Showing 126001 words to 129000 words out of 186303 words
kadan yana amsa gaisuwarta
Sai da ya dan nutsu ya fuskanceta, da yannayi na serious bayan ya ji jikinta da sauki ya ce" Yumnah, ina so na sake maki magana a kan kula da mutunta Mama da HAJIA, ban kamaki da wani laifin da zan tuhumeki ba, ama ina dan tsintar wasu yannayi naki da basa min a wajen mahaifiyata, ki kula, nan din ba wajen da za'a kawo wargi bane, ki mutuntata su Yumnah ko dan haihuwata da suka yi!"
Kai ta sada, muryarta a rarabe ta ce" Ka yi hakuri, ba abinda kake tunani bane, raina ne a bace"
Bai sake cewa komai ba sai mikewa da ya yi ya haura sama
Ajiyar zuciya ta sauke ta sake dauko wayarta ta dannawa mahaifiyarta kira, magana suke yi tunda safe kan maganar tarewar nan, lalle mahaifiyarta ta kwontar mata da hankali kan maganar, yanzu haka zata koma dakinta ne ta yi jiran sakon da za'a kawo mata, ta san cewa kamar yadda Mamanta ta fada maza basa son mace ruftata a bari ta taren sune zasu fitar da ita da nasu baiwar da Allah ya masu, ta kuma sake sanyaya mata zuciya cewar ta dakata ta gani ita dake dauke da cikinsa ta san ta gama shiga gaban du wata banza, danma babansu ya hannata fitowa da da kanta zata zo ta kawo mata dukkan abinda ta fada din
A bangaren HAJIA kuwa tunda safe ta fice a gidan ta tafi kasuwa da direba, sai kusan karfe daya na rana ta dawo a lokacin manyan motocin kampanin furniture sun karaso har biyu shake da kayan daki na kasa da kasa sunna ciki sunna nasu aikin ta wuce bangaren su Mama ta je ta zube kayan da sisiyo ta saka Mama a gaba du irin kunyar da take ji ta sakata karanta mata abubuwan ita kuma tana warewa daki daki kaya irin na gyaran mata masu inganci har suka gama ta kwashi abinta da nufin zuwa ta fara dafawa ta saka a frij , maman kuwa ta yi murmushi tana girgiza kai cike da kunyar lamarin nan na HAJIA , sai dai ba halin nunawa ta shirya ta yi ficewarta itama dan zata je ne ta daidaita harkar kunshin Khausar din da kitso da dilkar da za'a yi mata a gidan HAJIA FUSAM GIDAN KANSHI
Da gaske dai tarewar Khausar ta tabata dan Aba ya bada amanar ta tare din tunda har mijinta ya bukaci haka kamar yadda baba ya nuna
Wunin ranar Yumnah bata kuma fitowa ba, abinci kuwa dama rabonta da shi tun anaa gobe auren aminiyar mijinta, idan ta ji yinwa takan samawa kanta ne bata bi ta cikinsa, dan ta kula idan ta bashi ko a'a ba zai zauna da yinwa ba tunda kakarsa na gefe
A bangaren TAUFEEK kuwa sai dare ya dawo gidan, yauma shi dai ya samu Yumnah a bangarenta, gwargwadon iyawarsa ya kwatanta bata kulawa , ko dan abinda ke cikinta, sannan har ga Allah yana so ya bata darajar ta daidai misali, dan baya so ya shiga hakinta ko kadan, Khausar kuwa dama yau bai ganta a wajen aiki ba, bai kuma je gidan ba, dan ya dan tsinci cewar tana cen tana kuka, bashi da amsar bawa kansa sai girgiza kai da ya yi ya ci gaba da lamuransa, abu daya ne ya sani rikici ne Mai kwanoni da Malan muntari sun daurawa kansu, mai kuncewa fitar ransa ne daga gangar jikinsa, gwarama Yumnah da Khausar su ba kansu lafiya ko su yi, zai kasance mai raka du wani mai doguwar tafiya ne har su kai inda yake so bi'izinilah
A gidan su KHausar Hajia Fusam ce da kanta ta yiwa gidan dira tun a lokacin da Mama ta je mata da bukatarta suka yi magana irin ta manya suka kuma shirya cikin harka ta manya, da kanta ta dauki motarta bayan Maman ta mata kwatance ta kuma sanarwa Maman su KHausar din cewa za'a zo a shiga kimtsa Khausar din
Kaya ne ta je da su na kasa da kasa, ko da ta karasa su Rukaya ne suka tayata saka kayan cikin gidan Aba dan da yawansu
Du irin yadda Khausar ta rikice da bayanin wai kwana biyu kawai zata je gidan su TAUFEEK matsayin mata a wajen TAUFEEK sai da Mama ta mata magana daya da ta sakata sakarwa ta zubawa sarautar Allah ido
Hajia Fusam ta fara ne da hada hadin da zai goge kunshin da aka yiwa Khausar ta shafa mata aka bari na dan lokaci kankani aka wanke da ruwan dumi, sai kuma ta kawo hadin da ta yi dan dora Khausar din a kujera hadi na mamaki ta saka Khausar din mikewa ta shafeta da shi ama fir ta ki yarda har wasu sassan jikinta sai ita da kanta ta shafa irin su Mamanta da cinyoyinta da mazaunanta, ita dai Fusam ta bata damarta dan ko ba komai budurwa take mai kunya abinda dai ya tabatar shine ko'ina ya samu sannan ta haudata kujerar nan ta rufeta da rigar da ake rufewa aka bar fuskarta kadai a waje
Hayaki na ratsata har cije lebe take yi dan sosai yake ratsata, gefe guda kuwa Hajia Fusam na aikin hade haden gyaran fuska da lebe da kuma na raba rabar cinyoyi da mazaunai, hadi dai na mamaki , ga kuma hadin madara mai sanyi da ta sakawa zuma ta mata da magani mai kyau da inganci namu jikake na wajen Maman khair tana yi tana kafa mata tana sha har suka gama aka sauka aka nufi bayi dan wanke kwanin
Tana fitowa Fusam ta kama dirzarta da dilka, tamkar zata kwaye mata fata dan kuwa bata yi mata da sauki ba , sosai ta darjeta har tana yan hawaye , shima aka darwaye da ruwan dumi aka kuma hauda mata kurkum hadi mai madara sannan ta dawo fuskarta ta shafa mata hadin tumatur,....a wannan rana dai Khausar ta ga ikon Allah dan hadi kan hadi ake juye mata ga na sha a gefe sai da ta ji cikinta tamkar zai fashe, ga lebenta da aka samu da nasa hadin aka darje shi da bruch har sai da ya ringa wani irin MUSMUS a ido bale a tabawa , kafin ta kare da sakata a babar robar Mama ta wanki cikin rantsatsen turaren mata masu daraja, su turarukan nan kala uku ne, dama aikinsu ratsa jikin mace ne dan ba'a shiga da pant sai da ta shiga ya zauna ta rufa jikinta da zani sai dan zabura take yi saboda zafin ruwan da aka zuba turaran ciki
Tana zaune a cikin ruwan Fusam ta ajiye kujerar tsuguno a bayanta ta shiga gyara mata gashin kanta ta hanya shafa mata hadin lallen da ta hada shi da sinadaren gyaran gashi da kuma turaren gashi mai nutsatsen kanshi bayan ta rereda shi ta ringa fesa hadin danyar cita da kananfari da ta markada ta matse ruwa ruwan ta zuba a abin fesawa ta fefesa mata shi sosai sannan ta saka mata hular kan ta daure mata shi tam
Sai kusan magariba suka gama shirin yau, tana tsaye a kanta har ta dauro alwallah bayan ta kuma yin wanka da wani hadin ta zo ta tayata shafa man da ta hada mata mai karra laushi da santsin fata ta sakata a gaba ta ci dahuwar kazar amarya mai ridi da nonon rakumi ta kuma bata tsumi matsayin ruwa sannan ta zauna har suka yi sallar isha ta masu salama bayan ta tabatar mata gobe idan Allah ya kaimu zata dawo tun da duku duku duku mai kunshi da mai kitso , sannan ta tafi
Bayan tafiyarta sosai Khausar ta so tsundumuwa a tunani, sai dai wani irin kanshi da laushin shinfidar da aka yi mata ya luliyata a barci mai nauyin gaske, ko ba komai wannan dirza da ta sha da gasuwa da ruwan dumi sun isa su sakata barci koda bata yi niya ba
Mama kam ta kwana saman salaya
Tana neman alkhairin auren nan da kuma adu'ar Allah ya kade dukkan wata fitinar dake iya kunnowa, ya kawota da sauki, fatanta yarinyarta ta amshi aurenta ta kuma je ta yi biyayya a dakin mijinta, sun yi magana sosai a kan tarewar, Aba ya nuna damuwarsa na yana so ya yi mata kayan daki ama Baba mai kwanoni ya daureshi da jijiyoyin jikinsa ya hannashi maganar kayan dakin, duda haka tanadin da ya yi dan kayan dakin da garar sai ya zuba kaf a Gara , ya yi niya zai mata Gara ta mamaki, mamama ta yarda da haka, babu abinda ya gigitasu harda makota irin akwatunan da aka kawo, ta san aure wani lamari ne na Ubangiji, lalle Khausar ta yi goshi na mamaki, maganar akwatunnan Khausar har gidan su tsohon saurayinta ya kai, wace ta kai maganar kuma ita ta kawowa mama cewar mamansa na cewa auren jari aka yi, Maman kuwa ta bata amsar ai ba laifi bane, ba haramun bane !
Babar rana
Rana bata karya sai dai uwar diya ta ji kunya in ji yan magana
A dade ana yi kuma sai gaskiya
A yau ranar asabar ta kama babar ranar da ta zamto ranar tarewar Khausar a dakin mijinta, amini a gareta, abokinta bisa hukuncin ubangiji ba tare da shirinta ko yardar ta ba sai dan hakan shine a rubuce a kundun tarihinta, tsayin shekaru tana rayuwarta tare da kalolin tsangwamar mutane da tsangwamarta ta kanta, a yanzu ta amsa kiran matar AURE, auren da take yiwa kallon wasan yara, wanda ta gama yarda har a zuciyarta cewa ta girmami wannan aure nema ake yi a hadata da shi dan ta shiga uku, sai dai ta makara, domin sauko ta yi ba tare da ta san shi a hanya ya kwana ba, a daidai wannan lokacin da magariba ta sanyo kai ya zamto a dole Mama ta cire kunyar y'ar fari ita da yar uwarta suka tsaya a dokin kofar dakin Aba suka hanna mutane shigowa
Wato wani irin taro ne na mamaki ya dauka har anguwar ba iya gidan Aban ba
Mama bata yi gaya ba, hakama Khausar, dama dama su Aisha sun gayyaci daidaikun kawayensu , sai ga abin mamaki matan anguwa tun kafin magariba ta rufa suke shigowa kowace kuma da haramar rakiyar amarya Khausar, domin da yawa daurin auren a wai suke jinsa, an daura din wasu basu san waye angon ba, irin yadda ta yi rayuwarta kuwa zasu so su ga wanene wannan ango!
[7/19, 3:17 PM] Maman Aslam: ππππβ€βπ©Ήβ€βπ©Ήππππ
*DA CIWO A ZUCIYATA*
ππππβ€βπ©Ήβ€βπ©Ήππππ
_MALLAKIN_
*SAJIDA NIJAR*
*FREE BOOK NE* 4οΈβ£9οΈβ£
*GARABASA, GARABASA, PROMOTION, PROMOTION DIN LITATAFAN MARUBUCIYAR A KAN FARASHI MAI SAUKI 1K, YAN NIJAR KUWA 1000 FRANCS CEFA*
1: Duk karyar kada
2: Yar mahaukaciya
3: Neman na kaina
4: Bani da zabi
5: Bak'a ce
6: Kutkale
7: Makauniya ce
8: Mage
9: Duk nisan jifa
10: Idan ka raina inda kake
11: Dutse
12: Alkalamin kadarata
13: Bani da zabi
14: Dakika Biyar
15:Wata kokowar
16: Aure yakin mata
17: Ni zan ladabi
18: Daga tafia daukar soja
*Dukansu a kan farashi mai sauki, zaka saka dubu guda ne domin promotion ne nake yi, ka tuntubeni kan layina kamar haka +227 93 81 16 18, Sajida Nijar*
Now
*Da CIWO A ZUCIYATA*
*Tallah, tallah, tallah*
*SECRET DE LA FEMME DU MANGA*
_Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata, nesa tazo kusa,Amarya ,Uwar gida,Ango da mai gida Har ma da yan mata da samari shin kuna sane da cewa HAJIYA FUSAM ta shirya tsaf domin gwangwaje ku da turarakunta masu dankaran kamshi? Tare Kayan gyaram jiki na musamman ,wanda daga nesa kamshin ki kadai ya wadatar ya isar da sakon zuwanki waje,gidan ki kuwa sai ya zam abun kwatance wajen kamshi, kar na cika ku da surutu bara in fara zayyano su_
Farar Humura
Bakar Humura
Humura special,
humura de bain
Humura epicΓ©
Lait de nuit
Parfums dΓ©sodorisant
Parfums rideau et dras
Lait de nuit
Alkam
Kulakcam
*WaΙannan kadan ne daga bangaren turaran ruwa*
Gagab, sandal flex, Durot, durus, sandal fleur, tafarce, farce, sandal bangui, sandal, hypotonic sandal, al'ut, coktail creation VIP, Gajiji, Mankaji, turaran wutar labule da cafet, Aba malan, boulettes
*Munada bangaren gyaran jiki kamar haka:*
mai mai saka santsin jiki, mai mai kanshi, Kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi santsi da laushi, kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi fari, Sabulu mai saka fata ta yi haske, sabulu mai saka fata ta yi santsi, sabulu mai goge yanayin fata, mai wanda baya saka fari mai gyara fata
Sayen na gari mai da kudi gida,sai an gwada akan san na kwaraiππ
Hajiya Fusam na zaune a kasar Niger domin yin magana da ita kai tsaye tuntuΙi wannan number 97 82 44 94
*SECRET DE LA FEMME DU MANGA*
Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mataπππππ
Nasiha Aba ke yi mata, yana zaune ne saman kujera Khausar na zaune bakin katifar Aban
Du yadda Aba ya so kar ta yi kuka , shima kar ya yin sai gashi shine ya fara sada kansa yana mai fashewa da kukan da ba sauti
Ya Allah, Allah mai iko Allah mai amsa adu'ar bawansa
Ashe zai ga wannan rana?
Ashe zai ga auren Khausar dinsa? Auren da yake kyautatawa zaton ba hadi ne suka yi daga sama dan jin dadinsu ba? "Ya Allah alfarmar fiyayen halitta ka zaunar da y'ata a dakinta, ka kade duk wata fitina ka sa ta zamto mai biyayya wa mijinta" Aba ya fada bayan ya dago kansa yana kallonta
A rikice ta idasa fashewa da kukan itama ta sauko tana rarafowa har daf da kafar Aban ta dora kanta a hannunsa, kan da ya sha kitso , hannun da ya sha lalle , idannuwanta kawai aka sakawa kwali sai dan jan baki mai ruwan kasa dan a boye hasken jan lebenta wa kowani mutun ya zamto na mijinta ne shi shi kadai, a birkice ainun tana fitar da dadadan sanyayan kanshin lafayar dake jikinta da kuma kanshin fatar jikinta ta daban ta ce" Aba, Aba ba zan iya ba, Aba Ni babu inda zan je"
A tausashe sosai Abanta ya rike fuskarta yana murmushi ya ce" Dan ina kuka?"
Khausar ta gyada kai ta ce" dan kana kuka Abana na fasa auren !"
Abanta ya saki yar dariyar da bai shiryawa ba, a hankali ya ce" Kukan farin ciki nake yi, kukan jin dadi nake yi, kukan godiyar Allah nake yi, kin ga ai mun gama maganar rikicin kin fasa auren ko? Ai zaki je ki zauna mu gani ko?, Y'ar Aba, ki kasance mai biyayya, kar ki saki ki yadda tarbiyyar ki komai rintsi, ki sani ba wayonki ko dabarar ki ko rashin kunyar ki zata saka a so ki ba, ki kasance mai biyayya mai gaskiya mai addini da tsoron Allah, wannan shine zai ja gabanki har zuwa aljannah, kin ga tun dazu ina jin hayaniyar cewar motoci sun karaso , nima zan zo gidan ai kin ga ina zuwa wajen hajia ko? Zan zo gobe goben nan in sha Allah, kuma kin ga aikinki zaki ci gaba da tafiya ko? Share hawayen nan kar na gani kin ji?"
Khausar na sauke ajiyar zuciya mahaifinta na sake rarashinta a cen kofa kuwa motoci ne na mamaki suka zo daukan amarya wanda tun a nan kallo ya koma sama, shawo ya dau Giwa
Ba wasu motoci Masu yawa bane dan ba zasu wuce goma ba, ama a cikinsu aminai ne na kusa da kusan PROFESSEUR, a yau ya sauka a kasar dan zuwa daukan bestyn besty, wato kawar amini ce kuma aminiyar amini, shi kuma a yau yake da maganar hayata irin wace ya tanadar masu
A hankali ya yi murmushi ya kuma kashe kiran da ya shigo wayarsa na Professeur
A kalla kiran nan ya kai na hudu da yake masa idan ya daga sai ya yi shiru ya ki fadin komai
Lalle shi yake da godiyar yiwa baba da ya kasance uba jajirtacen da bai bar professeur summa a kan bege ba
Dan buga masa madubin da aka yi ana miko masa waya ya saka shi sake sakin murmushi a hankali ya karra a kunnansa yana janyo doguwar salama
A zuciyarsa ya amsa salamar ne? Ko baima amsa ba? Allah masani, abinda ya fada shine" Yaya na ga har tara zata yi shiru?"
Dariya Alhusain ya yi kasa kasa ya ce" Inspector an hanna mana Besty fa, wai sai gobe"
Shiru ya yi, irin shirun nan na daukewa gaba daya tamkar wanda ya ajiye wayar, a hankali ya furta" Baka iya ware abin wasa da wanda ba na wasa ba?"
Wannan karron Alhusain ya bushe da dariyar da ta saka TAUFEEK katse wayarsa ya sake yin kicin kicin ya zubawa Hajia ido wace ta ci uban bando sai kai kawo take yi ta tara tsofafin irinta a falo har wannan lokacin basu tafi ba wai amsar amarya zasu yi
Sai da suka yi ido hudu Hajia ta saki murmushi ta wani gyara tsayuwa ta ce" Kai wai wani kinibibin kake min a daka ne ? Ko auren dolen zaka kunce? Kawai ka kara gaba malan ka sa sai shigowa nake da salama Ni da dakina!, In dai Khausara ce a nan zata tare tunda auren dole na maka sai mai kwanoni ya san abin yi , aikin banza!"
Sshi dai bai tankata ba, har ta gama ta fice tana yade yaden habaici ta koma bangaren Mama, wace ke zaune a baban falon yau itama, itace zaune darr sai bakinta dake zaune tare da ita kowane cikin shiga ta alfarma an dafa abinci na alfarma an ci yanzun jiran saukar amarya ake yi dan a amsheta sai kowa ya kama gabansa, sai dai a taron nan kaf babu matan mai kwanoni da Yumnah, domin ita Yumnah tana cen dakinta ta rufe tana nata shagalin, vidio call da kawarta bayan ta gama waya da mahaifiyarta, du cikin kwontar mata da hankali suke yi, burinsu ta kwontar da hankalinta ta kuma fara aiwatar da abinda suka shirya tun a yau, dan babu abinda zai sa su yarda TAUFEEK da Khausar su zama abu daya!
Sai kusan tara da rabi motocin daukan amarya suka karaso
Mutunci irin na Hajia FUSAM tare take da kanwarta a rakiyar amarya , tana rike da wani mahaukacin turaren alfarma cikinsa fulawowi ne bayan nada nata lafayar da ta