Showing 60001 words to 63000 words out of 186303 words
yan matan gidan ta amso da kwali da jan baki wai aro kafin a jima ta je kasuwa ta siyowa Khausara pankeke
A tsaye yake a kofar dakin, cikin shiga ta kayan aiki , ama babu abinda zai iya ce maka ga aikin
Kanshi yake fitarwa ta ko'ina, hannunsa dauke da agogon dake nuna masa takwas ta kusa , gashi a tsaye ya kasa shuga saboda Bakin hajia da kalaman da take fada tun dazun sai yake ganninsu da jinsu wani iri
Turare ne Hajia ta rike kuuuuuuu tana fesa mata , sai kuna ta dauko wanda ta zo da shi nata ne da ta siya wajen HAJIA FUSAM mai turaren yan gayu ta bude shima ta yi mata feshin albarka dan sai da dakin ya dauki kanshin gaba daya sannan ta rufe tana fadin" Yauwa ko ke fa, ga farar rigar ga kuma dan karamin hijabin, ki je ki dawo mi je wajen tela Allah ya tsare bara na ba direba abincinki"
Daga daga nan Hajiar ta wuce da kwondon da ta zuba mata abinci lafiyaye ta bi ta kicin
Ajiyar zuciya ya sauke ya girgiza kai sannan ya daga labulen da niyar ce nata ta zo su gudu kafin hajia ta dawo ta hadasa masa ciwon barin kai
Hankali ya zuba mata ido, Atampa ce a jikinta mai haske, dinkin doguwar riga ne wanda ya dan mata yawa daga wajen tumbi dan zazagewar da tumbin ke yi ama kuma ya rike cinyoyinta tak dan kamar nan jikin ya karra komawa, sai dan madaidaicin hijab din da Hajiar tace shi zata saka ta yi tsuru tana tunanin halin da take iya shiga idan ta fita a haka domin ta san babu inda zata iya zuwa
Da ido yake kallon fuskarta gannin ikon Allah su jan baki, su kwali su pankeke in ji hajia, daidai itama ta dubo gannin an dage, dan haka ta ja numfashi da sauri ta karaso inda yake tsayen, hakan ya saka dadade, nutsatse, hautsinanen, fitinanen kanshin turaren fara isowa kafin ita, a dan rikice ta ce" Dan Allah dauko min hijabin baba freind idan na fita sai na saka, ni kam na bani da rikicin hajia wai a haka zan fita fa"
Idannuwansa ya dauke a kanta ya sauke kan uwar daban, ita dai matar nan baba a wajen mai kwanoni, da ta dawo fuska na mata gyatsine kamar tsantsamen kunnun safe, ta wani cakare irin ko wace wace tana sake kankance ido ko ganne shi ne bata yi ko me take nufi oho?
Fuska ya daure sosai yana kallonta ya ce"
Wannan tsohuwa bata son zaman lafiya🙄🙄🙄
*ALLAH BAI SAUKAR DA CIWO BA SAI DA YA SAUKAR DA MAGANINSA*
Ni ce dai Fareeda Abdallah, na sake dawo muku da tallen magungunanmu da zuwa yanzu bazan iya ƙayyade yawan waɗanda suka dace da biyan buƙata sanadiyyar amfani da maganinmu ba. Alhamdulillah! Ƴar'uwa ki gwada, wataƙila warakarki na tattare da maganinmu.
Haihuwa ce baki taɓa yi ba ko kuwa jinkiri kike samu sanadiyyar planning ko kuma haka kawai? Muna da ingantaccen maganin rashin haihuwa ga mace da namiji, wanda za ki bada sadakar 2k ga matsalar ko wane ɓangare. In sha Allah za ki dawo da godiyarki bayan amfani da maganinmu.
Sanyi (infection) ne yayi miki yawa yake saka ki ciwon mara, zubar farin ruwa, ƙaiƙayi, ƙuraje, ɗauke ni'ima, har ma ya saka mijinki ya dinga miki gani-gani saboda bakya gamsar da shi? Da naira 3k zamu haɗa miki magungunan da za kisha ke da Oga in dai kika yi amfani da su ku da sanyi har abada in Allah ya yarda.
Muna sayar da ingantaccen haɗin sabaya, wanda zai sa nonuwanki su cicciko, hatta fatar jikinki sai ta murje sanadiyyar shan kunun sabayarmu. 2500 bokiti 1litter.
Muna da maganin wankin nono ga mai ciki da mai shayarwa, wanda indai kikai amfani da shi yaronki zaiyi tubarakallah, ba ruwanki da laulayi. Muna da ingantaccen maganin Daji (Cancer), typhoid, maleria, yaron da yayi nauyin ƙafa, da sauran cututtukan da ban ambata ba.
Muna aika maganinmu ko ina tsakanin Nijar da Nigeria, ga masu buƙatar magani da gaske su tuntuɓeni akan lambar wayata 07039080978, ko 09077591726
Noted: *MAI SON MAGANINMU IDAN BA A KADUNA YAKE BA, SHI ZAI YI KUDIN MOTARSA HAR ZUWA INDA YAKE, BABU INDA BAMA TURAWA IN SHA ALLAH.....SAI KUN ZO*
💔💔💔💔❤🩹❤🩹💔💔💔💔
*DA CIWO A ZUCIYATA*
💔💔💔💔❤🩹❤🩹💔💔💔💔
_MALLAKIN_
*SAJIDA NIJAR*
*FREE BOOK NE* 2️⃣2️⃣
LITATAFAN MARUBUCIYAR
Duk karyar kada
Yar mahaukaciya
Neman na kaina
Bani da zabi
Bak'a ce
Kutkale
Makauniya ce
Mage
Duk nisan jifa
Idan ka raina inda kake
Dutse
Alkalamin kadarata
Bani da zabi
Dakika Biyar
Now
*Da CIWO A ZUCIYATA*
*Tallah, tallah, tallah*
*SECRET DE LA FEMME DU MANGA*
_Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata, nesa tazo kusa,Amarya ,Uwar gida,Ango da mai gida Har ma da yan mata da samari shin kuna sane da cewa HAJIYA FUSAM ta shirya tsaf domin gwangwaje ku da turarakunta masu dankaran kamshi? Tare Kayan gyaram jiki na musamman ,wanda daga nesa kamshin ki kadai ya wadatar ya isar da sakon zuwanki waje,gidan ki kuwa sai ya zam abun kwatance wajen kamshi, kar na cika ku da surutu bara in fara zayyano su_
Farar Humura
Bakar Humura
Humura special,
humura de bain
Humura epicé
Lait de nuit
Parfums désodorisant
Parfums rideau et dras
Lait de nuit
Alkam
Kulakcam
*Waɗannan kadan ne daga bangaren turaran ruwa*
Gagab, sandal flex, Durot, durus, sandal fleur, tafarce, farce, sandal bangui, sandal, hypotonic sandal, al'ut, coktail creation VIP, Gajiji, Mankaji, turaran wutar labule da cafet, Aba malan, boulettes
*Munada bangaren gyaran jiki kamar haka:*
mai mai saka santsin jiki, mai mai kanshi, Kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi santsi da laushi, kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi fari, Sabulu mai saka fata ta yi haske, sabulu mai saka fata ta yi santsi, sabulu mai goge yanayin fata, mai wanda baya saka fari mai gyara fata
Sayen na gari mai da kudi gida,sai an gwada akan san na kwarai💃💃
Hajiya Fusam na zaune a kasar Niger domin yin magana da ita kai tsaye tuntuɓi wannan number 97 82 44 94
*SECRET DE LA FEMME DU MANGA*
Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata💃💃💃💃💃
Fuska a hade ya ce" Ke, je dauko hijab baba maza ki sameni a mota !"
Daga haka ya juya ya yi gaba ko gaisar da Hajiar bai yi ba
Khausar ta yi tsuru tsuru ta kalli Hajia ta kalli hanyar da ya bi ya fita ta gaza koda daga kafarta ne bale ta dauko din, haka kuma ta gaza bin bayansa
Hajia kuwa ta ja ta harde hannayenta ta ce" Yau sai na ga ni uwar mai kwanoni zaki ji magana ko wancen marar jin tsoron Allahn!"
Khausr ta hadiye yawu da kyar
A hankali ta ce" Hajia na tafi sai na sauko"
Hajia ta washe baki tana gyada kai ta ce" Ni na san nice zaki fi kauna yar nan, a dawo lafiya ina nan ina jiranki"
Tamkar an zare mata laka ta samu ta fito tana ta rungume hannu a kirji ta nufi motar dake parker dan alamun tsayuwar motar suka nuna mata yana ciki
Da sauri ta samu ta fada motar ta rufo tana sauke ajiyar zuciya
Juyowar da zata yi sai da gabanta ya fadi sakamakon kaifin da idannuwansa sukai mata a fuska yana binta da kallon me nace maki?
Fuska ta marairaice ta ce" Yaya kake so na yi ne? Hajia fa na tsaye ka san ai ba zai taba yiwuwa na take maganarta ba ko?"
Motar ya kunna , cike da jin haushi ya ce" Hakane, sai nine ai maraininki, nace nine tawa maganar ba a bakin komai ba, tunda na kula baki dauki damuwata a komai ba, jiyan nan kin rainan hankali abinda na hannaki kin sake yi, kuma yau kin kuma yi, sai ki ci gaba, ki ci gaba Khausar!"
Daga haka ya ci gaba da tukin
Sunna shigowa harabar asibitin ya lalubo face masque ya saka a fuskarsa cikin dabara sannan ya parker dan nesa ƙadan yana jiran ta gama saka farar rigar da baby hijab din, domin ba abinda ya dameta a nan ta cire dayan hijab din ta ajiye ta saka karamin fari kal mai kyan gaske ta kuma saka farar rigar
Da yannayin tsokana ta dube shi ta ce" Ka kuwa san yanzu tsaf bake iya maka allura na maka karin ruwa da komai da komai?"
Ido ya zuba mata, yadda take saki murmushi irin an fa fara kwarewar nan ya saka shi yin murmushin shima aman bai ce mata komai ba
Ta dora da fadin" Na tabata idan ka samu kaima shekarar badi in sha Allah nice nan zan koya maka, dan bani kwondona na tafi "
Kwondon ya juya baya ya dauko ya bata, sannan ya dakattar da ita ya dan daga farin kyalen da aka rufe kwondon ya saka kudi a ciki a hankali ya ce" A dawo lafiya likita"
Kudin ta kalla tana zarro ido ta ce" Wannan fa?"
Shima ya zarro mata idon ya ce" Kudin kifi da dambu ne "
Idon a zarre ta ce" kuma duka wannan? Wannan ai sai na ciyar da likitocin emrgncy da shi "
Ya yi murmushi ya ce" Ki tafi mana ana jirana fa"
Murmushin ta yi itama tana kudurta zata dawo masa da kudinsa in ta sauka, dan babu abinda zata siya ga abincin nan Hajia ta zubo mata zai isheta ne, sai kawai t dan ja baya tana masa alamun sai an jima sannan ta juya ta nufi ciki
A wannan ranarma sun sha aiki, aikin da a yanzu take iya cewa idan bata fita ba sai ta ji wani bari na zuciyarta na cen, du irin abinda idannuwanta ke iya ganni na tashin hankali abin ya zame mata wani jigo na barin zuciyarta domin a ranta take gama yarda cewar fitarta aiki taimako ne wa al'uma da ita kanta, idan tana taimakon marar lafiya a yanzu tana jin wata irin nutsuwa a cen kasan zuciyarta, in ta ga an samu an fitar da mutun lafiya daga emrgncy sai ta ji wata salama tamkar mutumen nan danginta ne
Yau da wuri aka salameta, hakan har ya bata mamaki, domin tun bayan sallar la'asar aka ce ta shirya ta tafi gida, dama fitowar tasu suka sani basu san komawarsu ba, domin emrgncy ko manyan ma'aikata kan fita su je wani sa'in saukarsu ta zamto ba yadda suka sn zasu sauka ba, dan idan wani aikin ya samu dole su zauna, domin wani lokacin hargitsewa gidan ke yi sosai sai gyaran Allah
Da murmushi ta fito saboda tsokanarta da abokin aikinta ya yi cewar yau za'a je a sha barci an tashi da wuri su Hajia Khausar
Bata taba tunanin iya gannin TAUFEEK a wajen masu parking din motoci ba, sai ganninsa ta yi, hakan ya bata mamaki ainun, harma ta kasa boyewa ta ce" Aa, yaya aka yi ka san lokacin tashina bayan ba lokaci ne a kayade ba?"
Dan murmushi ya yi yana basarwa ya bi kwondonta da kallo, ya ce" Baki ci komai ba hala tun safe?"
Murmushi ta yi bayan ta shiga motar tana jan abu ta rufe ta ce" Na zatama zan iya ci tunda na zo da shi, sai kawai na manta da shi kwata kwata, sai yanzu da na shiga cenza kayana na ganshi kuma ka ga har ya fara bacewa ba damar na kyautar tunda nima ba zan iya ci ba"
Kai ya gyada ya tayar da motar ya dauki hanyar gidansu da ita
Bata ce komai ba, sai dai a zuciyarta ta ji dadin hakan dan ita kadai ta san irin kewar ahalinta da take yi, komai dadin gidan wasu gwara naka, dan a jiya an mata gata iya gata an hadata da wani luntsumemen gado da ac, ama zuciyarta sai ta ringa kwadayin inama ta samu yar katifarta da motsin ahalinta a kusa da ita? Dandai bata da yada zata yi da Hajia ne , kuma ko ba komai dan matsawar daga gidan ya taimaketa ainun dan ta samu zuciyarta ta dan saku da irin aibatatan da mutane suka ringa yi
"Karfe bakwai zan dawo na daukeki na maidama matar cen ke " ya fada a hankali bayan ya tsaya a kofar gidan
Murmushi ta yi ta bude motar ta fice da kwondon abincin dan a juyewa busashe ta wanke flsk din da aka zuba
Sosai suka sha fira da Mama, Mama bata yi mata fadan da ta yi tunanin zata yi mata ba, saima rarashi da ta samu na ban mamaki da kuma ban baki
Da kula Mama ta ce" Komai da kika gani na rayuwa mukadari ne, ban ce maki takurarwar mutane ba zata dameki ba dan kuwa hakan na iya damunki fiye da tunanin bawa, ama abinda na sani shine mu iyayenki zamu ci gaba da binki da addu'a har Allah ya fitar maki da miji na gari, Khausar a jiya Mujaheed ya zo da dare nema sosai , Abanku ya fita ya same shi, shin akoy wata matsala tsakaninki da shi ne da ban sani ba?"
Khausar ta yi dan shiru gabanta na dan faduwa, a sanyaye ta girgizawa Mama kai
Mama ta tabe baki ta ce" Kin san mahaifinki bai cika buden abu ba, a yadda dai na dan tsinci abin kamar ya fara kokonta a kan tarenku da mutumen , harma ya bashi damar ya fito idan da gaske yake, in ba haka ba kuwa ya yi hakuri kawai, ...........hakan ya sa na tsatsamci akoy abinda yake faruwa da baya birge abanku"
Khausar ta yi tsuru gabanta na faduwa zuciyarta cike da tunanin ko wani abu ne ya faru?
Mama ta ce" To ki kula, kafin komai mutuncinki ya fi komai a duniya, ki sani idan da rabon ki yi aure ko shekara nawa zaki dauka a duniya sunnanki mace , budurwa, kar ki yarda ko menene ya taba maki mutunci , kuma ko wani irin hargitsi ya tunkaro rayuwarki ki san cewa Allah ya haliceki shi ya dora maki ba kowa ba, ....., Sai maganar auren kannenki, a jiya fa iyayen wajen mijin rukaya sun nuna da wuri suke so, dan a cewarsu sati biyu, da kyar dai abanku ya tsaida abin nan da wata daya, kennan dole mu zauna mu yi shawara mu ga abinda zai fishemu ko?"
Da mamaki ta ce" Ka8, da wuri haka Mama, na zatama sa kai bayan babar sallah?"
Mama ta ce" Nima na zaci hakan, ama kin ga yadda Allah ya yi"
Khausar ta yi murmushi ta yi addu'ar Allah ya nuna masu ranar da rai da lafiya
Nan suka hade suka yi ta zantawa har baba ya dawo gida shima ya hadu da su ya ringa tsokanar Khausar yar gidan Hajia ya ce" Kin ga, TAUFEEK ya zo ya maidawa Hajia ke tun kafin ta tardoni tace ni na kwaceki"
Dariya Mama ke yi ta kama baki ta ce" Ni ai jiya na sha dariya Ni kadai, Hajia fa hararena take yi wai ban san ciwon Khausar ba"
Aba ya ce" Nima cewa ta yi ba sannin ciwon yar aka yi ba"
Nan fa aka dauko caftar Hajia, Khausar ta ringa dariya dan walahi sai yanzu ta idasa sakewa har ta ji wasai a ranta, ta fada masu turaren da hajiar ta mata jiya da yau da safe, ai kam kannenta da iyayenta aka rasa mai ba dan uwansa hakuri dariya suke bilhaki, Aisha ta ce" Ni walahi tsoronta nake ji, idan tana fadan nan sai na ji kamar zata iya marina, kuma ita babu wanda ta bari, harta yaya TAUFEEK fa sai ku ji ta yanko shi , shi kuwa abin mamaki idan ya zura ido ya kalleta sai ka ga ya dauke kansa kamar Allah bai yi ruwanta ba, sam baya kulata"
KHausar ta ce" Ke na rabaki da TAUFEEK, shi ai du lokacin da kake shirye ku yi balaki ne na zai biyaka ba, ki ga fa idan ina fushi da shi na yi na yi ya biye min sai kawai ya kare min kall9 ya dauke kai, ni kuwa hakan irin haushin da yake bani, sai in ga a banza kennan ban samu muka raba hali ba"
Mama na dariya ta ce" To ai shi ba mashiririci bane da zai tsaya karamar yarinya ta fada ya fada"
Haka suka yi ta sharfi sunna fara'a, a hankali kuma mutane na lekowa sunna sake yin barka da arziki da fatan Allah ya nuna masu ranar auren
Zuwan TAUFEEK ya saka suka mike sukai mata rakiya, su uku, Aisha , Rukaya, da Auta har wajen motar
A lokacin da ta bude ta shige a gaban idannuwanta yan zaman anguwar suke lekowa, ita kuwa ta cire kanta bata kula kowa ba ta shiga neman layin Mujaheed
Sai da suka kusa isa gidan ya daga wayar, cikin dan basarwa ya ce" Batan numba aka yi ba?"
Khausar ta yi dan murmushi a hankali ta ce" Barka da warhaka Elhaji"
Elhaji Mujaheed ya amsata shima da kula
Khausar ta ce" sai yanzu na ga misscall dinka, shine nace ko zaka iya zuwa nan gidan su TAUFEEK da yake a nan zan kwana? Idan har dare bai yi ba?"
TAUFEEK dake tuki yana amsa waya ya dan kalleta kadan, sai kuma ya dauke kansa ya ci gaba da tukin
Bai dai san me suka tatauna ba har suka karaso gida dan shi bai gama tasa wayar ba har sai da suka iso ya fice yana amsa wayar, ita kuma ta ciro kwanukan ta nufi bangaren Hajia da su
Samu ta yi Hajiar bata nan, mai aikinta ta shaida mata tana bangaren su Mama, dan haka sai kawai ta shige bayi ta yi wanka ta fito ta cenza kayanta sannan ta zauna ta hada lipton mai zafi ta shiga sha a hankali tana dan duba agogo domin Elhaji Mujaheed yace ta bashi minti ashirin gayanan zuwa
A lokacin da ya sanar mata yana cen babar kofa bai samu shigowa ba a dole ta mike ta shiga neman layin TAUFEEK, sai dai ta yi ta yi bai daga ba, gashi hajia bata dawo ba, abindama ya dan sakata kin bin hajiar da kuma kin zuwa ta gaisar da su mai aikin na hajiar cewa ta yi an zo an yi kiran hajiar ana fada a cen, hakan ya sa ta yi zamanta dan ba zata je kotai kotai bayan ta ji abinda aka fada ba
Hijab ta saka ta Hajia dan ta nemi nata sama ko