Showing 108001 words to 111000 words out of 186303 words

Chapter 37 - DA CIWO A ZUCIYATA COMPLT BY SAJIDA.txt

09 Nov 2024

18792

karra tabatar mata da wahala idan akoy hankali a tare da kwakwaluwar Yumnar, sai ta yi watsi da duk wata girmamawar da take jin zata iya yi mata ta kuma daukarwa ranta abar gabarta ce kuma wace zata yi iya yinta dan gannin ta nuna mata ba haka ake rike namiji ba, koda sakaran namiji ne bale TAUFEEK MAI KWANONI, Kadara a cikin manyan kadarorin jinsin maza, bijimi kuma hamshaki a duniyar maza....
..


A hankali ta mike ta koma ta shige cikinsu ta kuma saki kunnayenta a firarsu, fira irin ta munafuntar junna da ha'intar junna a tsakaninsu, wace suke yi domin ta sun gaza gane ci gaba take samu a kowani kwana na duniya, sun gaza shafa mata lafiya su rayu hankali kwonce kamar yadda take rayuwarta , a gaban junna sunna nunawa junna kauna a bayan junna sunna ji kamar su kashe junna, a tsakaninsu ma sunna ha'intar junna, ta yi zaman nan ne kunnayenta na jiye mata ire irin zagin da suke sakarwa na habaici wa Mama, cewar dan kawai ana auren kawar danta ta baje harda su gaya kamar tana aurar da y'ar cikinta, sunna fadi cewa ana wasa da arzikin mijinsu ana takama ana gwaninta,
Haka ta yi ta zama , zaman da take gannin bata lokaci ne domin ba wannan firar take son ji ba, maganar taba lafiyar Ƴaƴansu , uba a garesu sannan mafarkinta take son ganewa shin Hajiar ta aikata aikin ko bata aikata ba? Idan ta aikata lalle lalle zata je ta sanarwa Elhaji baba sai dai ko wace wace!


Wasa farin girki in ji yan magana, karamin abu sai da ya girgiza Hajia domin komawar da ta so yi gidan su KHausar tana ji tana gani ta kasa , haka har dare ya yi tana bangaren TAUFEEK, a dole matarsa ta gane shi din ne ba lafia itama ta tare kusa da shi, ya zamto Mama abinci kawai take turo masu bayan hajiar ta yi kiranta tana fadan yau ita da mai kwanoni ne


A gidan su TAUFEEK ake wannan lamari, a gidan su KHausar kuwa karshe sai da Mama ta samu Khausar din ta yi mata wankin baban bargo kafin ta tsagaita kukan da take yi, Maman ta fice ta barta a dakinta tare da yan uwanta har kusan magariba sunna tausarta


Bayan sallar isha aka zo daukan Rukaya, cikin girmamawa da rarashi Rukayar ta sake sada kanta ta ce" Aunty, dan Allah ko menene ki fadawa Allah, Aunty kar ki manta a kulun adu'armu kennan, burinmu kennan, yau ba iya mu ba na tabata du wani masoyinmu yana cikin farin cikin wannan ranar, kuma Aunty yayanmu ne fa, kaf duniya babu wanda ya sanki ya iya zama da ke sama da shi, ba za'a yi wanda zai iya kular mana da ke kamarsa ba, aunty idan soyayyar ce ke kin san cewa........"


"Rukaya, a sanina shekara uku cif na baki a duniya, idan kika kuskura kika ci gaba da kawo min zancen rainin nan tsaf zan fafala maki mari na bata ran du wani mai ji da ke, kin ga tashi ki tafi kawai!" Khausar ta fada tana jan hijabinta ta share hawayenta


A'isha ta saki murmushi tana sakin labulen dakin na khausar ta yi gaba abinta, ita kam bama zata tunkari yayar tasu yau ba, shagali kuwa tana zuwa gida alwallah zata daura ta hau darduma duma wanda baya son gannin lamarin to Allah ya saka katangar karfe da su, ita kuma yayarsu tana rigimar TAUFEEK? TAUFEEK fa? Zasu gani lokaci dai!


Da wannan du aka watse aka bar Khausar da Mama a gidan, Mama kuwa ta yi banza da ita dan ko abinci da aka bata ta ki ci kyaleta ta yi tace in dai yinwa ce zata fitar da ita da kanta!


Kusan karfe goma sha daya Maman ta daga labule fuska a hade ta ce " ki zo in ji babanku!"


Khausar ta sauke numfashi tana jin yadda kanta ke sarra mata, uwa uba yinwar dake kwakularta ga kuma tashin hankali
A haka ta fito ta karasa dakin mahaifinsu ta yi salama ta rakube tana jira a bata izinin shiga , a ranta ta gama sani cewar mahaifinta in dai ya ga yau abincima bata ci ba to fa zai tsinke wannan lamari mai kama da almara wai ita da auren Besty


Gyaran murya Aba ya yi yana cire asuwakin dake bakinsa a tausashe yannayin fuskarsa bayane da kyakyawar fara'ar da sam ta kasa barin fuskarsa ya bata damar shiga falon nasa


Abinka da mai saida turare, dakin na Aba yau kamar turaren ya bude ya bade dakin nasa da shi, kanshi ta ko'ina haka kuma a tsaftace tsaf tsaf kamar yadda Mama ta saba sam ba zaka shiga dakin nan ka same shi da dati ba
A kasa ta zauna nesa da su kadan tana jan hijabinta ta rufe fuskarta sosai da shi bayan ta ga shadar da abanta ya maka yau, watau dinki ne sabo aba ya cancara na wannan rana shada ce fara kal a jikinsa , sai kawai ta ji wani irin kuka ya kubce mata wanda ta kasa rikewa a gaban wanda ta saba yiwa shagwaba wato mahaifi


Aba ya kalli mama yana dan zarro ido, ita kuma ta sake shaka , ji take yi inama in ta tashi ta dane y'ar nan ta daka babu abinda za'a yi? Sai dai ta jima da Sannin waye mahaifin ƴaƴanta a kan yaransa, bale Khausar da ta zamto wace ya fi tausayi ya fi ji a zuciyarsa


Da yannayin nunin tashin hankali Aba ya ce" subahanallah, Khausar kuka kuma?"


Ai kam ba ta ji ya tanka ba? A hankali ta ja jiki tana mundulawa ta karasa daf da shi ta bude kumatun nan da suka haye dan ɗorawa kai fitina tana kallonsa ta ce" Aba ba dole na yi kuka ba, dole na yi kuka Abana, shikenan wai sai na ji wai an ce wai da TAUFEEK ne aka yi, yo Aba TAUFEEK fa , TAUFEEK fa Abana abokina ne, mu sha yawon mu mu sayi awara ne, Aba har zance nice nan mai raka TAUFEEK, kuma sai ace wai shine mijina?"


"To Khausar din Aba me ya fi amininka ya zama mijinka dadi a duniyar nan ta Allah?" Aban ya fada a tausashe yana fuskantarta sosai, Mama kuwa ta dantse lebe , ji take yi inama inama ya bata dama ta dan gagaurawa Khausar mari jama'a? Wannan rashin Sannin ciwon kai har ina?


Khausar ta ja hanci ta ce" Ina , Aba ba dadi ko daya, ba dadi, to Aba an raina junna ai, TAUFEEK ya jima da rainani nima haka, auren nan kuwa ai sai baba da yaro ko?, Ana so namijin ya zama baba macen kuwa yarinya ba wai Ni da TAUFEEK ba Abana, Aba to yaya zan yi a wajen aiki? Shine babanmu fa, kuma shi wai dayan mema na masa ya fasa aurena?"


Abanta ya sauke numfashi, cike da hikima ya ce" Ni kam yar gidan aba wani lokacin sai in ga kamar Khausar dina bata fi shekara biyar ba, tsakani da Allah mutumen da a tsaye ya fi ki tsayi , a shekaru ya baki na kirki ne kike yiwa wannan zaurancen? Kuma kike cewa aiki wani aikin kuma ke da aka daura maki aure? "


A zabure Khausar ta dubi Abanta, bakinta har yana rawa ta ce" Abana aikin? Abana aikin da ya zamto burina kuma cikon farin cikinmu baki daya? Abana dan girman Allah kar a taba lamarin aikina domin Ni aikina ina yinsa ne ba dan badangarci ba, da farko na zabi fanin lafiya ne dan na taimaki bayin Allan, sai kuma ina fa bukatar aiki dan na tallafawa iyayena, Abana banda aikina banda aikina"


"To wai Khausar kafin ki fara aikin Bama ci ne ko Bama sha ne ko Bama daura sutura ne?, Ki fa kiyayeni da abu kamar wace bata godewa Allah ba, yaya zakina abu kamar na jahila? Auren ai ya fi aikin daraja in kuma mijin ya ki ba zaki yi ba, ke baki ga farin cikin fuskar mahaifinki na raguwa ba ? Dan kin sani sarai komai kankantar shirmenki daga masa hankali yake, inama ya bani dama in nuna maki yadda ake godewa Ubangiji? Shashancin banza malan, ke yau mu kam ranar farin ciki ce a wajen mu in bata maki ba je ki rufe dakin ki dora daga inda kika tsaya, ana wani taroki dubeki kina jibgewa dan kin ga abanki ko? Shi TAUFEEK din bai ce baya yi ba sai ke ? Ki c............"


Aba da ya zubawa bakin Mama ido yana kifta idon yana kallonta ya yi kyaftun da ya sakata dubansa a wayance haka kuma ta ja bakinta ta yi shiru ta mike tana tatara abinda batama san me zata yi da su ba ta yi waje, sosai take sama dalilin Khausar idan har ta samu dama kuma tasss zata mamaketa walahi!


Aba ya jinjina kai bayan ya ga ficewar Maman, sai kuma ya saki murmushi gannin Khausar ta yi tsamo tsamo ta sake rakubewa kusa da shi , watau farar kura ga tsoro ga ban tsoro ko? Shine aka raina ake yiwa daru


A tausashensa ya ce"


💔💔💔💔❤‍🩹❤‍🩹💔💔💔💔




*DA CIWO A ZUCIYATA*




💔💔💔💔❤‍🩹❤‍🩹💔💔💔💔


_MALLAKIN_


*SAJIDA NIJAR*


*FREE BOOK NE* 4️⃣2️⃣


*GARABASA, GARABASA, PROMOTION, PROMOTION DIN LITATAFAN MARUBUCIYAR A KAN FARASHI MAI SAUKI 1K, YAN NIJAR KUWA 1000 FRANCS CEFA*


1: Duk karyar kada


2: Yar mahaukaciya


3: Neman na kaina


4: Bani da zabi


5: Bak'a ce


6: Kutkale


7: Makauniya ce


8: Mage


9: Duk nisan jifa


10: Idan ka raina inda kake


11: Dutse


12: Alkalamin kadarata


13: Bani da zabi


14: Dakika Biyar


15:Wata kokowar


16: Aure yakin mata


17: Ni zan ladabi


18: Daga tafia daukar soja


*Dukansu a kan farashi mai sauki, zaka saka dubu guda ne domin promotion ne nake yi, ka tuntubeni kan layina kamar haka +227 93 81 16 18, Sajida Nijar*


Now


*Da CIWO A ZUCIYATA*






*Tallah, tallah, tallah*


*SECRET DE LA FEMME DU MANGA*


_Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata, nesa tazo kusa,Amarya ,Uwar gida,Ango da mai gida Har ma da yan mata da samari shin kuna sane da cewa HAJIYA FUSAM ta shirya tsaf domin gwangwaje ku da turarakunta masu dankaran kamshi? Tare Kayan gyaram jiki na musamman ,wanda daga nesa kamshin ki kadai ya wadatar ya isar da sakon zuwanki waje,gidan ki kuwa sai ya zam abun kwatance wajen kamshi, kar na cika ku da surutu bara in fara zayyano su_


Farar Humura
Bakar Humura
Humura special,
humura de bain
Humura epicé
Lait de nuit
Parfums désodorisant
Parfums rideau et dras
Lait de nuit
Alkam
Kulakcam
*Waɗannan kadan ne daga bangaren turaran ruwa*
Gagab, sandal flex, Durot, durus, sandal fleur, tafarce, farce, sandal bangui, sandal, hypotonic sandal, al'ut, coktail creation VIP, Gajiji, Mankaji, turaran wutar labule da cafet, Aba malan, boulettes


*Munada bangaren gyaran jiki kamar haka:*
mai mai saka santsin jiki, mai mai kanshi, Kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi santsi da laushi, kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi fari, Sabulu mai saka fata ta yi haske, sabulu mai saka fata ta yi santsi, sabulu mai goge yanayin fata, mai wanda baya saka fari mai gyara fata


Sayen na gari mai da kudi gida,sai an gwada akan san na kwarai💃💃
Hajiya Fusam na zaune a kasar Niger domin yin magana da ita kai tsaye tuntuɓi wannan number 97 82 44 94
*SECRET DE LA FEMME DU MANGA*
Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata💃💃💃💃💃








A tausashensa ya fuskanci Khausar, a nutse ya ce" Kin ga, yar gidan Abanta, yarinyana mai albarka, yar arziki gajera yayar A'isha share hawayen mu yi magana kin ji? Share hawayenki mu yi magana"


Khausar ta ringa sauke ajiyar zuciya tana kallon mahaifinta, a hankali ta ringa share hawayenta har ta share tasss tana kallonsa tana kuma sauraronsa


Aba ya ce" A sanina Khausar dina tana da ilimin addini daidai gwargwado ko?"


Khausar ta gyada kai tana kallon mahaifinta


Aba ya ce" To menene abin rikicewar nan har haka?, Menene Khausar? Fada min menene na tashin hankalin har haka?"


Ido kawai Khausar ke tsurawa waje guda, a cikin zuciyarta tarin amsoshin tambayar Aba, sai dai karfin da sukai mata a harshenta ba zata taba iya kwatantawa Aba haka din shine dalilinta,
A sanyaye ta sada kanta ta ce" Abana, gani na yi tsakaninmu bamu taba magana makamanciyar haka ba, kuma fa Abana TAUFEEK ne fa, shi dinma Hajia tace bai san da zancen aure ba na dole aka masa, kuma Aba me duniya zata kalleni? Dama a anguwa ana min wannan zaton ana zagina da haka, kuma ban san shi ne na masa ya fasa aurena ba sai kawai ace da TAUFEEK?"


Aba ya gyada kansa ya ce" to Ni a bayanin nan ban ga wanda ya zama rikaken hujar da zan yi duba da ita har in fuskanci kin yiwuwar auren nan ba yar gidan Aba, inace na hore ku da jin tsoron Allah kadai da kuma kiyaye hakokin musulunci, yaushe kika fara damuwa da zagin yan anguwa? Ai da kin jima a kasan kasa Khausar dan kuwa ai an jima ana zagin namu ko?, Ko dan karatun nan naki ai babu abinda bamu gani ba, Ni na fi so in akoy wani dalilinki ki sanar min sai mu duba ko yar gidan Aba? Kuma shi aure ai zuwa ake yi da zuciya daya a zauna , idan har zaman bai yiwu bane ake yin hakuri ko? Sannan maganar aikinki Elhaji ne da kansa ya ce min a jibin nan zaki koma bakin aikin ki, a gobe za'a kawo lefenki da kuma direbanki dan yace a yi hakuri da maganar shiga adaidaitar , tarewa kuma da an ce a yi da gagawa sai yace a bari har su Elhaji karamin su dawo daga haji sai ki tare, kin ga ai muna tare ko yar gidan Aba?"


Khausar ta ringa kallon mahaifinta, tana gannin wani annuri a tare da shi wanda du yadda yake son boyewa ya ki boyuwa, haka kuma bayanansa sun mata wani irin girma da neman shiga kwakwaluwarta, Bama irin maganar aure zaunawa ake yi idan ta yiwu ake yinsa, hakan na nufin idan ta dawo tace masa auren nan fa ba zata yiwu ba zai raba? Kai in kuwa haka ne tana iya yin shiru har su hadu da TAUFEEK su yi shawara, ta tabata shima zai ce ne eh wannan aure son iyayensu ne ba nasu ba,


Aba ya sake fuskantarta ya ce" Haka kuma, a kulun ina horarki ko me ya tunkaroki komin rikicewarsa da rikita zuciyarsa ki fadawa Allah, ki kai kukanki wajen ubangiji, ki bashi zabi kin ji yar gidan Aba, Ni kam sai in ce alkhairin ne fa, ki duba ki ga kulun adu'armu kennan fa, nan har cewa kika yi in kai ki masalaci in ba kowane nema ke dai a maki auren kema ko? Kuma yanzu Allah ya kawo sai ki ringa rigima? So kike yi hankalina ya tashi ne ?"


A hankali Khausar ta girgiza kanta tana jin wani irin tausayin mahaifin nata na ratsa mata zuciya
A sanyaye ta ce" Abana ka yi hakuri ka ji? In sha Allah zanma gani ne tunda kace auren ai in zai yiwu ake yi ko Aba?"


Mahaifinta ya amsata, yana sake gannin tamkar wata yar jaririyarsa ne Khausar din, sam baya gannin girmanta, idan ta yi wani abin kuwa gaba daya yake gannin rashin wayonta ƙarara, cikin hikima ya idasa kashe borin rigimar, bale da ta ji cewar zata je aikinta a jibi jibinnan sai ta ringa jin kamarma auren an riga an rabashi ne,


Da wannan ta fito daga dakin mahaifinta, sai tunane tunane take yi, to ita jama'a yanzun idan ta ga TAUFEEK ta ce masa me yace mata me? Tashin hankali wanda ba'a saka masa rana


Ido hudu suka yi da Mama, Maman ta sakar mata harara da sauri ta sada kanta ta shige dakinta tana jan hanci ta cire zumbulelen hijab din da ta wuni da shi dan dole, ita daya sai tura baki take yi ta nemi waje ta zauna saman katifarta da yar karamar rigar dake jikinta ta barci ta shiga murza manyan cinyoyinta tana sauke ajiyar zuciya tana kallon wayarta zuciyarta cike da tunani kala kala, ita daya sai ta ja tsaki, ta yi kyaftu ta yi wannan ta yi wannan , tunani ya yi mata yawa


Mama kuwa dake tsakar gida bata koma daki wajen Aba ba, tana zaune ne da autanta suka gama waya da Rukaya wace ke shaida mata cewar gobe da safe mai kitso da kunshi zasu zo a yiwa auntyn tasu dan Allah maman ta tirsasata ta zauna a yi mata tunda an ce jibi zata koma aiki sunna so ta koma a matsayin amaryar , Allah ya taimake su yanzun auntyn tasu ita da kanta tana dan gyara fuskarta in zata fita, dama fannin turare ba'a maganarsa da tsafta domin Khausar akoy tsafta




Washe gari


Kusan karfe bakwai na safe Hajia Fatahiya ta yi salama a bangaren TAUFEEK sannan ta dakata kamar yadda Mama, fa Hajia nawarah da shi kan Mai kwanonin ke tsaye sunna jira a basu damar shiga, sakamakon zuwan Hajia ta wanke su tassss ta dawo bangaren domin a nan ta kwana ita da Yumnah a falon tana yi tana leka shi har asubahi ta yi itace ta koma ta aniya taimaka masa har ya mike bayan yana iyawa tace zata raka shi har bayin sai da ya kiya ne ta samu ta fice ta je bangaren Aban ta masa tasss sannan ta bi daki daki ta masu tasss ta koma harda hawayenta wai magidanci ba lafiya bata ga kafar kowa ba


Yumnah ta ja numfashi, ranta cike da jin haushin Hajiar nan, ta sakata ta soya wainar kwai ta zauna tana bashi a cokali kamar ita ta haifeshi, shi kuwa sai wani lumshe ido yake yi jikinsa har yanzu da zafi ama ya ki zuwa asibitin kuma ya ki korar wannan masifafiyar tsohuwar ta saka mata falo banda kaurin jiji babu abinda yake yi wai ita bata iya zama sai da turaran wuta, du tarin turaran wutarsu ta je ta kwaso jijinta ta ringa maka masu a falo kamar gidanta


Mikewa ta yi ta je ta bude dan yadda

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login