Showing 381001 words to 384000 words out of 420383 words
Chapter 128 - SAI KA AURENI DOLE BY AYSHA A BAGUDU.txt
bikinku ?
"Ai wallahil azim haushinku nake ji gaba dayanku har Ammi da Umman Su'ad idan kowa yayi abinda yaga dama ita Umman Su'ad bai kamata ta dinga karfafawa Ammi zuciya ba "kamar batasan ciwonta ba'
" well daman nasan nafita damuwa da Su'ad d'in.
"karka ce haka Ak mahaifiyarta ce fa ta dai yi kara ne saboda kwanciyar hankalin Ammi,"dan malam dakata karka cikani da magana
"kwanciyar hankalin banza da wofi mutun yarasa d'a sukutum guda amman ya zauna yana.. sai kuma yayi shiru yakasa k'arasa abinda yaso fad'a.
"yanzu dai ka sausautawa zuciyarka In sha Allahu tana hannu nagari kamar yadda Ummanta ta fad'a inji cewar musty .. Ak ya runtse mayatattun idanunsa da suka gama sauyawa zuwa jajja sannan yacigaba da mgn
"Musty bansan yadda zanyi da rayuwata ba, bansa inda zanga su'ad ba, zuciyata zata buga idan narasa ta wallahi mutuwa zanyi muddin na rasata ka taimakeni musty ka ajiye hidimar bikin nan ka tayani neman matata da cikin jikinta "cool down Mana zamu ganta Inshaallahu yanzu dai kana ina?
"ina ikoyi express "
"Ok ka d!aure ka k'araso gida yanzu ,nan yashiga gaya masa abinda ya faru wani irin wawan birki ak yaja kiiiiiiii wanda yasa Musty tsorata tare da furta kalmar inna lillahi wa inna ilaihi rajiun,
"kayi tuki ahankali fa ya fad'i haka tare dayin
dayasanin gaya masa abinda ya faru , shiru Ak yayi zuciyarsa na beting sannan yasoma magana cikin
sanyi murya,
"da gaske kake yi Musty? nannauyen ajiyar zuciya Musty ya sauke kana "yace Allah kuwa.
"Daman na dad'e da wannan tunani Ammi ce takasa fahimtata ganinsn zuwa yanzu amman fa akwai tashin hankali fa..musty yace "ka dai kayi tuki ahankali sai ka karaso muna hospital Droctor Rak "ok gani nan zuwa just give me 20 minti.....
ko cikakken minti shabiyar basuyi da gama wayar ba sai gashi ya iso hospital d'in Musty ya tarosa suka jera zuwa cikin d'anki da aka kwantar da Taufeeq sai da gaban Ammi ya fad'i sanda tagansa yayi wani irin rama tamkar wanda yayi shekara da ciwo bakinsa ya bushe wanda ya nuna ala'mun baya cin abinci kasa hak'uri tayi tashiga goge hawaye, shi kuma yakarasa gaban gadon da Taufeeq ke kwance yana jan numfashi ahankali yana fitarwa ya tsura masa ido yana kallonsa,
wanda wannan tsayuwar tasa yasa madam shema cike da wayyo da dabara ta kwace hannun Taufeek cikin na Salema.....
wani irin kunya Umman Su'ad ta tsincin kanta cikin d'an haka yasa ta mike tsaye tsam taja baya kad'an ta jingina bayanta da bangon d'akin tamkar wace aka dasata wani sabon tashin hankali ta tsinci kanta ciki,wasu hawaye masu dumi suka sake yin nasarar biyo fuskarta tana k'ok'arin sharesu..
tsawon minti goma AK na tsaye akansa yana dubansa kafin daga bisani ya d'an saci kallon Umman su'ad ta kasan idanunsa "wato ma kukan masoyinta take bata d'iyarta data nema tarasa ba?
gutun tsaki yaja akasan zuciyarsa sannan ya juya cike da izza zai bar d'akin yaji saukar muryar Ammi cikin kunnuwansa "Abdul ina zaka kuma?
batare da ya juyo ba yacigaba da tafiya "zanje naci gaba da bulayin neman matata tunda bata da gatan da zai iya nemota da ya wuceni ..
Ammi ta mik'e daga zaunen datake tace "dakata Abdul ya tsaya cak kamar yadda tabashi umarni har takaraso garesa ta kai hannunta cike da tausayawa halin dayake ciki ta dafa kafad'arsa.
sannan tace "su'ad na da gata wanda kai kanka kasan da haka..
yayi saurin katse ammi ta hanyar cewa "ni bansan da wani gata datake dashi ba "Ammi ki duba fa cikinku babu wanda yayi k'ok'ari tayani nemo matata kowa hidimar biki ya sanya agaba "ke Dady eiman Musty umman s. .sai yayi shiru tare da dungule hannunsa ya naushi iska" amman babu komai zan cigaba da nemanta koda kuwa hakan zaiyi sanadiyyar rayuwata" daman kince kar na kuskura na sake zuwa gareki matsawar babu Su'ad zan tafi neman matata tunda ni ta zame min dole..
yak'a rasa maganar kamar zai zubda hawaye wanda hakan yasa kukan Umman su'ad tsananta eiman takaraso itama "yaya dan Allah k.... "banason jin komai daga bakinki kema aurenki ne agabanki ,"ku barni ni kad'ai dina ma na isa nemota a duk fad'in duniyar nan yakarasa maganar tare da sanya kai yabar d'akin.
Umman Su'ad ta fashe da kuka abubuwa gaba d'aya sun cunkushe mata gaba daya duniyar ta tsaya mata cak gaba d'aya kalmominsa na mata nuni da bata damu da diyar cikinta ba yarinyar da ita kad'ai tasan iya wahalar datasha akanta duk duniya babu wanda zai so Su'ad kamar ita dan itace silar zuwanta duniya kuka take sosai har da shesheka Ammi ta rungumeta ajikinta tana rarrashi gaba d'aya tarasa me zatace mata..
tafiya yake Musty na biye dashi abaya "meyasa kakeyin irin haka?
"gaba d'aya maganganuka babu d'a'a acikinsa ko babu komai bazaka fita jin d'acin ranshi su'ad ba "karya kake Musty ya juyo a fusace yana nunasa da yatsan hannusa "nace karya ne wannan maganar banza ce tunda abun nan ya faru kaga hawayenta?
"ko kaga ta nuna damuwarta sai yanzu data sake cin karo da masoyinta tana kuka saboda ta tsinci masoyinta cikin wani hali .
ak yakira sunan Musty tare da rik'o tafin hanunsa ya d'aura daidai tsatin zuciyarsa dake dokawa da karfi"kaji yadda zuciyata ke beting?
" zuciyata na bugawa ne akan su'ad wallahi duk nafiku sonta da bukatarta a halin yanzu "Allah na rokeka ka sake wulakata rayuwar Zeey datayi silar rabani da matata ,"ya Allah kar ka sausautawa lamarunta Allah ka sake had'ata da mugayen alkaba'i iri ir... "ummmmmm Ak karkayi haka Musty yayi saurin d'aura hannusa kan bakinsa domin hanasa karasa abinda yake son fad'i "ko babu komai Zeey yar'uwarka ce," halaka ta zumunci ta had'aku taci darajar danganta dake tsakaninku ka yafe mata abinda tayi maka "kama barta taji da lalurar dake damunta.
a matukar harzuke ya fizge hannun Musty daga bakinsa yaja tsaki ya juya yasoma tafiya ,yabar Musty tsaye agurin yana kallonsa cike da tausayawa kai tsaye gurin motarsa ya zarce ya shige ya fizgeta a guje ya bar harabar hospital. .
har zuwa washegari Taufeeq bai farfad'o ba gbdy yan'uwa na tare dashi anatayi masa addua AK ma ya sake zuwa ya duba yanayin jikinsa .
yayinda Ammi ta bukaci akawo mata ruwa cikin cup tayi addua sosai had'e da d'ago 'kansa tabashi ya sha sannan ta shafa a kansa zuwa fuskarsa, haka ta dinga yi masa har tsawon a wani takwas sannan akasamu ya sauke naunauyen ajiyar zuciya hade da dafe gefen 'kansa dayaji yana matsananci sara masa sannan ahankali ya ware kyakkyawa idanunsa a saman celling d'akin.
zuwa wani lokaci yasoma kallon d'akin da jama'ar dake tsaye akansa ,sunyi masa tsuru da idanu suna kallonsa.
adduar still Ammi keyi tare da sauran Jamar dake tsaye akansa ,yayinda Shemah ke zubda ruwan hawaye tana karanto duk addua datazo bakinta tana shafamasa saman goshinsa, Salema ma addua takeyi tana cigaba da kuka tana son isa inda yake kwance amman takasa aikata hakan gudun kar Ak ya isketa a gurinsa yayi mata wata fassarar daban.
tana jin aranta gara ta tsaya inda take tacigaba dayi masa addua..
d'agowa yayi ahankali saboda jin kansa dayayi akan cinyar mutun .. karaf sukayi 4eyes idanunsa ya tsarke cikin idanun wata daban ba salemarsa ba da zuciyarsa taci karo daita ba, "k'ok'ari tashi yayi a matukar tsorace yacigaba da kallon jamar d'akin daga k'asan zuciyarsa yake tunanin ko wacece wannan matar dake tare dashi ba Salemarsa ba ...?
A hannkali kuma komai yashiga dawo masa daki daki lokacin da idanunsa ya sauka akan salemarsa dake tsaye tana kallonsa tana zubda hawaye wasu na sake gangaro mata, ita din ma kwayar idanunshi take kallo kirjinta na wani irin bugawa daf daf!!
sautin muryar Ammi yaji ta doki cikin dodon kunneshi wanda yasa ya d'auke idanunsa akan Umman su'ad ya maida kanta "tabbass wannan yar uwarsa ce mafi soyuwa arayuwarsa.." Taufeek d'ina Ammi takirasa ya kasa amsawa illa idanu daya zuba mata ta matso kusa dashi sosai "kayi min magana dan Allah ina kwad'ayin na sake jin sautin muryarka acikin kunnuwana domin tabbatar da dawowarka cikin wannan duniyar..
Ahankali ya bude bakinsa da kyar yace "Aunty Baraka.... yakira sunan Ammi cikin sanyi muryarsa me dadin sauraro "ina hajiya ta ina umman mahmud da mahmud suke..?
take Shemah ta tsinci kanta cikin mummunar faduwar gaba sakamakon abinda taji yace wani sabon tashin hankali ta tsinci kanta ciki .. ..
Ammi tace" Masha Allah, Allah abun godiya "Allah mun gode maka daka nuna min wannan rana Alhamdullahi "ashe zan sake riskar farinciki irin wannan?
kowa a d'akin babu abinda yake furtawa sai kalmar Alhamdullahi Allah mun gode maka daka nuna mana wannan ranar ...... Ammi tacigaba da magana bayan ta sake yin kusa dashi sosai tana fuskantarshi " abinda nake so ka fuskanta nasan bayan halin daka tsinci kanka cikin jirgi baka cikin natsuwarka duba da yanayin tambayar matarka da d'anka dakayi a halin yanzu, "ala hakikanin gaskiya mun rasa Hajiya asanadin labarin mutuwarku da muka samu labari, nan dai tashiga labarta masa abubuwa da suka faru tun daga farko har k'arshe yayinda shi karan kansa kwakwalwar kansa ke hasko masa wasu abubuwa kafin jirginsu ya kone, shi dai yasan yana rungume da matarsa a wannan lokacin rungume kawai yake daita amman gaba d'aya, hankalinsa da tunaninsa na gurin Salema yana tunani halin dazata tsinci kanta idan taji labarin mutuwarsa yaji wani abu tamkar guguwa ya raba tsakaninsa da matarsa zuwa wani b'angare daban inda kanshi ya bugi wani makeken dutse daga nan bai sake sanin abinda ya faru dashi ba hawaye kawai Taufeek ke zubarwa yana sake hasko wannan tashin hankali me girma da bazai ta'ba mancewa dashi ba ...
yayinda Shemah ke faman kallonsu tana son gano wasu abubuwan dake faruwa daki daki idan zata fahimci zantuttukan da Ammi keyi ,matarsa da d'ansa sun dade da rasuwa" to wacece wannan Salemar datayi sanadiyyar dawo dashi cikin duniyar tunaninsa?
wanda d'anuwanta yayi iya k'ok'arinsa na yaga ya dawo dashi abun ya faskara har mutuwa ta riskeshi.......
hawaye yake ta zubarwa sakamakon rasa mahaifiyarsa da matarsa da d'ansa dayayi sannan ya maida ganinsa ga salemarsa mafi kusanci da zuciyarsa dake tsaye har wannan lokacin kuka take.
ahankali ya yafitota da hannunsa ala'mun tazo gareshi hawaye take zubarwa tana cigaba da kallonsa ta kasa zuwa inda yake har sai da Ammi tace "salema kije gareshi dan Allah da taimakon Allah da taimakonki ,muka samu wannan faricikin da muka dad'e da fidda rai da samunsa, "dan Allah ki taimaka kije gareshi yakara samun natsuwar zuciya ahankali Umma Su'ad tasoma daga kafafonta domin isa garesa tana karasawa tasamu guri ta zauna daga bakin gadon tana satar kallonsa wanda shi d'in ma kallonta yake cike da tausayawa sai dai shi ba wannan zaman datayi yaso ,yaso ne tana karasowa ta rungumeshi ajikinta amman duk da haka sai daya kamo tafin hannuta cikin nasa ya dinga massaging ahankali ahankali yana cigaba da dubanta tare da jin wani irin sauyi na daban agaba daya ilahirin sansar jikinsa ,takoina ajikinta jike yake sharkaf da ruwa gumi tun daga samanta har kasanta ....ahankali yasoma magana cikin sanyi murya yayinda idanunsa ke kanta "salemat...... yakira sunanta tare da kai hannunsa yana shafa cikinta "salemat ina cikina?
"ina baby'nah dana barki dashi ?
"ina abinda kika haifa min?
"tashi muje a yau zan sake dangana kaina ga mahaifinki a karo na biyu domin yabani aurenki dan muddin ina raye kece abokiyar rayuwata bazan iya rayuwa da kowa ce irin mace ba matukar bake bace .. yatashi daga zaunen dayake akan gadon tare da janyo hannuta ya soma tafiya da ita yana mata magana sunyi taku d'aya zuwa biyu kenan sukaji shemah ta buga wani irin salati me karfi tare da fashewa da wani matsananci kuka me k'arfi wani irin tafasa zuciyarta take tamkar ana diga mata ruwan dalma, akirjinta
kuma tamkar zai faso waje saboda tsananin tashin hankali.... ..
da kishin daya turnuketa, ta dubeshi tana hawaye tace "Mahbub ni kuma ina makomar aurena da kai? "mekake tunani akaina?
wani irin kallo Taufeek yake binta dashi me cike da tsantsar mamaki da tashin hanki sannan ya nunata da yatsan hannusa "ke kuma daga ina? "aure fa kikace waye mijin naki anan ?
"a ina nasanki da har kike min wasu zantuttuka wand'anda kwakwalwa bazasu iya dauka ba? bansaki ba bansan daga inda kike ba asalima yau ce rana ta farko dana soma ganinki a rayuwata ....
cikin rawar murya tace " nasani nasani Mahbub bazaka tuna koni wacece gareka ba sannan bazaka ta'ba sanina ba da matsayina a gurinka ba," tunda kayi lossing memory dinka na tsawon shekaru masu yawa da suka gabata amman kasani ni matarka ce ta suna da igiyoyin aurenka uku rassss suka rataya akaina," sannan muka rayu tsawon shekaru tare ,tsawon shekarun da mukayi rayuwa da kai na kasance ina maka wani irin so da uwa kad'ai takema d'anta, kullun kuma ina maka fatan samun lafiya domin sanin wani abu daya danganceka da danginka "sanadin yayana kasamu garkuwa cigaba da rayuwa a doro duniya yayana shine silar komai daka zama a yaxxu...
" yayana yayi wahala da kai daga kasar haihuwarka har zuwa wata kasar daban batare da yasan ko kai waye ba." ya inganta rayuwaka alokacin da kai kanka bakasan halin dakake ciki ba ,amman dan yanzu ka dawo haiyacinka shine zaka manta dani...
cikin abinda bai fi second biyu ba gumi ya rufe shi ya dimauce cikin karfin hali irin nashi ya bude baki yana son furta kalma koda guda daya ce gareta amman ya kasa bayaga girgiza kanshi daya dinga yi yana kallonta da Ammi dake tsaye akansu tana kallonsu cike da matsanancin tausayawa dan tasan wani tashin hankalin ke kokarin sake kunowa cikin rayuwar d'an uwata.. ....
shemah takaraso inda Ammi ke tsaye tare da kamo hannuta cikin nata tana zubda hawaye "hakika nasan yayana yayi kuskure arayuwarsa, kuskurensa kuwa shine amincewa da yayi ya aura min d'an uwanki alhalin yasan yana cikin dimuwar, da watan wata rana zai iya dawowa haiyacinsa wanda gashi hakan yakasance , a yau abubuwa masu radadi da ciwo suna kokarin dawowa cikin rayuwata ciki kuwa har da ciwon zuwan wannan ranar da mahbub d'ina zai tabbatar min da bai sani ba kosanin aurensa dake kaina ba.
Ammi ta rike hannunta sosai cikin nata jikinta na kirrrrma "ki daina kuka haka ni kaina na tabbatar da ke din matarsa ce duba ga yanayinku a lokacin da bai dawo hankalinsa ba "dole nayi kuka saboda nasoma hango karshen zamana dashi duk da bazan so rabuwa da abinda na rayu dashi sama da wasu shekaru ba.
"mun rayu tare da mahbub , mahbub mutun ne me fara'a dasanin darajar d'an adam sannan kullun muna tare dashi sai dai idan baya k'asar, komai tare mukeyi matsawar muna guri d'aya bamu tabayin nisa kmr irin yadda muke a yanzu ba,
"yau ace mun haihuwa dashi nasan ko yaranmu ya kalla wannan kawai ya isa ya tabbatar masa da matsayina agurinsa.
A sanyaye Ammi ta katseta "karkice haka ki ma daina wad'an nan zantuttuka yadda kukayi mu'alamarku kad'ai zai sa ya iya kankarewa ba.. amman zance aurenki dake kansa yana nan har yanzu kina nan amatsayin matarsa ..
take yaji zuciyarsa ta tsaya cak gaba d'aya ta daina bugawa na wani lokacin sannan ahankali tacigaba da bugawa da karfi maganganunta ba iya kunnensa kad'ai ya tsaya ba har cikin zuciyarsa yake jin komai yasoma karasowa gareta yana son ta karyata abinda tace yazama karya ne ba gaskiya ba,
"wani irin aure kuma?
tun kafin yakarasa gareta Ammi ta dakatar dashi ta hanyar cewa "ka tsaya ko kasamu guri ka zauna zance aurenka da ita gaskiya ne tabbas babu k'arya takarasa maganar tana maida idanunta kan shema "
zanso naji yadda akayi kuka tsinci d'anuwana da kuma irin taimakon da kukayi masa..
tunda Ammi ta tsai dashi yake aikawa shemah wani irin Kallon me tattare da alajabi yayinda har lokacin hannunsa ke cikin na Umman su'ad wace ke tsaye sai kifkifta idanunwa take da sake zurfafa tunanin rayuwarta da tarin soyayyarsa gareta," bazantar da rayuwata datayi Sanadinsa iyayenta danginta tana wassafa ina ma komai dake faruwa a halin yanzu karya kunnuwanta suke jiyo mata ba gaskiya bane.." Taufeek d'inta bai da auren kowace mace akansa zasuyi rayuwarsu daga ita sai shi.. yadda Salema ke zurfafa tunaninta haka itama shemah ke tunani, sai dai nata tunanin yasha banban da wanda salema take har zuwa sanda ta matso kusa dashi suna fuskantar junansu.
"ka daina tantama ko jin mamaki abinda nace ni din nan matarka ce mahbub tacigaba da kallonsa tana zurfafa tunanin gidanta da rayuwar da sukayi ina ma ace wannan abun daya faru tazo ta tafi ne da yanzu duk tsiya suna tare kwance guri daya ko zaune suna hira da mijinta ma'aboci zolaya da kokarin danne fushinsa. take ta fara tariyo rayuwarsu dasukayi a baya da dalilin haduwarsu....
*asalin faruwar lamari*
mu asalin yan kasar Nigeria ne kasancewar mahaifinmu haifafen Nigeria ne, mahaifiyarmu ce haifaffiyar k'asar koria gaba da baya.
karatu ne ya kawo mahaifinmu engening Nura kasar koria har Allah ya had'ashi da mahaifiyarmu me suna polina, polina ita ce d'iya ta uku gurin iyayenta wanda tunda ga kanta iyayenta suka tsaida haihuwa atsarinsu yara uku sun isheshesu rayuwa.
A loakinci polina ce tasoma nunawa mahaifinmu soyayya ta fitar hankali saboda a kallon farkon data soma yi masa taji Allah ya dauki soyayarsa yasaka mata cikin zuciyarta ,ta yadda take jin bazata iya hakura dashi ba , batayi sanya a gwiwa ba gurin sanar masa inda shi kuma yaki amincewa da hakan ,ya nuna mata bazai iya soyayya da itaba saboda addini da aladarsu ba daya ba.
"ta bishi tayi magiyar duniya da salon jan hankali amman yaki yarda saboda hudubar mahaifinsa garesa domin kafin
19, September 2025
Aisha Auwal
Wow