Showing 66001 words to 69000 words out of 186303 words
nan yan mata
Gaba daya sai Khausar ta rasa abun cewa, ta rasa me zata ce, ta rasa ta inda zata yiwa Mama godiya, ta gaza zaune ta gaza tsaye har sai da Maman ta nuna mata bafa ta son haka ta yi addu'a kawai ta yi shiru ita yarta ce dan ta mata alkhairi ba wani abu bane
Da zumudin wannan ta koma bangaren Hajia, nan fa Hajia ta saku daga yannayin da take ta ringa shiwa Mama albarka kamar irin an yiwa bakuwarta alkhairin nan, sosai ta ringa sakawa Mama albarka bama da ta ji cewa zasu je wajen dinki da sauransu a goben, da wannan farin cikin suka kwonta barci
Washe gari kusan karfe tara na safe tana tsakar gida ta dora tukunya saman murhu tana tukawa Hajia tuwo na masara da tace tana sha'awa ta ajiye karamar kujera ta yi zama irin na tuka tuwon domin ko hijab bata da shi , haka kuma ta nanade zanin jikinta ya dan yi sama kadan ta yi zaman nan na gantsarewa kadan tana dirkar tukin tuwon mai aikin Hajia na gefe tana mamakin Khausar din domin bata san cewa ta iya tuka tuwo haka ba
Salamar Hajiar wace ta fita tun da sasafe ita da Magidanci ne ya saka Khausar dan dagowa tana amsawa hadi da fadin" Hajia har kun dawo?......"
Sai kuma ta yi shiru sanadiyar gannin TAUFEEK ya shigo da waya a kunnensa shi sarkin amsa waya sai ky a hannunsa yana dan yiwa hajia Alamun ta tsaya dan juyawa zai yi kasuwa
Ido hudun da suka yi da ita da shi ya saka shi binta da kallo sakamakon hayakin da yake ganni na tashi a gabanta, nan idannuwansa suka yi arba da irin zaman da yarinyar nan ta yi rabi da rabin cinyoyinta du sun sauka daga marainiyar kujerar nan ta nade hannun riga ta wani yada zama kamar an mata gorin haka tana tuka tuwon da bai san wa ya sakata aikinsa ba
Cire kansa ya yi ya maida kan Hajia zai yi magana, sai ya ga Hajia tana wani rinrintse ido tana wani tabo baki tamkar ba daga wajen rasuwa ta fito yanzun ba tana rus kuka har ana bata hakuri kamar jikanta ne ya rasu wato shi
Ido ya kifta a sanyaye yana kallon yannayin Hajiar, dan a gaskiya in dai Hajia wani abin ta saka a ranta yau zai fito mata a mutun ya mata nasiha
Kasa kasa hajiar ta matso har tana dan dage ta ce"
ππππβ€βπ©Ήβ€βπ©Ήππππ
*DA CIWO A ZUCIYATA*
ππππβ€βπ©Ήβ€βπ©Ήππππ
_MALLAKIN_
*SAJIDA NIJAR*
*FREE BOOK NE* 2οΈβ£4οΈβ£
LITATAFAN MARUBUCIYAR
Duk karyar kada
Yar mahaukaciya
Neman na kaina
Bani da zabi
Bak'a ce
Kutkale
Makauniya ce
Mage
Duk nisan jifa
Idan ka raina inda kake
Dutse
Alkalamin kadarata
Bani da zabi
Dakika Biyar
Now
*Da CIWO A ZUCIYATA*
*Tallah, tallah, tallah*
*SECRET DE LA FEMME DU MANGA*
_Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata, nesa tazo kusa,Amarya ,Uwar gida,Ango da mai gida Har ma da yan mata da samari shin kuna sane da cewa HAJIYA FUSAM ta shirya tsaf domin gwangwaje ku da turarakunta masu dankaran kamshi? Tare Kayan gyaram jiki na musamman ,wanda daga nesa kamshin ki kadai ya wadatar ya isar da sakon zuwanki waje,gidan ki kuwa sai ya zam abun kwatance wajen kamshi, kar na cika ku da surutu bara in fara zayyano su_
Farar Humura
Bakar Humura
Humura special,
humura de bain
Humura epicΓ©
Lait de nuit
Parfums dΓ©sodorisant
Parfums rideau et dras
Lait de nuit
Alkam
Kulakcam
*WaΙannan kadan ne daga bangaren turaran ruwa*
Gagab, sandal flex, Durot, durus, sandal fleur, tafarce, farce, sandal bangui, sandal, hypotonic sandal, al'ut, coktail creation VIP, Gajiji, Mankaji, turaran wutar labule da cafet, Aba malan, boulettes
*Munada bangaren gyaran jiki kamar haka:*
mai mai saka santsin jiki, mai mai kanshi, Kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi santsi da laushi, kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi fari, Sabulu mai saka fata ta yi haske, sabulu mai saka fata ta yi santsi, sabulu mai goge yanayin fata, mai wanda baya saka fari mai gyara fata
Sayen na gari mai da kudi gida,sai an gwada akan san na kwaraiππ
Hajiya Fusam na zaune a kasar Niger domin yin magana da ita kai tsaye tuntuΙi wannan number 97 82 44 94
*SECRET DE LA FEMME DU MANGA*
Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mataπππππ
Kasa kasa Hajiar ta matso har tana dan dage ta ce" Ka ga mata, wannan sunne mata, irin matan da na so ace ka wanko ka kawo min, wa'inda na san du gajiyar da ka kwaso to fa kana da wajen saukewa, magidanci irin matan nan ina iya rantse maka idan suka rike namiji an gama, ama sai ka je ka dauko mace gatacen sai shegen shafa pankeke, yo in yar nan ta yarda ta koyi shafa pankeke ai an kade, ina mana bakin cikin rasata Allah ma kuwa!"
Gata dai fuska du ta fara nuna alamun daf take da zagwonyewa dan tsufa, ama bakinta ko amon muryarta bai cenza ba, shi a yau in ba dan mai kwanoni ba da matar nan sai ya saka an zo an ririketa an sauke mata aljannun kanta, ama ba komai zai kyaleta ne har su tafi haji shi ya san yaya zai yi da ita
Banza ya mata ya juya zai bar gidan, Hajia ta daga murya ta ce" Au na bata maka rai Hala dan nace wancen abar kamar muciya? Na fada in ranka ya kiya ka kawo mace mai dima dima mana ka gani in an zageka dilla malan"
A hankali Khausar dake rage wutar nan ta dan dago ta kalli Hajia, an yi katari itama ta kallota sai ta karaso tana sakin murmushi ta ce" Yar nan tuki ake? Sannu ke kuwa tashi ki yi wanka ku tafi mana tace karfe goma zaku tafi fa, tashi maza dan watsa ki dan sha na sha kin ga na karbo maki wani na farin jinnin yanzunnan wajen malan, je ki yi wanka kafin ki fito na saka maki a nono sai ki sha "
Khausar ta amsa hajia da to, domin bata da amsar da ta wuce wannan ta mike ta je dan shiryawar ta barawa mai aikin Hajiar sauran aikin,
Tana gama shiryawa ta dauki wayarta da nufin kiran TAUFEEK, dan ta ji yaya maganar wajen aiki ne yau? Kamar yadda Mama tace shin yana da hanyar da zai sanar masu ba tare da an mata fadan rashin zuwan ba, sai kuma ta dakata da wayar a hannunta tana tuna abinda ya faru jiya, ko yau ba wani gaisuwar da suka saba suka yi ba dan sai take jin wani iri a cen kasan zuciyarta da tarin tunanin me hakan ke nufi, sun dai gaisa da murmushi ama bata wani tsaya ta ji daga gareshi ko ta masa tambayar iyali ba
Salama ta yiwa Hajia ta wuce bangaren su Maman bayan hajiar ta shaida mata ta bar kayan za'a mika mota
Yau dinma sai da aka bata damar shiga kafin ta shiga baban falon
Mutanen dake falon ta fara bi da kallo kafin ta gaishe su, sai dai a cikinsu yar budurwa matashiya daya ta amsata itama a dan fizge ta dauke kanta
Ido ta zubawa Yumnah gannin sai da ta dubeta ta watsar
Tana shirin hawa saman sai ga Maman na saukowa da yar karamar jakkar hannu
Yumnah ce ta fara mikewa tana dan sosa gaban goshinta alamu na dan jin kunyar surukar nan ta shiga gaisar da Mama
Da dan sauri Maman ta amsa ta karasa saukowa ta dan dube su baki daya ta ce " Barkarku da hutawa, zamu dan fita ne da Khausar sai mun dawo"
Hajia Nuwairah ta yi kamar bata jita ba sai yarinyar wajenta da take riko wato hamdiya ce ta karasa da dan sauri tana sake gaisar da Maman
Jakar hannunta da Hamdiya ta so karba Maman ta dan rike da kula sosai tana mata murmushi ta ce" Na gode yata yi zamanki ai ba wani nauyi Allah ya maki albarka"
Hamdiya ta amsa tana dan sinne kai irin girmamawar nan tana kuma.jin dadin adu'ar Maman a ranta, a cen kasan zuciyarta kuwa ba abunda ke faranta mata a yanzu irin ta faranta ran yayansu ta hanyar yin abinda Yayansu ke so
Mama kuwa daga haka ta fice tare da KHAUSAR suka yi tafiyarsu
Cike da isa irin tata Hajia Nuwairah ta dan sake kallon yannayin Yumnah, sai kuma ta saki dan murmushi tana dauke dubanta cikin basarwa ta ce" Ya haka Yumnah na zata tare ne zaku fita da srakuwar taki?"
Yumnah ta juyo da dan sauri, dan kamarma wace ta afka tunani ta kalli Hajia Nuwairah, sai ta ga hankalinta ba a kanta yake gana daya ba, tana dan yi nata firar ne kuma tana maida hankali kan Hamdiya
Dan numfashi ta fitar, sai kuma ta juya tana fadin" Bara na koma Hajia dama gaishe da ku na leko"
Daga haka ta yi gaba
Tan fita Hajia Nuwairah ta mike ta kama kunnen Hamdiya ta ja da karfi ta yi wajen kicin dinta da ita danma kar a fito a sameta da ita a haka
Rai bace tana rike da kunnenta ta ce" Ke na tambayeki, Hajia fatima kanwar uwarki ce?"
Da sauri Hamdiya ke girgiza kai tana ji kamar Hajiar zata tsinke mata kunne ne
Murya a kausashe ta ce" To ki kula, bana son rainin hankali da shishigin tsiya, ba abinda ya hadaki da ita, ko gaisuwar kirki na ga kin kuma yi mata sai na wulakantaki sannan na maida ke gidan ubanki, dan ba zai yiwu ba na dauko ki na kawo ki kashe ni kina shiga gindin kishiyata da ba kaunata take yi ba, ke shaida ce a gidan nan dan ta haifi namiji daya kwal ba irin abinda ba'a mana a kanta da danta, to ba zai yiwu ku da kuke nawa ta kwace min ba kin fahimta?"
Kai take gyadawa har idannuwanta sun cika da kwala kafin ta saketa ta fita da sauri ta haura sama ita kuwa Hajiar ta ja tsaki tana sake hade fuska domin abin ya bata haushi ainun, sai dai wata hanyar da ta hango ta baraka ta sanyaya mata zuciya, domin ta tabata in dai har abinda ta gani a idannuwan Yumnah kishin wancen yarinyar ne to fa zata bi ta nan ta sa rashin jituwa tsakanin Hajiar da Yumnah, tana ji tana gani sarakuwar Ιan nata sai dai ta hangota ba dai su yi wata taraya ta zumunci ko fahimtar junna ba!
Sosai Khausar ta ji dadin fitar nan, sun je an aunata, daga nan suka je Hajia ta daukar mata takalma masu kyan gaske harda kafa ciki mai dan karamin hls a jikinsa fari kal mai kyan gaske, harfa kayan kwaliya, daga nan suka wuce wajen HAJUA FUSAM, nan fa ta sha kallo ta nemi rikicewa har ta ji wani irin sha'awar son ta ringa gyara jikinta irin na matar da kayan aikin matar, lalle mata sunna gyara, tun daga su dilka, kurkum, kujera, rigar dilka, itacen dilka, turare kai komai da komai dai a wajen matar nan akoy masu kyau da inganci , turatukan da Mama ta daukar mata sai da ta ji kamar ta bude ta yi ta sinsina a hancinta, turaruka masu kanshi , sanyin kanshi da saka nutsuwa a zuciya, daga nan suka wuce gidan aminiyar Maman , nanma sakonta ta amsa sannan suka wuce gidan su KHausar din dan Maman ta yiwa Maman su KHausar din barka da abin arziki, nan ta shaida mata an saka ranar ance nan da wata daya sannan ta ringa godiya dan Khausar ta kasa r8ke murnarta ta sanarwa Maman komai da komai , har maman ta rasa abin fada , sun jima sunna zantawa kafin su tafi gida
Da wannan Khausar ta karra kusan sati a gidan su TAUFEEK, a kulun zata je wajen aikinta ta dawo ne, kuma a kulun din shine zai ajiyeta ya je ya daukota, ko fushi fushin da ta so masa na yannayin matarsa sharewa ta yi ta daukarwa kanta alkawarin zata gane me hakan ke nufi dan ta dauki mataki, Yumnah dai ba sa'arta bace ba sa'ar yinta bace, ko tana da wata matsala da itane bata sani ba zata bi a hankali idan ta gane sai ta magance in mai magantuwa ce, in kuwa ba mai magantuwa bace sai ta kama kanta, dan ba zata taba yarda wani abu na rashin da'a ya shiga tsakaninta da ita ba, bata ga dalili ba
Ranar da zata koma gida sai da ta ji ba dadi a ranta, Hajia fadi take ta yi zamanta mana, itama ta yi sabo da ita harda na mamaki, dan Khausar akoy dadin zama ga girmama manya ga rashin kiywa, da kyar dai ta iya tafia bayan an cika boot da tsarabe tsarabe da dinkunnanta da kayayakinta tamkar wace ta je wata kasar ta shekare, Mama kuwa ta sakata daki ta mata nasiha mai kama da fada fada, ta yi mata nuni kan yafa dace ta dan gyara, sosai ta hadata da mutanen arzikin da zasu sake gogar da ita a hanya mai kyau ba lalataciya ba, irin tarayar nan da koda baka son gyarawa idan ka yi tsai ka ga yadda mutane ke gyarawar kaima sai ka tsinci kanka a ciki tsamo tsamo
A lokacin da ya ajiyeta gida murna wajen yan uwanta ba'a magana
Haka su mama ke saka albarka a tarin arzikin da ta dawo da shi, yan anguwa kuwa sunna leke da zunde da bakinsu da mamakin inda ta je har ta jima haka,
Ko da Baba ya dawo shima farin ciki kamar me, kasa boyewa ya yi, nan ta nuna zata raraba kayan da yan uwanta Baba kuwa ya nuna aa ko daya summa ai ga sababin kaya nan na aure ta ajiye abinta itama ta ringa sakawa
Haka baba ke daga yan jakunkunnan da takalma yana fadin" Ai zaki saka ko khausar din Aba?" Ita kuma tana dariya da fadin" Baba bara ka gani zan saka duka kaffff, kuma harda kwali"
Ita dai Mama dariya take yi a ranta tana ayana' Allah ya sa Khausar din ta saka"
Kwonci tashi har lokacin auren yan uwanta ya karaso, aka sha biki har biki dan kuwa an yi taro yan uwa da aminan arziki haka yan anguwa sun yi karra sosai an samu tarin gudunmuwa harda na mamaki, dama Aba bai yi sanya ba ya masu abinda ya dace daidai karfinsa haka kuma an ci an sha da anki din atampa daya da suka fitar har dare ya yi aka raka kowace dakinta, ya zamto a gidan a yanzu Khausar ta sake tsintar kanta daga ita sai ita domin Auta namiji ne kuma bama dakinsu daya ba, shi dakin Aba yake kwana
Wannan sabon kadaici ya so ya dameta sosai, dan kuwa har sai da Mama ta yi da gaske sannan ta dan saku, ba dan ta warware ta cire komai a rai ba, sai dan irga yan kwanakin da take tunanin itana tana iya wayar gari da sunnan amarya dan kuwa a irgenta kwana duka duka hudu ya rage alkawarin Mujaheed da ya mata cewar za'a kawo sadakinta
Sai dai shiru, Aba bai yi mata zancen an tuntubeshi kan maganar ba, ko aiki da take zuwa kuzarinta ragage ne, duda an kusa yayeta dan a yanzu ta haura wata biyu cikin na ukunta take, aiki ta koye shi daidai gwargwado, ama kuzari ya ragu a jikinta saboda tunani da neman mafita a cen kasan zuciyarta
Ba sai an fada mata ba, damuwar iyayenta a duniya a yanzun itace
Ba sai sun tsangwameta ko sun hannata zaman lafiya ba, ta kalli fuskarsu su kalli tata du safiya ta Allah a matsayinta da shekarunta sun isa su dami kwakwaluwarta da kwonciyar hankalinta
Wannan dalilin ya sa koda yaushe wayarta a hannunta take, kunnenta kuwa na sauraro dan son jin sauti daga gare shi, sai dai kwana biyu na ragewa watan ya cika sai ta neme shi dif ta rasa, domin kiran da yake mata na sasafe da darenma idan ba zai zo ba sai ta nema ta rasa
Sannu a hankali kwanakin da take irgawa suka shige, nan fa abin ya fara bayana a jikinta domin nan da nan ta fara neman fita a hayacinta, bata fahimtar komai har sai da aka bata kwana biyu a wajen aiki a tunaninsu bata da lafiya ne
Wannan damuwa tata ta saka Mama a damuwa har ta tirketa ta ji dalilin rashin cin abincinta da yawan tunaninta
Jin abinda yake faruwa ya saka Mama ranta ya baci, a gaskiya abin nan ya fara kona mata rai, ita da kanta a irgenta sau uku kennan Mujaheed yana fadin yau gobe, dan haka ta samu Aba da maganar ta sanar masa
Su dukansu basu zaci cewa Fada Aba zai rufesu da shi ba sai da ta fada din, ta inda yake shiga ba ta nan yake fita ba, cewarsa in har ya yi niya ya shirya to ya fito din in kuwa bai fito ba ba lalle ba dole shi baya neman rabuwa karfi da yaji da yarsa, kuma ya amshi kadararsa ko wace iri ce!, Bacin ran wannan ya saka shi ficewa ya bar masu gidan tunda duku duku ya ki dawowa
Sun wuni cikin tashin hankalin nan wani ya sake samunsu, domin kusan karfe hudu na yama aka yi salama cewar ta yi bako ana mata magana a kofar gida.............
ππππβ€βπ©Ήβ€βπ©Ήππππ
*DA CIWO A ZUCIYATA*
ππππβ€βπ©Ήβ€βπ©Ήππππ
_MALLAKIN_
*SAJIDA NIJAR*
*FREE BOOK NE* 2οΈβ£5οΈβ£
LITATAFAN MARUBUCIYAR
Duk karyar kada
Yar mahaukaciya
Neman na kaina
Bani da zabi
Bak'a ce
Kutkale
Makauniya ce
Mage
Duk nisan jifa
Idan ka raina inda kake
Dutse
Alkalamin kadarata
Bani da zabi
Dakika Biyar
Now
*Da CIWO A ZUCIYATA*
*Tallah, tallah, tallah*
*SECRET DE LA FEMME DU MANGA*
_Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata, nesa tazo kusa,Amarya ,Uwar gida,Ango da mai gida Har ma da yan mata da samari shin kuna sane da cewa HAJIYA FUSAM ta shirya tsaf domin gwangwaje ku da turarakunta masu dankaran kamshi? Tare Kayan gyaram jiki na musamman ,wanda daga nesa kamshin ki kadai ya wadatar ya isar da sakon zuwanki waje,gidan ki