na yau ba musamman tozali dayayi da mutumin dayayi sanadin rabashi da tilon d'iyarsa mafi soyuwa acikin ransa....
mutumin da ya aikata masa babban laifi da har ya koma ga mahalinsa bazai tab'a mantawa ba "mutumin da yayiwa diyarsa abu mafi muni da yankan kauna anan take jikin dattijo Alhaji Mahmud ya d'auki rawa shigowar Yusuf ce yasamu madogara , domin dafashi yayi sannan ya iya cigaba da tafiya har zuwa mazauninsa batare da ya iya cewa komai ba.
tsawon minti goma da zamansa idanunsa na kan Tauffek yana kare masa kallo "ko da me ya sake zuwa masa?
dan har lokacin bai san da zuwa Salima ba dan Sulaiman bai yarda ya sanar masa ba gudun abinda zai je ya dawo.
Dady da kanin mahaifin Taufeek ne sukayi karfin halin gaisheshi ya amsa yana girgiza kai sannan Taufeek ya mike daga inda yake zaune yakaraso zuwa ga mahaifin Salema ya durk'usa har k'asa ya gaisheshi babu yabo babu fallasa ya amsa masa sannan "yace ina diyata Salima....?
"wannan kalmar tasanyaya zuciyar Taufeek bai d'auka zai iya tambayar sa ita ba dan haka zuciyarsa na harbawa yace "tare muke tana cikin gida.
naunayen ajiyar zuciya dattijon ya sauke daga bisani k'anin mahaifin Taufeek yasoma magana akan musababbin abinda ya kawosu da kuma abubuwan da suka faru lokacin da Salima tazo musu da zance ciki.
shiru Alhaji Mahmud yayi yana sauraronsu "wato dai dole sai da aka cakud'a masa zuri da diyar gaba da fatiha ?" shi yanxu me zai ce wannan ma cikin kaddararsa ce babu yadda zayi bai isa hana hakan faruwa ba.
numfasawa yayi kana yace "nima bayin kaina bane akan dukkanin abinda ya faru alokacin har da sharrin sihiri da aka dinga jifana dashi nan suka shiga jajantawa juna inda daga karshe suka nemi auren Salima gurinsa batare da wani b'ata lokaci ba ya amince da wannan auren a karo na biyu wanda take Dady yabada sadaki aka d'aura auren Salima da Taufeeq murna gurin Taufeek ba'a kama hannu yaro ji yake tamkar an tsundumashi a aljanna ne..
Salima na tare da mahaifiyarta taji wannan abun farinciki ,mahaifinta ya aminta da zabinta a karo na biyu har yasanya hannunsa cikin lamarin aurenta sabanin shekarun baya.
Addu'a sosai mahaifin Salima yayi musu tareda zaman lafiya me d'orewa yasama rayuwar aurensu albarka.
hayaniyar dataji yana tashi cikin gidan yasan ta mik'ewa daga kwance datake acikin d'akin, tunda tazo gidan wannan shine karo na farko dataji sautin hayaniyar mutane bila adadin irin hk ahankali take takowa har zuwa cikin parlour'n inda idanunta suka sauka akan mutane datafi buk'ata ganinsu acikin rayuwarta mahaifinta da mahaifiyarta.
zaune gaban dattijon da tun zuwanta gidan ganinta dashi bai fi sau biyu ba shima a boye sakamakon kin yarda da kakarta tayi su hadu dashi.......
mmn sudais ce
💗💗💗💗💗💗
SAI KA AURENI DOLE
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
~NA~
*AYSHA A BAGUDO*
Dedicated To
Hauwa A Usman
Jiddar
YA SAMI'U
THE ALL HEARING
page 84
........gaba d'aynsu da mamaki suke binta da kallo banda Taufeeq da Alhaji Mahmud da basu san ko wacece tsaye a gabansu ba, illa tsabar kamar da dattijon yaga tayi masa da sirikinsa dake zaune agabansa.
cike da buguwar zuciya Ammi tace "daman kina nan mamana muke ta nemanki?
" babu inda bamu nemeki ba mamana ....takarasa maganar hawayen farincikin ganinta ya ciciko a kwarnin idanunta, "bata san irin son datake mata ba... "a da can baya ta d'auka maraicin rashin mahaifiyanta ne ya haddasawa zuciyarta kamuwa da matsanancin soyayyarta ,sai yanxu fahimci soyayyyar yarinyar daban, na mahaifinta daban ammi ta saka gefen hijab dinta ta goge hawayen daya soma biyo kuncinta.
Su'ad ta narke fuska tamkar zatayi kuka itama dan tasan tabbas ammi zata shiga wani hali adalilin rashinta, tana kokarin isa inda ammi take, mamma tace "zo nan Su'adullahi karki yi kuka yau ranar farin ciki ce garemu gbdy ahankali tacigaba da takowa zuwa inda mamma take ta zauna tsakiyarsu ita da ammi tana jin wani irin sanyi dad'i ta kasa cigaba da kallon fuskar Ammi datayi mata zuru tana kallonta cike da matsanancin mamaki .
shi kuwa Taufik tunda yaji furunci Ammi yasan itace d'iyar da yabar cikinta kuma ko ba'a gaya masa ba yasan jininsa ce, diyar salimarsa tunda suna fizgar kama daita.
shi k'ansa Alhaji Mahmud kallon Su'ad yake tare da kallon Mamma, ganin Alhaji Mahmud na neman k'arin bayani akan Su'ad yasa Mamma taci gaba da magana tare da rik'o hannu su'ad cikin nata.
" na boye maka ita ne saka makon wani dalili nawa, amman tunda k'arshen komai ya bayyana dole na bayyana maka, ita koda kuwa bata bayyana kanta ba.
"wata daya daya gabata ina zaune Saifullahi yazo min da ita wai a tapa yaganta tana neman gidan nan, inda daga karshe yace min daman yasanta tun a Nigeria shine likinta dake kula da lafiyarta, lokacin data sanar min cewa ita d'in d'iyar salima ce, nashiga wani yanayi me cike da rudu da tashin hankali daga baya damuwar ta juye zuwa tsantsar farin cikin sanin halinka da nuna rashin kulawa da damuwarka a tun barin salima gidan nan, yasa nayi tunanin boyeta har zuwa wani lokaci.
"na kaita masaukin danafi buk'atar ta zauna mun dad'e muna tantaunawa akan mahaifiyarta inda take sanar min da duk abinda ta yafaru da ita bayan barinta gida har zuwa auren d'an yayar mahaifinta datayi da mutuwar aurenta.... mamma takarasa maganr tare da yin shiru tana kallonsu daya bayan daya Ammi ta kasa boye farin cikinta ta matso su'ad sosai ta rungumeta tsam ajikinta tana godiya ga Allah gabadaya takasa boye tsantsar farin cikinta "mun yi kewarki mamana mun shiga tashin hankali rashinki ashe kina nan tare da kakarki kin manta damu ko kina nan kina jin dadinkiko ?
"Allah sarki shiyasa Ummanki tace in kwantar da hankalina jikinta nabata kina hannun na gari "ashe gsky ta fad'a Allah mun gode maka daka kawo mana k'arshen wahalarmu ,kalli nan ta nuna mata inda prof Taufeeq ke zaune wannan shine mahaifinki wanda yayi silar zuwanki duniya "Taufeeq ga d'iyar cikinka.
idanunta ta meida kansa tana kare masa kallo Sir mahbub " kenan hasashenta zai zama gskiya?
"Sir mahbub shine mahaifinta , tasha kawar da zuciyar datake karyata hakan gareta ta yaya hkn zata kasance ?
a she kasan cewarsa na nan zuwa ,wani irin kukan farinciki ne ya kufce mata wanda bata san sanda ta mike tsaye da kyar hade da dafe kasan mararta ta isa gabansa ta durkushe har kasa bisa gwiwowinta tana kuka ahankali ya d'aura hannunsa bisa kanta yana jin wani irin sanyi da farin cikin mara misaltuwa na kai kawo a gbdy ilahiri gangar jikinsa.
"yau ga diyar da salimarsa ta haifa masa, diyar daya bari aciki ya tafi kasar spain, itace ta girma haka har tayi aure ..
cikin muryar kuka su'ad tace" zan kiraka da baba ka amsa min ya mahaifina" tsawon rayuwata nayi kwad'ayin wada zan kira da haka narasa sai yau "babana ina sonka bazan ta'ba kinka ba duk da kayi sanadin zuwana duniya bata hanyar dabata dace ba .......
" nima ina tsananin sonki diyata tun kina ciki nake mutuwar sonki da kwad'ayin ganin zuwanki duniya, Allah be kaddaro faruwan hkn ba har sai munyi wasu shekaru kafin muga juna, ta riko hannwansa duka cikin nata tana kallon fuskarsa tabbas shine dai mahaifinta da mahaifiyarta ta nuna mata hotonsa kuma shine dai me gidan Abdulkabir, furta sunan ak da zuciyarta tayi yasa ta runtsa idanunta dan bata son kawowa zuciyarta shi .
mutumin data so kamar rai da ajali amman ya barta akan macen daya ya sha gaya mata baya sonta a can baya..
tacigaba da kallon mahaifinta tana jin tsantsar soyayyarsa na ratsata tana son ubanta bata da kamarsa ,duk da kasancewarta yar gaba da fatiha amman dole za'a kirasa da sunan mahaifinta, wannan farincikin kad'ai ya isa takarasa rayuwar datayi saura cikin jin dade.
" sun dade tana kuka shima prof kukan yake har salima "to yane zasuyi da kaddarar da gifta musu kowani bawa da silar zuwansa duniya sannan babu wanda ya isa ya gujewa kaddararsa.
a tsanake ta mike ta karasa ga kakanta wanda yayi shiru yana kallonsu cike da matsanancin tausayawa "kayi hakuri ka yafewa iyayena abinda suka aikata maka arayuwarsu ,samuwata a duniya ,kadarrasu ce babu tsimi babu dabara dole sai hkn ta faru "amman dan Allah kayi hakuri kabarsu su auri junansu a karo na biyu ina bukatar sucigaba da rayuwa a inuwa d'aya koda ban kasance cikakkiyar d'iya ba ina buk'atarsu atare ina son ganinsu cikin inuwa d'aya ka ..taimakeni dan Allah kabarsu su auri juna.... takarasa fad'ar hk tana me had'e hannunwanta duka tana rokonsa tana kuka ...
atsanake Alhaji mahmud ya kai hannunsa yakamota ta zauna gefensa yana murmushi irin nasu na manya cike da jin dadi kana yace "raguwar mata kawai dube yadda kike kuka dagani lusarin miji kike aure ,wannan kukan hk kamar zaki had'iyi zuciya cikin muryar kuka tace "please granpa ka ceci rayuwa iyayena suna bukatar junansu ...
murmushi yayi dan yaga ala'mun bata fahimci komai daya faru ba yasa yasoma magana cikin wasa da dry "ai tuni wannan maganar ta dad'e da wucewa acikin zuciyata" ni kaina cike da muradin sake d'aura idanuna akan iyayenki dake kanki nakeyi a kullun ," kaddara kuma mutun bai isa ya kankarewa kansa faruwata ba, zance auren iyayenki kuma tuni iyayenki sun mallaki junansu matsayin ma'aurata .
ta juyo da wani irin sauri zuciyarta na wani irin harbawa tana kallonsu atare suka gyad'a mata kai ala'mun hk ne "Alhamdullahi ta furta a k'asan ranta "Allah na gode maka daka nuna min wannan rana "a she wannan ranar zata zomin nan kusa ban sani ba ?
ta isa ta rugume iyayenta daya bayan daya tana murna Ammi tasa aka kira minsters da Dady dasuke parlour'n bak'i suzo suga ikon Allah, ai kuwa sun sha mamaki ganin su'ad nan dai akayi ta farinciki da murnar faruwar hk daga karshe ammi ta nasarwa su'ad Ak bai saketa ba da aurensa akanta jikinta na rawa tace "Ammi ya sakeni fa alokacin har tambayarsa Zeey tayi yace duka sakin yayi min idan ma duhun daya tsinci kansa ciki ne yasashi manta ai akwai shida tabbacin sakina dayayi barinaje na kawo miki ta mik'e cikin sauri ammi tabi bayanta da kallon cikin jikinta yafito sai dai bakowa zai tabbatar da cike gareta ba, kasamcewar cikin zumbulelen hijab take bata fi minti goma ba ta sake fitowa rike da farar takarda bata bude ba ta mik'awa Ammi.
Ammi ta numfasa kana tasoma bude farar takarda ta duba tana sakin murmushi tare da mikawa Dady shima dubawa yayi sannan ya mik'awa minster haka suka dinga pacing din takarda atsakaninsu har Prof Taufeek sai daya gani sannan Ammi ta janyo hannuta "zo ki zauna diyata da ala'mun tunda aka baki takadar fargaba bai barki kin budeta ba?
"amshi ki duba ki gani mijinki bai sake ki ba har yanzu igiyoyin aurensa na kanki jikinta na kirma ta amsa abinda tagani ya kusan zautar da tunaninta "to me hkn yake nufi Abdul bai saketa ba ....?
farinciki yakamata tayi ko akasin hk? tayiwa kanta tmbyr cike da matsanancin tsoro da tashin hankali wannan wace irin rana ce gareta me cike da tarin fariciki?
sosai ta tsurawa takadar idanu babu komai rubuce illa farar takarda empty , parlour'n ya d'auki shiru zuwa wani lokaci kafin daga baya Alhaji mahmud yayi musu nasiha me ratsa jiki daya danganci rayuwa aure sannan yasanyawa rayuwar auren salima albarka tare da fatan zaman lafiya me dourewa a tsakaninta da mijinta ..
bayan karramawa da mutunta ka da akayi musu ta fanin abinci na ban girma har da zaga dagin sukayi na
kusa ,sannan suka d'auki hanyar komawa gida cike da matsanancin farinciki da zumar wani sati Prof taufeek zai dawo ya d'auke salima tun cikin jirgi ambasodor yace "kar agayawa Ak abarshi tukun har zuwa wani lokaci ..
Daren ranar da Salima ta kwana gidan su sam ahalinta babu wanda ya runtsa yadda suka ga rana haka suka ga dare suna hiran yaushe gamo.
da suka isa gida ma Dady ya sake jawa Ammi kunne sosai akan karta kuskura ta sanarwa AK inda su'ad take har sai ya kara shiga hankalinsa .
******
ranar kusan kwanan farinciki Prof taufeek yayi duk kulawar da shema ke masa bai masa ba, hankalinsa gbdy na gurin sahebar ransa, gidansa dake banana estate ya yanke shawarar nan salema zata Zauna ita kuma shema zata cigaba a 1 thousand 4 ,cikin satin yayi duk abinda yakamata akan tarewar salima.
ranar lahadi yan'uwan salema suka dira agidan ammi ,an musu tarba ta musamman da mutunraka daga karshe sukaje sukaga inda salema zata zauna, iyayen salema sun nuna mata gata fiyye da tuninata ,duk da prof taufeek yace karsuyi wahalar kawo komai , amman sai da sukayi duk abinda sukasan anawa duk wata diya me kima da daraja agidan aurenta.
umman su'ad ta tare a hadadden gidanta wanda yasha kayan alatun more rayuwar duniya ,ahankali take bin d'akin da kallo tana mamakin irin duniyar prof ya kashe kamar wasu auren saurayi da budurwa ta dade zaune tare da rafka uban tagumi cikin zullumi da rashin sani madafa, yadda take hango rawar kansa akanta kad'ai yake d'aga mata hankali domin abubuwa yake kmr wani sabon matashin ango, abu me mahinmmaci datake hangowa atattare dashi bai wuce tsagwaron kauna dayake mata ba, musamman soyayyarta datake hangowa a yanzu acikin kwayar idanunsa.
yashigo d'akin bayan yayi wanka sanye cikin wata haddiyar jallabiya ruwan coffee colour yana baza kamshi me sanyi dadi ya jingina bynsa da jikin murfin k'ofar shigowa d'akin yana kallonta cikin hadadden shirinta dan sanye take cikin laulausar rigar bacci cike da matsanancin farinciki bakinsa ya kasa rufuwa yacigaba da kallonta "a yau bazei iya kwantata tarin murna da farinciki zuwan wannan ranar ba wannan lokacin, lokacine dayake cike da tsantsar nishadi da farinciki,tsawon lokaci yana tsaye agurin yana kallonta ,sihirtaccen kamshin turarenta na bugar masa da zuciya kafin ahankali yasoma takowa zuwa inda take itama ahankali ta taso suka rungume junansu suna murna kasancen ma'urata "cikin kunneta yayi mata rad'a "kina nan kamar yadda nasanki da wannan kamshi naki dake zautar dani," muje akwai tanadi me mahimmanci danayi mana daga yanzu mun shiga duniyar farinciki babu mu babu bak'inciki arayuwarmu .
yasoma tafiya daita har suka k'arasa atare suka zauna a bakin gado tare da riko tafin hannuta wani irin lumshe idanu yayi domin shi kad'ai yasan irin farincikin daya tsincin kansa saboda zamowarta mallakinsa, kallonsa tayi tare da sakin laulausan murmushi domin tasan tunanin dayake bai wuce kasan cewarsu tare cikin inuwa daya ba.
ta shafi gefen fuskarsa tare da bud'e bakinta tace "abban su'ad ..
ya bude kyakkyawa idanunsa ya zuba mata yana kallonta batare da yace komai ba "muje muyi alwala muyi sallah domin godiya ga mahalinmu daya nuna mana zuwan wannan rana..
yayi murmushi "ranar da muka so ganinta tun ganinyar kurciya ba Allah bai yin ba sai yanzu" tashi muje d'an ala hakikanin gaskiya jina nake tamkar sabon matashi "kai abban su'ad kafa tsufa..
"tsufa fa kikace ai namiji baya tsufa most especial agurin macen dayake tsantsar so," duk wani kulawa da gatan da kika rasa a shekarun baya zan tabbatar dana baki shi a yau..
"ni dai babu ruwana ni yanzu na girma nabarwa yara ,yayi laulausar murmushinsa bayi suka shiga sukayi alwala suka fito rike da hannun juna kamar zasu hadiye junansu yana gaya mata kalamai masu sanyi bayan sun idar da sallah ta kasa motsi tana zaune akan sallaya tana dubansa dan oredy shi ya rigada ya mik'e tsaye har ya isa kan gado maganganunsa kunya suke bata hannunsa ya yafitota ala'mun tazo sun dad'e suna bawa junansu kulawa daga k'arshe suka sake shiga bayi domin yin wanka tsarki ranar baccin barawo kasa dcaukarsu yayi da zarar sun runtsa idanunsu da zumar yin bacci sai subud'e domin ganinsu suke kamar zasu nemi juna su rasa acikin kwanaki wata irin kulawa Prof taufeek ke bawa Umman su'ad wadan hkn ke sake tabbatar mata da taufeek dinta daban yake acikin mazajen duniya, har take da yakinin bakowani nmj ne ke wulakanta mace ba byn ya amshi budurcinta a waje,