Showing 174001 words to 177000 words out of 420383 words
Chapter 59 - SAI KA AURENI DOLE BY AYSHA A BAGUDU.txt
irinsa ba .
sai faman wage bakinsa yake yana murmushi yayinda take mutanen dake gurin suka shiga ihun ga ango na salema....... ga ango na salema yayinda wasu daga cikin yan dakin hjy harira suka dinga hadawa da hailbaici ango na salema ko taki ko taso kaine dai zaka kasance uban ya'yanta sannan ka mallaki wannan hadaddiyar surar jikin nata. andaura auren ne? naji wata daga cikin yar'uwarmu ta furta hkn alokacin da numfashin ke daf da daukewa ya bude baki yana murmushinsa me karamin bakinciki yace ai... tun kafin ya furta abinda zai fada wanda ni alokacin na tabbatar da abinda yake son fada kenan nasoma mgn kasa kasa narasa taufeek.....narasa taufeek kafin kace me tuni na xube kasa sumammiya.....parlour 'n ne yakarade da ihun mutane wanda ya hankaltar da sauran jama'a firfitowa daga sauran dakuna.
saukar ruwa naji ajikina wanda bansa wanda ya kelaya min shi ba na farfado sai dai numfashina bai dawo daidai ba dan hk aka wuce dani hospital...
mmn sudais ce
💗💗💗💗💗💗
SAI KA AURENI DOLE
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
AYSHA A BAGUDO
dedicated to
hauwa A usman
allah's messenger saw said purication is haif of faith
page 45
lokacin da aka kaini hospital rai hannun Allah sbd babu wani ala'mun numfashin atare dani. gadan gadan likitoci suka amsheni sukashiga aikinsu akaina ,domin kokarin dawo da numfashina .
amman duk iyakacin kokarinsu naganin numfashina ya dawo gangar jikina ya gagara samuwa .
yayinda ilahirin hospital din ya cika makil da dandazon dangina dana abokan ango.
kowa kagani agurin yayi jugun tare da zabga tagumi.
shi kansa ango hankalinsa a matukar tashe yake, so yake yasan halin da nake .
mamma kuwa tafi kowa shiga tashin hankali kuka take wiwi tmkr zata mutu tana daura dukkan laifin kan mahaifina da danginsa fada take zasu kashe min yarinya akan ra'ayinsu na banza.
likitoci kuwa sai kai kawo suke akaina abu kmr wasa sai danayi kwana da yini ban motsa ba yayinda likitoci ke kaina, daga karshe suka yanke shawara'r sakani cikin scanner domin asa a wani hali nake ciki ina raye ne ko na mutu..
byn awa uku da sakani cikin scanner aka fito dani .
aka nufi dakin majinyata dani aka kwantar aka daura min drip sakamakon ganowa da likitoci suka ina raye numfashina yayi sezin .
sai dana kusan sati daya kwance bansn a wani hali nake ciki ba ,sannan ban san hidimar da dangina da yan'uwana keyi akaina ba.
lokacin dana farka babu abinda ke fitowa daga cikin bakina sai yakub ka sakeni ni ba matarka ba.. ce, kai ba mijina bane ...ni taufeek nake so km shi zan aura banasonka ka sake .
hk na dinga sambatu ina fisge fisge sannan na lumshe idanuna ina jan numfashi da kyar wasu zafafan hawaye na zubo wa saman kuncina .
lokacin da doctor yashigo dubani saurin karasowa yayi lokacin dayaga halin danake ciki yadda jikina ke kirrma zafafan hawaye na gangarowa ta gefen idanuna wanda ya jika pillow da kaina ke ajiye akai .
ina jin motsin shigowa dakin na zabura na mike ina kasakeni yakub wallahi bazan zauna da kai ba.. sai km naga bashi bane likita ne dan hk na koma na kwanta ina sambatu allura bacci yayi min wanda take bacci yayi nasarar daukata amman har lokacin jikina bai bar rawa ba.
Bayan alluran baccin da akamin ya gama aikinsa ya sakeni a zabure na sake farkawa ina ihun kuka ina sambatu ina cewa yakub kasake ni ka sakeni wallahi bana sonka kasakeni kasake bana sonka yakub wallahi taufeek nake so ba kai ba ina furta hk ina kuka kmr raina zai fita sai faman fisge fisge nakeyi a hankali mamma ta matso kusa dani takai hannunta kaina ta dafa tana shafawa tare da kama hannuna tana murzawa tace salimat kinatsu kidawo cikin haiyacinki wayace miki andaura miki auren da yakub ai ..ba'a daura ba... salimat tace mamma da bakinshi fa naji yana fada cewan andaura a'a salimat zeje dai daurin aure ne amma sam ba'akaiga daurawa ba. Kinjiko kisamu natsuwa dan Allah kiyita furta kalmar innalillahi zaki samu natsuwa zuciya kuma zakiga komai yazo miki da tsauki.
kwana biyu tsakani aka sallameni. tundaga cikin mota da zamu koma gida naga yanayin iyayena da yayyena ya sauya ,sai kallo na kawai suke fuskarsu cike da mamaki ni km ko ajikina domin atunanina kallon tausayawa 'su kemin shi kuwa babana banda tsuma babu abinda yake na lura kmr ma Allah Allah yake mu isa gida. muna isa gida muka yada zango a parlour babana kasancewar akwai mutane zugu da sukaxo biki basu rigada sun koma ba.
muna shiga babana ya fincikoni ya maka da kujera yana huci kafin na mike naji yace kin cuceni salema kin gurbata min xuriya.kin min tabon da har in mutu bazan taba mantawa dashi ba ke kadai da allah yabani mace amman kin zamemin masifa ni dawood diyata ke dauke da cik...
jire ne ko kuwa buguwar zuciya ne tasameni daga tsaye sbd ji nayi kaina tare da gangar jikina suna juyawa gabadaya idanuwana sun rufe bani ganin komai da lalube nasamu na isa jikin bango na jigina jikina ina kallon iyayena da yan'uwana a matukar tsorace ahankali na sulale nayi zaman yan bori wato na mimike kafafuna na waresu tmkr yadda kananun yara kanyi.
can kmr daga sama naji ana furta kalmar inna lillahi wa inna ilaihi rajiun sai kawai naji nima nakama kalma nashiga furtata ina maimaitawa bude idanuna nayi ahankali tmkr na masu bacci naga mahaifina tsaye yana sake furta kalmar inna lillahi wa inna ilaihi rajiun shida mahaifiyata rike da sakamakon likita a hannunsa yana sake duba farar takarda ..
ni kaina kalmar nacigaba da furtawa daga inda nake sbd halin tashin hankali danake ciki .
take naji numfashina na kokarin daukewa adaidai lokacin danake jin sautin muryar babana ciki kuka cikin agidan.... ni dawood cikin shege acikin gidana har na tsawon wata uku..?
yakarasa mgnr tare da yowa kaina gadan gadan yana huci ubawan yayi miki ciki shege?
yayi min tmbyr yana daukeni da wani gigitaccen mari ...
mamma takaraso garesa cikin yanayi na rudani da tashin hankali ta rike hannunsa kabari abi komai ahankali musan wanda yayi mata cikin.
ya fixge hannunsa yana nunata da yatsansa ala'mun ta kiyeyesa.
ni km na dan yi murmushin da bansa sanda yafito ya bayyana akan fuskata ba sbd na tabbatar matsawar ciki gareni babu tantama na taufeek ne,
cikin karfin hali naji mgnr ta fito daga cikin bakina nace baba matsawar likita ya tabbatar da ciki gareni to cikin taufeek ne ..gbdy daga mamma har baba atare suka zaro idanu waje.. kenan da gaske ciki ne dake?
inji cewar yayyye wadan suka hada baki gurin furta hk .
batare da wani tsoro ko fargaba ba na daga musu kaina ala'mun eh nan fa babana yashiga dukana takoina tare da allah wadai dani dukana yake yana dukan cikina da iyakacin karfinsa.
" su yaya yusif suka rikesa suna kuka suna bashi hk.. yana cikin dukana mamma ta zube kasa suka barshi yacigaba da dukana sukayi kan mamma suka shiga jijigata gaddafi ne ya nufi fridge ya dauko ruwa aka shafa mata ta farfado tana sauke numfashin tare da cewa ya kasheta ko..?
ni kuwa har lokacin banana bai bar dukana ba sai da yayi min jina jina tare da canza min halita sannan yaje har dakina ya dauko akwatin kayana ya dinga watsa min a harabar gidanmu zo ki bar min gidana.. wallah bazan barki ki haifamin "dan "shege acikin gidana ba .
"mamma wace tagama farfadowa ta mike tsaye tana kirrma karka min hk dawood karka kora min yarinya duniya karkayi sanadiyar rugujewar rayuwarta.
ki min shr ai duk da hadin bakinki yarinya tasoma lallacewa wallahi kinji na ratsen miki saleema baza sake kara second 1 acikin gidana ba sai tabarshi .
ke km idan kikayi kuskuren sake cewa komai abakacin aurenki wani irin firgitaccen ihu nasaka tare da daura hannuwansa duka bisa kaina wayyohlly Allah nakaraso inda mamma take tsaye kmr andasata tana xubda hawaye.
nace dan girman allah mamma karkice komai kiyi hkr kiyi shr banason tawa matsalar ta shafeki yanxu zan bar gidan kmr yadda baba yace kimin addua acikin zuciyarki ke uwace nasan duk inda nake adduarki zatayi tasiri gareni..
kimin addua mamma ina bukatar adduaki ko zanga daidai arayuwata ina cikin mgn mahaifina yakaraso a zuciye yasoma jana da akwatin kayana daga yau ni ba ubanki bane....
" bana bukatar sake ganin fuskarki arayuwata kije duk inda zaki a fadin duniya nan amman ina tabbatar miki duk abinda kikayi sai aminki ninkinsa yana kokarin ingizani waje yayyena sukayi sautin isa gabansa suna bashi hakuri atsawace yace wallahi kuka sake mgn zan tsine muku take kowanensu yaja baya suna kuka turani waje yayi tare da kullo get din gidan sannan ya juyo yana fuskatar mamma da yan'uwana duk wanda ya nemi inda salema take ko taimaka mata arayuwa ban yafe ba... ..sannan ya juya yana layi ya nufi dakinsa.
ina daga waje ina jin sautin kukan mahaifiyata da yan'uwana.. amman bani da damar shiga cikin gidan
natsaya ina kallon gidan da'aka haifeni nataso acikinsa cikin farinciki amman yau gashi zanbarshi ba dan ina so ba.
na dauki jakata ina kuka nasoma kokarin daga kafafuna abu na farko dayasoma zuwa cikin zuciyata ina zanga taufeek ...tafiya nayi sosai acikin wannan dare kusan ta awa daya kafin naxo ainihin inda zan samu mota sbd daga uguwarmu zuwa tashar mota akwai nisa sosai . da kyar nakaraso tashar tapa juga juga abinka da ba'a saba tafiyar wahala ba.
koda naxo tasha babu mota me zuwa Nigeria duk motocin sun gama tashi .
"idan ma akwai motar da wani kudi zan shiga motar ..?
dan hk ahankali nasamu wani dan dakali na zauna ina kuka tare da kalle kalle yan tsirarun mutane dake kai kawo a bakin titin ina nan zaune sai ga wasu custom su biyu kowanensu sanye da uniform sun karaso jikin wata mota crv suna zantawa da ala'mun dayan dake rike da farar leda ne yarako abokinsa ko dan'wa.
acikin tautaunawarsu ne naji shi dayan yace Nigeria zashi ina jin hk nayi saurin mikewa jikina na rawa amman na kasa isa inda suke har dayan ya juya yayi tafiyarsa shi kuwa dayan ya juyo zai bude murfin motarsa muka hada ido dashi.
ya bar abinda zaiyi yakaraso gareni tare da cewa yan mmata ina zuwa ne? da sauri nace Nigeria, Nigeria ya sake maimaita sannan yace ok nima can na nufa ko zan iya rage miki hanya? nayi saurin cewa eh ok muje ya bude min gaban mota nashiga na zauna shima yazagaya yashiga ya zauna ya tayar muka bar gurin.
tafiyar awa 3 ce takawomu *yanoba* hk nagani a rubuce sannan ya juyo ya tmbyeni wani unguwa zani gamu a nigeria nan fa nasoma duru duru da idanu nace ai bansa unguwar dazani ba ka taimakeni da gurin bacci har zuwa gobe da safe .
yayi shr yana kallona duk da yanayina bai nuna masa ko ni yar hannu bace ..
ok badamuwa zan taimakamiki dan hk kai tsaye gidansa ya kaini inda ya saukeni adakinsa. yace naje nayi wanka nace a'a sbd
ban damu da nayi wanka ba dan bashine agabana ba.
ina zaune yagama duk abinda zaiyi yace sake cewa naje nayi wanka nace a'a nagode nayi da safe idan naje inda zani.
kallona yake aransa yace zai dana .
nagane hkn ne sbd yanayinsa danagani yana kallona yana lasar lips yace nayi kwanciyata. har yafita ya dawo ya tmbyi sunana nace salema ....yace suna me dadi yadace da me sunan nayi dan murmushin wanda bai kai zuci.
byn ya fita na bude akwatin kayana inda jakata take na dauko diary din prof taufeek yabani nasoma dubawa ahankali full address dinsa da numbobin waya har guda uku na bude wani shafin abinda nagani ne yasa gabana faduwa da sauri na gyara zama ina sake dubawa ga abinda nagani arubuce..
_yau 3 ga watan mach shekara ta dubu biyu da dari hudu dana sadu dake saduwa ta karshe daman tunda na fara saduwa dake ban taba yin realize ajikinki ba, amman yau dana sadu dake na zuba miki spam dina ajikinki km sai dana daidaici lokacin period dinki yayi sauran 14 days km adaidai wannan lokacin na tabbatar inda ba Allah ne ya kiyaye ba zaki iya samun ciki sbd kwayenyen haihuwarki sun fara farfashewa a wannan lokacin daidai mace zata iya daukar ciki so inafatan na dasa miki kwaina acikin mahaifarki sbd ina son ki haifa min "da" ko "ya"wanda zaki dinga kalla kina jin dadi a cikin ranki sannan yasa kiji nishadi acikin rayuwarki wanda kullun idan kika kalleshi zaki tuno dani killa sanadiyar hk ki biyoni kasata......_
ina kaiwa karshe rubutun hawayena suka sake balle min ahankali na furta gani cikin Nigeria taufeek burina layunkanka suyi saurin sadani da kai.
na runtse idanuna ina kuka.... ina tunanin yan gidanmu..
dayake na tsargu da mutumin yayi masauki sai na kasa baci nayi shr na runtse idanuna kmr me bacci.
cikin dare kawai naji ansoma lalubata na farka afirgice ina zare idanu mutumin nagani tsirara haihuwar uwarsa yana kokarin kai hannusa jikina na fashe da wani irin razananniyar kuka ina rokonsa tare da ce masa ni ba yar isaka bace sai yace ai yasani kawai taimaka masa zanyi yace tunda ya daura idanuna akanka naji bazan iya hakura ba ina jin hk na miki tsaye jikina na rawa nace wallahi wannan jikin yafi karfinka...
yasoma motsani ina ja da baya matso yayi sosai yana lumshe ido kmr wani tsohon maye .
ina kokarin tutturesa yayinda firgici da tsoro yasani sakar wani rikitatccen kuka nan fa muka fara kokuwa dashi daga karshe Allah yabani nasara akansa na ingizasa baya da iyakacin larfina wanda hkn yayi sanadiyar bayana ya amsa da karfi. yayi baya kafafunsa sukayi sama tmkr me shirin yin dungure garin ya dawo da kafafunsa ya buge min ciki take naji marata ta daure ban tsaya wata wata ba na dauki jakata na rataya wanda diary din taufeek ke ciki na bar gidan aguje shima yabiyo byna yana ihun kiran sunana gudun bala'i nake a saman titi batare dana san inda zani ba ina kuka ina kiran sunan mahaifiyata gbdy tsoron abinda mutumin yayi yunkurin yi dani yasa tsoron daren ya kaurace acikin idanuna .
burina alokacin nasamu inda zan fake ko mataimaki daidai wata youtown na hango wata kwana wace haske wuta ya haskaka gurin nayi saurin bin hanyar tare da shigewa inda naga hasken ina adduar neman tsari har bakin gurin mutumin yaxo yana kiran sunana salema ki tsaya na fasa abinda nayi niyyar miki ina kallon ya tsaya yana waige waige ta inda zai ganni bai gani ba ya juya ni km na dinga jan ajiyar zuciya ina saukewa sannan na durkushe kasa ina wani irin kuka sai alokacin nasan inda nashigo ashe church ne sakamakon ganin ganguna da kujeru jere da cross.
ranar ban iya na runtsa ba tunda sanyi safiya na fito atsorace kar masu gurin suzo na samu guri bakin titi na zauna har garin allah yawaye ina zaune na saka wancan na kwance wancan ina tunani ta ina zansoma neman taufeek har kusan shabiyu ina gurin zaune tun bana jin yunwa da kishirwa har nazo nasoma ji daga inda nake zaune na hango tsayuwar wani mutun da baro gabansa wanda ke cike da kayan marmari ahankali na mike jikina babu kwari na isa gurinsa na gaishe shi cikin harshen tsadadden frach ya nuna min baya ji nayi masa turanci na ma dai the same sai kawai nayi masa mgn da gauranci hausata dabata gama bin bakina ba.
ka taimaki ne dan Allah kabani lemo ko guda daya ne yunwa nake ji ni bakuwace agarin nan.. mutumin ya tsura min ido yana kallona yadda yake kallona din ne na tabbatar da tausayina ne ke shigar jikinsa. amadadin yabani lemun dana tmby sai naga ya nufi gurin wata me tsaida abinci ya siyo har da ruwa wanda banyi tunanin ko ni zai bawa ba amman ga mamakina yana karasowa ya mike min plet din abinci ungo kici jikina na rawa na amsa ina masa godiya nasoma ci hannu baka hannu kwarya dan bazan iya cewa ga tun lokacin dana ci abinci irin hk byn nagama ci na sha ruwa yabani lemu guda uku cikin bakar leda sosai nayi masa godiya na tmbayesa masa inda zan samu massallaci ya nuna min sannan nakoma inda nake zaune tun farko .
shi km yacigaba da kasuwancinsa ina zaune gurin har yamma babu wani cigaba domin banda yadda za'a yi nasamu waya .
" shi km wanna mutumi yagama kasuwancinsa yayi min sallama ya wuce.
a massallaci danayi salolina na kwana ina kuka lagos ba kmr sauran garuruwa bane. Gari ne wanda basa amsar bako ko tausayawa bako washegari na sake zuwa gurin mutumin jiya nan na wuni byn na tmbyeshi aron waya yabani na kira numbobin da taufeek ya rubuta min .
kiran duniya nayiwa layikun taufeek amman ba'a dagaba.
nashiga matsananci damuwa gabadaya na sake birkicewa nafita haiyacina bani kaina ba hatta cikin dake jikina yana cikin damuwa sbd yadda nake jin marata na daure min atakaice miki su'ad sai dana kwana uku ina neman layinsa daren kwana uku ne ya waiwaiyi kiran danayi masa.
ya kira mutumin danayi amfani da wayarsa ya dauka ya gaisheshi yake fada masa wata yarinya ce keson waya dashi.
misalin karfe 11 mutumin ya zo har indanake zaune kafin mutane sugama watsewa nashiga cikin masallaci na kwana ya mika min waya yace number danake takira ce takira .
jikina har rawa yake gurin amsar wayar nasoma Bin layinsa kira daya ya dauka ina jin saurin muryarsa bansan sanda hawaye yasom gangaro min ba na kasa mgn shima tunda yace hello.. hello yayi shr bai sake cewa komai ba yana jira daga gareni .
"sai dana numfasa na sauka naunauyen ajiyar zuciya da karfi nace he... llo... kawai naji yace my loulooooooo... ya furta
19, September 2025
Aisha Auwal
Wow