Showing 33001 words to 36000 words out of 186303 words
hakan kamar ai ba daidai bane kau?
Ido ya zuba mata, fuskarta ita ta fi bashi mamaki, kwaliyar dake zane a saman fuskar nata ta fi bashi mamaki, sai dai bai san cewa abin mamakin a gaba ba sai da ya dan so gannin meye yankawar da Hajia ke fada ya dan kalli yannayin shigar jikinta a dan gurguje ba da nufin komai ba sai dan ya ga wani hijab ne ta saka wai HAJIA ke wannan surutun sai ya ga wani ikon Allahn da ya so sakashi kyatsa rantsuwar sam bamaa ita bace ta hanyar dauke kansa da sauri ya juyo barin hajia , sai dai yanna kallon Hajiar ya ga ta tsatsareshi da ido da duba wani kala daban irin marar kyau din nan kuma da ido tana aniyar neman yin tsegumi da shi bayan cin naman wani haramun ne dan haka ya kauce idannuwansa ya hade fuska sannan ya mike tsaye daga zaunen da yake ya daga kafarsa zai karasa sai ya ji hannunsa rike taf a na hajia,
Dubanta ya yi sannan ya kalli hannun nasa ya ce" Sakeni mana"
Sai a lokacin Hajia ta saki hannun tana sakin harare ta ringa lekawa ta ga ya karasa inda KAUSAR ke tsaye ya mata nuni da ta wuce ciki, sumui sumui ta yi cikin ta tsaya shi kuwa ya karasa ya tsaya gabanta da sauri yana hade fuska ya bude baki zai yi magana ya ga HAJIA ta masu tsuru tsuru sai zarro ido take yi hakan ya sa ya sake jin wani takaici ya lulube shi ya ce" Hajia meye wai?"
Hajia ta tabe baki ta ce " Meye kuwa, miya ce, me zaka fada mata ne?"
Ikon Allah....., Ya ayyana a zuciyarsa ya zamto sunna kallon kallo su ukun
Yannayinta da sanyi ta ce" Ka yi hakuri besty gidan kwaliya muka tsaya shi yasa fa bamu karaso da wuri ba, ka tambayima su Aisha "
Da bacin rai ya ce" Haka fa, gama katt na gani, yanzu meye anfanin haka KAUSAR? Kefa ba wata yarinya bace da zaki biyewa yara ki je ki yi wannan abin ki biyo titi, yanzu ko kunya bakya ji???"
"Yo kunyar uban wa kake so ta ji ? Yau ga jaraba auren wani shegen ke kanta da za'a hannata yafe ta zaga gari? Da yafen nan take na rantse da huwa rahamanu Ιan nan na tabata da yanzu y'ar nan ta yada na biyar ko na shida ta dauki wani cikin dan bana tunanin akoy shahashan da zai iya hakura da y'ar nan,kuma nice nan makaryaciyarka zaka ga yadda zata yi kasuwa, dama abinda ke hijabin nan kennan???" Hajia ta fada, hankali kwonce har tana dafe haba
Gaba daya wata irin kunya ce ta nemi halaka KAUSAR
A tsayen da take sai ta duke tana rufe fuskarta a cinyoyinta ta furta" innalilahi HAJIA, na shiga uku aa fa"
TAUFEEK dake tsaye ya rasa wanene ya dace ya yiwa wa'azin jin tsoron Allah a tsakanin Hajia da ita wannan yarinyar da ta tashi tana rufarta a kamilance ta wani saki jiki kamar ba KAUSAR ba? Kai wannan abu ya bakanta masa rai menene wannan shashancin?
Rai bace ya juya, har ya nufi falon ya dawo ya nunota da yatsa ya ce" kin ga daga falon nan in kafarki ta fita waje sai na saba maki KAUSAR, ba zan kyaleki da mutuncinki ki ringa yawo haka ba, shirme kawai kin iya sakani gaba ki wankeni in na dan yi wani abin kamar wata ta Allah kece ke yawo haka, an ji kunya!"
Ya idasa fada ya yi gaba
Hajia dake rike da haba al'ajabi na neman sakata marmaren yan maye na iya shegen Elhaji karami ta duko ta gyara daurinta ta nuno KAUSAR da yatsa ta ce" ki ji ni da kyau , ni nan nice uwar uban elhaji karami, kin ga kuwa na ga duniya gannin idona, nice zan fada maki mai fisheki, in bamu maki aure ba kwadaki zamu yi mu cinye ne? Kin ga kwaliyarki ba rashin kunya ko rashin kamun kai a ciki, Allah na tuba yo alherin nan ai ba kowa ke samu ba, tashi maza kada su baza su ki shige jama'a babu abinda za'a yi, in banda bakin hali irin na Elhaji karami in aka hannaki kwaliyar kika rasa mijin shi zai ji dadi ne! Ana abu ba tsoron Allah sam? Tashi maza wataya bikin amini kike shagali maki gani ya mutu dan bantan uba !"
To fa, Hajia kin kuwa zo da tsoron Allah anya?ππππππ Hajiar shagali
ππππβ€βπ©Ήβ€βπ©Ήππππ
*DA CIWO A ZUCIYATA*
ππππβ€βπ©Ήβ€βπ©Ήππππ
_MALLAKIN_
*SAJIDA NIJAR*
*FREE BOOK NE* 1οΈβ£3οΈβ£
LITATAFAN MARUBUCIYAR
Duk karyar kada
Yar mahaukaciya
Neman na kaina
Bani da zabi
Bak'a ce
Kutkale
Makauniya ce
Mage
Duk nisan jifa
Idan ka raina inda kake
Dutse
Alkalamin kadarata
Bani da zabi
Dakika Biyar
Now
*Da CIWO A ZUCIYATA*
*Tallah, tallah, tallah*
*SECRET DE LA FEMME DU MANGA*
_Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata, nesa tazo kusa,Amarya ,Uwar gida,Ango da mai gida Har ma da yan mata da samari shin kuna sane da cewa HAJIYA FUSAM ta shirya tsaf domin gwangwaje ku da turarakunta masu dankaran kamshi? Tare Kayan gyaram jiki na musamman ,wanda daga nesa kamshin ki kadai ya wadatar ya isar da sakon zuwanki waje,gidan ki kuwa sai ya zam abun kwatance wajen kamshi, kar na cika ku da surutu bara in fara zayyano su_
Farar Humura
Bakar Humura
Humura special,
humura de bain
Humura epicΓ©
Lait de nuit
Parfums dΓ©sodorisant
Parfums rideau et dras
Lait de nuit
Alkam
Kulakcam
*WaΙannan kadan ne daga bangaren turaran ruwa*
Gagab, sandal flex, Durot, durus, sandal fleur, tafarce, farce, sandal bangui, sandal, hypotonic sandal, al'ut, coktail creation VIP, Gajiji, Mankaji, turaran wutar labule da cafet, Aba malan, boulettes
*Munada bangaren gyaran jiki kamar haka:*
mai mai saka santsin jiki, mai mai kanshi, Kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi santsi da laushi, kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi fari, Sabulu mai saka fata ta yi haske, sabulu mai saka fata ta yi santsi, sabulu mai goge yanayin fata, mai wanda baya saka fari mai gyara fata
Sayen na gari mai da kudi gida,sai an gwada akan san na kwaraiππ
Hajiya Fusam na zaune a kasar Niger domin yin magana da ita kai tsaye tuntuΙi wannan number 97 82 44 94
*SECRET DE LA FEMME DU MANGA*
Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mataπππππ
Dawowarsa da hijab din hajia na sallah rike a hannunsa ya saka hajiar yin shiru da bakinta daga hudubar da take yiwa KAUSAR ta zuba ido tana kallonsa
Fuska a daure ya ajiye mata hijab din gefenta, murya cen ciki ya ce" I'm hungry,,,,"
Daga haka ya juya ya koma wajen zamansa fuskar nan tasa zaka rantse wani mugun abu akai masa
Kausar ta saka hijab din bayan ta dubi yannayin hajia , a hankali ta zame dan kwalin dake ciki ta cire sannan ta iya mikewa tana jin wani nauyi na kwaliyar a ranta ta sake dakatawa tana dyban HAJIA
Hajia ta hade hannayenta wajen kirjinta kasa kasa ta ce" Je zuba masa abincin sai mu dinke a daka na gama baki shawara, kin san dama shi magidanci tuwonma sai an zuba masa, matarsa dai zata ga iya shege, jibi keya uwa mun aikata sabo irin yadda yake harararmu, je zuba masa sai mu gama maganar "
Ajiyar zuciya ta sake saukewa a hankali ta karasa inda suke zaune, Salisu na magana, Adamu na dariya yana duba abinda yake nuna masa, shi kuwa TAUFEEK din yana zaune ne yana kallon shima abinda suke yiwa dariyar wanda sam shi bai ga wani abin dariya a nan ba, wasu yan mata ne a tiktok ke tikr rawa tamkar zasu karya kaffafuwa sai kace wasu jakai, shine suka ga abin birgewa a nan
Plate ta karo a kicin din HAJIA ta zo cikin nutsuwa ta zauna ta bude abincin ta shiga zubawa a zuciyarta tana ta tunanin abinda ta masa da yake jin haushinta, bata san ta inda zata kamo ba, batama san takamaiman laifinta ba, ta yiwu dan ta fito ba hijab ne, bai san itama fin karfinta su Aisha suka yi ba, da bata fito din a haka ba, lalle tana tausayawa YUMNAH, koda yake ta yiwu kuma in dai mai saukin kai da jin magana ce ba zata wahala a wajen mijin nata mai tsatsauran ra'ayi ba
A hankali ta dago dubanta dan tana ji yadda abokanansa ke fira da raha,ama shi ya wani kyale su sunna ta zuba su kadai bayan gayar nan idan tana tune tasa ce
Da idannuwanta ta bi inda ya zubawa ido, wato hannayenta dake rike da cokali mai dan girma tana zuba abincin, Wa'inda suke dauke da jan kunshi irin na yan mata da aka yi kata itama ta cancana abinta
A hankali ta sake zuba idannuwanta a saman fuskarsa, hakan ya sa suka yi ido hudu da shi
Bata saba dan sun yi ido hudu da TAUFEEK, TAUFEEK din abokinta ta fauke dubanta ba, ko yanzu da suke kallon ido cikin ido sai bata janye nata ba bale shi da take fadin kulun bashi da kunyar kallon idon mutun ya janye
A saman labanta ta iya budawa kadan, kasa kasa sosai ta ce" Me yake damunka ne?, Fushin me kake yi? Wate ya bata maka rai?"
Har ta ajiye maganarta yana kallon yannayin da ta yin, bai bata amsa ba ya janye dubansa a kanta ya maida wajen abokansa dake tataunawa sunna ta sako shi a ciki daga shi har ita
Tana gama zubawa ta so zama, sai dai da ido TAUFEEK ya mata alamun ta tafi, hakan ya saka ta shaka, shaka irin ta jin haushi harma ta gaza hakura ta sauke masa duba mai shige da harara kasa kasa sai dai a kausashe ta ce" Malan in nice baka son gani a taron naka na yi tafiyata mana? Me na maka tunda na zo kake bina da kallo irin na tsana?, In wani ya taba ka ka huce a kansa mana sai mu dake tare da kai kuma a rana baba irin wannan? Karma ka kula nin TAUFEEK sai me?"
Tana gama fada ta yi gaba da tafia irin ta sauro mai bayanar da irin tata baiwar wace ba kowa keda ita ba ama kuma idon kowa na iya ganni
Wani takaicin ya sake shaka har ya saka hannunsa ya talabe habarsa dan takaici da rashin madafa
Abincin sama sama ya iya cinsa dan ya riga ya gama fice masa a rai da abubuwan dake faruwa da shi a yau din
Sai da suka gama suka fice da abokansa wajen da taron ya fi yawa yana ji kamar kansa zai buga dan ciwo, domin hayaniyar tana nema ne ta fi karfin kwakwaluwarsa
Kusan karfe hudu na yama a dole ya mike ya shiga cikin gidansu dan irin hayaniyar dake ta tashi sama sama
Ikon Allah ta tsaya yake kallo a lokacin da ya ga iyalan mai kwanoni sunna raba hali tamkar an aiko su, fada ne ko mema zai kirayi abin? Shi dai ya ga abin tamkar ba na masu hankali ba kuma kunnayensa na nema su sanar masa wace ake son takalowa
Idannuwansa ne suka sauka a kan Maman su KHAUSAR dake tsaye da waren takalmi a hannunta , takalmin da ya san mamalakinsa , watau mahaifiyarsa
Wanzuwarsa a wajen ya saka yawanci kame bakinsu suka yi shiru, domin TAUFEEK bako yake a inda yake so a ganshi bako, sanane shi a hali na dabanci da jagaliya idan halin hakan ya kama, TAUFEEK mutun ne mai hali kala uku a rayuwa, a gaban tsagera shi din baban tsagera ne, a gaban iyayensa yana da ladabi da biyaya da kishinsu, sai mace daya tak dake taka shi ta masa rashin kunya son ranta, ita kuwa baya fatan a wayi gari ta ga kalarsa da yan gari suka sani, ya fi so ya ci gaba da kasancewa mutun mai matukar laushi, sanyi, rashin sannin ciwon kai a gabanta, dan tana da daraja da mahinmancin da baya so idan ta gane waye shi ta tsorata da shi,
Hular dake kansa ya cire a hankali yana sake bin yayar hajia da wani kallo mai kama da daf yake da budar bakinsa ya yi mata barin mahaukaciya komai girmanta da tsufanta kuwa, domin abu daya ne ta taka take fada daga bakinta wanda a duniyar nan baya tunani wuta ko mashi zasu hanna shi farautar mai zaginta, watau mahaifiyarsa, shi fa komai girmanka ka girmama iyayensa to fa zaka more shi fiye da tunaninka, idn kuwa ka yarda, ka kuskure, wata motsarariyar giyarka ta saka ka take masa martabar masu martaba babu abinda zai hanna shi aikata aiki irin na yaren da basu da tarbiya ta hanya watsa hannayens aa fuskarka ya ce da kai UWAKA ko kuwa ya ja baya ya shige ka kowa ya mutu a huta
Da sauri hajia ta kama hannun yar uwarta tana fadin" Wai menene kuka tsaya kunna kallon mutane ba zaku iya raba fada bane jama'a? Dan Allah kowa ya kama gabansa tunda abin hakane, yaya zaku taru kunna kallon abu na faruwa ama kowa ya ja ya hade hannunsa ya nade yana kallo? Wannan ai sam bai dace ba"
Da mamaki yar uwar tata ta kalleta jin furucinta, kasancewarta ita ta izata sosai kan su zo a yita ta kare kuma sai ta ji magana irin haka? Zata yi magana ta ga kula da abinda bata kula da shi ba da farko, watau TAUFEEK tsaye ya jinginu da abin labule idannuwan nan nasa sun kade sun yi jajir tamkar wanda ke shirin hadiye dan mutun yana bin kowa da kallo
Bata iya yin maganar ba sai hannunta da ta warce ta shiga haurawa cike da takaici
Hajiya Fatahiya ta saki yar guda tana sake yafa gyalenta ta ce" Wai rashin kunyar karya, ki ci gaba mana mu gani buge ko zobe zai ci nasara"
Hajia Nawarah da abin mayarwar ama ta yi shiru ta bari zata rama ne, saima kokarin korar mutanen da aka tara na arziki ta shiga yi tana fadin tunda hakane kowa ya watse ai an ci an sha sauran sa yi
A hankali ya dago daga inda ya jinginar ya nufo inda HAJIA Nawarah ke tsaye
Gaban Maman KHAUSAR kuwa sai da ya kwonci kwonci ya fadi, a dan firgice ta zuba masa ido tana tunanin abin yi, domin mahaifiyarsa ne ta sakata zuwa dan kar ta bari ya aikata wani abin a wajen nan in dai ya ji hayaniyar da ake yi
Har ya kusa cin mata da sauri Mama ta yi raf da hannunsa na dama tana cicira ido , muryarta a raunane ta ce" Aya D'an nan ina zaka je ne haka?"
Dakatawar da ya yi, niyarsa ya warci hannunsa da karfin da zai saka wanda ya rike masa watsuwa a kasa, sai dai muryar da ya ji ya saka shi sake ambaton Allah, sannan a hankali ya juyo yana dan kakaro murmushi ya ce" Mama, hajia ce zan cewa kar ta kori kowa, a ci gaba fa biki kawai"
Kai Mama ta gyada da sauri ta ce" To to to, ai ina iya fada mata ka je kawai abinka zan sanar mata in sha Allah "
Hannun nasa da ta rike ya sake kallo, a hankali ya sauke yar ajiyar zuciya sannan ya yi gaba bayan ta sakar masa hannun
Yana tafia Maman ta sake sauke ajiyar zuciya tana ta Adu'a a ranta sannan ta samu ta shiga bada hakurin laifin da bata san waye ta aikata ba
Tsaki Hajia Nawarah ta ja sannan ta haye ta nufi dakinta
Tana shiga ta tarda yayarta sai masifa take yi kamar zata tashi sama
Zama ta yi saman kujera tana kallon yayar tata da ta ce" a kan me zaki hanna ni magana dan wannnan ya shigo? Bakima son bata bikin nan na ga alama, in ba shi ba kina ji kina ganni a ringa tafka maki wulakanci dan ana auren dan so? Ke baki haihu bane ko shegu kika haifa? Da ki bari na fada na ci uwar babar tasa idan ya so na ga abinda ya is aya yi, in shine karshen marar kunyar duniya ya rama mata"
Murmushi mai ciwo Nawarah ta yi tana cire rigarta dan wanka zara shiga domin ta gama hada gumi ta ce" Ba zaki gane ba, ko a haka mun cakulata domin mutun ce da bata son hayaniya, sgi yasa bata cika zama a falo bama , wai ita y'ar gayu bata son hayaniya, na tabata tana cen tana hawaye, abinda ya sa na hanna ki magana na rantse maki da wanda raina ke hannunsa yana iya zabga maki mari a kan uwarsa, kuma babu abinda za'a yi, ke in fada maki aunty saima abin ya kare a kanmu domin yana iya hannaki shigowa gidansa a kan d'ansa, dan ko ya masa fada na bai kyauta ba ya mari mai shekaru to fa zai dawo ya min wanda ya dame nasa ya shanye, abinda na so uwar ta biye min mu hadu mu lakada mata dukan tsiya, sai wannan banzar yar kazagin nata ta jata ta haudata ciki, kuma ta dawo ta dauke takalminta daya da ta yar, na so koda takalmin ne mu samu mu ba kawar nan taki dake fadin a kawo takalminta a ga aiki da cikawa, Aunty da ace inda hurumin kashewa ko rayawa matar cen bayan na kashetama sai na koneta kurmus, domin ta tare min gaba ta tare min baya, na rasa abu da yawa sanadiyarta, ana min kallon Hajiar mai kwanoni ni ba kowa bace idan tana waje, a dai je sha'ani kawai, ama na yiwa kaina alkawari ko ba dade ko ba jima sai na ga bayan matar cen!"
Jikinsa da tarin nauyi ya fice a falon yana sake dane abinda yake ji a cen kasan zuciyarsa
A lokacin da ya zo shiga bangaren Hajiarsa, watau kakarsa ya ja yaa tsaya dole sakamakon gannin kanwarsa tsaye ta kafe shi da ido tana hawaye
Fuskarta ya sake kafewa da ido abubuwa da yawa na ratsa kwonyarsa, ciki harda wani abu mai kama da kamar ya ji haushinta, wanda ya tabata ba komai ne ya janyo masa jin haka ba sai wulakancin da mahaifiyarta ta gama bazawa yanzu a cikin falon cen
Da