Showing 1 words to 3000 words out of 186303 words
๏ปฟ๐๐๐๐โคโ๐ฉนโคโ๐ฉน๐๐๐๐
*DA CIWO A ZUCIYATA*
๐๐๐๐โคโ๐ฉนโคโ๐ฉน๐๐๐๐
_MALLAKIN_
*SAJIDA NIJAR*
*FREE BOOK NE* 1๏ธโฃ
LITATAFAN MARUBUCIYAR
Duk karyar kada
Yar mahaukaciya
Neman na kaina
Bani da zabi
Bak'a ce
Kutkale
Makauniya ce
Mage
Duk nisan jifa
Idan ka raina inda kake
Dutse
Alkalamin kadarata
Bani da zabi
Dakika Biyar
Now
*Da CIWO A ZUCIYATA*
*Tallah, tallah, tallah*
*SECRET DE LA FEMME DU MANGA*
_Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata, nesa tazo kusa,Amarya ,Uwar gida,Ango da mai gida Har ma da yan mata da samari shin kuna sane da cewa HAJIYA FUSAM ta shirya tsaf domin gwangwaje ku da turarakunta masu dankaran kamshi? Tare Kayan gyaram jiki na musamman ,wanda daga nesa kamshin ki kadai ya wadatar ya isar da sakon zuwanki waje,gidan ki kuwa sai ya zam abun kwatance wajen kamshi, kar na cika ku da surutu bara in fara zayyano su_
Farar Humura
Bakar Humura
Humura special,
humura de bain
Humura epicรฉ
Lait de nuit
Parfums dรฉsodorisant
Parfums rideau et dras
Lait de nuit
Alkam
Kulakcam
*Waษannan kadan ne daga bangaren turaran ruwa*
Gagab, sandal flex, Durot, durus, sandal fleur, tafarce, farce, sandal bangui, sandal, hypotonic sandal, al'ut, coktail creation VIP, Gajiji, Mankaji, turaran wutar labule da cafet, Aba malan, boulettes
*Munada bangaren gyaran jiki kamar haka:*
mai mai saka santsin jiki, mai mai kanshi, Kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi santsi da laushi, kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi fari, Sabulu mai saka fata ta yi haske, sabulu mai saka fata ta yi santsi, sabulu mai goge yanayin fata, mai wanda baya saka fari mai gyara fata
Sayen na gari mai da kudi gida,sai an gwada akan san na kwarai๐๐
Hajiya Fusam na zaune a kasar Niger domin yin magana da ita kai tsaye tuntuษi wannan number 97 82 44 94
*SECRET DE LA FEMME DU MANGA*
Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata๐๐๐๐๐
Tunda suka yi sallar asubahi suka yi aduo'insu kamar yadda suka saba ita ta koma ta dan kwontar da hakarkarinta, domin dama ta cika dare ne sosai tana bitar karatun jarabawar da zata gabatar a yau din a makaranta wace daga ita in sha Allah kuma sai ta karshe wace sunna yi zasu samu damar fara zuwa asibiti dan kula da mararsa lafiya ko nace koyon aikin jinya kafin su rike makamin kula da marar lafiya........., Yan uwanta kuwa su biyun watau RUKAYA da AISHA sai suka shiga hana habarsu kamar yadda ya zame masu jiki kama daga gurje tafin kafa, wanka da wuri dan gyara fuska da dai sauransu a matsayinsu da matasan yan mata masu ji da kansu da tsarin kyau daidai nasu da kuma iya wanka dan samun cikar burinsu watau birge wanda suka san sunna iya birgewa a hanyarsu ta zuwa ko ta dawowa daga makarantar summa
Sai da karfe bakwai ta yi mahaifiyarsu ta dage labule sanye cikin zumbulelen hijabinta wanda ke yi kamar zai tadeta ta fadi ama kuma baya tadetan dan damatsunnan hannayenta ke dauke shi da zarar ta motsa ta fan leka kanta tana kallonsu da dan murmushi ta sake amsa gaisuwarsu sannan ta ce" Oh Allah, ana nan ana fama da hodar ? Ina ita dayar take ban ji motsinta ba bayan tace jarabawa ne da ita yau din?"
Firgigit ta farka a barcin da take yi, mundul taundula daga saman shamakakiyar katifarta wace kwonciyar da ta yi a sama ta sake matse katifar sosai ya zamto ta takure sosai katifar dan dama ba wani auki ne da katifar ba gashi kuma ta hayeta ba ko dan juyawan nan
Hularta ta laluba ta warto ta kabeta ta dora saman gashinta da bai fi kamu biyu ba dan bata da tsayin gashi sai cika sosai a kanta sannan ta kama ta mike daga zaunen da ta yi da abin magagin barci ta kalli Aisha ta ce" Karfe nawa ne Aishe?"
Aisha ta duba yar karamar wayarta ta sanar mata bakwai ta yi, ta dora da fadin" Bamu tasheki ba dan ko takwas saura kika farka ba lati kike yi ba tunda wankan kawai ne kike yi"
Ita dai da sauri cikin yannayin halitarta wace kana iya tunanin idan har ta motsa to fa da shasheka zata yi motsin, sai dai abin mamaki jikinta da ya fi shekarunta bai hanna mata motsawa da kaza kaza ba ta yi bayi tana hangen Mamanta na batse mata bokicin da ta ajiye dan jan ruwa a rijiyar gidansu ta duba sabulunta yana nan dan haka da gudu ta fito ta kinkimi ruwan ta yi bayin da shi ta ajiye abinta sannan ta shiga tubewa dan yin wankan
A wajen wankan ne kawai ta dan dauki lokaci, dan akoyta kale kalen jiki irin na tsaftar jiki, koda yake sai ta yi anfani da lemun tsami ta darji hamatarta da du wanu lungu na jikinta wanda ke iya daukan gumi har ya bada wani wari daban irin na jikin dan adam bale ita mai tsoka a jiki masha Allah, kafin take yin wankan ta fito cikin sauri ta yi dakinsu ta warci uniforme dinta dake saman kujera ta kabe ta shiga zurawa bayan ta saka rigar mamanta da kafcecen pant dinta sannan ta zumbula hijabinta ta sake tsalake yan uwanta da har yanzun basu gama nasu shirin ba tana murmushi ta daga masu hannu da fadin" By sisters, sai mun hade"
Rukaya ta dago ta fara zuba idannuwanta a takalman da yar uwar tata ta saka takalma ne yan soso plat sun shamuge abinsu , bayan tana da takalma taki biyu bayansu ama dan yau tana jarabawa abin ya karra kwabewa takalmin kirkima ba zata tsaya ta saka ba haka zata tafi
Kai kawai ta girgiza domin ta san ba sauraronta zata yi ba in dai ta wannan fannin ne , ita a nata tsarin rayuwar tun da ta gama fahimtar rayuwarta ta gane me take ciki ta yi waje ta ajiye abubuwan nan gefe , ta riga ta sani ne bata lokaci ne a gareta ita, dan haka ta fi dauko fannin da zai gyarata wanda zata iya birge kanta da kanta da kuma Wa'inda ke tare da ita, shine karatunta da kuma nema cikin tarin rashin gajiyawa da rashin son jikin da Allah ya yi mata a cikin irin nata ni'imomin itama
Dari biyu yau aka bata, hakan ya sa take tafe tana sakin murmushi da irin tafiyar nan ta gagawa dan a hasashenta in sha Allah minti ashirin da uku zai sadata da ajinta hakan zai yi mata sauran minti goma sha takwas kafin a shiga aji kennan zata karya abinta kafin ta shige, wanda makarantar ke dan nesa da gidansu kadan ama kuma baya mata nisa dan ita a kafa take tafiyarta ta kuma dawo abinta, yan uwanta ne ke bata mamaki, tasu makarantar ta fi kusa da gida fiye da tata , ama idan ka ga sun yi tafiyar kafa ranar tai masu daren kure ba gaba ba baya sai gyaran ubangiji kawai
Cikin saurinta ta karasa wajen aunty mai dambu ta zaro dari biyunta ta mika mata ta sanar mata dambu na saba'in zata maka mata tana ta sakin murmushi tana bin hannun Aunty mai Dambu dake zuba mata da kallo, ta sani ne yau zata kile abinta dan kuwa mai cin na arba'in ya kara talatin ai zai more iya morewa
Zama ta yi nan ta wanke hannu ta maida hankali ta ci dambun nan sannan ta sayi ruwa daya ta shanye tasss kafin ta mike tana sauke ajiyar zuciya hadi da sakin murmushi domin hankalinta ya kwonta bata da matsala da cikinta takarda kuwa a je a gabza cen dama ba matsalarta bace , watau karatu
Kasancewar ranar jarabawa ce, wa'indama basu cika zuwa makarantar ba, da masu zuwa a lati du sun iso tun kafin a shiga, hakan ya sa makarantar ta cika da wuri inda hankalin daliban du ya kakasu gida gida, domin karara zaka ga halaya uku a tare da daliban mabambanta,
Wasu zaka ga hankalinsu Kwonce yake dan sun sani sun dauka sun kuma yi iya kokarinsu sun riga sun sani idan sun shiga ajin nan da izinin Allah ba zasu fito a tutar babu ba, watau ko yayane zasu dauki na dauka ko su cinye baki daya
Wasun zaka ga sunna ta fama da bude litafi sunna ta bitar abinda ba zai zauna masu a kai ba, saima ya zubar da dan wanda suka cika dare sunna dauka domin dama basu cika leka litafin ba sai irin wannan dama ta samu ta jarabawa, sai ko daidaikun da zaka ga wayarsu ce a hannunsu hankalinsu kwonce, yawanci ya'yan baba da rai ne da suke tunanin tunda babansu ya tara to fa basu da matsala da damun kansu da yin karatu ko faman fafutukar samun takarda , wannan din ba shine a gabansu ba, gidansu an tara a yi sama a yi kasa su kam sun san ko abokin baba ne zai basu aiki a wajen da ya dace da su, shi yasa basu da damuwa a abinda zasu tarar na jarabawar su ci ko su ki ci matsalar wanda ya daurawa kansa matsalar ne, kai hasalima sun zo makarantar ne dan kar a yi masu fada a gida dan iyayensu ne ke so su yi karatun ba wai su ba!
Hankali Kwonce ta nufo hanyar ajin nasu, inda yawancin daliban suke, tana tafe tana dan gaisawa da kusan du wanda ta hadu da shi faran faran da murmushinta domin ita dai ba gwali takeda na son birge wani ba, bata kuma zo makaranta dan ta birge wane ko ta bata da wane ba, wannan shiriritar ba da ita ba, to ita batama ga anfanin hakan ba sam, ana ta kai wa yake ta kafa in ba shirmen wasu daliban bama.................
"Abokina, ga fa mutuniyar cen tafe, ka ga kamarma sidar hannu ake ko me aka samu da safiyar nan?" Kamal ya fada yana dan murmushin shakiyanci yana kallonta da irin tafiyar da take yi ba abinda ya dadata da kasa , bata da damuwar komai sai ta abinda yake gabanta, wanda hakan abin mamaki ne a wajen samari da yan matan yanzu, duba da irin yadda kowa ke rike da nasa akidar na kin raini, da ษorawa kai abinda ya fi karfin kai dai da sauransu...........
Fuska ya dan gimshe ya kalli inda take zuwan sannan ya maida dubansa kansa fuskarsa a dan gimshe ya ce" Ka fa san bana son haka ko? Na sha fada maka ka mutuntata ko ka shafa mata lafiya, kowa ya yi ta kansa ko?"
Zai bashi amsa ta karaso inda suke tsaye fuskarta dauke da madaukakin murmushin gannin ya ji maganarta har ya zo din kamar yadda ta masa maganar jiya da yama da suka rabu daga wajen exercice cewar ya tabata ya zo aji a kan lokaci ya kuma yi exam din nan a cike kar ya saki ya ki zuwa fa?
Tsayawa ta yi dan daf da shi ta ce" Bani abin kunnen bawan Allah?"
Murmushi ya yi yana fan shafa bayan kansa ya cire abinda ke cikin kunnensa ya mika mata da wayarsa kirar iPhone 11 pr ita kuwa ta kashe ta bude jakarta inda ta san ba zata fashe ba ta saka masa a ciki sannan ta rufe ta sake dubansa ta ce" Ka dauki shafukan fa na fada maka jiyan kuwa?"
Shnayayun idannuwansa ya dan bude kamar wani mai shan abin maye bayan babu abinda yake sha haka yannayin idannuwansa suke ya dan kalleta kadan ya kuma gyada kai, shi fa du ba wannam bane a gabansa, abinda yake gabansa aikin da Mahaifinsa ya saka shi yace kuma karfe takwas da rabi ya zamto yana bakin shagonsu na wajen sabon gari dan a sauke kaya a gabansa ya kuma daidaita komai , yau dai wunnin yau sam bashi da wani lokaci gaskiya, shi yasa ya yi safiya ya zo dan baya so su raba hali saboda jarabawar nan, idan dai ta ga ya zo ai ba zata ji haushi ba ko ta yi fadan bai zo ba yana wasa da karatu
Da jin dadi ta yi gaba dan duba sunnanta ta barsu ko ci kanka bata cewa Kamal ba, haka shima da ido ya rakata kafin ya dauke kai yana girgiza kansa yana tunanin ta yiwu tun fadan da aka yi ne bata masa magana take masa gaba, bai sani ba cewar ita ba maganar gaba a cikin tsarin rayuwarta ,idan har ta kula cewar zamanta da kai akoy wani abu mai kama da wulakanci ko cin zarafi ne zata janye jikinta cikin salama ba tare da ta yi naci ko ta dorawa kanta abinda zai dameta ba,
Hasalima abokin nasu da suke takama da shi shine ya yi mata nacin son kasancewa aboki a wajenta itama, daga wannan bata tunanin akoy wani abu da zai sa ta zamto abokiyar gabarsu, ko fadan da aka yi budurwarsa ce take tunanin meye tsakaninsu haka? Kamal din wajen fada mata bafa soyaya sai ya yi aiki da munanan kalamai da suka sa ta daina gannin kimarsa....., Lalle ita talaka ce, ama a cikinsu ai talakawan da yawa,haka kuma yannayin jikinta ita baya damunta dan ta san Allah ya haliceta haka , haka kuma yake son ganninta, bata tunanin wani bawa zai iya tsayawa ya zageta a duniya dan kawai ita din tana da jiki da ake kiranta da yar lukuta saboda shi, ba kuma ta tunanin bata je neman alfarmar wani wani ba zai wulakantata ba, idan sun kula zumunci ne da zamani yazo da shi tsakanin namiji da mace na abotaka, nata kawancen bai kaucewa tsarin adininta ba domin akida gareta shi kuma yana da addini, layin rayuwarsu ba daya bane dan shi yana zuwa makaranta ne dan yaki da jahilci , dauke kewa, jin dadin mu'amala da jama'a, inda ita kuma take karatu dan samun abin sakawa a baka gobe idan Allah ya nufa!, Ita karatu ne take yi da dukkan karfinta dan bata da madafar da ta wuce bin abinda ya dace dan ta samu rabauta itama da nutsuwar zuciya, shi kuwa wadinnann ya dade a cikinsu domin ya
๐๐๐๐โคโ๐ฉนโคโ๐ฉน๐๐๐๐
*DA CIWO A ZUCIYATA*
๐๐๐๐โคโ๐ฉนโคโ๐ฉน๐๐๐๐
_MALLAKIN_
*SAJIDA NIJAR*
*FREE BOOK NE* 2๏ธโฃ
LITATAFAN MARUBUCIYAR
Duk karyar kada
Yar mahaukaciya
Neman na kaina
Bani da zabi
Bak'a ce
Kutkale
Makauniya ce
Mage
Duk nisan jifa
Idan ka raina inda kake
Dutse
Alkalamin kadarata
Bani da zabi
Dakika Biyar
Now
*Da CIWO A ZUCIYATA*
*Tallah, tallah, tallah*
*SECRET DE LA FEMME DU MANGA*
_Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata, nesa tazo kusa,Amarya ,Uwar gida,Ango da mai gida Har ma da yan mata da samari shin kuna sane da cewa HAJIYA FUSAM ta shirya tsaf domin gwangwaje ku da turarakunta masu dankaran kamshi? Tare Kayan gyaram jiki na musamman ,wanda daga nesa kamshin ki kadai ya wadatar ya isar da sakon zuwanki waje,gidan ki kuwa sai ya zam abun kwatance wajen kamshi, kar na cika ku da surutu bara in fara zayyano su_
Farar Humura
Bakar Humura
Humura special,
humura de bain
Humura epicรฉ
Lait de nuit
Parfums dรฉsodorisant
Parfums rideau et dras
Lait de nuit
Alkam
Kulakcam
*Waษannan kadan ne daga bangaren turaran ruwa*
Gagab, sandal flex, Durot, durus, sandal fleur, tafarce, farce, sandal bangui, sandal, hypotonic sandal, al'ut, coktail creation VIP, Gajiji, Mankaji, turaran wutar labule da cafet, Aba malan, boulettes
*Munada bangaren gyaran jiki kamar haka:*
mai mai saka santsin jiki, mai mai kanshi, Kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi santsi da laushi, kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi fari, Sabulu mai saka fata ta yi haske, sabulu mai saka fata ta yi santsi, sabulu mai goge yanayin fata, mai wanda baya saka fari mai gyara fata
Sayen na gari mai da kudi gida,sai an gwada akan san na kwarai๐๐
Hajiya Fusam na zaune a kasar Niger domin yin magana da ita kai tsaye tuntuษi wannan number 97 82 44 94
*SECRET DE LA FEMME DU MANGA*
Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata๐๐๐๐๐
A lokacin da ta shigo gidan kowa yana nan
Bata tsaya tsaye tsaye ba alwallah ta daura kawai ta shige dakinsu ta zauna ta bude litafinta tana yi tana kallon yan uwanta dake hira da makociyarsu wace ta shigo su kuwa sunna tsakar gida da mamansu sunna tataunawa kan shirye shiryen auren y'arta budurwa
Aisha ce ta kula da yannayinta domin sosai yannayin nata ke nuni da ranta a bace yake, dan haka da kula ta ce" Hajia sister wai waye ya tabo ki haka?"
Kallonta *KAUSAR* ta yi a hankali , sai kuma ta kalli inda mamansu ke fadin maza Rukaya ta fito ta zuba masu abinci su ci
Dan sa'ida ta ji a ranta, domin har ga Allah tafiyar da ta yi dambun nan gaba daya kamar bata ci komai ba take ji, du ya yi kasa, dan haka ta kasa ba Aisha amsa har Rukaya ta zubo abincin ta shigo da shi dakin lokaci daya kuma suka mike sunna fita dan Maman ce ta shiga fadan kar su kumkume daki su ci abinci
Du a tsakar gidan suka zauna saman tabarma da kwanon da Aisha ta janyo masu ruwan rijiyar ta ajiye sula shiga cin abincin a cikin kwano daya gaba dayansu cikin nutsuwa
Ajiyar zuciya makociyar Mama watau maman Naรฏma ta sauke a ranta tana jin tausayin Maman da ฦดaฦดanta......., Har ga Allah abin a tausaya ne idan aka yi dubi da yan matan sun fa kai sun kawo ama shiru ko daya ba'a aurar ba, su jira suke yi KAUSAR ta samu miji, wace idan har rayuwarta za'a zauna a duba babu wannan tsarin a cikin tsarin rayuwarta......., Babu wanda zai ce yau ya taba gannin saurayi a matsayin na KAUSAR, yarinyar kamar wata mai bakin aljani ita din da kantama bata da alamun ta damu da wata magana ta d'a namiji a rayuwarta, wani fannin kuwa har ga Allah ana yi mata duba ne na wace bata bada wani dan motsin da zai nuna cewa ta dan itama mace ce tana cikin layin mata a rayuwa ba, ko me yasa ta zabi