Showing 405001 words to 408000 words out of 420383 words
Chapter 136 - SAI KA AURENI DOLE BY AYSHA A BAGUDU.txt
su'ad wace ta dade da shigo cikin parlour'n da turtsetsen cikinta daya soma girma, ta tsaya abakin kofar tun soma wayarsa tana dubansa ahankali , kmr ance ya waigo inda take tsaye idanunsa suka sauka akanta ta mugun tsaresa da fararen idanunta tana kallonsa.
ganinta yasa gbdy ya nemi bacin ransa ya rasa , ajiye system dinsa yayi akan kujera ya mike tsaye ya nufi gurinta yayi tsuguno agabanta tare da riko tafukan hannayenta yana murza yan yatsun hannunta ahankali muryarsa a kasalance yace "love you bbynah ya fad'i hk yana me shafo cikinta yana jin tsantsar farinciki "ya bby nah yake?
ta kirkiro murmushin dole tare da yi masa fari da idanu take yaji tamkar ya sume agurin ya mike tsaye yana dubanta ita din ma shi take kallo ahankali ta kai d'an yatsanta tana shafa lab'bansa kusan minti goma tana shafa lip's dinsa batare da tace masa komai ba duk da mgn take son yi masa akan wayar dataji yagama a yanzu ,amman tana jin tsoro abinda zai mata.
" tarasa wani irin halintar mutun ne abdul dinta, ya fiyye zafin zuciya da saurin fushi akan komai kwanakin baya taji ya furta ya yafewa akil abinda yayi masa. atunaninta mutuwarsa a yanzu zaiji babu dadi aransa ,matsawar yafiyar dayayi masa da gaske ne yakamata ace yaje gaisuwar mutuwarsa.
ahankali tasanyawa jikinta jarumta tare da karfin halin soma mgn ta hanyar somawa da kiran sunansa "abdul...
" rungumeta tsam yayi ajikinsa amadadin ya amsa mata.
"da hankalinka da tunaninka kana muslimi ka rinka biyewa sharrin zuciya dana sheid'an ," haba mijina ka daina wannan akidar d'aukar zafi irin hk abinda yarigada ya wuce abar shi a ya wuce,bafa zaka taba kankare faruwa hkn ba acikin kaddararka..
"ya abdul... yayi saurin d'agowa tare da waigowa bayansa yaga ko eiman ce takirasa da hakan ,sai dai bai ga kowa ba hkn ya tabbatar masa da ita din ce takirasa da hkn "ya abdul meye matsayina agurinka?
ak ya rausayar da k'ansa sannan yasoma mgn ahankali "bazan iya misalta matsayinki ba agurina, sai dai nasan kin zarta komai azuciyata" kece komai na, kece duniyar abdulkabir kece rayuwarsa, "rayuwar da babu ke acikinta is nothing "kin taka matsayi iri iri acikin zuciyata har bansa abinda, zance ba..
" to ina son dan Allah da girman matsayina gareka kayi hakuri komai ya wuce acikin zuciyarka ,ka shirya kuje ta'aziyar akil idan kayi hkn zanji dadi sosai .
ak yayi murmushi yana dubanta ita da cikin jikinta " angama uwar gidana a duniya da lahira zanyi yadda kikace .
Allah ya jikan muslimai gbdy yasa idan tamu mutuwar tazo mucika da kyau da imani ..
"ameen nagode sosai mijina Allah yabarni da kai muddin rai "yace ameen tare da kissing din cikinta .
hannunsa ta riko zuwa bedroom dinsu taja shi suka lula wata duniyar me cike da gardi da sikarin dadi.
rungume take ajikinsa tana aikin sarrafa shi ta yadda zaiji dadi sosai, a zuciyarsa yana me k'ara sakankancewa su'ad dinsa ta bance acikin tarin mata ,su'ad ita ce kalar macen data dace dashi, ya sake sakin sanyayiyar ajiyar xuciya ya kai hannunsa yana shafa tsakiyar bayanta .
washegari su'ad na tashi daga bacci brush kad'ai tasamu tayi ta nufi kitchen dan tasamar musu abinda zasuci ak kuma ya nufi bathroom yayi wanka yayi sallah yana gama sallah shima kitchen yabiyota dan ya taimaka mata dan tunda cikinta ya tsufa dashi akeyin komai agidan, tunda ta hana a d'aukar mata me aiki acewarta bazata d'auki me aiki ba tun yanzu sai nan gaba.
tana cikin fere dankali yakaraso ya tsaya abayanta ya riko hannuta dake rike da wuka ta waigo ahankali tana masa murmushi "no karbashi na kusan gamawa "ya girgiza kai "aikin me nakeyi da zan zauna ina kallo kina aiki?
tayi tsadadden murmushinta dake kara mata kyau tare da kai bakinta kan lip's dinsa ta tsotsa sannan suka cigaba da aikin, har datagama, sai data kammala table sannan ta nufi bathroom tayo wanka ta shirya tsaf cikin kananan kaya riga da wando, dan cikinta baya hanata sanya duk kayan dataga dama ,tayi kyau sosai sai baza kamshi take tana isa dining ak dake zaune zaman jiranta ya tsura mata mayatattun idanunsa yana kallon yadda take tafiya komai nata a natse takeyinsa sam bata da rawar Kai, ahankali taja kujera xata zauna "no no kin mata ga gurin zamanki yayi mata nuni da kan cinyarsa?
tayi murmushi ta zauna kan cinyarsa tana shafa fuskarsa sai da suka gama lashe lashe da tande tande sannan fa suka fara cin abinci tana bashi yana bata har suka koshi .
ak yakarasa sabon gidansa dake sun shine estate har ma sun tare mutane nata zuwa tayasu murna.
mahaifan su'ad sun zo dubata lokacin da umman su'ad taganta zubawa su'ad ido tayi tana kallon yadda tasauya dan tunda ta dawo basu zo gidan ba sai da ammi ta matsa musu tukun .
ahankali ta dinga kallon irin dukiyar da ak ya kashewa diyarta, su'ad kuwa sai murna take bata kitchen bata parlour, tana kokarin had'o musu ababen motsa baki.
ko nauyin cikin jikinta bataji ak ya fito ya gaisa dasu a dakile yace "shi zai fita dan har lokacin bai daina jin haushinsu ba.
ko Allah yasanya alkhairi da suke masa bai tsaya amsawa ba yayi gaba.
"shi gbdy yarasa meyasa baya sonsu hatta d'an burbushin son dayakewa sir mahbub ya kau a yanzu dayasan shine asalin uncle dinsa ne kuma uban da yayi silar zuwan Matarsa duniya ..
yana fita umman su'ad tace "su'ad ki zauna ki huta mufa akoshenmu muke ,mu xo muga inda kike da tabbatar da lafiyarki. su'ad tayi murmushi "haba umma meye nayi doctor ma yace na dinga motsa jikina sosai, can tayi k!asa da muryarta sosai ta yadda babanta baxai ji abinda zata fada ba "ummanah Allah Allah nake na haifi cikin jikina nabaku kusamu masu debe muku kewa a gida ..
umma ta jinjina kai tare da duban inda mahaifinta yake zaune dan shima burinsa kenan ta haifa masa ya'ya, bata sawa ranta samun kyautar daga garesu ba saboda tasan yadda AK yake bazai ta'ba yarda da hkn ba ,dan hk ma bazata wahalar da ranta gurin sanyawa ranta ba.
da zasu tafi taji kmr karsu tafi su barta dan taji dadin kasancewa tare da iyayenta sosai, kwana biyu tsakani ammi taxo ta iske ak yana zaune a parlour tayi sallama yana ganinta yayi saurin tashi ya tarota hkn yayi daidai da shigowar su'ad cikin parlour'n ta nufi ammi ta rungumeta tana murna ganinta "wayyo Allah amminah nifa yar gata ce gaba da baya shekaranjiya su abba da umma sukaxo yau kuma ga ammina ..
"ammi ki zauna ta nufi hanyar kitchen da d'an saurinta ammi tabita da kallo ganin yadda tayi bala'in kyau tamkr ata'bata jini ya fito ga cikin jikinta yayi mata dass kmr an kife kwarya tazama wata abar sha'awa ,ak ya gaishe da ammi ta amsa cikin sakin fuska su'ad ta karrama ammi da abun mots baki har sai da ammi tace abarta hk ya isa ba xama taxoyi ba taxo ne ta dubasu .
ammi bata wani jima ba tace zata wuce suka rakota har harabar gidan inda take cewa ak "kai yakamata fa su'ad ta dawo gida haihuwa hkn saboda haihuwar fari ce i think cikinta yashiga wata takwas da doriya?
ak najin hk take yayi kicin kicin da rai sannan yace "eh lisafinki hk ne sai dai babu inda zata ammi nifa bana ra'ayin zuwa wanka jegon nan da'ake wani zuwa kwata kwata baya cikin tsarina..
ran ammi yasoma 'bace ta dubi su'ad dake tsaye tana dubansu tace "ke karki soma yarda da wannan tsarin nasa cutarki zai yi, ki hadva kayanki wani sati zanzo na tafi dake ..
su'ad tayi saurin cewa 'to ammi ko ma nabiki ne yanzu mu wuce, AK ya watsa mata harara tare da cewa "babu fa inda zaki malama dakike wani saurin amsawa ," ammi muje na sauke ki dan Allah , nifa yanzu abun a tausayamin ne zamanta kusadani shine kwanciyar hankalina idan kuma kin matsa lallai sai takoma gida sai dai mu tattaro mu dawo gabadaya .
"da wannan dabarar yasamu yaje ya kai ammi ya dawo ya iske su'ad zaune tana shan Fruit , bayanta ya zagayo tare da d'aura kansa a kafafarta yana goga mata sumar kanshi "sannu da zuwa har ka dawo?
yace "uhm "yanzu ni ba abun tausayi bane da kike kokarin barina 'yar kulawar ma danake samu tayi rauni ko ,"to abarmin ke ko kallon fuskarki na dingayi.
su'ad tayi murmushi tace "abdul kenan babu hakuri "amman ai kasan ina iyakar kokarina akanka ko ?
"yanzu me kake so ka fad'a min ko goyo ne zan goyaka i promise you .
yayi dry yace "dawani karfi zaki goyani?
"da karfina mana ya kwashe da wata dry yace" ai ko ina hawa bayanki zaki fara nakudar dole "kija min maseefa ina zaman zamana, ta lagwabe ajikinsa yana wasa da jelar kitson kanta.
lokacin da cikin su'ad yacika wata tara yayi wani irin girma na ban mamaki kowa yaganta sai yayi mata sannu zama da kyar tashi da kyar ,shi kansa AK daya hanata komawa gidan ammi a takure yake dan yayi bala'i tausaya mata gani Yadda ta kunbura dan EDD dinta ya cika har ya wuce,amman haihuwa shiru ammi ta sake yiwa ak zance "abdul ka kawo yarinyar na ta haihu a gida saboda kai daita duk baku da exprence akan haihuwa ,kar haihuwar tazo mata cikin dare kurasa yadda zakuyi dan komai zai iya faruwa azo ana da'ansani zantukkan ammi suka sanyaya masa jiki ,gashi baya son rasa matarsa wannan tunanin yasa yaji hankalinsa ya tashi matuka dan hk ya tattarata yayi gidan ammi daita tunda ta koma gidan ammi kullun yana gidan safe da yamma har ammi tace "ya tattaro kayansa kawai ya dawo shima hb wani irin jaraba ne da tsohon ciki baza'a bar yarinya ya huta ba a dinga na nukurkusanta kenan .
yana jin zantuttuka ammi kuma yasan sarai abinda take nufi, amman ya make tunda shi yasan bawani abu yake mata ba daya wuce kulawa, shi kansa tausayi take bashi a halin datake ciki gbdy ma jiyayi sha'awarsa ta tsaya cak, hkn ya tabbatar masa da ita din yake so bawani abu nata ba.
ranar wata al'hamis su'ad ta tashi da ciwon nakuda kafin akaita hospital har ta haihu agida ,ta haifi 'yan'biyu mace da nmj ,santalelen yaronta kamar ubansa sak tmkr yayi kaki, da santaleliyar yarinyarta kamarta sak ,kuma duk suna cikin koshin lfy ita da bby's," fad'ar murna gun ak da ammi da umman su'ad har ma da dagin tmkr bata baki baki ne.
bakin ak yaki rufuwa saboda tsananin murna da farinciki rana suna bby's sukaci sunan dady da ammi baraka da Adam ake kiran nmj da farhan macen kuma da ihsan, bakaramin 'barnar kudi ak yayi ba a wannan haihuwar da aka masa. dan hatta ma'aikatansa sai da suka san me gidansu yana cikin farinciki dan har karin albashi yayi musu, hk ma umman su'ad da danginta sunyi kokari matuka ,madam ma shemah ba'a barta abaya wajen nuna bajinta, yan biyu sun sha Kyauta agurin jamar gari .
su'ad tacigaba da zama wankan jego tare da ammi, tana samun kulawa sosai dan wani lokacin idan yaran sun tashi cikin dare su'ad na tashi ,itama ammi ke tashi su'ad nabawa daya nono ita kuma ammi zata had'awa daya madara dan nono uwar bazai ishesu ba.
su'ad na tare da ammi har byn arbain, sai da sukayi wata uku sannan suka fara shirin komawa, ammi tasamar mata mai aiki domin kula da yaran.
********
yau tsayin wata uku kenan da rasa zeey dakayi ,mafi yawa daga cikin yan'uwa sun taya mama jimamin abinda ya faru wasu kuma Allah ya kara suke mata ,acewarsu kyakyayi koma kan mashekiya ne ya faru da zeey ,ita dai mama a kowani lokaci ta tuna da tilon diyarta sai ta zubda hawaye hkn yasa duk idanunta sun gama kod'ewa tarasa wazata tunkara da matsalarta, domin a nemo mata diyarta ko babu komai takasance tare daita, yafi batasan inda take ba.
yanxu hk duk abun duniya yabi ya dameta kallo daya zakayiwa mama kasan tana cikin tashin hankali .
shekaran twins daya da rabi su'ad ta sake haihuwa tasu d'a namiji aka sanya masa emran ko wannan haihuwar bakaramin murna ak yayi ba.
*bayan shekara hudu*
duk inda mutun ya kai ga tunanin su'ad zatakasance ta wuce gurin ,ta had'u takoina zuciyarta na tsaye kyam akan kaunar mijinta da yaranta guda uku da allah ya albarkace da samu.
tabangaren ak ma sosai yake jin dadin zama daita saboda yadda take tsantsar kulawa dashi, saboda tana bashi farinciki sosai basu da matsala idan ma akwai matsalar bata wuce guri daya ba,guri daya kuwa shine bai wuce yadda take runtse idanunta ta murzawa zuciyarsa rashin tausayi ba akan baro masa yara datake agidan ummanta ba ,a duk sanda zata sai ta baro daya daga cikisu ko ihsan ko farhan, wanda hkn ke maseefar 'bata masa rai .
kuma yasha gaya mata baya son yaransa nayi nisa dashi , akwai sanda taje yini gidan ta dawo babu ihsan ,ko zama bai bari tayi ba gbdy ya hanata sukuni, ya dinga zuba mata ruwan bala'i "yace takoma taje ta d'auko masa yarinyarsa tabashi hkrin duniya yaki .
ta dinga tunanin yadda zata koma ta amso yarinyar.
ganin bata da niyyar komawa ya mike a harzuke yana huci yace "kinsa Allah wallahi bazaki zauna cikin gidan nan ba sai kin koma ki zo min da yarinyata idan ba hk abakacin aurenki , hk tanaji tana gani tasa direbanta ya meidaita ta d'auko yarinyar akasamu zaman lfy .
ko gidan ammi baya yarda akaisu kwana sai yini kuma tasan dan duk kar suje gurin mahaifiyarta ne, Amman ta danni zuciyarta dan a zauna lfy ,acikin wannan lokacin sulaiman kanin salema ya bude campany buga atamfofi duk wata atamfa dazakaje conotoun dominta zaka samu a
S. M .Y wanda sanadin hk zamansa yafi karfi a Nigeria har yayi aure anan lagos .
yan biyu dinta sunyi wayo sosai kmr ba 3years ba magana abakinsu kmr me ,duk abinda akayi agidan babansu na dawo zasu gaya masa wata rana, tazo gidansu gaida ummanta kmr yadda tasaba xuwa lokaci zuwa lokaci ,dazata wuce tabar twin's da suyiwa grama dinsu hutu dan tun last week suka samu hutun school, kuma tun lokacin suka dameta zasu gurin grama da granfa "tace suje su tmbyi babansu idan yabarsu shikenan.
AK ya amince suje sai da kwana biyu yace suyi su dawo, zuwan nasu bawai yaso hkn bane kawai dai babu yadda zayi ne.
yanzu dazata barsu bakaramin dadi sukaji ba sunata murna da tsalle tsalle ita kanta umman murna take da kasancewarsu har waje tarakata tana mata nasihohi akan zaman aure masu ratsa zuciya .
washegari hayaniyar farhan da ihsan ne suka tashi prof daga bacci sai faman tsalle tsalle suke acikin parlour'n dole tasanya ya fito suna ganinsa suka ruga aguje suna rige rige suka makaleshi suna murna ganinsa, hk yayi da shigowar umma cikin falon tace "halan nan kun matsa dan tsohon mijina ko?
prof yayi murmushi yana shafa kan yaran yace "yanzu waye babba acikinku?
kowanensu yayi saurin cewa "ni ne granpa"
prof ya km yin murmushi yace "to shikenan gbdynku duk manya ne tunda babu wanda ya girmi wani yaran sukayita tsalle murna Umman su'ad tace "gafa table can yagama kammalauwa kada kabiye ma wadan nan yaran.
prof yace "ai gamu nan zuwa da yammanshi aka kawo mahmud dan gidan sulaiman nan fa gidan ya sake hargitsewa da guje guje umma ta dinga kafkaf da yaran ak, dan kar suji ciwo ga yaran da shegen kiriniyar tsiya, tafison yadda sukaxo lfy su koma lfy batare da wani abu ya ta'ba lfyr jikinsu ba.
bayan kwana biyu AK yaga ba'a dawo masa da yaransa ba, kuma daman ya aiyana aransa ba'za'a dawo dasu on-time ba kmr yadda yace suyi kwana biyu su dawo, dan hk daga office kai tsaye gidan umman su'ad ya wuce.
Sallama yayi fuskarsa a d'aure kmr wanda aka aikowa da sakon mutuwa sannan yakarasa shigowa cikin parlour'n ,umma dake tsaye cikin kitchen tana kamawa me aikinta aikin daya danganci na me gidan ne kasancewar a gurinta yake .
tsai tayi da ranta tare da cire hannuta cikin aikin ta amsa sallamarsa ta fito daga cikin kitchen din tana dubansa ranta a sake.
ya ja ya tsaya yana gaisheta muryarsa adake yaransa najin sautin muryasa suka fito da sauri suna murnar ganinsa.
ihsan tazo da gudu ta rumgumeshi tana cewa" Dady'na oyoyo "kaima kazo gidan grama ne?tayi mgn cikin muryarta na yara.
Zuciyarsa tayi sanyi kad'an saboda ganin fuskar kyakkyawar diyarsa mafi soyuwa cikin ranshi, ya d'aura hannushisa bisa kanta yana shafawa had'e da lumshe mayatattun idanunsa farhan shima ya yakaraso jikinsa shima suka makaleshi , sanye farhan yake cikin farar singlet da gajeren wando irin na kananun yara .
Umma wace taji wani iri ajikinta sbd jin kunyar sirikin nata tace "ga gurin zama ka zauna Man ta fadi hk tana Me nuna masa kan kujera , girgiza kanshi yayi alamun a'a tare da cewa "
Kai farhan ina kayanku suke nazo wucewa daku ne.... ?
take yaran suka d'auke wuta suka sauya walwalarsu ta d'auke dan suna matukar jin dadin zaman gidan, dan grama dinsu na kula dasu sosai Duk abinda suke so shi take musu .
farhan ne yasoma mgn "Dady pls kabarmu muna enjoy din zama da grama..
ya kamo hannu yaron kmr zaiyi mgn sai km ya fasa