Showing 186001 words to 189000 words out of 420383 words

Chapter 63 - SAI KA AURENI DOLE BY AYSHA A BAGUDU.txt

dakin cikin zurfin tunani .
ahankali umma ta daga kan su'ad ta zauna a saman gadon ta meida kanta bisa cinyarta tare da daura hannuta akan sumar kanta tana shafawa ahankali ahankali .
"sannan ta kira sunanta cikin sanyi murya su'adullah.......
ahankali su'ad ta dago tare da sauke fararen idanunta bisa fuskar mahaifiyarta ,wanda kallo daya zaka yi mata ka tabbatar da cewa ba cikin natsuwa da walwala da kwanciyar hankali take ba .
tun byn da ummanta ta gaya mata komai dangane da rayuwarta ta kasa samun natsuwar zuciya.
umma taja ajiyar zuciya ta sauke kana numfasa.

"tace kiyi hkr diyata ki cire tarin damuwar danake hangowa cikin ranki da kwayar idanunki.
" ki kara daukar abinda ya Faru a matsayin kaddararki kenan ,babu tsumi babu dabara ta hk za'a samar dake, banyi tunanin byn nagaya miki komai daya faru tsakanina da mahaifinki zaki yi hkr ki rungumi kaddaraki irin hk ba,amman sai gashi kin bani mamaki fiyye da yadda nayi zato.
" sannan ni kaina naji dadin yadda kika fuskanceni da wankakar zuciya wanda nasan hkn yana da nasaba da zurfin ilmin da kika samu .
ita kaddaraka duk yadda tazowa mutun arayuwa hk zai amsheta ya rungumeta da hannu biyu biyu .
"dan hk ki tashi kije kiyi sallah tun lokacinta bai wuce ba.
tunda umma tasoma mgn batayi yunkurin cewa komai ba, amman duk bayaninta yana shiga cikin kunneta da ilahirin gangar jikinta ,yayinda take jin kanta ita din ba kowa bace face shegiya mara gata da galihu.

tana matukar jin ciwo da radadin kasancewarta yar gaba da fatiha, amman ya zatayi da rayuwar data samar daita?
ahankali ta mike tsaye daga kan cinyar umma tasoma daga kafafuwanta cikin sanyi jiki ta nufi bayi idanunta cike da ruwan hawaye , komai na rayuwar duniya yagama fice mata arai ,inda tasan hk iyayenta suka biyewa son zuciyarsu da batayi kasadar risking din life din ba.
alwala tasoma yi tana kuka har da shesheka wanda ummanta dake zaune daki tana jiyota itama kukan nadama da danasani take.

*******
washegari da safe tun karfe biyar saura AK ya tashi a bacci duk da cewar bai samu wani ishashen baccin kirki ba .
sbd tunanin halin da zeey dinsa take ciki, sai wajajen uku da rabi na dare sannan bacci barawo yasamu nasarar daukarsa.
jikinsa a sanyaye ya mike ya nufi bathroom yasamu yayi brush sannan yayi wanka tare da dauro alwala gbdy ya fito daga bayi ,yayi sallah sai lokacin ya kunna wayoyinsa da caji yakare tun jiya sbd kiraye kirayen police dan bincikar inda zeey take.
cikin hk cal din ammi yashigo lumshe mayatattun idanunsa yayi yana tuna halin daya barta jiya a sanadin rashin Zeey, kiran na kokarin tsinkewa ya daga "har yana jiyo lokacin data sauke ajiyar zuciya.
kafin tayi yunkurin cewa wani abu ya gaisheta muryar a kasalance yana sake lumshe mayatattun idanunsa.

a dan fusace ammi "tace abdulkabir ashe zaka iya runtsawa batare da kasan a wani hali zainab take ciki ba araye ko a mace?
" amman babu komai kacigaba da baccinka tunda ko mutuwa tayi baka da hasara sai mu Iyayenta muke da hasara.

runtse mayatattun idanunsa yayi sosai yana jin dacin mgnr da mahaifiyarsa ta gaya masa, wato ma duk abinda yake da kokarinsa akan 'batan zeey bata gani ba, may be sai ya kashe kansa ne akan nemanta sannan zatasan irin tashin hankali dayake ciki yayi mgnr cikin ranshi.

"can cikin yayi mgnr wanda da ji kasan yana cikin damuwa "ammi ki tausaya min , ni kaina ina cikin tashin hankali maramisaltuwa akan rashin Zeey fiyye daku, amman bai kamata kice min wai ban damu da halin datake ba yayi mgnr yana sauke numfashi kasa kasa kmr zaiyi kuka.
"yanzu kana ina? "kana sabon gidanka ne ko km kana cikin gidan nan ? tayi masa tmbyr ajere. "anan gidan na kwana amman yanxu nake shirin fitowa .
"ok ka fito yanzu kasameni a part din dady .

bangaren su'ad kuwa tana kwance a kusa da ummanta tana tunani yayinda jikinta ke sake yin sanyi adalilin matsayinta arayuwa ,nadamar abinda ta aikatawa rayuwarta tasjigayi tana tsiyayar hawaye taji jiniyar yan'sanda ta karade unguwarsu kafin ta farga har sunyi sorrounding din kofar gidansu da bindigoginsu har wasu sun fara shigowa cikin harabar gidansu da speeker tare da kiran sunan "idan su'ad tana ciki ta gaugauta miko kanta tun kafin mu bincikota da kanmu , wanda hkn zai kara mata laifi me girma.

umma najin an ambaci sunan su'ad ta zabura ta mike jikinta na kirma sai km ta fashe da wani irin mahaukacin kuka kirjinta na bugawa "tace yaushe zan fita cikin tashin hankali ?
daga wannan sai wannan me km kikayi su'ad da police sukaxo nemanki hk ?
takarasa mgnr tana karasawa bakin window ta dan zuge labule ,police tagani bila'addadi zagaye da compound kowanensu rike da bindigarsa take gabanta ya tsanata bugawa baita ba hatta su'ad sai data tsinci kaina cikin yanayi tsoro da tashin hankali.
ta tsaya tana karewa kanta kallo tsab wandon laigis ne baki ajikinta wanda ya manne mata a jiki da riga yellow iya gwiwarta me dogon hannu isa boyfriend jaket dake saman rigar long sleeve din dake sanye ajikinta wanda yasa hannu yellow rigar bayyana .
ahankali takarasa inda jerin canvers din suke ta dauki flat black canvers dinta tasoma sanyawa kafafunta tana duban agogon bangon parlour'nsu har tagama kirjinta na wani irin mahukacin buga da karfi wanda tarasa dalilin jin hk ,sannan wannan shine Karo na farko data ji tsoro ya ziyarci zuciyarta a game da police amman taki yarda wannan tsoron ya bayyana kanshi har yayi tasiri , ta isa ta dauki karamin bakin mayafi ta yane sumar kanta dashi ta isa bakin kofa tasoma kokarin bude kofa , daidai lokacin da police suka iso jikin kofar dakinsu.
" umma tayi saurin dakatar daita ina zaki su'ad ?
ko kina hauka ne bakiga ke police ke nema ba amman kike kokarin sanya kai ,ki kai kanki garesu?
agigice umma takarasa jera mata wadan nan tbmbayoyin karki damu umma ki bari naje domin ni din me laifi ce agurinsu km zan amsa laifina ,fatana kimin addua Allah yasa wannan fitar da zanyi yazamo silar shiriyata yasa wahalata tazo karshe kenan ,ni kaina nagaji da irin wannan rayuwar da nakeyi amman babu yadda zanyi sbd nice da kaina na jefa rayuwata cikin wannan tashin hankali maramisaltuwa tana kaiwa nan ta bude kofa ido 4 sukayi da police tsaye agabanta ya tsaita cikinta da bindiga.

umma tayi saurin fitowa tana kuka ta rike hannu su'ad gam cikin nata "babu inda zaki su'ad sai dai atafi dani , amman bazan bari su tafi dake ba sai nasan dalili .

daya daga cikin police din wanda ke jin hausa yace hjy karki yi mana irin wannan tmbyr idan kin damu kisan abinda tayi kina iya biyo mu office dinmu daga baya sai ki san abinda tayi.

"yanzu dai ta wuce muje su'ad tasoma kokarin zare hannuta cikin na ummanta amman umma ta rike hannuta gam tana kuka wiwi tmkr ranta zai fita tana basu hkr karsu tafi mata da yarinya ...

dayan police din "yace karki damu hjy da zarar mun gaba bincikenmu akanta muka tabbatar da bata da hannu ciki abinda muke zarginta zamu dawo miki daita har gida cikin koshin lfy .

hk umma naji tana gani aka tasa ketar su'ad gaba zuwa byn motar police suka bar gurin sai police station. itama take tabi bayansu.

suna isa umman su'ad na fitowa acikin adaidaita wanda kusan tare suka iso ,akayi upstairs daita police zagaye daita xuwa wani daki ita km umma tasamu guri ta tsaya jugun tana kuka.

ahankali aka soma yiwa su'ad tmbayoyi abinda ya dangaci rayuwarta ita km tana basu amsa daki daki hankalinta akwance tmkr wace bata cikin damuwa, har zuwa kan batan zeey kai tsaye batare da wata fargaba ba ko tsoro ta bayyanawa police zeey na hannuta ,wanda hkn yasa aka nufi office din commissioner daita .
yace kar a kuskura ata lafiyar jikinta suje daita inda ta boye zeey sannan idan sun dauko zeey, su dawo masa da su'ad akwai tmbayoyin da zai mata.

gaba police suka tasa su'da har bariga inda su ore ke tsare da Zeey suna gana mata azaba suna karasawa gurin sukayi sorrounding din gurin suka shiga harbe harbe dan su tashi hankalinsu ore.

******
shi kuwa AK koda yashigo part din dady ya iske hjy mahaifiyar dady'nsa da maman zeey sai ammi dake tsaye goye da hannuwanta duka abaya tana sintiri wanda yake nuna ala'mun tafisu shiga tashin hankali.
"bakinsa dauke da sallama yakarasa shigowa cikin parlour'n sosai zuwa inda dady yake zaune yana shan coffe hankalinsa kwance har abun yaso bashi haushi ,wato ma shi dady bai damu da abinda yake faruwa ba.

"dady ya karba masa sallamarsa fuskarsa a daure yacigaba da kurba coffe dinsa .
ahankali AK ya bude bakinsa ya gaida dady da sauran mutanen dake zaune agurin.

"cikin dakewa dady ya kar'ba masa tare da cewa masa ya ake ciki da zance masu bincike akan 'batan zainab?
sai daya sauke naunauyen ajiyar zuciya sannan "yace police na kan aikinsu yanzu hk nasan sun isa gidan su yarinyar nan....

shr ne ya dan ratsa parlour'n can dady ya ajiye cup din coffe dake hannusa ya waigo tsaitin da AK yake zaune yana dubansa sannan yace ina fatan basawa kayi ayi arest dinta ba?
ya jefa masa tmbyr ransa abace.

tun kafin AK yace wani abu ammi "tayi saurin cewa dan girman allah dady meyasa kake irin hk?

"meyasa kafi son tantiriyar yarinyar nan akan jininka ?

ranta a bace ta maida idanunta kan AK ta tsura masa idanunta "karkayi sanya akan daukar hukunci akan duk me hannu acikin batan zainab .

"hjy tace shine abinda ya dace ita yarinyar da ake zargi wacece ita?

" waye ubanta agarin nan da zaka dinga daure mata gindi ?
"ko dole ne sai jikana ya aureta nace dole ne sai aureta, kai adamu hjy takira sunansa kafi idona tun wuri wlh banason jin ka sake cewa komai akan mgnr nan matsawar ba goyon baya zaka bamu.

"cike da sanyi murya dady yace hjy kiyi hkr amman ni nasan abinda nakeyi , shiyasa nace abi lamarin nan ahankali ita kanta baraka ta kasa fahimtata ne kawai amman zanyi kmr yadda kikace din .

"da dai yafiye maka muhawara ce ta barke tsakaninsu ta yadda za'a yi,cikin hk kiran police yashigo wayar ak ,yana dauka suka sanar masa da sun gano inda zeey take yanzu hk suna tare da su'ad din domin ta su shiga inda ta boyeta ,AK ya zabura ya mike tsaye yana cigaba da receive din cal ,yana duban iyayensa dake zaune tsuru tsuru sannan "yace ok idan anga zeey din kuzo min daita gida kai tsaye ita km yarinyar da gang dinta ayi aresting dinsu ok sir.

hmmmm...! dady ya sake naunayen ajiyar zuciya tare da numfasawa sannan ya fara mgn "hakika abdulkabir kana son biyewa son ran mahaifiyarka domin sake aikata babban kuskuren, wanda ita kanta zata iya shiga matsala daga baya.
kuskuren da suka tafka a baya nake gudar mata sake faruwarsa ,amman taki fahimatata ,ke kanki hjy da ke ma, ya nuna maman zeey babu abinda bakusani ba ni kaina bawai ina bawa abdulkabir goyon bayan auren yarinyar bane dole, abinda zai je ya dawo din nake gudun afkuwarsa, amman babu komai tashi kaje.

uhm dady ka daina kokarin hada yarona da maseefun da suka faru abaya da yarda allah babu abinda zai sameshi sai alkhari km muddin ina raye...... datse harshenta tayi da sauri sbd wani irin kallo da dady ya wurgama sannan yace "ki karasa man ai kinsan illar abinda hkn ya jawo wanda daga baya nadama ce zalla mara amfani.
dady naga fadar hk yayi daidai da jiniyar police ya karade unguwar suka karaso gidan.
gbdynsu suka mike tsaye sukayi waje ranga ranga AK yaga an fito da zeey dinsa rai hannun Allah rege regen karasawa gareta suke gbdynsu, yayinda mutane dake cikin part din ammi dana baki suka firfito harabar gidan.

cikin sauri AK ya isa gareta yana fadin "zeey me suka miki, ina ke miki ciwo ?

gbdy AK ya rude sai jera mata tmbayoyin yakeyi ya ma rasa me yakamata ya farayi mata zeey kuwa cikin tamboyinsa babu wanda ta samu damar amsawa illa wani irin nishi da take fiddawa da sallati samakon jin jiki datayi dan bakaramar azaba taci agurinsu ore ba.
ga babu ci babu sha a kwana dayan datayi agurinsu babu irin azabar da basu gana mata ba. gani irin juyi datake tana rike ciki ai ak bai san sanda ya mike cikin gigicwa ya nufi dakinsa a guje dan dauko makulin .

dube dube yake yi cikin dakin nashi yama rasa inda key din yake dan gbdy a rude yake.
can ya hangoshi saman mirrow da sauri ya dauko ya fito dakin ya dawo da gudu inda jama'a ke tsaye cirkocirko suna kuka ita km zeey sai murkususu take ajikin ammi tana rike ciki da sauri yakaraso ya amsheta daidai lokacin da numfashinta ya dauke cak ...
durkursawa yayi kasa yana kiran sunanta zainab... Zainab.... tare taba kumatunta amman ina babu numfashi atare daita dangi suka taru akansa suna kuka tare da tmbyr ta mutuko?
hk ma police din dake tsaye sukayi kansu suna kallonta take suka gane suma tayi ,daman tunda suka dauko a sume take sai da suka yayyafa mata ruwa ta farka sun so wucewa hospital daita amman jin yace suzo masa daita yasa, hada baki police sukayi gurin cewa suma tayi ba mutuwa tayi ba.
ai AK najin hk daukarta yayi da sauri, ammi na masa mgnr yabi ahankali ya tsaya wani ya tukasu amman ina hankalinsa kwata kwata baya jikinsa dan ko jinta bai yi, inda motarsa ke pake ya nufa , yakarsa ya bude kofar baya ya kwantar daita aunty bilkisu kanwar mahaifin zeey da aunty malika suka shiga motar hankalinsu a tashe shima cikin hanzari ya zagaya yashiga mazaunin direba , me gadin na ganin hk yayi saurin wangeme masa get din gidan.
aguje AK ya fige motar kai tsaye asibitinsu ya nufa daita.
likitoci suka amsheta cikin gaugauwa suka nufi imagecy room daita tsawon lokaci suna kanta suna kokarin dawo da numfashinta .

zeey kuwa sai farkawa tayi ta ganta a gadon hospital, ta fahimci hkn ne ta hanyar ganin wata nurse a tsaye akanta ,dan tana bude idonta daita ta fara cin karo.
tana kokarin sanya mata karin ruwa tayi saurin hanzarin mikewa zaune tana rarraba ido tare da tunanin abinda daya haddasa mata zuwa hospital, aunty bilki ce takaraso gareta jikinta a matukar sanyaye sai dai kallo daya tayi mata abinda ya faru yashiga dawowa cikin kwanyarta, idanunta kmr gauta al'amar taci uwar wahalar da kuka ta koshi, km har lokacin kuka take.

ta rike cikinta tana murkususu yunwa ga makoshinta ya bushe, nurse tasoma yunkurin rike hannuta zeey ta fizge hannuta daga rikon da nurse tayi mata ta kamkame jikinta waje daya tana mgn ahankali "wayyohhly Allah mutuwa zanyi yunwa nake ji kubani abinci naci sabatun yunwa take amman babu wanda yaji sbd muryarta a dace take.
sai km tayi luuu! ta zame kan gadon ta sume daga aunty bilki har nurse suka gigice har aka rasa wanda zaiyi wani abu akai .
aunty bilki tayo kanta tana girgizata cike da matsanancin tashin hankali da kiran sunanta cikin karaji, yayinda kukan datake rikewa tun dazu ya kwace mata.
ita kuwa nurse da gudu ta fice daga dakin zuwa kiran doctor atare suka dawo dakin da doctor a wannan karon har da ammi da maman zeey da AK suka biyo bayansu.

da likita da nures suka shiga yayyafa mata ruwa ai kuwa ta bude idaunta tare da sakin wata ajiyar zuciya ahankali danunta ya dauro akan AK dake tsaye kusa daita hannunta cikin nasa ,yayinda fuskarsa take tattare cikin yanayin na rudani. doctor naga dubata ya juya tare da cewa yana son ganin ak zuwa office dinsa.

koda daya shiga office din likinta, kujerar dake facing ta likitan yaja ya zauna suna fuskantar juna yana tmbyrsa meye matsalar zeey ,ahankali doctor yasoma bayani atsanake.

" bata tare da wata matsala byn raunukan dake jikinta sai km yunwa dake dawainiya daita, amman ka kwantar da hankalinka Inshaallahu zata samu sauki zamuyi duk abinda yakamata,amman yanzu a hanzarta kawo mata abinci da ruwan zafi.
AK ya mike tsaye tare da cewa " yanzu kuwa za'a kawo mata yayi sallami da doctor tare da kiran aunty bilki ya damka mata wasu kudi a hannunta koda za'a bukaci wani abu sannan yagayawa ammi abinda ake bukata, tare da ammi da aunty malika suka baro hospital din ya saukesu agida shi km ya wuce xuwa police station.

kai tsaye office din commissionier ya zarce yana cika yana batsewa yana shiga ya iske su'ad tsaye tare da commission suna zantawa a tsakaninsu shi kuwa AK ko kallon inda take tsaye baiyi ba yasamu guri ya zauna yana watsa mata kallon baza, itama abanzace take kallonsa kmr yadda yake aiko mata da nashi kallo zuciyarta na tafasa. rainshi yayi maseefar baci ganin kallon banza da take masa.

" hkn yasa bai san sanda yace dan ubanki ni kikewa wannan banza kallo?
dakata mlm ta katseshi tare da daga masa hannu karka sake zagin ubana idan kai baka san ciwon naka uban ba ,ni nasan ciwon nawa takarasa mgnr tana harararsa...
" ance ubanki waye shi uban naki da baza'a zageshi ba ?
"kai ma dan uban...atsawace ya dakatar daita ta hanyar daga hannunsa zai zabga mata Mari ,yaji sautin wata muryar ta doki dodon kunnensa

Chapters

Related Ebooks
19, September 2025
Aisha Auwal

Wow

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login