Showing 393001 words to 396000 words out of 420383 words

Chapter 132 - SAI KA AURENI DOLE BY AYSHA A BAGUDU.txt

su kaddara ce haka kmr yadda nata kaddarar yakasance tare dashi.

shema ta kawo mata ziyara inda ta bar gidan batare da tashiryawa hkn ba saboda ganin yadda taufeeq ke nuna kulawarsa akan umman su'ad.
bayan tafiyar shemah umman su'ad ta hararesa tare da cewa "kai ko ..

"menayi umman su'ad?

"dan Allah meyasa kakeyin hk ?

"Ko bakasan ka girma bane kai fa kaka ne yanzu?

ya janyo hannunta ta fada jikinsa "gsky ne amman yazanyi kurciyata nake son gyarawa a soyayya babu wani zance tsufa yakarasa mgnr yana lumshe mata idanu ta mike ta nufi kitchen "bazan iya da rashin kunyarka ba Allah.

"ya girgiza kai yacigaba da karanta jaridar daily trust yana murmushi wata irin soyayaya suka gudanar atsakaninsu, ji yake kmr yacinyeta duk inda tayi yana biye daita ko wajen aura tayya baya gajiya da ita kafin sati d'ayan da zai yi agurinta ya koma gurin shemah umman su'ad tagaji matuka, a cikon daren na bakwai suna lullube cikin bargo ya manneta ajikinsa gbdy ya hanata saka umman su'ad "tace kai wai menene haka...?

"yanzu fa ka girma amman sai naji kamar karfi kak'ara, "amu'amularmu a lokacin baya baka wuce kayi sau biyu amman yanzu daya kamata karage malam shine kuzarinka ke sake karuwa..?

murmushi yayi yana dubanta sannan yace "da menayi?

"ai yanzu ne nake jina a d'an shila na, gani ga sahibar rayuwata, jina nake kamar matashi d'an 30yrs tayi murmushi ba ita tasamu kanta ba sai daya koma gurin shema wanda komawarsa bai sa ya barta ta huta ba, dan kiran safe daban na rana daban na dare daban shemah duk abinda zaiyi da idanun take binsa, abun ma baya damunta dan bai rageta da komai ba daman kuma a soyayya dole tasirin wata zai fi nawata ita dai burinta su kasance tare muddin rai.

************
har lokacin Ak bai hakura da neman su'ad gbdy yagama haukacewa tuburan ne kawai baiyi ba kowa yagansa sai ya tausaya masa, sanin inda su'ad take ne yasa Ammi da Dady sake janyosa cikin lamarinsu, sukayita rarrashisa da bashi baki tare da bashi shawarar ya koma bakin aikinsa dan ma musty na tsaye akan komai da abubuwan sun sake tabarbarewa.


alokacin haushin kowa yake ji cikin zuciyarsa most especial iyayenta da sukayi buris da lamarinta suka sanyawa zuciyarsu salama babu abinda suke sai cin duniyarsu da tsinke.

hakika idan kaga Ak bazaka ce wannan matashin mutumin bane me ji da kansa da izza tare da nuna iko da isa. yayi wani irin baki ya rame ga kasunba ya tara, yaki yin aski da kyar Dady yasamu ya shawo kansa akan zai koma bakin aikinsa.

Ranar da zai koma Dady da kanshi ya tasa shi gaba zuwa gurin aski aka masa aski suka dawo gida amman duk da hk Bai jin zai cigaba da zuwa office alhalin bai san inda matarsa take ba.

umman su'ad tayiwa Ammi magana akan yaka mata Abdul yasan inda su'ad take tunda har yanzu matsayin matarsa take "eh nima nayi tunanin haka amman dady'nsa yace "kar a sanar masa yanzu sai zuwa wani lokaci, dan ta haka ne zai sake sani mahimmancita a duk sanda ta dawo hannunsa.
umman su'ad tayi murmushi "nidai dan Allah kuyi hkr kubashi matarsa ya daina jin haushinmu atare sukayi dry sannan umman su'ad ta katse kiran takira mahaifiyarta suka gaisa har su'ad din sun dade suna hira.

tsaye yake a cikin tafkeken office dinsa wanda rabonshi da shigowa cikinsa tunda abin ya faru bai sake waiwaiyar komai nashi ba, yanzu da taimakon Ammi da Dady ne yasamu yazo gashi zuwan nasa bashida wani amfani ,tunda gashi ya kasa aiwatar da komai sai zariya yake acikin office din goye da hannunsa yana tunaninta ahankali ya waiwaiyo ya kalli hotonta da shine ya dauketa a koria "yace kingani ko hrt beat komai na rayuwata ya canza tunda kika tafi kika barni bana son jin dadi komai banason ayi min abinda zaisani naji dadi har nayi dariya saboda banason nayi dariya matukar bakece kika bani shi ba.

" murmushinki fuskarki da komai naki kawai nake son gani duk inda zanje nemanki naje ki taimakawa rayuwar mijinki ki dawo gareshi .. "mijinki na cikin mawuyacin hali na rashinki .
ya zagayo ya zauna tare da tsurawa system dinsa idanun yana cigaba da kallonta wanda hakan ya ke sake hargitsa masa kwakwalwa yashiga nemo sauran hotunanta .
zuciyarsa na dokawa tashiga yi masa gezo tana masa murmushi yana nan zaune yana kallonta har sanda sectary dinsa yashigo ya ajiye masa coffee ya juya ya fita awuni uku suka shud'e yana zaune babu abinda yayi sai aikin tunaninta yaji motsin shigowa office din.

ahankali ya bude mayatattun idanunsa da suke a runtse ya d'aurasu akan fuskar Musty yasoma kokarin k'arasowa inda Ak yake, tashi yayi daga zaune dayake ya dayo yana layi tamkar wani mashayi ya zauna akan doguwar kujerar gefenshi Musty ya zauna tun awa daya data wuce Ak suna tare da Musty ,musty ya kalleshi yace " haba abokina dan girman Allah ka saki ranka kalli yadda ka dawo a dan kwanaki da basu wuce wata daya ba?

"Na san abu da ciwo amman daurewa zakayi wani irin kallo yayi masa me had'e da harara "ka saki jikinka dan Allah kayi lamurar gabanka akwai abubuwa dayawa agabanmu wanda dole sai da taimakonka komai zai tafi daidai dan girman Allah ka daina fito da damuwar ka a gane.

Ak ya kalleshi ya girgiza kai "fito da damuwa yazama dole yanzu zaka had'a damuwata data iyayenta ?

"Musty kalli yadda na damu akanta kalli yadda nabi na k'are akan su'ad banida lokacin kaina wallahi bana runtsawa yadda naga dare hk nake ganin rana.
Musty yayi murmushin takaici sannan yace " kaima kadamu daita ne saboda Allah Allah kakeyi kaga danka dake jikinta "kadamu da su'ad saboda cikin jikinta, zance iyayenta a kullun bazan daina fad'a maka bakafisu damuwa daita ba kai kanka yazakaji idan karasa cikin jikinta?

ya runtse mayatattun idanunsa yana jin zafin kalmar musty "wai meyasa musty bazai fahimce sa ba?

"meyasa bazai gane zahirin damuwarsa akan matarsa ba?

"shi yasan yana Allah Allah ya mallaki cikin jikinta amman wallahi yafi bukatarta akan duk abinda zata haifar masa, ita ya fara samu kafin yasamu cikin jikinta saboda idan tana kusa dashi shi kadai yasan irin farinciki dayake," yanzu bai san yadda zai misalta yadda yake ji ba sannan yace masa saboda cikin jikinta ya damu daita cikin da bai sani ba rayayye ne ko akasin hk?

ahankali ya furta "musty ansani nayi hasarar sosai ,ina matukar son matata aka gurbata min tunani akantan" ina son su'ad ina sonta sosai ina kaunarta har bansan yadda zan misalta maka ba ina jinta acikin nama jikina ban san haka so yake ba sai a yanzu dana rasa abinda nake so da muradi .
"kullun na tuna abubuwa da zeey tayi min alokacin baya sai naji wani iri daci ya tsaya min amakoshi ,tundaga lokacin dana waye gari banganta tare dani ba ban sake jin test din komai abakina ba why zaka dinga ganin ban damu daita "ka duba kaga yadda iyayenta ke rayuwarsu daya ne da yadda nike a rayuwata ayanzu?

" musty bazan ce kwata kwata basu damu daita ba, amman wallahi basu kaini damuwa daita ba babu abinda su'ad tasani wanda ya danganci rayuwar duniya batasan komai ba saini dana koyar daita bata da exprence din komai sai wanda na koyar daita ,kai kanka sheidani akan irin rayuwar damuka gudanar a koria daita ,komai a natse take yin sa ga hakuri dayanayina koda kuwa bata so ,ya runtse mayatattun idanunsa sosai hkn ne yasa musty jin kwalla ya kawo a idanunsa yayi saurin meidawa dan kar ak ya lura da hakan.

yayinda shi ak bai lura dashi ba yacigaba da magana " musty yaya zanyi da rayuwata?
" nasan damuwar rashinta shi zai yi sanadin mutu...

musty yayi saurin toshe masa baki "karkace haka dan Allah idan ka mutu ita kanta bazataji dadin rayuwar da babu kai acikinta, dan Allah kayi hakuri har na dawo daga tafiyar nan da zanyi kwana uku kacal zanyi na dawo duk yadda zaayi yi mu gano inda take zan bada gudumuwa ,"wannan tafiyar kai ya cancata kayita amman saboda yanayinka yasa na ajiye angoncina domin cigabanmu yakarasa mgnr cike da zolaya yana murmushi.

"kai kasani da wani banzar angonci ,duk abinda zakuyi , bazai taba kai wanda nayi da matata ba, zuwan musty ya dan kwantar masa da hankali har yasamu karfin gwiwa aiwatar da wasu ayyukan dake zube agabansa..



*********

bayan kwana biyu yana zaune a cikin office dinsa, aiki yake yi but lokaci zuwa lokacin zai waigo ya kalli hotonta sannan yacigaba da abinda yake ,bayasamu kuzarin yin komai sai wani abu daya danganceta na kusa dashi ,itace karfin ikonsa a wannan lokacin.
"a duk lokacin dazai d'aura kwayar idanunsa akan hotonta jinsayake tamkar rudanar taimako ce agaresa.
ya tsayar da aikin dayake tare da shagala gurin kallon hotonta wanda wani lokacin suke birkita masa tunani ya dawo tamkar mahaukaci ahankali yacigaba da kallon hotonta yana tunani baya ,tare da abubuwan da zuka faru kafin ya mallaketa matsayin mata sai dai kalma daya ce tafi kowace irin kalma mahimmanci da tsaya masa cikin kwalkwarsa har yayi mata babban ma'ajiyi a k'asan zuciyarsa.
bazai ta'ba manta wanda ba zai taba wannan kalmar ba "ina sonka abdulkabir .. ba yadda na iya dole na furta maka ina sonka batare da na shiryawa hkn ba, dan Allah kasoni ka aureni zan zamemaka tamkar baiwa agareka duk inda kaajiyeni zan zauna zan bi umarninka ,ka aureni kar narasa raina akanka ...
ya runtse mayatattun idanunsa "ashe sha'war dayake daita ma karfin ikontace ,damar samuwarta ta gahurta ajikinsa tunda ya rasa matarsa ya nemi duk wata sha'awarsa ya rasa amman tun asafiyar yau daya farka daga mafarkinta ya tsinci kanshi cikin wani irin yanayi jikinsa yake bashi komai ya kusan zuwa karshe garesa, domin kuwa yasawa ransa bazai iya aikata komai da wata mace ba byn ita hawaye suka gangaro masa "su'ad na hakura zancigaba da rayuwata haka babu komai....

wayarsa ce ta katseshi daga tunanin daya lula k'ara uku yana ji sai daga can ak yasa hannu ya lalubo wayar ya d'auka ya kara a kunnen daga dayan bangaren musty dake saukowa daga matattakalar jirgi yace "ak kana ina?

jin murya musty cikin yanayin farinciki shima ya tsinci kanshi ciki farinciki maramisaltuwa "ya'akayi ne musty ina office yanzu.

"gobe ne yakama dawowata amman murna ya hanani zama bazan iya jin wannan abun farincikin na kasa gaya makaba ..

"menene musty kasamo min inda su'ad take ne domin shi kadai abinda zanji yasanyani cikin farinciki?

"tabbass nasan wanda yasan inda take yanzu hk ina airport kazo kasameni yanzu "gaya min wace kasa taje ko garin dataje tabarni ina tangaliliyar rayuwa?

"kai dai kasameni yanxu a she an dade dasanin indatake akace aboye kar asanar ma ..ai baigama jin mezai fada ba ya mike a zabure yana kiran sunan musty, musty kuwa tuni ya katse kiran da gudun bala'i ak ya fito mataimakinsa ya biyosa abaya yana tambayarsa kafin kace me tuni escort dinsa da securities dinsa sun zagayeshi bai tsaya sauraronsu ba yashige mota yajata a guje suma suka biyo bayansa .

A airport din ma hk ya dinga gudu gudu sauri sauri zuwa lokacin har musty ya siya musu tiket din shiga conotoun yana tsaye yana jiran karasowarsa ak na arba da musty kuwa ya kankameshi ajikisa " aboki banida kamarka , ka nuna min kai masoyi ne na hakika tun da ake wannan tashin hankali sai yanzu ak yaji hawayen farincikin sun zubo masa .
musty rungumeshi a jikinsa saboda yana goge masa hawayen dayake dan baya son mutane su fuskancisu ..



mmn sudais ce

💗💗💗💗💗💗
SAI KA AURENI DOLE
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗



~NA~



*AYSHA A BAGUDO*



Dedicated To
Hauwa A Usman
Jiddar

YA HAKAM

THE MAKER OF IMMUTABLE
JUDGEMENTS

page 85

........Ahankali Musty ya zaresa ajikinsa yana dubansa, yayi matukar mamakin irin ramar dayaga Ak din ya sakeyi koma yace ya k'ara lalacewa kamar wanda yayi jinya a d'an kwanakin dayayi bai sanyashi acikin idanunsa ba.

" wani irin dad'in farin ciki ke d'awainiya da ruhinsa ya dinga jin kamar ya narke agurin saboda yadda yake ji ajikinsa,
wasu hawayen murna yacigaba da zubarwa "me zaicewa Musty arayuwa?

"Musty ya gama masa komai arayuwarsa tunda yasamo masa labarin inda bugun zuciyarsa take.

ya dinga kallon fuskar Musty yana tsantsar murna a hankali kuma ya dinga murmushi yana hawaye duk atare Musty ya kalleshi yana murmushi, shima farin ciki yake damuwa abokinsa tazo k'arshe zai dawo tamkar yadda yasanshi ada.

hannunsa yakamo suka nufi inda zasu shiga jirgi suna magana k'asa k'asa Musty yace "kayi addua friend Allah yasa ba'ayi dogon fushi da kai ba akan abubuwan da suka faru.

"Addu'a kullun cikin yinta nake a tun sanda lamarin nan ya faru,in sha Allahu bazatayi fushi da mijinta ba, tasan mijinta na tsananin sonta,tasan da ina cikin haiyacina bazan yi abubuwan duk da akace nayi ba, "nasan zata min uziri bisa ga kyawawan halaiyenta yak'a rasa fadar haka yana cizan lip's dinsa na kasa shi kad'ai yasan yadda yake jin zuciyarsa akanta.


Acikin jirgin ma kasa boye murnarsa yayi duk da wasi wasin da zuciyarsa ke yi,sai dai ya karfafa zuciyarsa da zai yi nasara akanta domin wani lokacin idan abubuwa suka daure masa, cikin sauki kuma zasu warware, Allah Allah ya dingayi jirgin ya sauka ya d'aura idanunsa akanta.

A natse yake takowa daga matattakalar benen jirgin yana jin wani irin farinciki from know where yana ziyarar ilahirin jikinsa ,koda bai d'aura kwayar idanunsa akanta ba,amman ruhinsa ya samu salama ,saboda jinsa a kasar da bugun zuciyarsa take zaune ciki , ahankali suka soma fitowa daga cikin jirgin har suka karasa saukowa gaba d'aya .

kai tsaye inda jerin motocin haya dake jire suka nufa batare da b'ata lokaci ba suka shiga motar direban yajasu.

"tafiyar minti talatin ce takawo su unguwar, Ahankali ya fito daga cikin motar bayan direban yagama daidaita parking a k'ofar gidan.

yayi shiru yana kallon yanayin tsarin ginin gidan ko ba'a gaya masa ba yasan gidan wani hamshakin me arziki ne, juyowa yayi yana tambayar direban daya kawosu "ka tabbatar da addrees d'in da muka baka kayi amfani dashi?

cikin harshensa turancinsa da bai gama k'warewa ba yace "nan ne gidan Alhaji Mahmud tsohon minister al'qallar kasuwanci da gine gine ta kasar Cotonou ............
kai kawai Ak ya jinjina yacigaba kallon tsarin gidan,yayinda Musty ya juya yana sallamar direban "kana mamakin ganin tushen su'ad ko? cewan "Musty

Ak yayi shiru yak'i cewa komai sai cizan lip's dinsa na kasa yake yi yana cigaba da kallon gidan ko shugaban k'asa albarka, Musty yaci gaba da magana "a wasu lokuta haka al'marin ubangiji yake ni kaina nayi mamaki ganin muhallinsu koda yake ai biri yayi kama da mutun dan yanayin Umman Su'ad d'in bai nuna daga gidan babu ta fito ba.


"rayuwa ce tazo mata a haka tunda Musty yasoma magana baice masa komai ba shima Musty yasan bazai ce komai d'in ba a irin wannan yanayin .

kai tsaye gurin securities din bakin get d'in suka nufa suka nemi ayi musu ison shiga cikin gidan cikin minti goma akabawa me gadi umarnin yashigo dasu.

A hadadden parlour'n mamma akayi musu masauki cike da girmamawa da mutuntaka ta tar'besu sukayi saurin durkushewa k'asa gabanta suka kwashi gaisuwa dan ko ba'a gaya musu matsayinta agidan ba sun sa itace tsohuwar gidan sakamakon tsantsar kamanninta da Umman su'ad ,domin babu abinda yarabasu sai yanayin girma ,ta amsa gaisuwarsu tana faman tsokanarsu "duk sai naga fuskarku a k'asa acikinku waye angon nawa?

Ak wanda har lokacin yake durkushe cikin tsantsar tsoro ko d'agowa ya kasayi a k'arshe ma ya sakeyin k'asa da kansa sosai cike da fargaba,sai dai zuciyarsa dake tsananin bugawa domin son ganin abincin ruhinsa.

Gaba d'aya zuciyarsa tak'i samun sukuni da natsuwa babu abinda take muradin gani tamkar matarsa .

Musty yayi murmushi sannan ya nuna mata Ak da yatsan hannusa "ga angon naki nan durkushe watakilla ya manta ba'a durkusawa mata ne.
atare sukayi murmushi amman banda AK dake kalle kallen ta inda zaiga fitowar sahibarsa..

"lallai kam da ala'mun mantuwa yayi masha Allah da mijin nawa ,na iya zaben miji nagani na fad'a, kodayake nima ba baya ba gurin kyau,watakilla ma shima abinda ya hango kenan ko ango na??


"maza tashi ka zauna kaji kar kafafunka suyi maka ciwo, ka saki jikinka tamkar kana gida, dan naga ala'mun kamar ka tsorata da ganina
suka sake yin wata dariyar suna dubansa.

shi dai Ak still bai ce dasu komai ba baya ga shafan bayan keyarsa dayayi ala'mun jin kunya.

Musty ya d'an saci kallonsa "wannan itace rana ta farko dayaga wannan tsigar tajin kunya atattare dashi ,sam shi mutun ne mara kunya mara jin tsoro me dakakkiyar zuciya akan komai.

" lallai mamma tasamu darajar me girma da diyarta ta kasa samu agurin sirikin nata.

Ahankali ma'aikatan gidan suka shiga kai kawo a tsakanin kitchen da cikin parlour'n ,an shirya dining table d'in dake can gefe guda nau'in abinci da abin sha ne iri iri wanda daman ka idar gidan kenan,
basa yin abinci kala daya sannan basa yin abinci kad'an saboda basu rabo da baki.

mik'ewa tsaye mamma tayi ahankali tare da cewa kuci abinci yanzu zan turo muku ita, Ak yayi saurin cewa" uhm dan Allah karki ce mata mune, Mamma ta dakata da tafiyar data soma tare da yin murmushi irin nasu na

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login