Showing 45001 words to 48000 words out of 420383 words

Chapter 16 - SAI KA AURENI DOLE BY AYSHA A BAGUDU.txt

ido yana kallonta ya tabbatar Itama tashiga damuwa fiyye dashi yasanya tafin hannushi ya shafo fuskarta zuwa kirjinta come on baby bana son ganinki cikin damuwa, onye Tayi raurau da idanunta alamun son yin kuka shiiiiii karki sake Ki min kuka ya fadi hk yana janyota zuwa jikinsa yana rarrashita tare da Shafa kwarin bayanta meyye abin kuka ni da nace zanje dake Dan hk Ki shirya kawai zanyi miki viza..
tayi murmushin jin dadi tana sake shigewa cikin jikinsa tare da shafo fadadden kirjinshi Tana lumshe ido..


Zeey tana zaune a parlour jugun Ta rasa meke damunta Duk abin duniya ya dameta tarasa meke Yi mata dadi Duk yadda taso tayi Domin kawar da AK daga cikin zuciyarta takasa .abin bakincikin ma akoda yaushe kaunarsa da soyayyarsa sake karuwa suke da shiga kowane shashi dake gangar jikinta tmkr daga sama Ta jiyo sautin muryarsa yana sallama tai firgigib Ta dawo cikin hayacinta maimakon Ta amsa sallamar da yayi sai MA ta dauke kanta tmkr bata ganshi ba. Ta mike a fusace zata bar parlour taji wani jiri yana neman daukarta dole tasa Ta koma ta zauna AK yakarasa inda Take zaune yace hb Zeey meye duniya.. Dan me Zaki kulla gaba atsakaninmu byn ni bance Miki bana sonki ba.
Zeey Ta watsa masa wata uwar harara ta motsa bakinta ni baka da abinda zakace min yaya. ka Min shr kawai AK yayi murmushi yana Dan kamo lip's dinsa na Kasa kai Dan Allah sister Ki daina fushi Dani Duk kin saka na tsinci kaina cikin Damuwa pls Zeey baby kada muyi hk dake .
Zeey tayi masa banza bata sake ce masa kala ba har yagama mgnrsa yagaji yace ta kawo masa fresh milk kmr tace masa bazataje ba sai km taga rashin dacewar hkn Dan hk Ta tashi ta nufi fridge Ta dauko masa tana bashi bata sake tsayawa ba tayi tafiyarta ta varshi nan...

Yau yaje gurin onye sai dai yataki rashin saa sbd yauMa fama take Da matsanancin ciwon mara ya yunkura zai tashi tayi saurin riko tafin hannushi yace maTa sannu Ki kwanta da yamma zanzo na kaiki hospital a shagwabe tace ni bazanje ba.
ya Kare mata kallon tsab yace sbd me bazaki ba?
Tace ni ni Nagaji da shan mganin hospital byn GA magani ciwona agida ..
AK ya tabe baki yanacigaba da kallonta aranshi kuwa yace baki da hankali idan har sai nayi sex dake zaki warke Ciwon Marar ya dade bai kasheki ba. Amman abayyane cewa yayi OK to ni zanje gurinsu musty in dawo naga yadda yanayin Jikinki yayi idan da sauki fine idan km babu dole kiga doctor..

Wasa Wasa fa shakuwa me tsanani tashiga tsakanin onye da AK kowane yana ji da dan'uwansa sannan basa kaunar ganin bacin rai juna GA special kulawar da onye kebawa AK ta wuce misali tmkr ta lasheshi hkn datake masa yasa shakuwarsu ya kara samun masuguni azuciyarsa kwata kwata itama bata iya komai sai dashi hk shima kowani hali yake yana tare da tunaninta musty da Malik babu abinda suke masa sai shegentaka wai da alamun ya kusan ruftawa cikin shaukin kaunarta ya tabe baki yana cewa Baku da hankali nifa ba sonta nike ba kawai dai a huta.
Ina jin dadin mu'amula daita kunga kuwa dole nabata , kulawa tunda nima ina morarta son raina.

Byn wani lokaci Dady yagayamasa yasoma shirinsa at any time zance tafiyarshi zai tashi. AK yace shi a shirye yake shi kawai yake jira komai na tafiyarsa yagama shiryawa.
Yayinda zuciyarsa shi kadai yasan abinda yake shiryawa wannan tafiyar tasa sannan yasoma yashiryawa onye nata shirin .

Gayadaya cikin kwanankin nan babu abinda yake ta kokari yin sai yaga yayiwa onye viza..


Ammi ta sake runtsa Zeey cikin daki Ta dinga y imata tmbayoyi iri akan abinda ke faruwa tsakaninta da AK Amman Zeey tayi zurfin ciki tace babu komai.

AK yashigo parlon gidan Amman bai ga, Zeey ba hkn yasa ya nufi kofar dakinsu yana yin nock cikin sanyayiyar muryarta tace waye?
AK yace mata nine taji shi Amman sai Ta shareshi tayi kmr bataji ba sai daya sake kiranta sannan Ta taso ta bude kofar tana. Masa mgn a yatsine lfy Kake ta buga min kofa hk?


AK yayi murmushin hade da langwabar da Kai yayi mgn kmr wani karamin Yaro yace haba my sister sbd me kike min hk gashi kina neman sa yunwa ta kashe miki ni .
kina sane da bana iya cin abinci kowa a gidan byn naki to Dan me zaki juya min baya ?daga kawai nafada miki gaskiyar dake cikin raina, ni bance bana sonki ba.... Ta yatsina fuska tana wurga masa katuwar harara sbd tagano yana son Raina mata wayo da hankali ne .
ta kai hannuta da niyyar ta rufe kofar AK ya rike handle din kofar yace why?
tare da tsura mata mayatattun idanunsa yana kare mata kallo gabadaya sai yaga Ta rame masa ta canza har wasu kasusuwane suka fito mata..
nan take taji jikinta yayi sanyi Ta dinga jin sbd idanunsa Data ji suna yawo a sansar jikinta da kokarin raunatata .
Dan hk Ta Saki kofar Ta juya gabadaya ilahiri jikinta rawa yake Duk da ta rame sosai Amman bombom dinta suna nan yadda suke babu abinda yasamesu yabi bayanta da kallon na wani second sannan yashigo Dakin yana me juyo daita suna fuskantar juna har suna jiyo numfashin junansu take gabanta yashiga dukan uku uku, muryarsa a kasalance haba sister ya zaki shige muje Kibani abinci yunwa nike ji.... Ta km sakar masa harara jikinta a Mace, yayi murmushi gefen baki yana kallon cikin kwayar idanunta pls Now kaje Ita wace take ACikin zuciyarka Ta baka abinci Amman bani Zeey ba. Takarasa mgnr Tana me juyawa har ta bude kofar bathroom taji an gizgota a harzuke ....ke ban son iskanci kodan kin ga ina lallabaki sai wani iskanci kikewa mutane.
gabadaya naga rainin hankalinki ya nemi zarta iyaka .
Dan Allah malama muje Ki hadamin abinda Zanci.

ko ana so dole ne?
Nace akwai wace zuciyata take so .?

Oya wuce kije kimin abinda zanci yakarasa fadar hk yana nuna mata kofar fita.. Muryata a sanyaye tace to katafi ina zuwa zan kawo maka..


Ya juya ahankali ya bar dakin yana murmushin daya kunshe ita km tabi bayansa da harara sai Data bata lokaci sannan Ta fito ta nufi kitchen ta hado masa abinci takawo Ta dire masa a gabansa zata juya ya Yi saurin riko hannunta cikin nasa yana murzawwa cike da natsuwa,ta kalleshi shima ita yake kallo tace bakasona sbd me zaka rike min hannu? Yayi mata banza yacigaba da murza tafin hanunta ,cikin nasa wanda hkn yayi narasar kashe mata jiki.
take jikinta yasoma sanyi yana mutuwa wata irin kasala tashiga yawo ajikinta ganin yana kokarin tada mata tsumin shawarta yasa tace ka sakar min hannu pls kaje ka rike hannun wace kake so......




Mmn sudais ce
💗💗💗💗💗💗
SAI KA AURENI DOLE
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗



~NA~



*AYSHA A BAGUDO*



~DEDICATED TO~
HAUWA A USMAN
JIDDARH


*qala rasulillahi sallallahu alaihi wasallam:*

*laa yahillu lilmusli an yahjura a khahu fauka salaat*

*Allah's messenger (s. a. w) said it's not permissible for a Muslim's to forsake his Muslim brother beyond three days*


Page 14


Yayi murmushin mugunta tare da sake damke hannuta sosai cikin nashi yana murzawa ahankali muryarsa a kasalance yace ai ita wace nike son ba sai na rike hannuta ba itace zata rike nawa, sbd tsabar tana son kmr yadda nike sonta. ki zauna kawai muci abinci wlh bana jin dadin yadda Duk kika canza min akan nace wata nike so ba ke ba ... Zeey ta yatsina fuskarta kmr zatayi kuka ,muryarta raunace tace ka kyaleni nayi tafiya .
"bazan kyaleki ba sai kin zauna muci abinci Dan nasan duk kwanakin nan bakya wani cin abinci Kalli yadda Duk kika rame Dan Allah..
A fusace tace to nace na koshi bazan ci ba ko dole ne ..

AK ya gyara zamansa yana tsareta da mayatattun idanunshi ai ko yarinya karyarki Tasha karya wlh sai kin zo mun ci .
IN ba hk ba na dauke Ki na daura Ki kan ciyoyina na dura miki Ta karfin tsiya. Ta rausayar da idaunta tana tabe baki zuciyarta na wani fizga tkmr zata fasa kirjinta ganin yanayin kallon datake masa yasa shi cewa ko kina ganin bazan iya bane kike wani kallona kmr wata wawiya.
tai tsuru tsuru da idanu domin tasan halinsa Zai iya komai yace.. Ita km tasan yanayinta Dan hk tace ka kyaleni zanci.
Yadda yanayin sautin muryarta ya fito yayi matseefar bashi dry Dan hk ya kyaleta tawani sauke ajiyar zuciya da karfi.

Ak yacigaba da cin abinsa batare da ya sake kulata ba .
ko ce mata wani Abu ita Kuwa Zeey dago kanta tayi tana satar kallon AK Wanda ya maida hankalinsa gurin cin abincinsa ya gama ta kwashe kayan abinci Ta nufi kitchen dasu data dawo maimakon Ta zauna a parlour sai ta nufi hanyar dakinsu.
Muryarsa a kausashe yace ke Ina km zaki? Ta tsaya tana kallonsa Ki zo ki zauna muyi hira bacci nike ji ya zabga mata katuwar harara ban yarda ba kawai kizo Ki min hirarrakin da kika saba min wayanda suke sakani nishadi..
Da gaske bacci nike ji da safe idan Allah ya kaimu zan maka ya sake watsa mata wani hararar ke dai kice zakiyi Min wayo ne. tayi murmushin jin dadi ganin har yanzu yana bata kulawar data dace bai canza mata ba. dakinsu Ta nufa tare da maida murfin kofar ta rufe Kai tsaye bayi tashige ta jingina bynta da jikin kofar Ta sanya hannuta duka ta dafe daidai saitin kirjinta sakamokan bugawa da yayi da karfi yayinda taji zuciyarta tana harbawa da sauri sauri tabbas bata taba tsammanin son da takewa AK ya kai hk ba.
Gabadaya ji take data rasashi gara tarasa rayuwarta domin Kuwa hkn zai fiyye mata kwanciyar hankali da sauki Akan taga AK yana rayuwa da wata baita ba bata Ankara ba sai dai taji saukar hawaye daga idanunta ahankali ta silale agurin .
durkushe bisa gwiwowinta tana cigaba da kuka jitake tmkr ta daura hannu bisa kanta ta rusa ihu kozata samu me kawo mata dauki akan halin tashin hankslin datake ciki da jin saukin tafarfasar da zuciyarta takeyi mata ..

wayyohhly Allah ka taimakeni kada narasa abdulkabir..

abdulkabir ya zamto wani jigo ne na rayuwata me matukar mahinmanci ina matsanancin sonshi banason rasa shi meyye aibuna da baza soni ba? Da kyar tasamu ta fito Ta rarrafa zuwa inda sabuwar shimfidar take ta kwanta lamo game da lumshe idanunwanta duka hawaye suka cigaba da silalawo akan fuskarta zuciyarta km tacigaba da harbawa hade da tafarfasa sakamakon matsanancin son AK dake cin zuciyarta..


Kwana biyu tsakani AK bai nufi inda onye take ba sai yammacin yau zaune yasameta cikin dakin tana karanta jaridar dailytrust tana ganinsa tayi xumbur Ta mike tare da ajiye magazine din dake hannuta ta nufoshi tana yauki ta rumgumeshi tsam tsam ajikinta tmkr wace zaa kwacewa shi Tana shakar dadadden kamshin turarensa me zautar da tunainta.
Ya lakuce mata hanci da alamun yau kina cikin nishadi?
Ya fadi hk yana kokarin cireta daga jikinsa suka zauna kan katifarta ta lumshe idanunta tana matsowa jikinsa cak ya dauketa ya daura bisa cinyoyinsa fada min meye sirrin wannan farinciki da nishadin da nike hangowa acikin kwayar idanunki domin na lura kina cikin nishadi onye tayi murmushin tace jin dadin ganinka on expecting ganinka kadai kan mantar dani komai, Ganinka nasa na dingajin kasala a ilahiri sansar jikina ganinka nasa nakasance cikin matsansncin farinciki AK son da nake maka bakina ba zai iya furta maka shi ba ..takarasa mgnr tana sanya idanunta cikin nashi tare da narkar dasu wanda hkn yasamu nasarar kashe Masa jiki AK ya lumshe mayatattun Idanunshi yana cizan lip's dinsa sannan yace nasani..
Nasan kina sona sosai fiyye da tunaninki tun ranar farko da muka soma haduwa nasan Kin fada tarkon sona .
Sai dai am sorry to say ni dai kina matsanancin birgeni Amman maganar so.. Yayi shr yakasa furtawa Ta tacigaba da kallonsa ka karasa Man baka sona ko abdulkabir..? A tarihin rayuwata banta jin wata ya Mace Ta birgeni ba kmr yadda kike birgeni. kin shiga rayuwata dayawa sai dai shi wannan son ne bazan taba miki karyar ina miki shi ba... Basani ba ko gaba ba..
ta rungumeshi ajikinta ni dai what I know I love you so much and I can't do without you honey dan Allah Kasoni ko yaya ne, daga nan suka shiga holewarsu da suka saba...

har misalin karfe shabiyu na rana Zeey tana kwance a daki Kirjinta ne yake Yi mata ciwo Amman sbd gudun tashin hankalin ammi taki fada GAnin bata da niyar tashi ne yasa iman ta nufi inda take kwance domin taga halin datake ciki aiko tana taba jikinta taji rau atafin hannuta da Sauri Ta janye hannuta ta nufi dakin ammi tasanar mata atare suka dawo ammi ce gaba iman tana bayanta ammi na tura kofar dakin ta hango Zeey kwance a kasa sai mayar da numfashin take sama sama tmkr me cutar Asma ammi tayi saurin karasawa inda take kwance a rikice ta janyota jikinta game da cewa subuhanallah Zeey me zan gani hk kwanciya akasa ?Allah ammi nima hk kawai naga ta dauki salon kwanciyar kasa ai ko sanyi Tayis ya isa ya saka cuta takamata inji cewar iman, meke miki ciwo Zainab, Zeey ta Kalli ammi ta nuna mata saitin zuciyarta subuhanallah to meyasa baki fada ba zaki zauna da ciwo hk ,ke iman jeki kicewa yayanki yazo yanzu yakaita hospital, iman Ta juya da sauri ta fice ta nufi part din AK wanda ke kwance suna waya da onye iman tayi nocking yace yes who is that it's me yaya ammi ce Ta aikoni ya Mike da kyar ya nufo kofar ya bude tare da kashe wayar iman tace wai ammi tace kazo ka kai aunty Zeey hospital bata da lfy meke damunta? Tace unhmm ina GA Dai kmr Ciwon kirji ne.. AK yace OK gani nan zuwa iman takoma dakinsu inda ammi ke rungume da Zeey har lokacin tasanar mata sakon AK ta taimaka suka shiryata ammi ta kamota ita da iman suka
fito farfajiyar gidan hkn yayi daidai da fitowarsa daga bangarensa yanayin yadda ya ganta yasanshi karasowa gun da sauri yace ammi hk jikin nata yayi tsanani sosai?

Ammi tace hk nima nagani narasa meke damunta duk kwanakin nan hk take..

Da Sauri ya tashin mota suka wuce hospital Kai tsaye emergency aka nufa da Zeey sbd yadda jikin nata ya kara tsanani cikin kankanin lokaci doctors suka taru akanta domin kokarin ceto ranta daga barin gangar jikinta ammi takira mahaifiyarta sanda tazo hankalinta yayi matukar tashi hk ma AK Shima hankalinsa ya tashi da ciwon zeey.

Cikin ikon Allah ba dauki wani lokaci ba doctor ya fito daga dakin da aka kwanantar da Zeey dr yakira ammi da AK sbd sune suka kawota yace yana son ganinsu a office dinsa.

Ammi da AK zaune gaban doctor byn Dr yayi yan rubuce rubuce akan file din Zeey ya cire medical glass din dake manne da idanunsa ya dubi ammi yace kece mahaifiyarta..?
Eh nice ya maida dubansa kan AK kai km kaine yayanta ko? Ak ya jinjina Kai batare daya amsa ba. Gud doctor ya sake duban ammi yace Hjy yarinki tana cikin damuwa me tsanani domin akwai abinda ke damunta wanda Ta saka shi cikin zuciyarta dalilin hk ma Ciwon xuciya ke daf da kamata ga jininta ya hau sosai ammi nagama sauraron bayanin likita Ta dafe kirji tace inna lillahi WA inna ilaihi rajiun Zainab da ciwon zuciya ga hawan jini wannan kankanuwar yarinyar da manya ciwoka hk? Ita kuwa Wace irin damuwa ce take Tare daita da har ta janyo mata wannan muguwar matsalar?

Doctor yacigaba da koro bayaninsa Dan hk ya kamata kuyi bincike ku gano menene matsalar domin a samu a magance mata ita domin gudun kara faruwar wani abu km a daina bata rai domin da zarar an bata mata rai hankalinta zai iya tashi sakamakon hkn km Ciwota zai iya tashi..

Ammin tace Inshaallahuu zamuyi iyakacin bakin kokarinmu Dr ya rubuta irin magungunan da masu lalura irin nata ke Amfani dashi.

Mahaifiyar Zeey da ammi da iman zaune jigun jigun suna kallon Zeey dake kwance an daura mata drip sai bacii take sakamakon allurar bacci daaka mata. AK yashigo dakin ya gaida mutane dakin tare da tmbyr me jiki da saukin muslinci suka hada baki har yanzu dai bata farka ba.

ya nemi kujera ya zauna sai byn da aka idar da sallar magriba Zeey ta farka mahaifiyarta dake kokarin sallame sallah takaraso gareta Dan ammi sun wuce tun dazu tai mata sannu ta amsa ahankali ta nunawa mahaifiyarta tana son tashin zaune Dan hk Ta taimakamata ta tashin Ta jinginar mata pillow.

Mahaiyarta ta tmbyeta ko zata iya shan tea Zeey ta girgiza kai alamun aa sbd me bazaki sha ba? Sbd bana jin dadin bakina.

Daman ai babu yadda za ayi kiji dadin bakinki sai dai ki daure mahaifiyarta taje Ta hado mata tea da kanta ta rinka bata tana sha.

Ammi da Dady har Iman suka shigo tare da sallama suka gaisa suna tmbyr me jiki gata nan da sauki har ta dan sha ruwan tea to Allah kara sauki..
Nan suka shiga hirar matsalar dake damun Zeey wanda daga karshe dady ya tashi yace Zaire je yaga doctor Kai tsaye ya nufi office din likita. yayinda ammi Ta zauna kusa da Zeey tana sake taba jikinta iman km ta ajiye kulolin abinci akan wata karamar dorowa daga gefen da gadon Zeey take ta dawo kusa da Zeey.

Byn kmr minti goma shIma AK yashigo cikin dakin yadda yaga Zeey atsakiyarsu yayi matukar farinciki ya matso sosai kusa da gadon yayi mata sannu Amman sai Ta shareshi AK ya tsiysyo freeemilk

Chapters

Related Ebooks
19, September 2025
Aisha Auwal

Wow

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login