Showing 90001 words to 93000 words out of 186303 words
din, ko kuwa wani kasurgumin dan rainin hankali ne, wai tafiya zai yi yana so kafin ya tafi a daura masu aure sai ya tafi ya dawo? A nufinsa tafiyar ba zai jima ba zai yi ta?, Lalle yana tare da baban lamari, ta yiwu kuma ADU'ARSU ce Allah ya amsa tashi daya ya kawo mijin ashe a kusa ma yake, kuma gashi ba za'a bata lokaci ba? Kai kuwa da sun ji dadinsu su kam, dan haka yanzunma aduar ta yi a kan lamarin sannan ta fice tana jiran Aban Khausar din
Sosai ta KWONTA da abin a ranta, abubuwa biyun nan, damuwar TAUFEEK sai kuma maganar bakonta, eh lalle bashi da laifi kuma kai tsaye da Mama ya zanta, a maganar nasihar mama kuwa kwarai ta shige ta, ama har yanzu tana jin haushin abin bata san dalili ba sai dai abu daya ta san zata iya aikatawa shine bin umarnin na Mama, zata je ta bashi hakurin ne , ama a cen kasan zuciyarta bata ji in har zata iya dawo da zumuncinsu irin na da ba
A bangarensa kuwa, a wannan dare Yumnah ta amshi maza iya maza, har sai da ta fara sarewa duniya domin bata taba tunanin bayan azabar da ta sha ta first night karatun na jiranta ba, dan kamar wanda wani ya kunno shi, ko shi din kansa cikin Sannin kansa yake? Abinda ya sani zuwa biyu rak da ya mata ba asalin shine abinda ya sa ya amayar da damuwarsa ba, dan ji yake yi kamar ya dan shafa bayan kwarya ne, sai dai gannin irin jigatar da ta yi sai ya daga mata kafa ya bata lafiya, ama ina tsabar ta wahala jikinta ya ki amsa tun karfe bakwai na safe ya gama kimtsawa sannan ya taimaka mata ya shigar da ita mota hankali kwonce ya nufi asibiti da ita, baya wani Dari dari, hasalima yana so ya ga ita din idan ta san waye shi me zata yi dan kuwa a kasan zuciyarsa ya gama yarda cewa a nan zai nunawa mata yana da zuciya shima a jikinsa!
Karfe goma Khausar ta nufi hawa matatakalar office dinsa kanta tsaye
Eh lalle ta ringa jin wani abu mai kama da shayi a zuciyyarta bale idan tana karra kusanta kanta da office din tana sake gannin girmansa a bayyane , sai dai wani gefe na zuciyyarta ke fada mata *TAUFEEK NE, BESTY DINTA* ko me ya zama shi dinta ne dai, da izinin ubangiji ta san zasu sasanta a wuce wajen fushin
Da nutsuwa ta kama abin budewar ta bude bayan ta dan buga , bakinta dauke da salama kasa kasa tana wara dubanta dan son hango shi
A hankali idannuwansu suka shige cikin na junna, Yumnah dake kwonce saman doguwar kujera idannuwanta lumshe tana aukin tunanin abinda ya tsaye mata a zuciya ta rasa mai bata amsa tun zuwansu asibitin nan da mijinta da irin gaisuwar da ake masa ana sir sir, da office din nan da suka shigo, yana shirye shiryen duba lafiyarta wanda hakan ya matukar bata mamaki duba da ai bai gama karatunsa ba, sai baban mamakin ya risketa wani likita ya shigo da wani file suka duba tare cikin dan gaggawa TAUFEEK nata ya shige cikin dakin cen, jim kadan sai gashi ya fito cikin shiga irin ta likita, likitanma baban Likita a gaban rigar da siririn rubutu an rubuta DOCTER TAUFEEK, wanda hakan ya kusan sumar da ita, har ya tabbatar mata yana zuwa zai je tiyatar gaggawa ya dawo ne, yanzu abin ya same shi, ya fice kusan awa biyu da rabi kennan tana kwoncen nan zuciyyarta ta gama cicira mata lisafi sai yi take ta rasa me zata fahimta dan abin nan ya zo mata a ba zata, tarin tambayoyin dake kwakwaluwarta kuwa tamkar zasu fasa mata kai ne, sai ta matar da ta jima bata gani ba , wato mayar mijinta ta shigo da shigar itama irin na likitocin, harma shigarta ta so tsoratata domin sket da riga ne na atampa masu ruwan blu a ciki sai riga fara dake saman su sai dan karamin mayafi sosai da ta dan yane kanta da shi , hannunta daya da agogo dayan ba komai , wuyanta da abin awo irin na likitoci, kaffafuwanta sanye da takalmi plate mai masifar kyau dan ya dauki yan kaffafuwanta da basu da girma, idannuwanta da kwali radau lebenta kuwa da dan jan baki madaidaici uwa uba kanshin da ta shigo da shi kanshi ne mai sanyi du irin kanshin da office din ke yi kuwa ana jin nata kanshi ne mai sanyin gaske da kuma nacin waje, sai kawai Yumnah ta zama mutun mutumi ta zubawa Khausar din ido ta kasa amsa koda gaisuwarta dan sai ta fara tsoron ko ba a duniyar mutane take ba yau? Domin wannan da take gani mace ce mai cikakken classs da kanshi bayan wace ta sani tamkar guzumar mace idan tana tafe take?
Bakinta ta dan dantse a hankali cike da takaicin sabon rashin mutuncin nan na Yumnah, tana kallonta ta yi salama ai ko salamar ce ta amsa ama sai ta wani kafeta da duba irin na rainin nan ba zata yi mata magana ba?
Cire kanta ta yi daga kanta ita dinma, dan kuwa ba zata yarda karamar yarinya ta nemi raina mata wayo ba, a tunaninta rukayama ta girmi Yumnah bale A'isha har a gangaro kanta, idanma wani abu na mata hayaki a kai ta nemi sa'anta ta yi da shi ba wai ita KHausar ba
Gannin kamar baya office din ta juyo a Nutsenta zata bar office din, nan Yumnah ta zubawa bayanta ido, domin ฦarara rigar likitocin ta dage saboda uban Bombon din dake bayanta wanda ya yi wani irin yanayi na heart ya yi dasss a jikinta yake kuma juyawa dan radin kansa ba tare da an saka son juyashi a rai ba , domin da aka so juya shi dan neman fitina da lalle an barawa mata abin duba na gani na fada a idannuwansu!
Handle din ta kama ta bude dan tafiyarta, a hankali idannuwanta suka sauka a saman fafadan kirjinsa wanda ke cikin riga mai dogon hannu baka sidik mai botura a gabanta hannun rigar daya a tatare har cen saman dantsensa hakan ya bayanar da girman hannun da yannayin karfi ya nuna kansa da irin jijiyoyin nan na kakarfan maza sai byro dake cikin hannun , dayan hannun kuwa rike da wani file ga dukkan alamu magana yake yi ta katse a lokacin da suka yi ido hudu da Khausar din
A hankali ya dauke dubansa daga saman fuskarta, itama a hankali ta ja baya ta basu hanya suka shigo domin bayanshi akoy docter biyu, dayar na rike da rigarsa ne , dayan kuwa baya rike da komai sunna ta zantawa ta yiwu kan aikin da suka gama yanzun ne
Kanta sade da girmamawa ta gaishe su a jimlace a matsayinsu na iyayen gidanta sannan ta juya a hankali da nufin barin office din , dan ta ga aiki ne suke yi gashima ya nuna kamar bai wani santa ba????
"Nurse...,......." Muryarsa ta katse mata hanzari, wata murya daban da wace ta sani, murya mai cike da isa da iza da kamala, murya mai cike da aji da hobasa
A hankali ta dakata, sannan ta juyo garesu, dan a wajen nan dai karamin kwarin idan tana da kwakwaluwa itace, dan haka ta dawo a Nutse ta dakata da ladabi ta ce" Yes Sir"
Bai bi ta kanta ba, saman kujerar nan ya karasa ya zauna yana dan wara hannayensa kadan , ya kai dubansa wajen doctor dake gaishe da Yumnah, ita kuwa ta wani gyara zama ta kile abinta tana amsawa cike da aji, dan zuwa yanzu tana daf da gane mijin nan nata fa kamar mataimakin oga ne a wajen nan ko yana kusa da mataimakin ogan
Sai da ya gama shan kanshinsa a jimlace ya miko mata katinsa, katin dake iya bata damar zuwa du inda take so a cikin asibitin kanta tsaye idan ta nuna , take kuma da hop din taba du abinda take so kanta tsaye, cike da basarwa ya ce" ki je cafetariat ki sama mana abinci"
Katin ta amsa, a hankali ta dan sake zuba masa ido, sai ta ga gaba daya duba ko na second daya TAUFEEK bai yi mata ba
A hankali ta juya jiki ba karfi zata tafi ta ji Muryar docter nan macen tana fadin" Sir sai na je na samo abincin mana, kawo katin , Nurse wacece sunnan ki?"
KHausar ta dakata ta juyo yanzunma jikin ba wani kwari ta ce" KHAUSAR "
Likitar ta karaso da nufin amsar katin, dan a ganninta wannan nurse din ta jiya jiyan nan bakuwa ina ita ina samun darajar zuwa aikensa uwa uba harda katinsa? Ina ba zai yiwu ba, sai dai bai bata damar hakan ba da wannan bakon yannayin nasa ya tare mata hanzari ya ce" A'a, ki barta ta je" ya ci gaba da duba takardunsu hankali kwonce ya yi watsi da su su dukansu! Watsi da su mana, daga maganar nan TAUFEEK bai sake cewa da su uffan ba har Khausar ta juya ta fice tamkar an zare mata laka
๐๐๐๐โคโ๐ฉนโคโ๐ฉน๐๐๐๐
*DA CIWO A ZUCIYATA*
๐๐๐๐โคโ๐ฉนโคโ๐ฉน๐๐๐๐
_MALLAKIN_
*SAJIDA NIJAR*
*FREE BOOK NE* 3๏ธโฃ4๏ธโฃ
*GARABASA, GARABASA, PROMOTION, PROMOTION DIN LITATAFAN MARUBUCIYAR A KAN FARASHI MAI SAUKI 1K, YAN NIJAR KUWA 1000 FRANCS CEFA*
1: Duk karyar kada
2: Yar mahaukaciya
3: Neman na kaina
4: Bani da zabi
5: Bak'a ce
6: Kutkale
7: Makauniya ce
8: Mage
9: Duk nisan jifa
10: Idan ka raina inda kake
11: Dutse
12: Alkalamin kadarata
13: Bani da zabi
14: Dakika Biyar
15:Wata kokowar
16: Aure yakin mata
17: Ni zan ladabi
18: Daga tafia daukar soja
*Dukansu a kan farashi mai sauki, zaka saka dubu guda ne domin promotion ne nake yi, ka tuntubeni kan layina kamar haka +227 93 81 16 18, Sajida Nijar*
Now
*Da CIWO A ZUCIYATA*
*Tallah, tallah, tallah*
*SECRET DE LA FEMME DU MANGA*
_Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata, nesa tazo kusa,Amarya ,Uwar gida,Ango da mai gida Har ma da yan mata da samari shin kuna sane da cewa HAJIYA FUSAM ta shirya tsaf domin gwangwaje ku da turarakunta masu dankaran kamshi? Tare Kayan gyaram jiki na musamman ,wanda daga nesa kamshin ki kadai ya wadatar ya isar da sakon zuwanki waje,gidan ki kuwa sai ya zam abun kwatance wajen kamshi, kar na cika ku da surutu bara in fara zayyano su_
Farar Humura
Bakar Humura
Humura special,
humura de bain
Humura epicรฉ
Lait de nuit
Parfums dรฉsodorisant
Parfums rideau et dras
Lait de nuit
Alkam
Kulakcam
*Waษannan kadan ne daga bangaren turaran ruwa*
Gagab, sandal flex, Durot, durus, sandal fleur, tafarce, farce, sandal bangui, sandal, hypotonic sandal, al'ut, coktail creation VIP, Gajiji, Mankaji, turaran wutar labule da cafet, Aba malan, boulettes
*Munada bangaren gyaran jiki kamar haka:*
mai mai saka santsin jiki, mai mai kanshi, Kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi santsi da laushi, kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi fari, Sabulu mai saka fata ta yi haske, sabulu mai saka fata ta yi santsi, sabulu mai goge yanayin fata, mai wanda baya saka fari mai gyara fata
Sayen na gari mai da kudi gida,sai an gwada akan san na kwarai๐๐
Hajiya Fusam na zaune a kasar Niger domin yin magana da ita kai tsaye tuntuษi wannan number 97 82 44 94
*SECRET DE LA FEMME DU MANGA*
Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata๐๐๐๐๐
Tunda ta fita a hankali ya samu hannayensa da danna computer dake gabansa ta hasko masa step step na asibitin baki daya, a hankali ya danna wanda ya ji yana da bukatar ganni sannan ya dan zuba ido yana kallon, haka kuma kunnayensa na wajen abokanan aikinsa dake aiki karkashinsa sunna zantawa kan abinda ya shafi aikinsu
A hankali ya dauke dubansa gannin ta shiga cafetariat din ya kai dubansa wajen da Yumnah ke zaune
Irin kallon da take masa ya saka shi dan lumshe mata ido sannan ya mata alamar yaya?
Murmushi ta sakar masa tana dan dauke dubanta, domin a zaman nan hauda mata jinni ne yake yi yana sauke mata tamkar hawan cenjin Naira da sauka, aiken nan da ya yiwa Khausar cike da basarwa ya matukar birgeta, sai dai tunanin wani abin kuma ya girmami wannan a zuciyyarta
Mintunna ฦalilan Khausar ta dawo hannayanta dauke da baban basket
Docter ce ta amsa dan haka ta karasa gaban table dinsa ta mika masa katin cike da kokari da kwarin gwuiwar da ta ba kanta ta ce" Ga katin"
A hankali ya dauke dubansa a kanta, da ido ya mata alamun ta ajiye saman table din
Da kyar ta iya cije lebenta ta Hanna kanta wani motsin da zai falasata ta ajiye katin sannan ta juya da nufin tafiyarta
"Ki je da Madam, ki aunata, bata da lafia " muryarsa ya sake katse mata hanzari
Sai da ta rintse idannuwanta, da kyar ta iya hadiyewa ta dakata har Yumnah ta gama shan kanshinta ta fito sai bubudewa take yi suka nufi labo
A lokacin da Khausar ke kokarin fitar da abubuwan bukata Yumnah na murmushi ta ce" Ai da kin barshi, ciwon nawa ba wani sai an auna na, furen soyayya na fara tsinka, wanda ya fi komai daraja da kowa a duniyar Mijina, wanda ya bani tun ranar da na zama halaliyarsa, ba kariya dan kar na samu baya kuma jin kunyar hakan!"
Har ga Allah, bata taba jin bacin rai irin na wannan lokacin dangane da rashin da'ar yarinyar nan ba
Hatta allurar dake hannunta sai da ta subuce ta fadi
Ba tare da ta bi ta kan allurar ba ta zubawa Yumnah ido, sai kuma ta zagayo a hankali tana sake Binta da kallo daga sama har kasa
Da kula sosai ta ce" Yumna, AKOY wata matsala tsakanina da ke ne wace ban san da zamanta ba?"
Yumnah ta wani gyatsine fuska ta ki bata amsa
Wani irin makuku da ya tsaye mata a wuya a lokacin sai ta ji koda korarta za'a yi yau saboda Yumnah a shirye take ta amshi korar
Rai bace ta damki hannun Yumnah ta juya da ita tana janta ta nufi office din nasa da ita, idannuwanta sun riga sun rufe ta manta waye shi a nan, kuma WACE Yumnah a duniyarsa
Tana buษe office din su docter zasu fito
Bata tsaya bi ta kansu ba ta idasa shiga idannuwanta har ruwa ruwa suke da yaji yaji da karfi ta karra janyo Yumnah wace ke tirjewa gabanta na faduwa ta tsayar da ita a gabansa
Da mamaki su docter ke neman dawowa, sai dai tunda ya ga abinda yake faruwa dama ya zubawa camerar ido lokaci daya kuma ya masu alamar su tafi da hannunsa sannan ya danna abin rufe office din ya rufe da kansa ya sake zuba mata ido tasa zuciyar shima tana wani iri kamar wanda yake cike da tsoron abinda zai fito daga bakinta dan irin yadda kirjinta ke sama yana kasa sai da ya ji nasa kirjin shima yana hakan
A rikice ta dube shi sannan ta kalli Yumnah ta ce" Bama zan tsaya jin abinda ke tsakanina da ke da ya sa kike min abubuwa na rashin da'a ba, da shi din zan yi kuma daga bakinsa nake son ji! , TAUFEEK me matarka ke nufi da magangannu wasu iri da take aika min tamkar Ni din abokiyar gabarta ce ko wani abin ya shiga tsakanina da ita? Haka ranar da na je nemanka yarinyar nan ta min tsaki da wasu abubuwa mararsa dadi, yau kuma kace na aunata tana fada min furen soyayya ta tsinka na halar wanda ba'a saka abinda za'a hanna daukansa? Ni fa yar Hausa ce ba bagwariya ba, kuma abinda take nufi da Ni ina daf da ganewa harma ina jin kamar zan mutu da haushinta in kuwa haka ne!"
Fada take hawaye na gama cika idannuwanta ta kalli Yumnah wace ta gama sarewa duniya daga idannuwan mijinta ta ce" Ke kuwa, wace irin shashasha ce da zaki yi tunanin abokina zai iya zamtowa abokin aikata masha'ata? Ko ba haka kike nufi ba kar na maki karya na kulaceki?"
A rikice Yumnah ta Dube shi, ta kuma dube ta ta ce" Aunty Khausar Ni kuma?"
Khausar ta dantse lebenta sai ga wani hawaye wani na bin wani sunna bin kuncinta, a raunane ainun ta ce" Ni ba mazinaciya bace, Allah ne shaidata, ba komai tsakanina da mijinki sai zumunci gayanan ki tambaye shi, shikennan dan na zama sharar shanye sai a ringa wulakanta ni? Ba za'a barni na ji da ciwon dake ZUCIYATA ba sai an rikita min lisafi? .... TAUFEEK me yasa ne? Me na yi da zafi ne?, Me yasa TAUFEEK kowa idan ya mike yake kokarin ganin ya wulakanta ni bayan na kasance mai kare mutuncina?......" Ta idasa a matukar raunane, a hankali ta dafe kanta jin irin juya matan da yake yi ta juya tana cire rigar jikinta dan kuwa ta sani ne wannan asibiti yau ko ta aba ce ai an koreta kennan dan ta san ta yiwa oga fitsara an gama
Kofar take kokowa da ita dan ta budu ama sam kofar ta ki ta budu
Ta ja ta ja ya fi a irga ama kofa ta nuna bata san tana yi ba
A rikice ya juyo dan neman agajin a bude mata , sai ta ga Yumnah ta nufi dakin da yake na cenza suturarsa ta shige da dan sauri shi kuwa yana tsayen nan yana kallon gefe fuskarsa ta yi wani irin kicin kicin kamar ba TAufik din HAJIA ba
A hankali ya kawo dubansa inda take tsaye kikam gabanta na dokawa tana ta nazari kala kala
Da hannunsa daya ya mata alamun ta zo nan, hakan ya sa ta dan wara dubanta tana kallonsa da son karrin bayani
Lebensa ya sake dantsewa ya mata nunin ta zo inda yake nufi, ama Khausar ta ki aikata hakan
A hankali ya cire tishu ya dan goge fuskarsa sannan ya jefa shi cikin abin shara ya mike tsayinsa da kyau ya nufo inda take tsaye
Tunda ya taho Khausar ta samu kanta da kallon gabas da yama, kudu da arewa cikin tunanin ina wajen buya ba tare da ta gane haka take tunani a ranta ba
A hankali take ja ba, TAUFEEK na matse mata waje har ta kai