Showing 132001 words to 135000 words out of 186303 words

Chapter 45 - DA CIWO A ZUCIYATA COMPLT BY SAJIDA.txt

09 Nov 2024

18758

zagina koda da wasa ne, dan ban iya zagin iyaye ba sai dai jikinki ya gaya maki!"


"KHAUSAR?" Ya furta a nutse yana kallonta


Yumnah kuwa wannan dama ita ta fi komai dadada mata, a rikice ta ririke ciki da kai tana ihun cikinta, kanta


Khausar ta yi galala tana binsu da kallo domin kansa ta yi ta aniya neman kaiwa kasa


Cike da yarda cewar dukan nata ta yi ya tareta ya dauketa ya nufi bakin bed da ita ya kwontar da ita sannan ya mike yana sake bin Khausar din da kallon da ya sakata rasa mene fasararsa ya ce" Kina sane cewar she's prgnt mene laifin da ta maki har zai kai duka?"


Wani irin abu na ba zata ne ya zo ya soki zuciyar Khausar wanda tashi daya tana iya kiransa cewa bata so ba TAUFEEK din ya sake goyon bayan Yumnah a karro na biyu , wanda bata taba jin hakan ba, har ta kasa furta masa kalmar A kawai take binsa da kallo


A hankali ya sake duban Yumnah dake nade kaffafuwanta tana nishin wahala tamkar wace zata yi bari cikin azabar nan ya sake maido dubansa kan Khausar dake tsaye tana kallonsa da kallon da bai taba ganni a tare da ita ba, domin sun kasance ne idan ya hayayako takan hayayakowa fiye da shi su zuba masifarsu su kuma shirya a tsakaninsu, sai yau ya ga kallonsa kawai take yi


Bai yi kasa da gwuiwa ba ya ce" A matsayinki na likita kin san ko wani abu ya hadaki da ita akoy hormone na ciki ko?, Why zaki daketa? Idan wani abu ya samu cikinta fa? , Ya rab me kuke son fara min ne daga hadaku a innuwa daya"


"TAUFEEK ya isa dan Allah!" Khausar ta fada tana sakin jakar hannunta kirjinta ba'a dokawa dan gaba daya sai ta ga ya goyi da bayan matarsa ne zai mata wulakanci , bayan a rikici sun yi sama da wannanma bai mata ciwon wannan ba


Rai bace ta ce" Bani da hankali ne zan daki cikinta? A kan me zan daki cikinta? An gaya maka ban san abinda nake yi bane?"


"Ki rage sautin amon muryarki a kan tawa!" Ya fada a kausashe yana tunkarota


Khausar ta rintse ido hawaye ya bale mata tana kallonsa ta ce" Ba zan rage ba, tunda Ni bani da gata sai a wulakantani ko? Ba zan rage ba TAUFEEK, ITANE matar so ko? A kan me zaka hau fada baka bi abinda ya faru ba? Ni sa'arta ce ko tana tunanin haukan da take yi yana gabana ne.........


Bata karasa maganar ba ya damki hannunta ya juya da nufin janta, sai kawai ta tubure ta yi kasa da nufin zaunawa a kasa dan babu inda zata bi shi sai dai a yi masifar a nan


Ikon Allah ya zubawa ido, bata taɓa tsamatar cewa wai TAUFEEK zai iya jijigarta ya warceta kamar ya warci dan karamin abu a hannunsa sai da ya juyo ya cicibeta ya dagata daga kasa ya juya da Itan ya tura dakinsa ya shiga da ita ya tura da ƙafarsa ta dama sannan ya saukota ya koma wajen kofar ya dana ky ya kuma juyowa kan Khausar wace ke zarro ido tana kallon abin al'ajabi TAUFEEK ne ya daukota kamar ya dauki karamin abu, sai gani ta yi ya nufota gadan gadan


Da sauri ta ringa ja baya, dan tsoron da ya shigo cikin kwakwaluwarta yana zuwa zai dauketa da mari ne, dan ba yau ba in dai sunna rikici sai ta yi nesa take masa ihu, a gabansa takan fadi abinda ta ga dama ne ama a sanyaye dan kar yace ta masa ihu


A rikice ta rintse ido jin ta hadu da kofar bayi,
Da sauri ta bude idannuwanta tana kallon yadda kirjinsa ke bugawa lokacin da ya ce" Na ce ki daina min ihu !"


"Taufe......................
TAUFEEK bai bata damar karasa kiran sunnansa ba ya janye hannayenta da take karewa tsakaninsu kamar wani kwarto zai tabata ba mijinta ba, a birkice ya janyota gaba daya jikinsa ba wata wata ya hade bakinsa da nata lokaci daya ya damko harshenta dake masa rashin kunyar a hankali ya rike a cikin bakinsa sai kuma ya lumshe idannuwansa hucin numfashinta na shiga hancinsa a hankali ya sake riƙe harshen sai kumaa cikin dabara ya hade da lebenta a sanyaye ainun ya shiga tsotsa ba tare da ya so aikata hakan a yanzu yanzu ba


Mutuwa ce? Ko summa ne? Khausar dai bata duniyar mutane sai ta zazafan abin dake sukan ilahirin jikinta lokaci daya ya bude jajayan idannuwansa ya saka dubansa cikin nata wanda ya sa a rikice ta maida nata duban ta rufe kirjinta na dokawa ama bai bari ba dan fitinaniyar rashin kunya sai da ya gaji dan kansa sannan ya talabata da hannu daya ya sakata a kijinsa ya rungumeta sosai a hankali yana sauke ajiyar zuciya kamar yau ya taba taba leben mace a duniya, muryarsa a shake ainun hancinsa a daidai kitson kanta ya ce" Khausar Please, kar ki rikitani na haike maki bayan ke din yarinya ce....., Khausar plz ki barni na kai wajen da nake son kaiwa idan na yarda cewa eh lalle yanzu *KINA SO NA* , ba hasashe ba......, I beg U kar ki saka na maki gagawa bayan sosai na koyi hakuri a kanki a rayuwata......"












Ya Salam........😌🙈🫣kashe TAUFEEK haka kake?


Jama'a ya yi sara da mutun sama domin Yumnah itace wace ke makale a kofar dakin tun fitowarsa da Khausar cike da farin cikin son jiyo kukan Khausar din, dan ta sani a kan cikinsa babu abinda ba zai aikata ba😒😏😏😏😏




















Cmmnt kari in sha Allah ☹️
[7/22, 5:11 AM] +234 806 670 8178: 💔💔💔💔❤‍🩹❤‍🩹💔💔💔💔




*DA CIWO A ZUCIYATA*




💔💔💔💔❤‍🩹❤‍🩹💔💔💔💔


_MALLAKIN_


*SAJIDA NIJAR*


*FREE BOOK NE* 5️⃣1️⃣


*GARABASA, GARABASA, PROMOTION, PROMOTION DIN LITATAFAN MARUBUCIYAR A KAN FARASHI MAI SAUKI 1K, YAN NIJAR KUWA 1000 FRANCS CEFA*


1: Duk karyar kada


2: Yar mahaukaciya


3: Neman na kaina


4: Bani da zabi


5: Bak'a ce


6: Kutkale


7: Makauniya ce


8: Mage


9: Duk nisan jifa


10: Idan ka raina inda kake


11: Dutse


12: Alkalamin kadarata


13: Bani da zabi


14: Dakika Biyar


15:Wata kokowar


16: Aure yakin mata


17: Ni zan ladabi


18: Daga tafia daukar soja


*Dukansu a kan farashi mai sauki, zaka saka dubu guda ne domin promotion ne nake yi, ka tuntubeni kan layina kamar haka +227 93 81 16 18, Sajida Nijar*


Now


*Da CIWO A ZUCIYATA*






*Tallah, tallah, tallah*


*SECRET DE LA FEMME DU MANGA*


_Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata, nesa tazo kusa,Amarya ,Uwar gida,Ango da mai gida Har ma da yan mata da samari shin kuna sane da cewa HAJIYA FUSAM ta shirya tsaf domin gwangwaje ku da turarakunta masu dankaran kamshi? Tare Kayan gyaram jiki na musamman ,wanda daga nesa kamshin ki kadai ya wadatar ya isar da sakon zuwanki waje,gidan ki kuwa sai ya zam abun kwatance wajen kamshi, kar na cika ku da surutu bara in fara zayyano su_


Farar Humura
Bakar Humura
Humura special,
humura de bain
Humura epicé
Lait de nuit
Parfums désodorisant
Parfums rideau et dras
Lait de nuit
Alkam
Kulakcam
*Waɗannan kadan ne daga bangaren turaran ruwa*
Gagab, sandal flex, Durot, durus, sandal fleur, tafarce, farce, sandal bangui, sandal, hypotonic sandal, al'ut, coktail creation VIP, Gajiji, Mankaji, turaran wutar labule da cafet, Aba malan, boulettes


*Munada bangaren gyaran jiki kamar haka:*
mai mai saka santsin jiki, mai mai kanshi, Kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi santsi da laushi, kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi fari, Sabulu mai saka fata ta yi haske, sabulu mai saka fata ta yi santsi, sabulu mai goge yanayin fata, mai wanda baya saka fari mai gyara fata


Sayen na gari mai da kudi gida,sai an gwada akan san na kwarai💃💃
Hajiya Fusam na zaune a kasar Niger domin yin magana da ita kai tsaye tuntuɓi wannan number 97 82 44 94
*SECRET DE LA FEMME DU MANGA*
Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata💃💃💃💃💃






Tamkar an zare lakar jikinta haka take ji a irin wannan lokacin, idannuwanta kuwa yadda ka san an saka masu gam ta rufe su ruf, haka kuma jikinta na rawa zuciyarta na dokawa


Ya Salam bata taɓa tsintar kanta da jin wata irin nutsuwa mai masifar karfi irin wannan ba, sai idan ta fuskanci alkibla, sai wata irin kunya da tsoro da mamaki da suka mamaye zuciyarta


A hankali take jin Hannunsa a bayanta yana dan taping alamun rarashi
Tare da rashin karfin gabai Khausar ta nemi zubewa a tsayen da suke


Yanzunma bai bata dama ba ya tareta sosai ya kaita har bakin bed dinsa wanda kallonsa kadai abin birgewa ne, ba dan wai ya fi nasu kwaliya ba, a'a, kawai yana dauke da classs ne


A hankali ya zauna daf da ita yana jin wani irin abu mai girma na taso masa hadi da nutsuwa a zuciyarsa


So yake yi ta bude idannuwanta, ama ta cure waje daya ta rintse ido ta kasa kwakwaran motsi bale har ta bude idannuwan nata


"Look at me An mata" ya fada a cen kasan makogwaronsa


Khausar ta sake rintse idannuwanta muryarta na dan rawa ta juya ta zubo kaffafuwanta kasa ta mike tana ta sosa keyarta ta ce" Zan je wajen aiki ne, kar, kar kar na makara"


Hannunta ya riko ta bayan nan ya maidota, bata shirya ba sai jinta ta yi Dar saman cinyarsa


A rikice ta mike tana yaye mayafinta ta juyo tana kallonsa ta ce" TAUFEEK, yau na shiga uku, A'uzubilahi mina shaidani rajim, nice a cinyarka?"


Murmushi ya saki na kirki, dan yanzun ya kasa rikewa, sannan ya karewa ɗinkin jikinta kallo ya ce" To a nan waye shedanin ne Matar likita?"


Amsa sai ta gagari bakinta ta zuba masa ido tana tunanin yana yi mata haka ne da gaya, dan ya ga tana tsorata dan haka ne yake yi mata,


"Bama wannan ba, yau ko Ni ba zan je aiki ba bale ke, zo mu yi fira, kin san irin yadda na yi missing din doguwar fira da ke kuwa? Tunda kika fara zantuka irin na yan maye nake tsoron doguwar fira da ke!" TAUFEEK ya fada yana kallonta, yana matukar jin dadin bakinsa da yadda yake doguwar firar nan da ita,
Dama yana fira da ita mai tsayi fiye da kowa a duniyarsa, bale yanzu da yake jin du wata damuwarsa ta kau sai godiyar mai sama


Khausar ta yi zaune saman cafet din nan ta rafka tagumi tana kallonsa ta ce" Du kamar ba kai ba, Ni kam yanzu nice na fara rikita a tunanin me yake damunka, TAUFEEK"


Fararan kaffafuwansa ya sauko ya zamto yana kallonta a hankali ya furta" kece ke damuna , wai tsaya mema matata ta maki kika daketa?"


Khausar ta dago da sauri, ba komai ya sakata dagowa har kamar a firgice ba jin kalmar matarsa da ta yi kai tsaye,
Kai ta juyar tana tunanin menene dalilin jin hakan nan da ta yi?


"Tell me" ya fada a hankali yana duban yannayin fuskarta kamar daga yannayin mamakinsa ya koma yannayin bacin rai


Dago dubanta ta yi, ta sake saukewa a kansa
A hankali ta budi baki da nufin fayace masa abinda matarsa tace mata, sai kawai ta ga a kan wani dalili har zata wani fayace masa? Idan ta yi hakan kamar ta hadashi da matarsa ne, dan haka ta dauke dubanta a kansa a hankali ta ce" Zagina ta yi, Ni kuma ba sa'arta bace idan ta kuma zagina zan kuma dukanta ne"


"A'a" TAUFEEK ya fada yana hade girar sama da ta kasa


Khausar ta sake juyowa tana kallonsa, fuskar a hade ya ce" Aa kar ki dakar min mata, haka kawai? Bama zata kuma zaginki ba, ama da duka ai sai a saka in gigice, Malama kawai kar a wani dakar min matata!"
Yana fada yana mikewa ne ya karasa wajen yar karamar wayarsa dake kuka ya dauka ya duba, gannin sunnan Hajia sai ya ajiye wayar ya juyo ya dan saci kallonta, gannin bakinta sai mutsu mutsutu yake yi ya saka shi yin gaba yana yin murmushin da bai bari ta ganshi ba


Yana fitowa dakin Yumnah ya koma


Yana budewa ya ganta zaune bakin gadonta hannayenta cushe a cikin gashin kanta tana kallon kasa ga wayarta a gefe yashe har madubin wayar a fashe


Kai taa dago ta zuba masa ido, zuciyarta na tafarfasa da kunna Bama kamar bakinsa da kuma gangar jikinsa baki daya


Zama ya yi bayan ya dauki wayar ya gani eh madubin wayar ne ya yi ratsa ratsa ya juyo zai yi mata magana muryarta cikin kuka ta ce" TAUFEEK, dama kana son Khausar ne?"


Idannuwansa ya zuba mata, fuskarsa na dauko yannayin zuciyarsa mai dauke da bacin ran halayan da take nunawa wa'inda sam baya so , kwarai kuma kama sunnansa da ta yi ya bashi mamaki dan rabonsa da ya ji ta kama sunnansa kai tsaye kam shi ya manta


A kausashe ya ce" Ban fahimci tamkayarki ba?"


Yumnah ta sake zuba masa idannuwanta da suka yi jajajir ta ce" TAUFEEK, dama kana son Khausar ne? Ko me yake faruwa da kai ne?, Na ga ka saka hannu ka dauki Khausar kuma ka kaita dakinka ka haɗa jikinka da nata?"


"Labe kika min ne?" Ya furta yana son tabatarwa


Yumnah ta yi tsuru tsuru ta kasa bashi amsar tambayar da ya yi mata


Rai bace ya ce" Saurara, ki kula, bana son shashanci Yumnah! Tambayar ina sonta ko bana sonta bai shafeki ba, amsar da nake so ki sani shine ki koyi zama da ita dan ba zan iya zama babu ita ba!, Ki kuma kiyaye yi min ciwon karya dan kar na kirki ya kama ki a ki yarda har ki yiwa kanki ila, labe kuwa idan shi zaki min fine, zaki hanna kanki da kanki ne!"
Yana gama fada ya mike ya yi tafiyarsa, ya barta zuciyarta tamkar zata fito ta bakinta irin yadda take bugawa, gashi wayarma da zata yi kiran Mamanta ta fasa, innalilahi Wa inna ilaihi raj'une bata haduwa da bugawar zuciya irin ta yau ba, nan da nan kanta ya dauki ciwo ta kwonta a nan tana gursheken kukanta, domin bata san yaya zata yi ba, ina zata saka ranta, lalle namiji namiji rigar kaya!


TAUFEEK kansa kan nasa ciwon yake yi masa sosai
A cikin zuciyarsa yana yin iya kokarinsa dan gannin ya kiyaye bata ransa a komai
Ama yana tsoron Yumnah da sababin halayan da take nunawa, ace ta nuna sumar karya, ta ringa zaburar karya dan ta hannashi kasancewa da iyalinsa? Baya so ya kai wajen da zai nuna mata shine mijinta kuma miji ga Khausar,, babu ɗaya da ta isa ta hanna shi kyautatawa daya dan shi ba solofiyon namiji bane


Yana fitowa da nufin zuwa bangaren Mai kwanoni ya kuma saka masu aiki a kawowa su KHausar abinci dan bai ga alamun wani zai girka ba ya yi turus gannin Hajia zaune da Hamdiya sai fada take yi tana fadin wannan ai wulakanci ne a sakawa baban falo sakata


Tunda ya fito ya yi turus din itama ta mike tana kare masa kallo daga kasa har sama, sai kuma ta yi wani dan murmushi ta ce" Magidanci sai yanzu aka sauko?"


Fuska ya hade ya ce" Daga ina?"


Hajia ta ce" Daga sama mana inace dakinka a sama yake?"


TAUFEEK ya tabe baki yanna kallon kwondon dake tare da su ya ce" Me kuke nema a nan da safiyar Allah?"


Hajia ta dan zarro ido tana fadin" Elhaji karami karfe tara ta gota fa,, kuma abin kari na je aka yi na kawo shine nake ta kiranka baka dagawa me kake yi a cikin ne haka?"


Ido ya zuba mata, tunani yake yi to shi anya ba ya shiga uku ba kuwa? Subahanalahi shin me wannan matar ke so da shi ne?


Hade fuskar ya sake yi ya ce da Hamdiya" Ke ajiye ki bace a nan"


Da sauri ta ajiye ta juya har kamar zata kifa ta nufi cen bangaren iyayen


TAUFEEK kuwa ya zubawa Hajia ido, shi walahi sai ya rasama me zai mata


Zagayeta ya yi ya yi tafiyarsa, ba zai iya ba sam, baban takaicinsa da yace mata yana iya Bara mata gidan tsaf ta hada taron iyayensa aka tabatar masa ko gidansa zai kaura da ita zai je, sai kawai ya sarewa duniya ya san ita din wata rikicin duniyarsa ce


Da ido ta bi shi har ya bacewa ganninta ta tabe baki ta tura kofar ta shiga tana haki da katon kwondon nan


Tana shiga ta ringa salama sama sama, sai a kan kunnen Khausar wace take zaune ta cika taf tamkar zata fashe ta mike tana amsawa ta dauki mayafinta ta yafa ya rufe kanta da jikinta sosai sannan ta fito ta sauko yana amsawa hadi da sakin fuskarta sosai ta duka tana gaishe da Hajia


Hajia ta zuba mata ido, sai kuma ta dafe haba cike da takaici ta ce" Aikin banza da na san garas kike babu mai sakani yi miki abincin safe, ku dai an yi shashashu walahi, na tabata bai ji gargadina bane, yaron nan so ake a shiga gabansa, dole in tashi tsaye, in ba lalaci ba irin na magidanci yau kwana bakwai da aka zarga maka nace har mace a wuyanka ama ka iya kwontawa ka tashi ras tana tafiya lafiyar Allah a gaban ka? Ko dai bashi da lafiya ne Ni dije?"


KHausar ji take dama kasa ta bude ta shige ta huta da lamarin Hajia,


To ita me zata cewa Hajia ne jama'a? Innalilahi wayo wayo tashin hankali


"Kin yi shiru khausara,, kin ga taso karya in ji ke din wani lalaci ya sa kika zuba masa ido bayan halal ne kuma wayo ne mace ta nuna ta san ciwon kanta ? Maza karbi ci in ji " Hajia ta fada tana loda mata abinci a plate, ba tare da ta damu tambayar inda Yumnah take ba, dan kwata kwata bata saka a ranta cewa zata samu arzikin gaisuwa daga yarinyar ba, domin kuwa du irin mugun kallon da take yi mata bata boyewa a kan idannuwanta ne, shi yasa gaba daya yarinyar ta fice mata a rai, ai ko ba komai sai ta girmama tsufanta, ama tana abu kamar babu manya a gidansu ko ba'a koya mata bin na gaba ba, walahi bata taɓa tunanin mahaifin Yumnah yana da mutunci har haka ba,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login