Showing 27001 words to 30000 words out of 186303 words
ra'ayi na iya bambanta, sai dai ta so su bata dama ta yi hanni irin na addinin musulunci ta kuma yi tuni da abinda aka sani, dan a ganninta yau macen da ta san ciwon kanta take kuma neman lahirarta zata yi domin Allah da kuma gyaran kanta, bayan wannan yaushe zaka saka damuwa a kan wanda aka halartawa irin hakan? Yau koda su biyu zai aura rana daya tanada abin fada ne? Wannan din kamar wata hanya ce da ta dauko wace ba zata bileta ko'ina ba, domin in har ta saka damuwar nan a ranta tabas ba zata rayu yadda take so ba, hakan na iya zama wata tawaya koma dalilin da zai ringa hadasa mata fitina da mijinta, bayan cewa namiji a waje da kuke saurayi da budurwa ne kake da damar ya tsaya ka tsaya in ta yiwu fine in ta bace kowa ya kama gabansa, daga bakin da ka zama malakinsa matarsa zaman zai cenza salo ne daga ka isa da shi zuwa ya isa da kai, watau rayuwa yar shawara yar samun matsaya mai kyau tare da yi masa biyaya, kai inma abinda ya shafi mata ne bama duka maza suke baka fuskar ka kawo masu maganar ba, tsaf za'a nuna maka ba huruminka bane kuma ka hakura kuwa ka zauna, domin wannan din ba cikakiyar hujar da zaka zo gidanku bane a kasarmu ta hausa
Mikewa ta yi bayan ta yi fatan Allah ya sanyaya ta yi gaba kamar yadda Mamanta ta umarta
Mahaifiyarsu kuwa ta dan girgiza kai cike da takaicin Y'ar tata ta fari, ita har mamaki take idan Fauziya na wani abin, kamar ba nononta ta sha ba , salo salo irin na ubanta, to ta je cen ta yi kanta ake ji ita dake zumunci kamar a hada kai da kishiya ita ta gano, na zata sakawa autarta sakaran ra'ayi tana zaune kalau ba
A gidan su KAUSAR kuwa a lokacin da ta koma ta samu mahaifiyarta rike da kudin nan a zaune ta balbaleta da fadan a kan me zata bari ya bata makudan kudi har haka? To kuwa za'a mayar dan ba zata ja mata rigima da babansu ba, da kyar Maman nata ta yarda cewa bata san ya ajiye ba da bata yarda ba, haka suka yi jigum jigum har abansu ya dawo ya tarar da abinda ya faru, nan ya sake yin nasa fadan shima yace aaba za'a karba ba dan haka ta sanar masa idan ya dawo a bashi, baya cikin amsar kyautar mazan zamani ba'a san me gobe zata yi ba in Allah bai yi su din ne mazan ya'yan ba a zo ana rikicin kudin da bashi da su bashi da inda zai hako su, dama shi haka ya hori ya'yansa, bai cika son irin kaye kayen kyautar samarin nan ba, in ba an san da maganarka har ta yi karfi ba a fara amsar irin abu dan jefi jefi kyauta irin ta sallah da sauransu ba, to kuwa koda sun amsa ba da sanninsa ko na mamansu bane, Mahaifin nata ne ya ajiye da kansa da nufin in ya dawo a mayar masa da abinsa
Washe gari kusan karfe goma da zai fita ya fitar da kudi masu yawa har kusan dubu talatin a cikin ajiyarsa ya ba mahaifiyarsu cewa ta ba KAUSAR ta samu wani abin da ta ga ya dace ta yiwa TAUFEEK kyauta na tayashi murnar aurensa, duda kadan ne ta kamanta , sannan suma zasu yiwa iyayensa daga bangarensu
Sosai Mama ta yi farin cikin haka, kuma kwarai ta san hakan ya yi, domin ko rijiya tana son kari kuma ita kula dadi ne da ita , idan har suka kamanta ta tabata za'a ji dadin hakan domin iyayen na TAUFEEK masu karamci ne, sosai ta yiwa mijinta godiya da fatan alkhairi, ita ta san auren namiji mai zuciya ya fi wani mai kudin, domin mijinta Allah ya masa zuciyar nema da kuma sannin ya kamata, mutun mai matukar jajircewa a kan iyalansa, azumin nan aka yi aka gama bai taba fashin yawon kasuwa ba, kuma a kadan yana shigowa da ribar dubu takwas in kasuwa ta yi mugun dadi har sama da haka, in kuwa kasuwa ta cije wani sa'in har kasa da biyar, a haka yake cire yan bukatunsu na su yan fruits haka ko kifi haka sauran kuwa ya juye a asusun da ta tabata yanzu kam ya yi nauyi sosai, kuma a haka ya cire na hidimtawa yaron da yake hidimtawa y'arsa, lalle zata iya cewa ita kam ta dace duniya da kiyama tana fatan ฦดaฦดanta su samu mazaje masu fahimta da fita hakin iyali
Bayan ya tafi ta samu su KAUSAR din a daki ta bata kudaden da suka sakata ihun murna da farin ciki, zuciyarta cike da kauna da tausayin mahaifinta, a duniya tana fatan Allah ya bata aikin da zata talafi mahaifinsu da mahaifiyarsu da shi, iyayenta sunne iyaye talakawa masu zuciyar fita hakin ya'yan da bata taba gani ba a duniya, tana sonsu tana tausaya masu tana taya su kula da tarbiyarta kuma ta yi alkawarin in sha Allah ba zata kasance daya daga cikin ya'yan dake jazawa iyayensu azabar ubangiji ta hanyar yada badala a doron kasa ba....nan fa suka shiga tunane tunane da neman abinda ya dace ta ba TAUFEEK matsayin gift, su ce wannan su ce wancen, har dai kansu ya kule suka rasa mafita, sun tsaya a tsakanin biyu, agogo ko Turare....sai dai shima sun fadi ne dan jin dadi dan kuwa ita ta san a turarukan TAUFEEK da wahala in yanada na kasa da dubu talatin , hakama agogon hannayensa bama zata iya kidaya kudinsu ba dan ta tabata masu tsadar gaske ne, maganar suka ajiye kan zasu bincika wajen kawayensu yan gayu su ji sunnayen turaruka sai su zabo na daidai kudin
Wannan kennan
___________________________________
Kwana biyu tsakani KAUSAR da A'isha suka shirya suka je gidan aminiyar Aishan, dan ta nacewa yayarta cewa dan Allah ta zo su je dan matar ta iya mak'up tana so su dauki ranar da zata masu domin aure dai yau saura kwana takwas cif, anko dinsu kansu daya ne kawai basu amsa ba
Da kyar suka samu gidan, domin ta jima rabonta da ita, sunna dai haduwa a school lokaci zuwa lokaci dan ita Usainar yanzu ta fi ba harkar kwaliyarta karfi babar mai harkar mak'up ce a garin
Sun samu tarba ta mutunci, sun kuma taki Sa'a ranar hutunta ce bata kwaliya dan haka suka zauna suka shiga fira
KAUSAR kam da hankali du ya dauku a irin sansanyan kanshin da falon matar ke yi na turaran wuta ta gaza hakuri ta ce" Kai Usaina ama dakin nan naki na kanshi mai dadi walahi, haka nake son kanshi mai sanyi da ratsa zuciya"
Murmushi Usaina ta yi tana fadin" Lah aunty ki ce kanshin akoyshi har yanzu? Kin kuwa san tun jiya da dare da na turarawa dakin ban turara yau ba, sai da yama nake son turarawa, ai matar nan ta iya hada turare na kasa da kasa, haka na fesawar da kuma humurar akoy wace sai ta yi sati a jikin tufafi kanshin na nan radau, ai baban Abdul baya hanna kudi in dai turaran HAJIA FUSAM za'a siya"
Aisha dake murmushin itama tana amsar wanda ta mikowa KAUSAR ta sinsina sai lumshe ido take yi itama ta sinsina ta ce" Kai, ama kawa wannan da tsada ko? Na san wannan in zaka shiga sia ka shirya"
Usaina ta sake mikewa ta dauko mata turarukan ta ce" Ke kuw kawata, abu mai kyau ai shi ke siyar da kansa, tsada kuma ai karkon kennan, balema har ga Allah kayanta ba tsada, ga kyautatawa, kw harda gift take sako maka bayan na kudinka fa, kin ga wannan gift din ne , in takarkare maki kin ga dai baban abdul babban mutun ne ko? To walahi turaranta ne yake aiki da shi yanzu, cewa yake yi ko irin wunin office ya kama shi in ya je sake alwallah haka zai ji kanshin na tashi a ruwan, ke abokiyar zamana tun tana jin haushin hakan har ta hakura , nan fa yake amsar turaran wutar wai in zai kwana wajenta ya je da shi, ke dai har abu ya isheta ta nemi Hajia FUSAM itama ta shige, ni yanzu a gidan nan kin ga harta maina a wajenta nake siya da sabulu nawa da na yaranki, kin san kuwa ai kyau ya sa na nace"
Itama Aisha yanzun dariya ta yi dole dan yadfa Usaina ta yi, sai take ji a zuciyarta kai dolema ta samu mu'amala da matar ko dan ta dan gyagyara masu harka, ah to magana ta kanshi da gyara wa ya ki? Bale ance da sauki ai kawai zata gwada sa'arta, tana shirin tambaytar numbar natar KAUSAR dake ta faman sinsinar na ruwan dake hannunta ta ce" Usaina kuma a ina take? Ina so, ni kam tunda kin ce harda na maza ina son na mazan"
Usaina ta ce" Aunty yar Nijar ce ai, yanzu haka dai tana damagaran kuma ba inda bata aika sako, ga numbartama +227 97 82 44 94 , sunnanta kuwa shine HAJIA FUSAM"
Numbar suka kwafa sunna jin farin cikin hakan, dan kuwa irin yadda turaran ke gyare a daure da wata fulawa mai kyau ta tabata a kanti ba zasu samu irinsa ba, dan kuwa hadawa ne take yi da tsararun nagartatun turarukanta su bata kanshi mai ma'ana da sace zuciya...., Sai daga baya nema suka tsayar da lokacin kwaliyar, ita da kanta ta ce su zo karfe goma ta masu kafin dai a dawo daga daurin aure in sha Allah
Sun dan jima a gidanta kafin suke yi mata salama,
Har sun kusa fita ta biyo su da sako leda baka ta mikawa KAUSAR tana murmushi ta ce" Aunty ga wannan, kin ga yannayin fatarmu kusan daya ce mu ba baki ba mu ba haske bau ba, ki ringa shafawa fuskar kafin ranar kwaliyar, na tabata sai kin siya da kanki a wajen hajia FUSAM"
Godiya sukai mata sosai
Wannan shine mafarin shirye shiryen auren TAUFEEK
Tunda satin auren ya kama kuwa ya zamto babu mai lokacin kansa, duka bangaren biyu cikin shige da ficen shirye shirye suke, harta Kausar ba'a barta a baya ba domin bata zauna ba ta yi nan ta yi nan, ga wani abinda ya faranta mata rai
๐๐๐๐โคโ๐ฉนโคโ๐ฉน๐๐๐๐
*DA CIWO A ZUCIYATA*
๐๐๐๐โคโ๐ฉนโคโ๐ฉน๐๐๐๐
_MALLAKIN_
*SAJIDA NIJAR*
*FREE BOOK NE* 1๏ธโฃ1๏ธโฃ
LITATAFAN MARUBUCIYAR
Duk karyar kada
Yar mahaukaciya
Neman na kaina
Bani da zabi
Bak'a ce
Kutkale
Makauniya ce
Mage
Duk nisan jifa
Idan ka raina inda kake
Dutse
Alkalamin kadarata
Bani da zabi
Dakika Biyar
Now
*Da CIWO A ZUCIYATA*
*Tallah, tallah, tallah*
*SECRET DE LA FEMME DU MANGA*
_Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata, nesa tazo kusa,Amarya ,Uwar gida,Ango da mai gida Har ma da yan mata da samari shin kuna sane da cewa HAJIYA FUSAM ta shirya tsaf domin gwangwaje ku da turarakunta masu dankaran kamshi? Tare Kayan gyaram jiki na musamman ,wanda daga nesa kamshin ki kadai ya wadatar ya isar da sakon zuwanki waje,gidan ki kuwa sai ya zam abun kwatance wajen kamshi, kar na cika ku da surutu bara in fara zayyano su_
Farar Humura
Bakar Humura
Humura special,
humura de bain
Humura epicรฉ
Lait de nuit
Parfums dรฉsodorisant
Parfums rideau et dras
Lait de nuit
Alkam
Kulakcam
*Waษannan kadan ne daga bangaren turaran ruwa*
Gagab, sandal flex, Durot, durus, sandal fleur, tafarce, farce, sandal bangui, sandal, hypotonic sandal, al'ut, coktail creation VIP, Gajiji, Mankaji, turaran wutar labule da cafet, Aba malan, boulettes
*Munada bangaren gyaran jiki kamar haka:*
mai mai saka santsin jiki, mai mai kanshi, Kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi santsi da laushi, kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi fari, Sabulu mai saka fata ta yi haske, sabulu mai saka fata ta yi santsi, sabulu mai goge yanayin fata, mai wanda baya saka fari mai gyara fata
Sayen na gari mai da kudi gida,sai an gwada akan san na kwarai๐๐
Hajiya Fusam na zaune a kasar Niger domin yin magana da ita kai tsaye tuntuษi wannan number 97 82 44 94
*SECRET DE LA FEMME DU MANGA*
Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata๐๐๐๐๐
Ga wani abinda ya faranta mata rai shine sakon kyautar da zata yiwa Taufeek, gefe guda kuwa Elhaji ya zo kuma ta mayar masa da kudin ama abin mamaki sai ya je ya duka da kansa gaban Mama yace da ita kudin nan ba rokarsa ta yi ba, haka kuma yana iya ba wanima a titi bale wace yake neman aure, da kyar Mama ta amshi kudin, shima dan ya bata kunya sosai irin yadda ya duka din, duda ta san ta girme shi sosai domin dan yanada mata da ya'ya ba wani baba bane, kawai kudi ne suka kwonta ya tara mata abinsa, su kuwa suke gasar haihuwa kamar yadda aka saba
Ana gobe auren Mama da makociyarta suka je gidan suka kai gumbar da suka yi da nono da siga a cikin manya kwala shar shar shar da ledar goron HAJIA suka tare a bangaren Hajiar dan kuwa basu je direct wajen Mamansa ba, wajen Hajiar suka sauka makociyar Mama sai mamakin wai dama nan ne gidan su TAUFEEK take yi, domin irin yadda suke ganninsa bajaja a anguwarsu sun zata da kudin ama bai kai haka ba, saima da ta ga abin mamaki kyautar nan da suka zo da ita kamar sun kawo duniya guda, domin HAJIA haka take murna tana farin ciki ta saka yan aiki suka dauka ta ja su Maman suka nufi ciki wajen matan nan wani kallon yacewa makociyar Mama gyara kar ki kifa, ga abin gyare gyare na tarban baki da murnar babar rana, ga yannayin matan kowace da irin nata salo, sai katon falon ya bada kala babu wajen da ba abin kallon talaka ba
A haka suka karasa sama wajen Mama suka wuce Hamdiya da bakuwarta ta sha kunshi da kitso kai kace itace amaryar dan a yau dinma dinkin dake jikinta an watsa da zinari ba kannanun kudo bane dan a yagawa kishiyoyi da bakinsu sai yadda hannu take tana karbar baki ta ko'ina dan sun yi gaya sosai ko dan su caji aljihun Elhaji wanda murnar wannan rana ta saka ya bude bakin aljihu fiye da da mikawa yake yi du abinda aka bukata ba kauron hannu
Sosai Mama ta yi farin cikin gannin sakon nan, nan take ta saka aka ringa sakawa a frij tana fadin an taimaketa ba sai ta yi ba, ta kuwa manta da maganar dan faro faro mai sanyi na baki, haka take yiwa Mama godiya har sai da ta ji kunya ta lulubeta sannan ta rike su Mama aka shiga hada hada har dai dare ya yi kafin ta sake su tana faman maimaicin fadin" Maman KAUSAR dan Allah fa a zo da wuri goben, kuma ki cewa KAUSAR na ga ta zo yau, koda yake TAUFEEK yace dazu ya leka ya kai mata shadarsu ta diner kuma ya ajiyesu wajen kunshi, ni dai kii fada mata saura gobe ta yi zamanta sai ta ga an hantse na ganta a nan"
Mama kam dariya take yi aka saka direba ya dawo da su gida da tarin alkhairi irin na girke girken gidan bikin da ake tata yi ana zubawa baki
Bayan tafiyar su Mama, Maman TAUFEEK na cikin hidindimu kira ya sameta daga wajen mijinta
Tana shiga ta same shi tsaye a falonsa na farko yannayin fuskarsa a hade tamkar wani abin ya bata masa rai
Tun kafin ta zauna ya tareta da yannayi na bacin rai ya ce" Me nake ji haka a wajen yan uwanki ne Umin Boy?, Yaya zaki ki saka su a lamarin hidimar auren nan bayan sunna nan sunna kaf kaf da ransu sunna fatan birgeki? Me yasa komai sai dai ki tare ko dan ke kika haifi Elhaji karami ne?"
Da mamaki ta kafe shi da ido, sai kuma ta sauke dubanta a kan matansa, sun sha kwaliya tamkar zasu je gasar kyau, kowace sai walwali take yi haka kuma fuskarsu a sake ainun da suka yi ifo hudu
A hankali ta ja numfashi muryarta a raunane ta ce" Ka yi hakuri, ba za'a sake ba, in bandama abin iyayen Elhaji karami har sai an saka su abu nasu? Ni a sama nake ina fama da bakin da suka zo daga gida ai gidan baki daya a hannunsu yake, inace harta masu dafa abincin maza da aka dauko kannin hajia ne ko menene?"
Wani irin makuku ya zo ya tokare wuyan Hajiar, har ga Allah ta tsani in ana kwatance a ringa nuna kanninta dan tuwo tuwo ne dan a habaicin da suke mata har nunawa ake yi kamar dan daudu, wani takaici ya kamata su da suka zo dan su saka yau ranar da ta fi kowace rana mahinmanci a duniyarta mijinta ya fatataketa ta yadda har a daura auren ba zata fahimci komai ba dan bacin rai su ga ta tsiya sai gashi dan bakin munafurci irin nata ta wani bashi hakuri tana sinne kai bakar munafuka
Elhaji kuwa sai ya cire kai daga yannayinta ya ce" To a kiyaye, taron nan shine na farko a gidana kuma shine mafi daraja da zan gabatar dan auren yarona ne baba kuma namiji daya kwal, babu wace zan saurarawa idan ta dagan hankali ciki harda ke mahaifiyarsa, ku je ku bani waje dan baki ne da ni kuka kirayeni na zata wani abin ne mai mahimmanci, in sha Allah gobe daurin auren safe zamu yi ina son gama abinda ke gabana na zo na dan huta"
Wannan shine bata lokaci bukata bata biya ba, a haka suka bar wajen nasa baki dayansu kowace ta nufi inda ta fi wayo, Mama kuwa ta ki nuna fushinta ta ci gaba fa hidindimunta sama da kasa domin su dakunnansu suka wuce , hakan ya sa ta rungumi abinta hankali kwonce ta ci gaba da hada hadarta da fatan du wani abu da suke nufi da ita ya kare masu dan ba zata biyewa fitintinnunsu a irin wannan babar ranar ba
A lokacin da su Maman KAUSAR suka